Showing 69001 words to 72000 words out of 176330 words
da ni maryam,saidai ga yadda lamarin Allah ya kasance,date din bikinku da abdallah yazo daya,kinga ma ko a
yanzun gidan ya fara cika da mutane wasu ma rabonsu da gidan nan an jima,kinga bazan iya tsallakesu ba na fita wani guri ba,amma nayi miki alqawarin bayan komai ya lafa wuni guda zanzo nayi a gidanki,hakanan zan dinga dubaki akai akai da yardar Allah''
kafin tace komai muryar abdallah ta ratso falon yana kiran mamin
''gani nan abdallah''
da azamarsa ya shigo hannunshi daya riqe da leda baqa mai kauri mai dauke da tambarin wani gurin saida kayan maza na ado,daya hannun kuma rafar yan dubu dubu ce daur
i biyu,cikin shigar qana nan kaya yake,sai ya sake wani dan banzan kyau,farar fatar nan tayi luf da ita tamkar rainon larabawa,ko dama can yafi yanayi da su din sam sai ka rantse babu abinda ya hadashi da nijeria ,sai ya danyi turus yna dubansu
''qaraso m
ana abdallah,ya ake ciki
?
''
ya qaraso ya zauna gefanta
''mami duka guest house din guda biyu sunyi kadan,yanzun dai hisham ya samar ma ragowar mutanen hotel''
''yayi kyau hakan,sai ayi total abiya kudin kwanakin da zasuyi da abincin da zasu ci basai an
yi jigilar kai musu daga nan ba''
'to''yace yana dora mata daurin kudaden kan cinyarta
''wannan fa na meye
?
''
''wani abokin aikina ne ya bani gudun mawarshi.......''yayi maganar yana qiqarin zaro wayarshi daga aljihu wadda keta faman ringing,ya kara a k
unnenshi kana ya niqe tsaye yana fadin
''gani nan zuwa''yadan dubi nami yana yin gaba
''mami ina zuwa''
''uhm,yanzu haka abincin na da nasa aka kaima baka ciba,kadai kula da cikinka abdallah''
''ok mami''ya fada yana mata murmushi gami da qarasa ficewa
a gurguje
nasiha ta mata sosai irin ta 'ya da mahaifiya kafin ta saka driver ya kaita zuwa gidan cikin kuka da kewar rabuwa da juna
ita ta ruqota suka dinga tsallake mutanen da suka fara cika gidan ta rakata har bakin motar sai da suka fice kana ta
juya ta koma ciki
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Tun lokacin da idanunsu sukayi tozali da katin daurin auren abdallan hankalinsu yayi qololuwar tashi
''wacce irin hasara nuke shirin tafkawa haka,me kuke tunanin zai faru matuqar muka bar abdallah yayi auren nan,cikin
watanni tara ko goma da yin surensu matarshi kan iya haihuwa,zata iya kasancewa ta haifi namiji ma,wannan shike nuna munyi bankwana da cikae burinmu
?
''
cewar nene dake faman safa da marwa,can cikin dakinsu zahariyya da zubaida kuwa kowa da abinda ya d
ameshi,zahariyya irin tunanin nene take,ba qaramin tashin hankali take ciki ba,burin da take da shi ya girme mata,yau idan abdallah yayi aure daidai yake da nisanta da dukiyar da suke kwadayin zareta daga hannun mamallakanta su su amfana da roman nata.
Afusace ta kalli zubaida dake zaune a cure can quryar gadon tana ta faman surfafa kuka wanda tunda labarin auren ya isa kunnenta itama ta hana kanta sukuni,kuka take tuquru kamar ba gobe,udanunta duka akumbure suke sun ui luhu luhu sosai daga jiya zuwa y
au
''dalla malama ki wa mutane shiru,banza shashasha mara kishin kanta bare yan uwanta,yasan dake din ai ya zabi ya auri wata ba'a gabanshi kike amma ke kin quntata rayuwarki saboda shi''
dama a fusace take maganar zahariyyan sai ta qara tunzurata
'
'anqi ayi shirun bazanyi shiru ba,kece babbar shashsha da bakison so na haqiqa ba,babu ruwanki da sha'ani na ehe''sai kuwa zahariyyan tayo kanta a zqbure tana cewa
''ni kike gayawa haka,yau zan nuna miki baya ga shekaru da na fiki na fiki iya rashin mutun
ci''dambe ne ya sarqe tsakaninsu har nene dak samanta ta jiyo hayaniyarsu ta sauko,da qyar ta iya rabasu tana fadin
''sai ku kashe kanku ai,yan iskan yara marasa hankali da tumani,mazq ku raba abun fada cikin taron mutane''
sai sukayi tsit suna maida
numfashi kowacce zuciya iya wuya,nene ta kalli zahariyya tace ''ki sameni a sama''ta juya ta fice ita kuma ta rufa mata baya,gware suka kusa yi da adnan wanda ke qoqarin hawa saman da gaggawa
''lafiyanka kuwa
?
''nenen ta tambayeshi bayan ta danja baya tan
a qare masa kallo
''muje sama nene akwai magana''ba tare da kowa ya sake tankawa ba suka duru saman gaba daya
''barin yarinyar gidan nan babban abun farinciki ne a garemu,mun riga da mun gama magana da malam na hayi ya tabbatar min da cewa zai mana a
iki ammafa matuqar tana cikin gidan nan babu lallai yayi tasiri,tana da wani irin dafa'i a jikinta tun na kakanni da iyayen kakanninta,tunanin da nake yanzu kenan ta yadda zamu gabatar da aikinmu don auren abdallah ba qaramar barazana bace da faduwa garemu
sai ga kuma kyakkyawan labarin da na jima banji irinsa ba,mun gode Allah faduwa tazo mana daidai da zama,yau din nan ba sai gobe ba zamu isa vurin,malam na hayi,kwana daya zamuyi a hanya zuwa jibi zamu dawo ya kama ranar daurin aure kenan ko ana gobe daur
in aure
?
''
ta tambayi,adman,sai da ya danyi tunani kadan sannan yace
''ana gobe daurin aure ne''
''to yayi,kai adnan ka zauna muje da,zahariyya,ka shiga ayi duk wata hidima da kai,banason a fahimci komai,zan sanar da haj bintu qanwar ubanku ce ba lafiy
a zamuje dubota''
a nan suka gama dukkan wani shiri da tsarinsu kana suka shirya ta gayawa mami abinda ta shirya gaya matan,cikin tausayawa mami tace ayi mata sannu Allah ya qara sauqi,idan sun isa zata kira su sai ta bata ta mata sannu
🍃🍂🍃🍂🍃
🍂
tun daga qofar gidan ta soma ganin alamun cika,mutanene maza da mata keta kai kawo,a haka ma ba'afara gudanar da bikin ba kenan ina ga kuma an fara,gefe driver din ya samu yayi parking,akwai sabo tsakaninsu da mutunci da girmama juna duk dacewa ya kus
a shekaru hamsin dattijon mutum ne mai hankali da nutsuwa,malam baaba direba ya kalleta bayan ya fito
''to malama meramu(haka yake kiranta sunan diyarahi ce ta fari data rasu),Allah ya sanya alkahairi yasa ayi a sa'a,ayita haquri da rayuwa,mu sai ranar d
aurin aure idan mun dawo daga na mai gida abdullahi''
kanta a sunkuye tace''na gode sosai baaba,Allah ya nuna mana''ya bude boot din motqr yana cewa
''bari in shigar miki da kayan ko''da sauri ta amshi jakar da ya fara fitowa da ita
''a'ah baaba,ka bars
hi ga yara zansa su shigar min da su''tayi kirqn yaran maqotan dake zaune can gefe da su wadanda da wasan qasa suke tayi da yan guje gje ganinta yasa suka bar abinda suke suka tsaya kallonta,kiransu tayi kunsan amarya da farinjini a guje suka taho dukkansu
har ana rige rigen zuwa,kqn ta qarasa mqganar ma sun fara zundumar kqyqn,nata suna shige mata da su cikin gida,dubu biyar ta qirgo cikin dubu dari biyun da mami ta bata tace ta riqe a hannunta tasan amarya kudi basa zama a hannunta,da fqri qin karba malam
baaba yayi
''idan da ni mai wadata ne meramu ai nine mai baki ma a matsayin gudun mawa,ke yarinya ce ta gari merama,babu komai tsakaninmu dake saidai muyi miki sai fatan alkhairi''
sai ya kuma karya maya zuciya
''indai ka daukeni 'ya baaba ka karbi
kudin nan,ayi min addu'a''da qyar ta shawo kansa ya karba yana sa mata albarka,sukayi bankwana ta shige gidan ta juya don shiga gidan,tun daga qofar gidan ta fara ganin canji,yasha fenti radau ruwan madara tun daga waje har cikin gidan
mutanene da su
ka kusa dosan ashirin a tsakar gidan,hira ce kawai ke tashi cike da farinciki,dangin mamanta ne da na babanta na nesa,na garin gaya da sauran garuruwa,sallamarta ya sanya su saka guda atare kowa na fadin albarkacin bakinsa ganin yadda tayi kyau ta canza ta
mkar ba maryam din ba ,kunya ta kamata ta qarasa gurinsu suka gaggaisa,maryam mai alkahiri,ce duk da yanayin gidansun hakan bai hanata idan ta dauki albashinta ta duba mabuqata sosai cikin dangin nasu ta taimaka musu da dan abinda ba'a rasa ba iya abinda z
ata iya
daga nan dakin mamanta ta wuce,nan din ma da mutane dakin yayi kaca kaca da kayyaki samiru da kayan robobi wadana aketa kwashewa za'a tafi jere,suka gagggaisa ta shige dakin gadon mama,ita da hindatu ne a dakin kayan sawa ne zube saman gadon s
unata aiki,gefan gadon ta samu ta zauna ta soma gaida maman,dafe bakinta hindatu tayi
''la la la adda maryam,tabdijan irin wannan canzawa haka gaskiya mami ta iya kiwo,za'a gigita ya abdur rahim kenan''alamu tayi mata da ido tayi shiru don Allah
''qa
raso maryamu ki fidda kayan da kike so za'a bada na bayarwa''
''um um mama kawai a bawa wadanda za'a bawa dim babu komai''hindatu ta janyo jakar bakko gaban maryam din tana fadin
''duba kayan nan adda maryam dinkunanki ne jiya adda raliya aiko idris dire
ba ya kawosu gobe zata amso miki sauran''
da daidaya ta dinga daga kayan,ba qaramin burgeta dinkunan sukayi ba duk ciki babu na kushewa
''Allah ya saka mata da alkhairi''ta fada bayan ta kammala dubawar
A bakin fanfo ta fito yin sallar la'asar ta ta
dda jamila ta fito ita kuma daga bandaki,gaba dqya ta fige ta lalace kamar mai cutar qanjamau,wani banzan kallo ta yiwa maryam din tare da jan tsaki,bata kulata ba ta bude fanfon ta kunnashi ta fara alwala,bata kai ga gamawa ba taji an bangajeta tayi taga
taga kamar zata fadi sauran qiris ta qume goshinta Allah ya taqaita mata ta dafe kan fanfon,miqewa tayi tana duban bayanta,binta ce a tsaye cike da tsabar rashin kunay tana girgiza,ta arkade jikinta da ya debi qura kana ta kalleta
''baki gani ne binta kik
a bugeni
?
''
''ina gani mana sai me
?
,dama jiran dawowarki nake cikin gidan nan,tsofaffin munafukai maciya amana masu aure mijin yar uwarsu''
duk da kalamanta sun mata ciwo amma sai da ta bata dariya,tsayawa tayi kallonta kawai,cikin yaran gidan susu goma
sha bakwai binta ita ce qanwarta ta tara,aqalla ta bata ahekaru kusan goma,sai taga ada ma ba ni ta kanta take ba sai ayanzu,ranar tqrihi a rayuwarsu,kada kai tayi tana sake yin murmushi ta juya don ci gaba da alwalarta kafin tace
''duk wadanda kika kira
da wadan nan sunayen ai aun riga da sunsan kansu,kinga kenan bada ni kike ba''
''dake nake mana,kuma idan kin isa ki tanka kiga yadda ake ruwan bala'i cikin gidan nan''
ta zubar da ruwan dake bakinta ta gyara daurin dankwalinta kana ta dafa kafadar binta
n
''mai abun fada baya fada,harkar girma muke da mutunci bata bala'i da masifa,ina da damar da zan miki dukan tsiya binta hakan ba gagarata zaiyi ba,amma bazanyi hakan ba abinda kuka shuka kuke girba ma kadai ya isheku duka mai taba qololuwar zuciya''ta s
ake mata kafada tayi dakinsu
''ki dakeni mana kinji ko karuwa kawai''
''ke kuwa tunda bata kulaki ba ai sai ki shafa mata lafiya''inji kulu dake diban ruwan wanka
''babu ruwanki munafukai,dama tun jiya naga kunatavrawar kai ke da uwarki a kansu''kul
u ba haquri kamar yadda bintan keji da kanga,take suka hau dambatawa,ragowar dangin babansu da basu je jere ba ne suka rabasu
Dawowar yan jere suka hau hirar gidanjan su maryam din yadda Allah ya musu baiwar samun mazauni mai kyau da qayatarwa ta,maga
nar ta qara hasala hadiza da yaranta wadanda suka zame mata qawaye,suke kuma tayata haukan da take ta faman yi,don tuni jikin huwaila yayi sanyi,saidai atafau hindatu ta hanata shiga jikinsu,tace sam baza'a maimaita abinda ya faru shekarar bara ba,an dai f
idda kayan sawa jakanku na da takalma cikin kayan maryam din an bawa yaranta kuku lubabatu da batulu,da murnarsu kuwa suka arba koba komai sun samu na fitar biki,wannan karbar ma da sukayi saida ya zama bala'i,hadiza da yayanta suka fito suna zubda ruwan r
ashin mutunci cikin dangin ubansu,hali kam sun saidashi,wanda baisan halisu ma ba ada ayanzun ya sani,kowa ya budi baki tir yake da halayensu
🎄🎍🌲🎍🎄🌲
Tara ga wata ya kama ranar talata ranar sukayi kamu,washegari laraba sukayi budan kai duk shiga
r da sukayi iri daya ne komai da komai ita da hindatu hatta da yari,alhamis aka musu wani wani dan reception na fulani wanda shiga ce ta fulani kowa da kowa yayi,ba qaramin qayatarwa tsarin nasu yayi ba,komai a tsare cikin nutsuwa da kwanciyar hankali
Ranar juma'a ya kama daurin aure,a gaya aka tsara za'a daura auren wannan karon,dalili da yasa kenan gidan ya zamto sai mata kawai mazan duka sun tafi gaya
Da yammacin gidan maman zahra suke zaune maqotansu,tana tsakiyar qawaye da 'yan uwa,tayi kyau
cikin shadda 'yar ubansu lemon green da akayiwa adon light blue,rigace da zani dinkin ba qaramin mata kyau yayi ba,tamkar wata fure haka ta koma,raliya na gefanta tana zuba mata abinci cikin plate kana ta miqa mata
''maryam,karbi kici,tunda aka fara sabgo
gin nan baki ci abincin kirki ba fa''
ya mutsa fuska
''banajin dadin bakina raliya,faduwar gaba nake fama da ita tun da safe''
murmushi tayi
''fargabar shiga sabuwar rayuwa ce,kowacce mace najin hakan har da bacin rai ranar daurin aurenta,wasu ma har
kuka suke kafin suji sanyi cikin zuciyarau,kiyita ambaton Allah''
kafin tace komai waurta ta fara kuwwa,a kasalance ta ciro mami ke kiranta,mirmushi tayi sanan tace
''Allah sarki mami na''
''tun da safe naso kiranki maryam,nasan tuni an daura tun sa
fe ko diyata girma ya hau kanta an zama manya''murmushi ta sake yi tace
''na yamma ne mami,suna can dai''
''to Allah yasa ayi a sa'a a gaida maman kice ina mata Allah ya sanya alkhairi''
''ameen mami,na gode''
batulu tayi sallama falon sanye da day
a daga cikin kayan da maryam ta bata an gyara mata daidai ita,sun mata kyau kuwa don duka yaran gidan nasu babu laifi akwai kyau irin na fulanin usuli
''adda maryam kizo kinyi baqi suna falon mama''cike da mamaki ta kalleta,gau ta zama adda,sunan da koda
wasa bata taba jin wani daga cikin uaran gidan ya kirata da shi ba idan ka dauke hindatu,hatta da isyaku autan gidan
''kice ina zuwa''ta bata amsa tana janyo mayafonta ta lullube jikinta,ta dubi suwaiba dake zaune gefe tace tazo ta rakata
da qyar ta samu
ta kutsa ta ahiga gidan nasu saboda yawan jama'a musamman da masu kidan qwarya suka baje hajarsu cikin qwarewa don daga cikin gidan sarki aka daukosu
qannenta shamsiyya,azara,balaraba da yasira na zaune daga gu guda an samu abinci suda yaransu anata
kwasa,sannu tayi,musu kafin ta shigesu,yasira da shamsiyya suka danyi qus qus kana suka tabe baki
''an samu duniya''inji azara
tayi sallama falon,maman ma zaune tayi kyau cikin dinkin atamfarya,sai ta koma kamar yarinya mai qananan shekaru,Allah ne kadai
yasan farincikin da take ciki,babu shakka komai yayi farko zaiyi qarshe,aure kuwa lokaci ne idan yazo ko ba'a shirya ba sai anyi shi,fata dai kada gaggawar anason ayi auren tasa aje ayi zaben tumun dare
abokan aikinta na na gurin haj atika,taji dadin zuw
ansu kuwa qwarai da gaske
qarfe shida suka fita meena event center suka gabatar da wata qwarya qwaryar dinner,ta maryam ce ita da qawaye da iyayenta,su hindatu kuwa tuni jabir yazo ya dauke matarshi suka wuce dinner,fir maryam tace ma abdur rahim bata
buqatar wata dinner,su din ma da zasuyi sai sun dawo,hindatu da jabir na mata dariya sukayi tafiyarsu,bashi kuwa ya dawo da ita gida ba sai daya saura na dare,maryam din zata soma mata fada tayi shigewarta bargo tayi kwanciyarta
''hindatu rawan kan amarc
i ya fara tabaki kenan''cewar raliya wadda ke gyara kwanciyar fadil,suna jinta tana musu dariya
🎄🎍🌲🎍🎄🎍🌲
tun qarfe biyar da rabi na yammacin ranar asabar motoci suka cika layin har suka musu kadan,tilas ya sanya wasu motocin suka dinga parkin
g a
bakin titin unguwar,moto cine na kere sa'a waccan tana wace wannan haka wannan ma haka,a nutse kowa ke zaban wadda zai shiga kasancewar tare za'a tafi,sai hindatu ta raka maryam din tukunna.
''da Allah malama kihi ki foto,kunzo kun sanya uwarku a
tsakiya kuna neman sata kuka,ina cewa ba'a kanku aka fara aure ba,haba da Allah''inji yayar mama hajiya aysha,hindatu da maryam dinne duqe gaban maman,maryam ta soma qoqarin taahi amma kuka yaci qarfinta ya hanata,sanye take da atamfa riga da simple zani a
n lullubeta ruf da wadataccen mayafi,hajiya aushan ce ta taimaka mata ta miqe ganim da gasken ta kasa miqewar,addu'o'in fatan alkhakri ta biyo yayan nata da shi.
caraf sukaji an damqe hindatu,jamila ce a zabure kamar mahaukaciya sabon kamu surutai tak
e zage zage da sumbatu kala kala
''shegiya tsinanniya,wallahi babu inda kika isa kije,gidan mijina nawa ne ni kadai,wallahi bazan baki damar cin irin daular da naci ba don uwar ubanki''ganin abin na gaske ne daya daga cikin qannen malam amadu sailuba ta q
araso ta daga hannu ta zabgawa jamilan mari
''saketa 'yar iskar yarinya mai kama da 'yar Allah bani,dul abinda kika aikata akayi muku shuru ba'ace muku komai ba bai isheku basai yau ranar da Allah ya tashi nina muku kuskurenku,shekara nawa kuna cutar amin
a baiwar Allah ta taba tadakai ta kalli waninku,tunda aka fara bikin nan baku,bar mutane an zauma lafiya ba,uwarku dai ta cuceku wallahi,kuma ki saketa tun kafin ki debi haqoranki a hannu,idan tsiyace kowa ma ya iyata''ba shiri ta saki hindatun taja da bay
a sai gata yaraf a qasa.
da gudu inna hadiza ta qaraso gurin,hannu ta dora a ka cikin qaraji tana fadin
''huwaila amina dake kanki sailuba,zaku kashemin 'ya,munafukai tsinannu,dama ai na dade da sanin kun fi son amina saboda 'yar garinku ce,to Allah
ya fiku kina ranar daukan fansa na tafe''
babu wanda yabi ta kanta,hssalima zamewa kowa ya dinga yi ko ruwan da za'a kwarawa jamilar an rasa me miqowa,su kansu sauran 'ya'yan nata na qofar gida suna jallin yadda motocin sukayi farin dangon daukar amare,kw
alliya kowaccensu taci tare da fatan daya daga cikin mamallakan motar ya taya
ta dubi sailuba sata zo wucewa tana sauri don kada ta rasa motar tafiya
''da Allah sailuba miqo min ruwa na kwarawa jamila kinga bata numfashi''kallon banza tayi mata
''ki
ci mutuncinmu kici na uwarmu kice zaki moremu,saidai ki nemi wata ta