Showing 93001 words to 96000 words out of 176330 words
ja hijabinta daga kan igiya tana fadin
''inna zanje gida,idan
na dawo r
yau to,idan kika ga ban dawo ba kuma sai gobe''
''to mero na gode Allah ya huta gajiya,ki gaida su azimin''
Bayan gaishe gaishe shiru,ne ya biyo baya inna tana kallon ikon Allah
''yanzu mairamu tun yaushe lalurar ta sameshi
οΌ
''a nutse tay
i mata bayani,kamq bqki innan tayi
''matsalar ku kenan mitanen binni,boko tasa baku da kulawa sam,ni kam ba wai zato ba amma wanna lalura ta yaron nan batayi kama da komai ba face sihiri,kuma kinsani sarai qanin kakanki masani ne kan irin wannna matsaloli
baki tuntiba ba,yanzu ma zuwa kukayi kenan idan qura ta lafa ku koma ba neman magani ya kawoku ba''
hisham ya guara zqma jin hanyar waraka na shirin samuwa
''a'a inna,har maganin ma mun zo mu nemeshi''
shiru tayi ma wasu 'yan mintina kana tace
''to Al
lah yasa adace,insha Allahu Allah zai kawo qarshen abun nan kusa''
maryam ta dubi inna wuron
''ina tsoho alhajin ne
οΌ
''
''kinsan watan tafiya gabas ne,bana Allah ya kirashi yana can qasa mai tsarki,ina tsammanin yau duka kwananahi uku da tafiya,amma
muna sa ran nan da sati uku zuwa hudu zasu dawo insha Allahu''
''Allah ya dawo da ahi lafiya''suka hada baki ita da hisham wajen fada
''daya dawo insha Allahu zan masa bayanin komai,idan rabo sai kuga ya warke''
''Allah yasa''inji hisham cike da fata.
In banda sannu babu abinda inna wuro kema abdallah,gaba daya tausayinshi ke damunta,irin wanna lalura mai fama da ita kadai yasan yanayin da yake ciki,da kanta ta bude musu wani daki can bangare daya,ba laifi dakin akwai girma,malale take da leda duk d
a cewa ba sabuwa bace,akwai labulaye a window da qofar,sai tsohuwar katifa da kujera qwaya daya,a ahare dakin yake fes kasancewar inna wuron bata lamuntar qazanta
hisham ya qarewa dakin kallo kana ya girgiza kai
''rayuwa mai juyi kuyi,Allah mai yadda yas
o''ta karanci me yake nufi,tabbas ita kanta ta sani abdallah dan gata dan gayu,young millonier yafi qarcin zama cikin qauye ma baki daya ba dakin ba.
maganar hisham ta katse mata zancan zucin da takeyi
''abdallaj bazai iya zama cikin dakin nan haka b
a maryam,zan ahiga na laluba inda zan samu kayqn buqata da za'a ma dakin kwaskwarima''kai ta jonjina babu bata lokaci ya fice,ta kalli abdallah suka hada ido uana mata nacin kallon nan nashi
''bari naje nayi alwala nayi sallaar la'asar,idan na dawo sai in
maka alwala kayi taka sallar''ta fada kanta aduqe sabida naugin idanunshi da take ji
kai ya jinjina mata kana itama ta fice.
Sai bayan sallar magariba sanna hisham ya dawo niqi niqi da kaya cikin akori kura,cikin mintina qalilan da taimakon yaran ma
qota da kuma taimakon mustafa aka gama ahigowa da komai,kayan daki ne da suka hada da katifa labulaye kujeru cusion guda biyu fanka ta tsaye carfet mai girma da zai iyacinye dakin,robobin wanka food falask har da risho dan madaidaici da set na tukwane,kaya
n sawa nashi da na maryam akwati wadda zata iya cinye musu kayan,duk dai wani kayan amfani da zasu iya buqata,hatta da kayan abinci ruwan roba da lemuka creet na qwai da sauransu
ba inna wuro ba hatta maryam ta jiniina siyayyar,sai da ya niqi tafiya har c
ikin jigawa sannan ya jado siyayyar,tunda su sinyi tsaki,yasunyo nisa da cikin birnin kano kuma basu qarasa jigawar ba.
A daren mustafa ya taimaka masa ya shimfida carfet da kujeru da katifa suka shimfida sabon zanin gadon cikin dakin hisham ya kwan
a tare da abdallah ita kuma ta kwana tare da inna wuro
ππππππ
zuwa goma na safe dakin ya zama gwanin sha'awa tamkar ba shi ba,sha daya na rana sai ga mutane daga company mtn sunzo hada solar,da mamaki maryam ta dubi hisham
''hidimar nan tayi y
awa hisham,sai kace zamu dawwama ne a garin
οΌ
''
murmushi yayi kana ya girgiza kai
''maryam kenan,baki san waye abdallah ba aguna,abdallah shine tsani na dukka wata rayuwa ko matsay da na take ko nake kan takawa a yanzun,ba don Abdallah ba ina zaton da tun
i na jima gidan mahaukata,abinda abdallah ya yimin bazan iya biyanshi ba,ya taimakamin da jikinsa da aljihunsa da lokacinsa ta qwaqwalwarsa ma baki daya,Allah ne kadai zai iya biyanshi abinda yayimin a rayuwa,babu abinda bazan iya bawa abdallah ba,wannan a
bun da nake masa ban masa kaso daya cikin darin abinda ya yimin ba,abdallah dan halak ne dole nima na nuna masa halacci''
kallo daya ta masa ta tabbatar daga qasan zuciyarsa abinda yake fita bawai daga fatar baki ba
cikin qasa da awa uku suka kammala
wearing din baki daya aka kunnata ta fara zuqar chargy,sai gidan ya zama abin kallo,al'ajabin yadda za'a samu hasken qwan lantarki daga hasken rana sukeyi har hakan yaso bawa hisham da maryam dariya,musamman yadda mero da inna wuro suka ce su kuwa zasu ga
ikon Allah.
Qarfe biyar sukayi sallama da hisham ya wuce katsina,kafin nan sai da ya danqa mata duk wasu takardu na abdallah da ya debo,qememe taqi karba tace sam,shi yafi cancanta ya riqesu a hannunsa
atm,card ya bata shima da fari cewa tayi bazata
karba ba don basu buqatar komai,yace a'a,kowanne lokaci buqata na iya kamasu,ta karba din don ya riga da ya kouawa mustafa yadda ake cirk kudin ta wani atm machine da suka gani cikin garin gaya,idan tana da buqata ta bashi ya ciro musu
''saidai akwai mag
ana daya,maryam gwamnati na fara matsantawa da hutun da mukace abdallah ya dauka ne,sabida akwai cases manya da ya fara aiwatarwa
kafin cutar nan ta sameshi,so na rasa me zan ce da su,don ina magana da su ne amatsayin abdallah''
shiru tayi na dan qanq
anin lokaci
''yanzu idan ka nemi alfaramar qarin watanni bitu zasu qara din
οΌ
''
''eh...don sunce na fadi iya kwanakin sa,zai dawo ba tare da ya sake dagawa ba,don qasa na da buqatarsa''
''to shikenan ka fada musu watannin biyun,kafin nan muga yadda Allah
zaiyi''
''Allah ya iya mana,ya bashi lafiya cikin sauri''
''ameen''inji maryam,ta rakashi ya yiwa inna wuro sallama cike da kewa ya tafi don a zamansa na kwama dayan har sun soma sabo
ππππππ
firgigit ta farka daga baccin da ya dauketa kan ab
un sallah,da sauri ga leqa fuskan abdallah dake baccinshi ta tabbata lafiyanshi lau,komawa tayi ta jingina da bangon dakin tana share zufa tare da tuno mafarkin da tayi,tabbas Allah ne ke mata ishara,sam kamar wadda aka dakawa gudumar mantuwa ta mance da m
afi yawa daga cikin addu'o'inta,ta waiwaya ahankali ta kunna wayarta ta kawo haske,qarfe uku,na dare agogon ya nuna mata,ba zata iya fita alokacin ta daura alwala ba din haka ta janyo carbinta taci gaba da ja tana ambaton Allah lokaci lokaci tana leqa abda
llah
ππππππ
Tana bakin murhun tana dama musu kunun duk da hanatan da inna wuron tayi qoqarin yi amma ta qiya,don tsakanin kwana ukun da sukayi cikin gidan indai ta kunna risho to abdallah zata dafawa wani abu,ta riga ta saba don rayuwar gidan s
un data tashi cikinta marabarta kadan ce da wannan
Mero ce tayi sallama ta shigo gidan,ta dubi maryam tace
''takwara ina kwana''ta waiwayo fuskarta dauke da 'yar fara'a ta amsa mata
''a'ah,mero,yanzu kuma sammako zuwa min aka koya kenan,kodon,kinga
kin samu abokiyar hira ne
οΌ
''inji inna wuro dake fitowa daga daki
dariya tayi
''wallahi kuwa inna,na samu larabawa abokan hira''haka take kiransu maryam sabida farin da suke da shi,duk da itama din farar bafulatana ce saidai nata farin baikai nasun ba
Ta shiga dakin inna wuro da suke zaune da mero,suna hira suna cin gyada marau marau,gefansu ta samu ta zauna kana tace da inna
''inna don Allah ina zan samu ganyan magarya
οΌ
''
''ganyan magarya me zakiyi da shi
οΌ
''
ta danyi murmushi,a zaton innan ko maga
nin mu na mata takeson ta hada
''akwai cikin kayan malam,amma ina tsammanin busashshiya ce,idan danya kike so saidai ko a yago miki can qofar gidan malam haladu''
''sai nasa yara su ciro miki,yaya abdullahi zakiyiwa magani
οΌ
''inji mero wadda ta cafe zanca
n,kallonta maryam din tayi,ta lura da yadda take yawan
kulawa da duk wani lamari da ya shafesu hakan yasa ta dan saki jikinta da ita
''eh''maryam tace mata,take ta miqe tana jawo hijabinta tana yafawa
''bari na kawo miki''ta fada tana ficewa,mero sunanta
maryam,tsirar gidaje biyu ne kawai tsakaninsu da gidan inna wuro,irin marasa shi din nan ne na azo a gani,hakan ya sanya hatta aurenta iyayenta suka kasa,hakan ya sanya take shigowa take taya inna wuro aikace aikacen gida,taci kuma na rana da dare wani lo
kaci harda na safe agidan bayan wanda tsoho malam yasa ake zubawa akai gidan naau sabida iyayenta da qannenta
zama tayi suka ci gaba da hira da inna wuron bayan ta mata tayin gyadar,cikin minti goma saiga mero da ganyan kore shar mai yawa kuwa,maryam
ta miqe tana mata sannu ta saka hannu zata karba
''bari na kai miki dakin ma''kafin tace wani abu har ta fice ta nufi dakin nasu,binta tayi da kallo har ta dagaabulen dakin ta shiga,duk da ta koma ta zauna amma sai hankalinta ya kasu jiyi ganin ahiru mero
n bata fito ba,miqewa tayi taa cewa inna wuro
''bari na daura alwala naga an kusa azahar inna''
''to...to,nima tashin zanyi''.
sai data daura alwalar sannan ta nufi dakin,kan kujerar dakin ta tadda meron tana faman zuba surutu idonta kan abdalladake
kwance,abdallah na daga kwancen yana kallonta
qarasa shigowa tayi
''kin manta bai da lafiya ne,mara lafiya baison surutu''ta fada tana qarasawa kan katifar
''amma meramu har mirmushi ya yimin fa''sai taji wani dim,ta waiga ta kalli abdallah,idanunshi n
a alaumshe sabanin dazun da yake tar a bude.
sauka tayi kawai ta janyo,abun salla ta shimfida sannan ta kalli mero
''ya kamata kije kiyi sallah ko,don lokaci yayi''
''shi kuma abdullahin fa
οΌ
''
''zaiyi shima''ta bata amsa tana tada kanbbarar sallah,
sai data kusa raka'a uku kafin meron ta tashi ta fita tana yiwa abdallah sallama
roba ta saka ta masa alwala sanna ta juyar dashi bangaren gabas,kafin ya idar ta zuba abinci cikin plate ta ajjiye,bayan ya gama ta dora mishi kan,fillow a saman cinyanshi do
n hisham yace a dinga barinshi wani lokaci ya dinga ci da kanshi don hannun ya dinga motsawa ya dinga jin qwarinshi sosai,ta koma saman kujera ta ta samu roba daya ta zuba ganyan magaryan tana gyarashi tare da cire qayoyin jiki
shirun da taji alamun b
ai fara ci ba ya sanyata dago kanta,hada idanu sukayi da sauri ta janye idonta,ta rasa dalilin da a kwanakin nan bata iya hada ido da shi na tsawon lokaci,jikinta yaci gaba da bata kallonta yake,a sace ta kuma daga kai zata saci kallonshi suka sake hada id
o,ya lumshe idon nashi da sauri ya bude,sign ne da ta lura yana yawan yi mata amfani da shi idan suka hada ido,batasan me yake nufi ba saidai a duk lokacin da yayi hakan takan tsinci kanta cikin wani irin feelings,wani
irin abu ne cikin qwayar idanun abdal
lan da bata taba ganinshi cikin idanun wani ba
ta janye idonta tana fadin
''kaci abinci kada ya huce''kai ya girgiza mata alamun a'a,babu yadda bata masa ba amma yaqi,qarahe sai daya bar abinda take yi din ta dawo kan katifar ta karbi plate din,ta de
bo ta miqa mishi,babu musu ya bude bakinshi ya karba yana kallon fuskarta,ganin ya karba sai ta ajjiye cokalin tana fadin ''bismillah to''tana maida fuskarta gefe
a tausashe taji an kamo habarta ana qoqarin juyo da fuskarta,qin kallonshi tayi kamar yadda
shima sam ya hanata sakewa har sai da suka sake hada ido,ture plate din abincin yayi da hannunshi guda kana ya jawota ta fada jikinshi.
tayi ta qoqarin tashi,saidai ya hanata,har mamakin yadda ya iya riqeta haka tayi,kamar zata yi kuka tace
''abdalla
h,bafa mu kadai bane cikin gidan nan ka sani''shiru taji,alamun bazai kulata ba,tilas ta haqura da yunqurin tashin tayi luf cikin jikinshi,ya lalubi hanninta ya saka nashi ciki ya jade yatsunsu guri guda tare da sauke ajiyar zuciya wadda ta haddasa mata sa
uyawar yanayin jikinta gaba daya,ta runtse ido tana jin fitar numfashinshi.
*_kuyi haquri da wannan_*
*mrs muhammad ce*
π
πππ
β
π½
β
π½
β
π½
[1:55pm, 9/24/2017] Huguma
π
:
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ
*ABADAN*
πΊ
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
ππΊππΊ
ππΊπ
πΊπ
π
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊπ
πΊππΊπ
πΊππΊ
ππΊ
π
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
π‘
*_home of expert and perfect writers_*
4
β£
6
β£
*_Annabi Muhammad S A W yace:duk wanda yaje gurin boka ko dan duba haqiqa ya kafircewa abinda annabi muhammad tazo da shi,hakanan ba za'a karbi sallarsa ta kwana arba'in ba(ba yafe masa su akayi ba,kuma ko yayi Allah baya buqata baxai kar
ba ba,babu wani abu da zaka/ki aikata ya zama kaffarar wannan zunubin da kikayi face ki tubarwar Allah tuba na haqiqa ba tuban muzuru ba,kuma kada ki yarda qafarki ta sake kusantar gurin bama zuwan ba,shin me kike tsammani idan Allah ya dauki ranki a gun k
o a hanyar zuwa kota dawowa
οΌ
,Allah ya kare mana imsninmu,ya,cire mana dukkan wani qulli dake zuciyoyinmu game da 'yan uwanmu musulmi)_*
*_Manzan Allah S A W yana cewa''ka tuna Allah lokacin da kake cikin jin dadi da yalwa,shi kuma sai ya tuna da kai lok
acin da ka shiga qunci da matsi da wahala(ba wai ka xauna kara zube ba don kana cikin jin dadi da wadatar rayuwa,ba zaka tashi addu'a ko tuna Allah da girma yake ba sai bala'i da masifu sun maka katutu,wannan kuskure ne babba,Allah yana fushi da bawan da b
aya roqarsa haka annsbi S A W yace mana,Allah kasa mu dace)_*
Saukar numfashinsa ne ya alamta mata bacci ya daukeshi,ta zare jikinta cikin dabara ta maye gurin da fillow,fuskarshi tarwai,kyawunshin nan mai daukar hankali yana nan,ta
zuba masa ido tana tuhumar kanta na wasu 'yan lokuta,ta janye idonta ta lumshesu hadi da sakin ajiyar zuciya,mero ta fado mata arai,sai ta ja siririn tsaki kana ta sauka daga katifar,hijabinta na kanta don haka abun sallah kawai ta gyara ta zauna akai baya
n bayan ta samu roba daban ta saka ganyen magaryar qwalli bakwai aciki,a nutse tayi bismillah cikin madaidaiciyar murya ta soma karanta suratul baqara cikin robar da ta zuba ganyan magaryar da ruwa aciki,da ka take karatun cikin daddadan sauti mai cike da
nutsuwa,don surar na daya daga cikin surorin data haddace saboda muhimmancin surar.
cikin barcinshi ya dinga jin tashin sautin karatun,sai ya gaza bude idonshi duk da ya farka,sosai yake jin dadin karatun,wani yanayi mai dadi na ratsashi,sannu a hanka
li ya dinga daga idanun nashi har ya kammala budesu gaba daya,ya zubesu fes kan fuskarta
kallonta yake da yadda bakinta ke motsawa cikin gwaninta da ita karanta alqur'ani da bawa kowanne harafi haqqinshi,ba kadan ba ta burgeshi,komai nata mai kyau ne da n
utsuwa,saita tunasar da ahi ahima wani bangare mai girma daya manta ko ya saki na karatunshi ya daina tilawa.
kan idanunahi ta kammala,ko kadan batasan yana kallonta ba har ta gama ta karanta falaq da nasi da suratul ikhlas aciki ta girgiza ahi sosai
har ruwan ya soma kumfa ta samu murfi ta rufe,ta zare hijabinta saboda zafin data fara ji sakamakon rashin kitso,Allah ya bata yalwar suma kamar yadda ala sana salin fulani ke da ita,ta zare ribbom dinta ta fara sake qoqarin tattara gashin guri gida donta
daureshi,bin sumar tata yayi da kallo,don iya zamansu bai taba ganin gaahibta haka ba,ba qaramn hirgeahi abin yayo ba,yana son mace mai yalwar gashi sosai,shi ua sanya yawancin lokuta a zamanin quruciya shi yakewa mami tsifa,rabi wasa rabi tsifa da haka su
ke gamawa,ya dan lumshe idonshi kana ya bude saboda wani abi da ya soki zuciyarahi da tunawa da mamin da yayi,qaunarta da kewarta ta zamar masa sabuwa.
ci gaba yayi da kallonta ganin yadda ta daureahi ta kuma nannade jelar kamar alkaki,ta juya don sak
e sanya hijabinta suka hada ido,gabanta ya fadi
''shikenan ya gama qaremin kallo''ta fada cikin zuciyarta,murmushi ya sakar mata ganin yadda take faman qoqarin sala hijabinta
''dubeta,kamar ba mijinta bane ni,banga marabarki da mutanen qauyen nan ba kam,
dama ina da ikon miqewa yau da sai na baki kunya fiye da haka yarinya''ya fada shima cikin zuciyarshi,fatanshi daya kada ta gudu,aikam addu'arsa bata ci ba don tana gama sanya hijabin ya gudu a dakin.
a bakin bishiyar darbejiya ta sameau zaune ita da
mero
''sannu maryamu,na kiyo ki ai kina karatu,har mero zata shiga nace ta qyaleki,hala abdullahin kike wa''
''eh inna wuro''
''ai yana da kyau kam haka din,qur'ani dama ai waraka ne''
''wani baccin ya koma
οΌ
''mero ta fada tana kallon qofar dakin nasu,s
ai data waiwaya itama ta dubi dakin kana ta dubeta ta girgiza kai
''amma aka barshi shi kadai,da fitowa akayi da shi ko inna wuro
οΌ
''inji mero ta fada tana duban inna wuro
''lallai kam yasha iska shima,duk da akwai fanka,amma ta Alla tafi lafiya''
ka
fin maryam ta kai ga miqewa har mero ta miqe ta fara yin gaba,da sauri maryam tace
''amma inna bazan iya dorashi kan kujerar ba ni kadai,ga mustafa baya nan''itama miqewar tayo
''muje,zaki iya in sha Allahu,ai jikin ya qara qwari ba kamar da ba''
tu
ni har mero ta isa dakin ta bude wheel cahir din ta tsaya agaban katifar abdallahn tana kallonshi,shima idonshin na kanta,wani abu maryam taji ya taba ranta sai ta