Showing 30001 words to 33000 words out of 176330 words
/>
''to,amma mami ban san inda saahen yake ba''
''idan kika fito cikin balcony gefen hannun damanki zaki miqehar sai kinzo qarshenta''
''to gani nan''
tsaf ta shiryasu cikin basket din mai kalan ja da fari,hijabinta ta z
ura mai hannu ta sanya slipper ta dauki basket din ta fito
a hankali take taka balcony din tana sake qara kallonta don bata taba yin area din ba tunda tazo gidan,sai taji kamar kada tafiyar ta qare saboda dadin da yanayin yayi mata,iskace take busawa mai
mai sanyi hade da qamshin qasa wanda hakan ke alamta lallai yau wani sashe na cikin garin kano yana samun saukar ruwan sama,kasancewar shigowar yanayin damina,duk da cewa har yau tasu area din basu samu ruwan ba saidai yawaitar haduwar hadari da bajewarsa
Qiris ya rage ta bangajeta Allah yasa tayi saurin cin burki,zubaida ce tsaye a gabanta tana huci,a zaton maryama bata da case don ita don haka tayi qoqarin gewayeta ta wuce,binta ta sakeyi ta sha gabanta
''lafiya
?
''maryam ta tambayi zubaidan cikin sanyin
nan nata
''kiyi qoqarin kame kanki daga cikin lamuran abdallah,don na fuskanci wani rawa kanki yake,bari in tuna miki idan kin manta,ke ba kowa bace cikin rayuwar abdallah face 'yar aiki wadda bata da maraba da baiwa,babu abunda abdallah zaici dake,garga
dinki kuma nake ba shawara bace''
ta mata kallon sama da qasa hade da bangazarta ta wuce,da kallo ta bita harda waiwaye,sai da ta bacewa ganinta sannan ta dawo kallon gabanta
sam abun vai bata haushi ba sai ma dariya wanda hakan ya sanyata murmusawa hade
da kada kai ita daya,idan banda abun zubaida ina zata kai abdallah
?
,me zata ci da shi,sam ko kadan ma ita dai dai da second bata taba qyasta wani abu wai tsakaninta da shi ba
da wannan tunanin ta qarasa sashen,da qyar ta samu ta iya shiga saboda tun daga
qofa ta soma ganin bambanci,hamshaqin parlour ne wanda zata iya cewa bata taba tozali da makamancinsa ido da ido ba saidai ko cikin hotuna
kusan shima komai na parlour din fari nesai ratsin maroon kadan da baqi
kujeru set uku ya lamushe don shi din ma b
a baye bane gun girma da kuma tsari,kowacce kujera na rukuninta daban,girmanshi baiyi yawa ba haka nan baiyi kadan ba,bisa can dining area din dake daura da matattakalar bene ta hangosu wanda hakan ke nuna mata sunyi ready ita suke jira
a nutse ta qarasa
ta soma serving dinsu mami da abdallanta na hirarsu,ta turawa kowa plate din tuwo da miyarshi ta sona kiciniyar bude flask din patatoes balls din
''meye haka
?
,wani sabon salon raini ne haka,ta yaya zaki raba mana plate ko yau kija fara sanin tare muke cin
abinci
?
''
abdallah ya fada cikin hade gira yana typing saqo a wayarshi
ta saki flask din da niyyar hade masu abincin a plate guda mami tace
''rabu da shi fitananne kawai,kalna mai sauqi kace hada mana sai ka ja wani dogon magana
?
''
''wallahi mami ke k
e shagwaba yarinyar nan da yawa,shi yasa kullum sai ta yima mutane shirme''
''Allah ko,ita ce ma kai''inji mamin
da daidai ta soma jera patatoes balls din cikin plate,saidai duk wanda ta dago ssi taga ya rabe biyu,tayi tsammanin tauri yayi da yawa yssa y
ake haka,don haka a hankali ta lallabashi ta gama jerawa cikin plate din ta tura musu,tana shirin sauka qasa mami tace ta zauna ta saka hannu suci tare,ce mata tayi taci nata ta qoshi
''kunyanki yayi yawa maryam,har yau kin kssa daukan kanki a matsayin di
yata ko
?
,shikenan tunda ba zaki ci da mu ba zauna muyi hira tare idan na kammala mu wuce''
tilas ta koma ta ja kujera daya ta zauna kanta na sunkuye a qasa,lokaci lokaci mami na jefata cikin hirar don ta sake cikinsu saidai kaifin idanun abdallah ya hanat
a,duk tunda ta zauna din qurar da ta kwasota ma bai duba ba duka ya tattara hankalinshi kan maminshi da plate din abincinsu
abdalla ne ya soma tsame hannunshi yana fadin
''mami turomin daya plate din''ta tura masan tana ci gaba da cin tuwonta don ita duk
a wadannan yame yamen basu dameta ba
hannunshi ya saka ua dauki guda daya,lokaci guda wata matsananciyar faduwar gaba da sameta,rashin yarda da patatoes balls din ya kamata cikin tazarar lokacin da bai wuce second biyar ba
kai balls din bakinsa yayi daid
ai da saukar hannun maryama kan nashi hannun ta buge da qarfi har yaji zafi,ba 6ata lokaci balls din ya fadi saman teburin cin abincin ya wargaje,wani ruwa yellow din ruwa ya soma fita daga tsakiyanshi wanda idan ba sani kayi ba zaka yi tsammani ruwan curr
y ne,wannan shi ya taimaka daga abdallah har mami basu kula da shi ba
zuciyarta taci gaba da tsananin bugu,tsoro qarara ya bayyana cikin fuskarta,tana tuna giftawar data gani dazu cikin kitchen da ta rasa ta
waye
?
,sa'an nan ta dawo da tunaninta kan dalili
n daukota don kula da abincin abdallah,guba ne fa
?
guba abdallah yaci sau biyu a baya,kada fa ayi amfani da damarta a aikata wani mummunan abu,a zafafe abdallah ya kalleta,ranshi yayi tsananin bacin da har ya gaza tambayarta sai mami ce tace
''a'ah,ya haka
maryamu
?
''
''barta mami,ai dama daga ganin wannan yarinyar bata da kunya,in banda tsabar rashin mutunci ya mutum yana.....''
dakatar da shi tayi tana kallon maryam wadda ke qoqarin daidaita natsuwarta don lalubo dalilin da zata bada wanda har ya kai ta
aikata abunda ta aikata din yanzun
ba shiri ta tsinci bakinta na fadin
''mam...mi na manta ne ba gishiri da magi cikin balls din,da muka tafi asibiti ashe ban zuba ba,kada kuma yaci yaji babu dadi a bakinsa''
''amma banda abun maryamu ai sai kice mishi
kawai kada yaci,next time ba haka ake gyara ba kin fahimta
?
''
da sauri take gyada kai tana cewa''eh mami,kayi haquri''
ta fada tana kallin abdallah,fararen idanunshi da ya zuba mata yana kallonta shi ya kuma sakata rudewa har ta rasa me zata aiwatar,ba s
hiri ta shiga tattara fasashen balls din dake gabanshi tana niyyar kwashewa taji ya riqe tsintsiyar hannunta
a razane ta dago idanunta suka shiga cikin nashi,ta danyi kusa da shi hakan ya sanya yaji kaifin idanun nata har qwaqwalwarshi
''daina kallona da
idanu sai kace na mage''maganar ta subuce masa
ya maye gurbinta a dan tsawace da fadin
''qarya kike,wannan bai kai dalili ba,na gano wani abu daban cikin ranki,akwai dalili amma ba wannan ba''
tuni qwalla suka cika mata idanu,cikin son kare kanta tace
''da gaske nake,ba qarya nayi ba ka yadda yaya abdallah''
''akan me zan yarda dake,bayan ire irenki biyu sun so ganin qarshen numfashi na a baya,kema kin biyo sahu ne
?
''ya fada yana huci
tuni qwallan da ta tara a idanunta suka cika suka zama hawaye,ba b
'ata lokaci suka soma gangarowa kuncinta,kuja ta qwace mata,tsoro da rauni suka mamayeta
''me kakayi haka ne abdallah,sakar mata hannu''mami ta fada cikun fushi
''mami yarinyar nan ban yarda da ita ba,baki ga reaction dinta bane
?
,aikina kenan mami nasan
reaction din masu laifi''
''ina ce nan ba a office din SS muke ba,ai kin naka baka gwadashi a baya ba sai akan maryam,comon bani son sakarci sakar mata hannu tun kafin in sabar maka''dolenshi ya saketa amma duk da haka bai barta ba binta yake da ido
''oy
a maryam,tattara kayan nan ki tafi kije ki kwanta gani nan tahowa''jikknta na rawa ta dinga hada kwanukan,tausayinta fal zuciyar mami tana ganin abdallah ne ya tsoratata
''abdallah,ka saurareni da kyau,ba da ka zan dauko maka maryam a matsayin cook ba,nay
i bincike mai kyau game da ita,nasan halayenta gaba da baya,baya ga haka nasha yin istihara game da zamanta da mu jikina na bani alkhairi ce ita,saboda haka ina mai tabbatar maka maryam ba zata taba iya cutar da wani dan adam ba balle mu,ni maminka nake ga
ya maka wanna maganar ba wata ba ka fahimceni
?
''a ladabce ya amsa mata
''kada ka sake mata irin haka,gaba daya ka tsoratata,ka kiyaye gaba,''
''insha Allahu bazan sake ba''tafiya taso yi amma ya kasa ya tsare ya hanata,sai da ya sata dariya kana ya mata
rakiya har bedroom dinta sannan ya dawo bangarenshi
maryam kuwa jiki na rawa ta isa dakin baccinta bayan ta tabbatar ta yiwa patatoes balls din mugun boyon da babu mai ganinshi sai ita,sam bata qaunar tashin hankaki a rayuwarta,kuka ta zauna tanayi riris
a bakin gadonta,lijaci mai tsawo ta dauka a haka kafin ta gane cewa kuka babu abunda zai amfanar da ita,ta tabbatar da cewa rayuwar cikin gidan akwai wani qulli da su su mamin basu san da shi ba,fargabarta daya kada wani abu ya samu abdallah ta sanadinta,i
dan ta fada wannan shingen wazai fiddata
bata da wannan gatan saidai yadda Allah kawai yayi da ita
har kusan uku na dare ta kasa runtsawa,sai da wayarta ta buga alarm na qarfe uku da rabi wato dai dai lokacin tashibta sallar dare kenan sanna ta shiga toi
let ta daura alwala
kusan dadewarta ta yau tana addu'a tafi ta kullum har sai da kiran assalatu ya rusketa,sallar asuba tayi ta dora da azkar zuwa qarfe bakwai ta fita kitchen
sam jikinta babu kuzari kamar yadda zuciyarta babu dadi,fuskarta kadai ka kall
a ta isheka amsa saboda ja da ta hada da kuma tasawa da idanunta suka danyi,a kasalance take hada musu break din wanda ya kaita har qarfe goma bata kammala ba saboda rashin qwarin jiki
goma da minti ashirin da shidda ta ji sallamar mami cikin kitchen din,
a hankali ta dago tana amsa mata kafin daga bisani ta rusuna ta gaidata bata damu da amsawa ba ta dora da tambayar maryam din cikin fuskar rashin jin dadi
''maryam,lafiya
?
,me ya samu fuskarki
?
,kada kice min kwanan kuka kikayi
?
,abdallah ne ko
?
''
zuciyarya
ta danyi rauni amma sai ta dake,ta dan murmusa kadan hadi da kada kanta
''ko baki fada ba na sani shine,kiyi haquri kinji maryam na mishi fada kuma insha Allahu haka ba zata sake faruwa ba,ni zan fita,ga wannan albashinki ne na wannan watan''ta fada tana
zaro rafar kudin daga jakarta sababbi kar da su
hannu biyu ta saka ta amsa sanna ta mata godiya
''nice da godiya maryam,inajin dadin zama dake,kina da kyawawan halaye da mutane da dama suka rasashi a wannan lokacin,fata na Allah ya baki miji na gari mar
yam wanda zai riqekibisa gaskiya da amana''
kunya maganar ta bawa maryam wanda yana daya dqga cikin halayenta dake burge mami
lura tayi da akwai magana a bakin maryam din
''kamar kina son cewa wani abu ko
?
''
''dama yau inason inje gida ne''
''hoo,mary
amu,wannan din ne kika kasa fada,banda abunki ai kinyi kara ma wata guda baki gansu ba,babu matsala zan yiwa driver magan ki shirya sai ya kaiki idan zaki dawo ki masa waya yazo ya daukeki,idqn baki dawo da wuri ba ma babu damuwa ni da wuri zan dawo gida y
au in yaso sai na mana dinner dinko,ki gaishemin da mutanan gidan da kyau kinji,zan ajjiye miki saqo a parlour idan kin tashi tafiya ki tafi musu da shi''
godiya sosai ta yiwa mamin tare da yaba karamcinta,tana kammala breakfast din ta shirya a gurguje ci
kin baqar abaya wadda ta sake fidda sirrin kyawunta ta kuma haska farar fatarta wadda ta sake fresh saboda zama gu daya da kuma sanyin a.c,kitchen ta koma ta juye duka patatoes balls din cikin leda bag ta daure ta jefa shi cikon jakarta,sai da ta tabbatar
ta
qulle duk inda tasan idan an shigo shi za'a iya samun matsala gun abinci ko abunsha da zasuyi amfani da shi sannan ta fita,hatta da breakfast sai data nemi alfarmar baba uwani ta kula da shi kafin abdallan yazo yaci
cikin motar ta zaro wayarta ta lalub
i number din raliya,har tayi ringing ta katse ba'a daga ba sai da ta sake kira,bugu daya ta daga
''sorry sis,fadil ne ya rudani da kuka na kasa daga kiran''sama sama suka gaisa,tana shirin tsokanarta taji muruarta ba yadda ta saba ji ba sai kawai ta share
tambayarta tayi zata iya samun nasir abban fadil a asibiti ko bai fita ba
''tun dazun ya fita,ina tsammanin ma yakai awa uku acan''godiya ta mata ta kashe wayar,kamar ta tambayeta lafiya
?
sai kuma taga bai kamata ba,idan da buqatar taji maryam ba mai boy
e mata bane,a mutunce ta cewa driver din zooroad zasu fara zuwa ya amsa mata sanna ya sauya akalar motar
*mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k:
💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺
*ABADAN*
🌺🌺
🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
🌺💖
💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺
▶
2
⃣
1
⃣
_yar fadakarwa_
_*shin ko kinsan gwalagwalan kwanakin da muke ciki 'yar u
wa
?
,kwanaki ne masu matuqar tsada da daraja har agun Allah madaukaki,kwanaki ne da ayyukan alkhairi suka fi soyuwa agun ubangiji a cikinsu,kwanaki ne mafi daukaka cikin kwanakin shekara,an karbo hadisi daga imamu bukhari r.a,annabi s.a.w yana cewa(babu was
u kwanaki da kyawawan ayyuka sukafi soyuwa agun ubangiji kamar kwanakin goman farko na watan zulhijja,sahabbai suka ce da annabi hatta jihadi saboda Allah
?
,annabi yace eh har jihadi,saidai mutumin da ya fita jihadi da ranshi da dukiyarshi bai dawo da komai
ba),shin me kike aikatawa na neman lada
?
,kada ki yarda su shude ba tare da kin amfana da komai ba,baki da
tabbacin ganin na wata shekarar,Allah ya karbi ibadun mu yasa mu dace ameen*_
🕋🕋🕋🕋🕋🕋🕋
Minti talatin suka isa asibitin da nasir ke aiki
,ta taradda marasa lafiya da suka rigata zuwa,hakan yasa tabi doka itama ta hau kan layi,don ta sani indai tace masa ta zo babu makawa sawa zaiyo ta ahiga kawai ita kuma ba zata so shiga haqqin wani ba
ko kafin azo kanta tuni ta qosa,jira ne na tsawon
awa guda da rabi kafin ta samu shiga,da mamaki yake dubanta tare da fadin
''yau kuma an tuna da mu kenan''
dan qaramin murmushi tayi kan ta haye kujerar da masu buqatar ganinshi ke zamansa
gaisawa sukayi yaso ya dan tsokaneta yadda auka saba sai kuma
ya fuskanci yanayonta ba yadda ya saba ganinta bane
madaidaiciyar handbag dinta ta zuge ta fidso da leda bag din ta dorata saman table dinshi
''taimako nake buqata daga gurinka nasir ko zaka iya yimin shi
?
''
''me zai hana maryam indai ba kaucewa add
ini ba''
''abunda ke cikin nan nake da buqatar a duba min ko akwai poising a ciki
?
''
ido ya dan zuba mata kamar mai buqatar qarin bayani,gganin bata da niyyar qara masa haske yasa ya kauda idonshi kana yace
''ok,ba damuwa,ga kujera can zauna bari na kir
a lab azo a dauka''
cikin mintina uku kacal wani matashi ya shigo sanye da farar labcoat ya dauki ledar ya fice
mintina arba'in din da yayi kafin ya dawo jinsu tayi kamar awa arba'in ne,tuna ni babu kalan wanda bata yishi ba,dawowarahin tayi daid
ai da kammala ganin patiente da nasir yayi,hakan ne ya bawa matashin damar zama tare da miqawa nasir result din ya ajjiye ledar a qasa yana duban fuskar nasir din
nuni ya yiwa maryam din da hannu kan ta taso idanunshi na cikin takardar,a sabule ta iso
gaban teburin ta samu kujera daya cikin biyun dake gun ta zauna
''maryama....taya aka samu irin wannan mummunar gubar cikin abinci
?
,kinsan nau'in guba iri wannan bamu da ita ma sosai cikin qasar nan
?
,guba ce da ke iya kashe mutum cikin mintunan da basu g
aza biyu ba,baya ga haka hatta da gawarka ma bata qyaleta ba sai ta narka duka kayan cikin mutum,dubi yadda ta maida wannan dankalin''ya mata nuni dashi dake cikin ledar da yasa matashin ya bude
A hankali ta maida firgitattun idanunta kan ledar,dankal
in ya zagwnye ya koma kamar ruwan kunu,hakanan gabaki daya kalarshi ta sauya zuwa kore da baqi,kumfa ce kawai ke tsattsafa a samanshi tamkar ya ahekara ne da sarrafawa ba kwana daya ba,wani irin tsoro ya sake kama maryam,da sauri ta maida idonta kan nasir,
cikin rawar murya tace
''ko zan iya ganinka kai daya
?
''
''why not
?
,sadam dan bamu guri''
office din ya rage daga ita sai shi,a hanakli ta zayyana masa dukkan abunda ta sani,ya jima yana jinjina kai kafin yace
''maryam akwai hadari mai girma tattare
da gidan,saidai abu guda da ban goyi bayanki ba barin gidan da kike shirin yi,barinki gidan ayanzu dai dai yake da mutuwar abdallah da maharfiyarshi,bayan kin gano matsalar da su basu san da ita ba,shawarar da zan baki shine kawai ki zama mai matuqar kula
da takatsantsan,abu na gaba shine ki riqe addu'a,qarfinta da kaifinta ya sha gaban duk wani kaidi da zalunci''
sun shafe fiye da mintuna talatin yana bata shawarwari wadanda syka sa taji hankalinta ya kwanta,nutsuwarta ta dan dawo,da kanshi suka zaga
ya can bayan asibitin sukayi haqa ya binne ledar patatoes din
''yanzun kuma sai ina
?
''ya tambayeta bayan sun isa bakin get din asibitin
''gida na nufa inje inga mama''
''gashi wani aikin yanzu zan koma ciki na qarasa kinga ai da na kaiki''
''ba damuwa,
zan hau adaidaita sahu yanzun zaka ga naje''
a gabanshi ta hau napep din ya biya mata ta wuce bayan ta masa godiya,murmushi kawai yayi
''kada ki damu,ke da raliya duka abu daya ne''
har qofan layinsu dan adaidaitan ya direta saboda babu damar sh
iga layin nasu,ba dob matsi ba sai don yawan