Showing 117001 words to 120000 words out of 176330 words
wata ruwayar ta muslim kuma yace nana aisha tace''na kasance ina kankare janaba daga tufafin Manzan Allah S A W (kamar bu
sashen maniyyi kenan)sai ya saka ya fita salla da tufafin_*
*_wannan shafin sadakarwa ne gareki dungurun gum baki dayansa SADNAF bama ke kadai ba har da 'ya'yana AFFAN DA IKRAM Allah ya rayasu ya yiwa rayuwarsu albarka,Allah ya bar zumunci_*
Idanunsa suka sake sauka kam yatsunta da take gutsirar shawarman da ita,yanayin yadda take ci kawai ya isa ya gaya maka kan tilas take ci din,don dama asalam ba cimarta bane da biyu tace ita don take so ga zatonta basai samo ba
ba qaramin kyau suka
yi masa ba,kasancewar yana gan da ita yasanya ya kamo hannunta
''yaushe kika yi wannan abun
?
''
ya fada yana kallon qwayar idonta,sai ta soma qoqarin zame hannin nata ba tare da ta bashi amsa ba
''maryam''ya kira sunanta can qasan maqoshi kamar maijin ba
rci,nan ma bata amsa masa ba ya kuma fuskanci bata da niyyar amsa masa din,sunkuyo da kanshi yayi ya tura yatsunta guda biyun cikin bakinshi ya soma tsotsa a tausashe har yana lumahe iso tamkar wanda ya samu wani abu mai dadi
wani irin abu ta dinga ji
yana tsirga mata tun daga tafin qafarta har qwaqwalwarta,take jikinta ya mutu baki daya hakanan ta rasa kuzaron hana shi sai idanunta ma da taja ta rufe tana ajiyar zuciya qasa qasa
A hankali ta bude idanunta jin ya daina shan hannun,wata iriyar kuny
a ta kamata kamar qasa ta tsage ta shige,ashe ita ua zubawa idanu tana kallonta bata sani ba
''uhmmm,madam,zan iya ci gaba
?
,na kamar kema kina enjoying ko
?
''ya fada yana kashe mata idonsa na hagu,bata san me zqtq ce ba don ya gama kunya tata saboda hakq k
awai saita fara hawaye tare da qoqarin zame hannunta saidai ko daya ya janata ya kama hannun ya riqe tsam ya kima zuba mata mayun idanunshi har tayi mutsumutsinta ta gana tq bada kai ta hanyar haqura tayi qasa da kanta kawai
Hannun ya sake mata bayan
ya gama kallonta iya son ranshi,jikinsa gaba dayq ya gama yin laushi muguwar kasala ta lullubeshi
''ta yaya zan iya wanka qarfe takwas na dare,kinga ina zaman zamana kin jawo min ko
?
''
rasa inda zata tsoma ranta tayi,sam abdallah bai da kunya kwata kwata
,lamuranshi yake gaba gadi,ko ita qaramar yarinyace ai ta gane abinda yake nufi bare da hankalinta
''ka jawowa kanka dai tunda bani na kirawoka ba''ta fada can qasan maqoshinta
''erhmmm,me kike cewa
?
''ya fadi yana matso da kunneshi,shaf ta mance yadda ab
dallan ke da shegen ji kamar maciji
''najiki sarai abinda kika fada,amma ba komai Allah zai saka min,nima na kusa aure in sha Allahu nan kusa na huta''wani abu ne ya takareta har batasan lokacin da dago kanta ba bayan ta dubeshi tace
''toni me ruwana
,idan ka tashi ka aure matan duniya ma baki daya sannan ne zansan ka cika jarababben ma.......''sai ta kasa qarasa fada saboda nauyi da maganar tayi mata da kuma yadda ya tsatstsareta da mayun idanunshi wanda bai gajiya da kallonta da su
ta cukuikuye
hijabinta gu daya ta miqe da sauri zata fice adakin,hannu daya yasa ya fincikota atausashe sai gata gabadaya ta fada saman cinyarshi
''babu inda zaki sai kin qarasa fadar abinda ke ranki''
kai ta girgiza gabanta na faduwa cike da danasanin fara furta mag
anar
''na gama magana ta ai''
''qarya kike,akwai saura''batasan sanda ta rantse ba
''wallahi babu''
''ummh,sanannan ne zaki san na cika jarababben mayen mata ko
?
,dama can ni mauen mata ne ai ko kin manta
?
idan baki sani na kuma to kibi a hankali don ta
kanki zan fara maitar tawa kafin na sallameki''
tamkar tace wayyo Allah haka taji,kansu sake cewa komai an dago labulen dakin,mairo ce riqe da laptop din abdallah
''yaya abdullahi wai meramun kitson da....''sai ta kasa qarasawa sakamakon ganin maryam
din kwance kan cinyar abdallahn,shi kuma ya mata rumfa da faffadan qirjinsa,hakanan sai maryam din ta samu kanta da sake narkewa kan cinyar abdallahn ta saki jikinta tare da saka idanunta cikin naahi sosai abinda bata taba yi ba,hakan yasa ya kasa daga id
onshi ya kalli mero din baison yayi missing kallon kyakkyawan oily brown eyes dinta ba dake matuqar jan hankalinshi,ganin ba wanda ya dago ya kalleta yasa sakin labulen bayan ta ajjiye masa laptop din ta fice a dakin
Sai da taga alamun fitarta sanna
ta janye idanunta,cikin fitar hayyaci ya kama fuskan tata don baison ta daina kallonshin sabida wasu zafafan abubuwa da yake karanta daga qwayar idanunta wanda shi kansa yasan bata san da su ba,satar amsa yake samu sosai ba tare da saninta ba,tana son qaa
ce fuskarta yace
''ko na aure duka matan duniyan ma meye naki a ciki''
cikin fushin da batasab ya fita ba tace
''wallahi kuwa,tunda ni dama yar amshin shata ce ba,na kusa sanin inda dare ya yimun,su mero na kusa ai baka da damuwa''
Dariya taso kama
shi hanin tsabar miskilanci da qarfin hali irin na mutum,ga gaskiya amma ka qita qiri qiri
''gaskiya ne''ya fada yana kamo hijabinta da take qoqarin,ficewa a dakin
''alfarma daya nakeso kiyimin don Allah,ruwa zaki dan duma ma min ki kaimin bandaki,idan i
nna ta tambayeki kice mata zafi nakeji duk da nasan halin innan sarai ba zata tambaya ba,amma idan da takura ki barshi sai naje nayi haka''
bata bari ta kalleshi ba don gaba daya ya gama kunyatata,har ga Allah ta dauka da wasa yake ba wankan zaiyi ba ashe
shi da gaske yake gaya mata sai qeya ta turo masa
''salon ta zaci wani abun mukayi''
''to haramun ne koma me mukayi din,'yar qauye kawai,ita innan ai ba yarinya bace,tafiyarki kawai zata kalla idan ma wani abu ne ta gane,idan baki wasa ba ma sai na gaya
mata munyi wani abun inga ya zakiyi''
tayi imani,kadan daga aikinshi ya kum kunyatata saboda haka kufce ta fice ta hada masa ruwan wankan
yar halak inna kam dauke kanta tayi abunta tana faman jan mero da hira,maryam din ma zama tayi can gefe tayi ts
uru tsuru cike da kunya tana son ganin reacting na inna wuri saidai babu abinda ta fahimta don hirarta kawai innar take,kafin ma abdallahn ya fito ta shige daki abunta ta kama wasu sabgogin,sai gun ya rage daga ita sai sister mero(lol)
maryam ta dan dubet
a
''wai nikam na tambayeki mana
?
''
''ina jinki''meron ta fada cikin tsoro tsoron kada ko wani abun maryam din zata yi mata
''bakisan cewa haramun bane shiga guri ba tare da kayiwa masu gurin sallama ba''shiru ta danyi don babu inda ilimin nata yakai,na
salla dai ta sameshi baina baina
''ai ina yin sallama,kune bakwa ji da wuri''
''waya gaya miki idan kayi sallama cewa akayi ka cusa kanka kawai,sallama na nufin neman izini,koda kayi sallama addini cewa yayi kada ka shiga sai an baka izini,haka Allah ua
fada cikin qur'aninsa mai girma''yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah kada kushiga wami gida da ba naku ba face sai kunyi nemi izini kuma kunyi sallama abisa ahlin gidan,wannan shine yafi alkhairi a gareku ko zaku fadaka,idan baku samu kowa a gidan ba k
ada ku shiga har sai an baku izinin shigar,idan kuma akace da ku koma to ku koma,wannan shine yafi tsarkakewa a gareku''kin fahimceni naga kina raba ido zancan Allah na karanto miki cikin qur'ani''kai ta gyada mata kawai
sai ta dora''kinga zancan Alla
h na gaya miki ko
?
so daga yau kada ki sake fado mana daki ba tare da na baki izini ba''sai ta dauke kanta can wani bangaren kamar bata jita ba,ran maryam ya dan sosu mai yarinyar ke nufi
''dake fa nake mero''ta fada cikin dan zafi zafi
''to ai abdullahi
ne yaci na shigo ko''
''ba ruwa na na gaya mii daga yau kada ki sake sai na baki izini,ko shi ina iya hanashi shiga,idan kuma baki ji ba ni da ke ne''
sai ta danji tsoro don maryam din bata taba mata magana irin haka ba,a sanyaye tace ''to''
🍂🍃🍂🍃
🍂
🍃
''duk abinda ta faru ko baki fada ba bintu na sani ba cikin hayyacinki kike ba,amma ki kwantar da hankakinki duk abinda yq samu bawa da sanin Allah,kuma abinda nakeso da ke,bana son ko kadan ki nunawa nene kinsan wani abu game da abinda ke faruwa di
n,abu na farko da zamu fara yi shine zamu raba sadaka makarantu makarantu na alarammomi a samu cikin addu'a,koda zamu nemi abdallah ba zamu nemeshi a bayyane ba saboda na tabbata babu wanda yasan halin da yake ciki koda qasa batasan wanne hali yake ciki sa
bida da ta sani da tuni na tabbatar an baza labarin cikin shafukan jaridu da mujallu,sabida haka yadda Allah ya rufawa al'amarin asiri muma cikin surri zamu ci gaba da bibiyarsa har Allah ya warware mana wanannan daurin gwarmai din,addu'a zaki duqufa yi ma
sa babu dare ba rana domi, addu'ar mahaifiya karbabbiyace kan 'ya'yanta''
''na gode qwarai kawu,Allah ya qara girma ya bar zumunci''
''ameen bintu kamar diya kke a gareni,irin hiyayyar da kika yiwa iyayenki irinta kike mana,hakanan kowa naki ne bab
u wanda baya morar arziqinki komai dukiyarka kuwa,to don me taqi matsalar ta taso ba zamu shiga ciki ba,abinda nake dak qara jaddada miki shine ko a fuska kada ki nuna mata abinda suka miki ya sakeki,kici gaba da binta ahakan,nayi imani addu'armu Allah baz
ai wofantar da ita ba''
''na gode kawu''haj bintu ta fada idanunta fal da qwalla zuciyarta kuma cike da taqini da qauna cikin rahamar Allah
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Kamar wani mahaukaci haka ya fado dakin futu futu da shi,tana kwance kan gadon dakin an tallafo
bayanta da filo,tun daga ranar da mugu yayi mata wannan dukan bata qara iya yin komai da kanta ba saidai a yi mata,ga baki na magana ga ido ga kunne amma dai qafafun da gangar jikin basa aiki
''yaya,adnan ka samota
?
''ta tambayeshi cikin zaquwa
tsaki
yaja ya zauna a gefanta cike da bala'i yace
''nifa na gaji,wallahi nene na gaji babu inda zan sake komawa,zuwana biyar dajin amma na kasa gane gidan sama ko qasa na nemeshi na rasa,shikenan mu haka zamu qare cikin wahala,wallahi baqin jininki muka debo wa
llahi,haba da Allah malam hauka ake
?
''
kwantar da murya tayi tamkar ita ce uwar ma
''haba adnan,zahariyya yar uwarka ce da baka da kamarta fa,ka daure kai kuwa mana da alamu wallahi tana cikin mawuyacin hali na neman taimakonmu''
a fusace ya kalleta
kamar mai shirin sharara mata mari
''jaka ce ta yimin gula a ciki
?
idan na koma wanann na zama alade,ke idan na koma ma Allah ya tsinemin,dazu fa ina tsammanin kurace ta tasanmin badan ina cikin mota ba da tuni yanzu na zama dan gari a lahira haka kawai a
kan wata banzar zahariyya da budurwata ma ta fiye min ita,nafsi nafsi fa kawai nene ehe''ya fada yana miqewa ta bishi da ido
janye janye janyen lokoki ya fara yi mata,da sauri tace da shi
''meye haka adnan,kasan fa na hanaka yimin bincike cikin daki
ko
?
,akwai surrukana da ajjiye ajjiye na fa''wani kallon banza ya juyo yayi mata yana fadin
''dama kin kwantar da hankalinki don yau ranar diban kaso na ne,zan dibi duk abinda nakeso don ma fuskanci wannan tafiyar babu nasara,odan yaso duk ranar da kika sa
mu nasarar kashe abdallahn ki nemo ki sai muci ganimar tare''iya bakin qoqarin hanashi da bakinta tayi amma a abanza,kallon tsiya ma bata isheshi ba balle yasa ran na arziqi,tana kallo ya dinga balle lockers dinta yana kwashe duk wata kadara tata yana hade
wa cikin wata 'yar jaka,kaf ya kammala ya tako gabanta yasa hannunshi ya tsinke sarqar gwal da ke wuyanta wanda garin fincikar har biyo shi tayi sabida rashin qarfin jiki,kuka ta fashe da shi
''kada ka yimin haka adanan,nifa mahaifiyarka ce,ni nasha wuya
gun haihuwarka na kawoka duniya''dariya ya sheqe da ita
''gaskiha nene kina da mantuwa,kefa kika ce farauta halak ce kuma ba'a barin ruwan gangare ace sai an dawo za'a diba,wanda ya samu dama ya dama,duk inda ka hadu da arziqi kayi qoqarin yagar rabonka d
on yanzu duniya sai kana da shi ake yi da kai duk fa hudubarki ce wanann,to kawai yau daya don ta dan ratsa da ke zaki hau raki,ai dama malami yanason ya koyawa dalibinsa karatu yaga yana aiki da shi pratically
''To banga abun damuwa ba don nayi aik
i da hudubarki,kyan da dama.....ya gaji uwarsa,sai haduwa ta gaba nene''
ya fada yana shirin barin dakin
''wallhi adnan idan ka sake ka tafi min da dukiya sai na tsine maka albarka,butulcin da zaka yimin kenan matsouaciyacin yaro
?
''dariya ya sheqe da ita
kana yace
''kin dade baki tsinemin ba nene,kinga idan ma kinso a sama miki lasifiqa a abaki duro ki hau kiyita gayawa duniya kin tsinewa adnan damuwarki ce,nidai na debe kasona don na gaji da gafara sa banqo qaho ba,idan na gurin abdallah ya samu kya iya
kirana muci tare,byeeee''ya fada yana daga mata hannu tare da sake rungume jakar da ya lodawa duk wata kadara ta nenen yana fucewa adakin
ihun barawo take ta faman zabga masa saidai a banza don babu kowa cikin gidan idan ba security dake bakin aikinsu ba
,su kuwa sunsan babu kowa cikin gidan daga ita sai danta don haka basu kulaa ba domin suna tsammanin ciwonta ne ya tashi wanda dukkansu sun dauka ciwon hauka ne ya sameta
hakanan ta qaraci ihunta ta fashe da kuka mai cin rai tana tsinewa adnan mummun
an tsinuwa a haka zubaida ta tadda ra,koda ta gama mata bayani dogon numfashi ta ja tana fadin
''tabdijan,nice zan tashi a tutar babu,wannan wace iriyar magana ce ma mara dadin ji,to wallahi bazan zauna da kyau na da komai ba rayuwa ta ta qare a tantal ba
taiti ba,a banza wancan tsinannen mai qirar sanudawa yazo yayi awon gaba da ni ko ya kasheni,gwara tun yanzu na samawa kaina mafita,zuwa zanyi na cire cikin nan na shiga sabuwar rayuwa,ga masoya ina sa su masu yawan gaske masu kudi na gani a fada,gwara naj
e wlh na yagi
rabona nima na kafa kaina''tana gama fadar haka ta haura gadon ta fara cire dan kunnen gwal dake kunnen nenen mai hade da banguls da zobensu wanda ta tabbata adnan bai kula da su bane,domin da ya kula da su babu abinda zai hanashi yin hauzi d
a su kamar yadda yayi da wadancan
''au kema zubaida haka zakiyi min,ashe dukkanku matsiyata ne,yayana na cikina babu mai tausayi na kune masu rusani
?
'''tsayawa tayi cak tana kallonta
''tab lallai ma nene,ke don Allah baki ji kunyar kanki ba
?
adnan ma
yayi miki haka ballanta na ni
?
''
''yanzu don adnan ya yimin haka kema sai ki biye masa
?
''
''hmmm,sai kuma kiyi,ina ga kin dade baki bata yawun bakinki ba,ai tunda kika ahiga tsakani na da abdallah kika min asirin da aka ciren sonsa to wlh babu ni babu au
re,rayuwar bariki ta fiyemin inda zan zuba jarin jikina na samu kudi''tana fadan haka tana sabule da lalube duk wani abu da yayi saura wanda adnan bai kai ga daukewa ba,cikin haka tayi katari da takardar wani gida ta dauke abinta,tana jin nenen na qwala ma
ta kira har ta koma rsine mata itama amma kallon arziqi bata iaheta ba tayi gaba abinta,don ta riga ta sani uwar tasu ba imani gareta don me ita zataji tausayinta kuma
?
,ai raba arne da makami ibada ne
A ranar bata bari ta kwanan ba ta hada ya nata ya
nata ta nufi gidan wata aminiyarta da ta jima tana mata hudubar shaidan kan cewa ta mori kyanta wlh ta qyale wani abdallah ta tsaya ta nace masa yana wulaqantata bayan ga samari nan da alhazawa na sonta ido rufe
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Duka hidimar ranar ita ta
karbeta don inna wuro da abdallah na gurin tsoho alhaji wanda ya sauka qasa nijeria da misalin sha biyu na rana,tayi mamakin ganin hisham shima ya iso a ranar
''ina sane da ranar dawowar tsoho alhaji a lissafe nake maryam,abdallah na raina da shi nake kw
ana da shi nake tashi ko yaushe''qwarai ta gasgata hakan tunda gashi taga zahiri
Gidan kusan a cike yake da yan sannu da zuwa wanda basu samu sararawar mutanen ba sai bayan sallar la'asar
Tsoho alhaji wanda asalin sunanshi muhammdu dattijo ne mai
cikar kamala da nutsuwa,dattijo ne da ya amsa sunan dattijo bawai muna dattijo ba,dattijo ne da kallo daya zaka masa kwarjininsa ya cika maka idanu,yadda matarsa inna wuro(fatima)ke da kirki haka shima yake
Murmushi ya saki har ya dan fidda sauti bay
an ya kammal jin dukkan wasu bayanai daga bakin maryam da abdallah hisham harma da inna wuro daga dan abinda ta sani
''in sha Allahu da izinin Allah indai sammun ne bi'iznillah na bada gaskiya ga Allag nan da kwanki bakwai zaka miqe abdullahi ka taka
qafa
funka komai yazo qarshe,zan yabaki miki maryam kinyi namijin qoqari qwarai da gaske tunda wuro ta gayamin ba haka kuka zo ba,kamar yadda naji bayanai daga bakinki,na abubuwan da kika dinga nasa amfani da su,ayoyo yine masu kyau matuqa da gaske,gakanna masu
tasiri qwarai da gaske wajen ruguza sihiri ko wanne iri ne bi'iznillahi ta'ala,yanzu akwai wasu magunguna da saiwayoyi da Allah ya horemin saninsu,yau basai gobe ba zan fara hadasu guri guda insha Allahu baka wuce kwana bakwai ka warke abdullahi kaci gaba
da haquri wannan wata jarrabawa ce Allah ya maka don ya gani shin zaka gode masa ne ko zaka butulce masa
?
,a baya ya maka duk wata ni'ima ta dukiya kyau ilimi nasaba da gata a yanzu ya amshe abinsa yayi ne duka don ya jarabci imaninka,to alhamdulillah bisa
dukkan alamu ka karbi duk wata jarrabawa daga gareshi kuma ina maka kyakkyawan fatan samun cikakken