Showing 171001 words to 174000 words out of 176330 words
din ya fiyemin rufin asiri''kuka sosai zahariyya takey
i nadama kam babu kalar wadda batayi ba game da bitewa son zuciya da tayi,yanzu gashi ta kaisu ta barosu,ganin haka ua sanya mami tayi aumarni a dauketa a shiga da ita don yi mata aikin,haka aka dauketa aka turata zuwa dakin
jira na kimanin awa guda s
ukayi wata nurse ta fito da yaron cikin zanin mamartashi saidai tuni rai yayi halinsa ya mutu sajamakon tun fari uwar bata samu kulawa mai kyau ba lokacin cikinsa da kuma wuyar da yasha lokacin haihuwa,ba qaramin haushi mami taji ba don bata iya shiru ba s
ai da tayi fada sosai,minti goma tsakani aka turo zahariyya iyama zuwa dakin hutu,da tambayar abinda ta haifa ra farka a bakinta mami ke gaya mata ya rasu,ajiyar zuciya ta saki
''gwara da Allah yasa ya mutu,haqiqa ya samu gata mai kyau da ya mutu din''mam
i ce ta tsawatar mata
''kada ki kuma fadin hak,kul''mirmushin yaqe tayi tace
''mami don bakisan dan waye ba,ta yaya aka sameshi ba,amma tunda kince haka bazan kuma fada ba,amma mami don Allah ku yafemin,ba shakka mun cika azzalumai,ba muyi muku sakayyar
data dace ba,haqiqa samun mutum irinki mami sai an tona,mai saka sharri da alkhairi,mai saka mummuna da mai kyau,ke mutum ce mami,a yanzu nake kwadayin inama ace tun fari kece kika haifeni,na tabbatar da tuni yanzu ina rayuwa ingantacciya ba irin wadda nak
e kai ba yanzu''
''ya isa duka mun yafe miki,ko Allah muna masa laifi ya yafe mana ballanta na mu 'yan adam''
''na gode mami,ko yanzu na mutu nasan
''da ikon Allah zan samu wani sassaucin''
''ba na ce miki ki daina maganar mutuwa bane zahariyya''
''n
a daina mami''ta fada kana taja idanunta ta rufe ruf tana saukar da ajiyar zuciya
Maryam tasa abdallah ya dauka shi da security dinsa taje su tafi gida itakam qnan zata kwana kafin gobe ta sanar da dangin zahariyya din a samu wanda zai dinga kwana da
ita,ba maryam ba har abdallah da yasan mamin farin sani mamaki take bashi,wata iriyar kubutacciyar zuciya Allah ya hadata da iya,basu ce komai ba suka juya suka tafi
************
kiran sallar asuba ya sa mami miqewa ta ajjiye wayarta dake hannunta wa
dda ta bude application na qur'ani tana karantawa cikin zuciyarta,kwana batayi bacci ba kusan sabonta ne saboda kowa yasan ma'aikatan lafiya da iya kwanan zaune
fara daura alwalarta kenan ta fara jiyo salatin zahariyya tana yi tana shaquwa,jade da ambaton
sunan Allah,da sauri ta saki alwalar ta koma cikin dakin da gudu,shaquwa take sosai idanunta a qaqqafe suna kallon sama,da sauri,mamin ta fara bata duk wani taimako da ya kamata a matsayinta na likita,saidai duk yadda takai ga son ceton rayuwar zahariyyan
wanda ya halicceta ya riga da ya wanzar mata da qaddararta,ta amsa kiran ubangijinta ta riga mu gidan gaskiya,duk dauriya irin ta mamin saida ta saki kuka,babi shakka mutuwa ishara ce izina ce hakanan abar tsori da fargaba ce ga duk wani abu ma rai,ba bil
'adama kadai na hatta da sauran halittu dake numfashi a doron qasa
*************
Gidan kawunta qanin mahaifinta can suka sada gawar din su suka fi haqqi da ita,cikin qanqanin lokaci aka mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya,shikenan duniyar,zancan
banza ce,idan kayi damara don ita ka kwance,don katsaham zata zo maka tace sai ka bar cikinta bata da buqatarka don wa'adinka ya cika na zama acikinta,kusan azahar mamin taga giftawar wata mace goye da yaro,tayi tsammanin daya dagq cikin dangin mahaifinau
zahariyyan ne mutanen qauyensu yan gaisuwa,sai data sake ganin wulgawar matar ta saka ido sosai sai taga kamar zubaida,matar dake gefanta ta taba tana tambayarta
''waccan kamar zubaida ko
οΌ
''da sauri matar ta amsa mata din cike da murna take,yau gata tana
zaune daura da haj bintu
''eh,zubaidan hajiya nene ba, ita ce mana kema kin kasa shaidata ko ke da kuka zauna tare ma tun tana qaramarta,hmmm duniya ce ai budurwar wawa,wadda ta ishi kowa riga da wando,uwarsu ta gama bata su ta lalata su yanzu yau gashi
yadda suka koma,dan ahege ne fa goye a bayanta,yanzu haka aikatau take wani guri tana ciyar da kanta,don babu wanda zai dauki jigilarta bayan lokacin da suke da ahi bani wanda suka morawa komai''ko kadan bayanan matar bai burge mami ba,jasalima haushi ta b
ata,cikin takaici tace da ita
''harshe yana iya kai mutum wuta nan da nan cikin qanqanin lokaci,anna bi yace idan kaga dan uwanka cikin wata musiba ka shiga aibata shi da yadashi,Allah yana iya yaye masa kai kuma ya jarrabceka da abinda ka aibata shi akai
din,abinda aka umarcemu da cewa duk lokacin da muka ga wani da,Allah ya jarabta da wani abu ko cuta ce ko makamancinta shibe *ALHAMDULILLAHIL LAZI AAFAANI MIMMAB TALAKA BIHI,WAFADDALANI ALA KASIRIN MIMMAN KHALAQA TAFDILA*,daga haka mamin ta miqe ta bata g
uri
Bayan zubaidan tabi wadda ta gani riqe da robar abinci ta zagaya can baya ta kunce qarmashshan danta daga goyo ta zaunar da shi kan cinyarta ya soma bashi abincin cikin robar,don tausayi sai da qwalla ta zubo mata,ta qarasa kusa da ita tana kiran
sunanta,sai kuwa tq zabura ta miqe zata gudu
''kada kije ko,ina zubaida''sai ta kira sunan mamin hawaye,na bin kuncinta,inda take ta qarasa tasa hannu ta amshi dan ta jata gefe guda
Tiryan tiryan ta debe abinda ya faru da ita bayan barinta gida,ashe
gun mugu ta gudu wanda shine uban danta,ba dadeea ta ganshi ya sato,nene yazo ya hadasu,ashe abinda yasa ya nuna yana sonta,cikin jikinta yakeso ta haife ya dauke yaron ya saidawa qungiyar asiri,tun daga rqnar data fuskanci haka suka shiga tashin hankali i
ta da nene wadda ta dawo tamkar tababbiya,duk da haka wani lokacin idan abun ya lafa mata sai ka gantq ras kamar mai hankali,ruqon Allah suka dinga yi cikin ikomsa Allah ya kawo abokan gabarsu suka murqushesu shine su kuma sukayi amfani da wannan damar suk
a tsere,yanzu haka nene na gidan mahaukata ita kuma tana aikin wanke wanke fidan wani saida abinci da shi take dan taimakon kanta da nenen
kuka sosai mamin tayi kana ta amshi adress din gidan aikin nata tace zata nemeta,itakam ko wani abu ne ai zubaid
a bata masu komai ba face kanta data zalunta ta biyewa son zuciyarta
ππππππ
Zaune suke gabanta tana saman kujeravtana rubuce rubucenta,ta sake dagiwa karo na biyu ya dubesu
''uhmmm,idan kun shirya yimin bayanin ina jinku''abdallah ne da maryam
kusan awa guda an rasa mai bayani tsakaninsu,sai kallon kallon,gaba daya ta fahimci sun maidata kakarsu,akwai surukuta tsakaninta da maryam don haka ta dubi abdallah
''gayamin meke faruwa
οΌ
''mutsu mutsu ua shiga yi kana cikin inda inda yace
''mami,kince
ne dama idan mukaji da matsala mu miki magana wata uku da ya wuce,to maryam ce tace tana jin abu kamar dutse a mararta''sguru mamin tayi tana nazari,babu shakka zatonta ya fara zama gaskiya,ta dade tana yiwa maryam din kallon mai cikin,jin shiru babu wanda
yayi maganar daga ita har shi ua sanya itama ta tsuke bakinta ta bisu da addu'a
kai tsaye dakin data ware cikin gidan ta sata ta shiga,ba tare da bata lokaci ba ta fara taba cikinta,kasa gasgata kanta tayi sai data saka na'urar scanning,hoton dan tay
in jariri radam ya bayyana kan fuskar na'ura,tsura ido sukayi shida maryam din suna kallon talabijin din,tsantsar farinciki da murnar mami kasa boyuwa tayi har sai da murmushi ya qwace mata
''tabbas,gabunta da wautar dan fari bata barinsa,hakanan tabarar
auta ma bata taba barinsa,Allah ya ahiryeku maryam da abdallah,ciki wata hudu amma daga ke harshi babu wanda ya fahimci hakan,wadan nan kam da aqauye kuke cewa zanyi ba mamaki,yarinya ta kusan cinye buhun kwaki amma bai isheku ku gane komai ba
οΌ
''wani uban
tsalle abdallah ya daka sai gashi gaban mamin saura kadan ya kada ita qarfin ba daya ba,ta dafe gadon da maryam ke kai tana fadin
''abdallah yi a hankaki mana''
''mami zan zama daddy fa kika ce,wayyo Allah na kana sina Allah''ya fada yana daga hannayensh
i sama
''janye mijinki maryam kada ya targada min kafada tun kafin jikan yazo na rasa hannun daukarsa''mamin ta fada cikin tsokana,kunya ta kama maryam don ta sadda kanta qasa,tabbas cikin abinda yasa ta kasa gane cikin ko mutanen da take tare da su baya
ga na fari ne tsahonta ya shanye cikin sai ya qara mata qiba kadan ta murje fatarta tayi kyau,har wani lokacin abdallah idan yana son tsokanarta zakaji yana ce mata
''diyana 'yar lukuta ta bawan Allah''sosai mamin ta zauna tana musu bayanin yadda zasu kul
a da cikin don ta fuskanci daga abdallan har maryam din jirgi daya ne ya kwasosu
_kuyi maneji da wannan_
*mrs muhammad ce*
π
πππ
β
π½
β
π½
β
π½
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ
*ABADAN*
πΊ
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
ππΊππΊ
ππΊπ
πΊπ
π
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊπ
πΊππΊπ
πΊππΊ
ππΊ
π
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
π‘
*_home of expert and perfect writers_*
πππππππ
βΆ
6
β£
9
β£
*Daga mu'az dan anas R.A yace:Manzan Allah S A W yace:((duk wanda yaci abinci sannan yace:ALHAMDU LILLAHIL LAZI AD'AMANI HAAZA WARAZAQA NIHI MIN GAIRI HAULIN MINNI WALA QUWWAH,an gafarta masa abinda ya gabata na daga zunubinsa*
*Manzan Allah
S A W yace:((babu abinda yake maida qaddara sai addu'a*
*LITTAFIN NAN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA DUK WATA BUDURWA DA AURE YA MATA JINKIRI ,DA KUMA DUKKAN WANI MUTUM DAYA TSINCI KANSA KO YA TABA TSINTAR KAN NASA A HALIN SIHIRI,MU SANI CEWA SHI HAQUR
I WANI ABUNE DA FARKONSA MADA CINE AMMA QARAHENSA ZUMA NE,BABU WANDA YA TABA YIN HAQURI INGANTACCEN HAQURI DAGA QARSHE YA TASHI BABU RIBA,BABU SHI,SAIDAI BA HAQIQANIN HAQURIN KAYI BA*
_BAYAN SHEKARA GOMA SHA HUDU_
Abdallah ne a gaba r
iqe da hannun matashin yaron dan kimanin shekara goma sha hudu suna magana qasa qasa,shi da yaron dukkansu sanye suke da doguwar riga yar asalin saudiyya,kansu lullube da hirahi da kewayayyen abun nam mai siffar zero,a bayansu kuma mami ce riqe da hannun w
asu kyawawan 'yammata guda biyu wadanda ba zasu wuce shekara biyar biyar ba,kallo daya zaka yiwa yaran ka bawa kanka amsa da cewa 'yan biyu ne suna tafe suna tsalle tsalle irin na yara,maryam na a gefansu riqe da wani yaron wanda shima irin shigarsu abdall
ah ce ajikinsa,dukkanau su kuma baqar doguwar riga ce ajikinsu kansu lullube da wadataccen mayafinta
Kana kallonsu ko ba'a fada maka ba kasan cike suke da farinciki,haka yake domin shekaran jiya aka fidda sakamakon gasar karatun qur'ani da akayi ta qa
sa baki daya wadda aka gabatar a qasar saudiyya,ABDUL_AHAD ABDALLAH ABDULKAREEM da ga MARYAM da ABDALLAH shi ya samu zuwa ta daya,abun ya girgiza qasashe da,dama ya kuma bada mamaki,yaro mai qarancin shekaru kamar wanan ya samu irin wanan baiwar ta haddace
qur'ani kana ya zubar da duk sauran abokan takararsa da suka fishi shekaru ya daga tutar ta daya
Wannan abu ba qaramin daukaka ya sake ja musu ba,kai ba abdul_ahad kadai ba,hatta da maryam ta samu qarin soyayya da qauna daga bangaren mami harma da ab
dallahnta,kyaututtuka kuwa babu kalar wadda abdul_ahad bai samu ba,ko a yanzun ma sun fito ne somin amsa gayyatar da sarkin saudiyya ya musu don cin abincin dare tare da su
**********
Basu suka dawo,ba sai misalin qarfe goma na dare agogon saudiyya,a
gajiye suka isa masaukinsu abdallah na sabe da yan biyu da sukayi bacci,abdul_ahad wanda shine babba kuma na riqe da hannun ABDUS SAMAD wanda keta faman gyangyadi,sai da suka isa qofan dakin mami abdul ahad suka ahige shida abdus samad kasancewar dukkansu
tare da kakar tasu suke kwana,maryam ta bi bayanau abdallah shima ya bita,kan gado ya sauke yan biyun a hankali,husaina ce ta fara farkawa wadda suke kira da AMATULLAH,tuni ta riqe abdallah da suke kira da ABBU,sarai ya gane me take nufi,so take tace a gu
nsu zata kwana kamar jiya bayan yau ya riga da yaci burin cin amarci da mamansu
''ya akayi rigimammiya''ya tambaya
''abbu ni a gunka fa zan kwana''
''a'ah ki kwanta anan,baki gani AMATUL JABBAR anan zata kwana
οΌ
''maqale kafada tayi
''nidai a gunka zan k
wana abbu don Allah''duk yadda yaso lallabata ta qiya,maryam na jinau tana sauyawa abdus samad kaya zuwa na barci,dariyarta take a ciki don yasan amatullah ta gama karya masa budget a yau kam,tana lura tun rana da irin kallon da yake jifanta,har tex ya mat
a ya kama musu hotel tazo suje sharp sharp yanzun zasu dawo amma ta qiya,don duka wunin ranar suna tare da yaran har ma da mamin,anata ude gifts da abdul ahad ya samu
''ummi ki yiwa diyarki magana,tafa matsanta min''ya fada qasa qasa yadda abdul_ahad
dake sanya socks a qafarshi yana shirin nacci da mami dake cikin toilet tana dauro alwala duka ba zasu jishi ba
baki ta tabe cikin tsokana tace
''meye nawa
οΌ
,itaku,ina cewa dazu ka siya mata ice cream ka hanamu kace mamarka ce
οΌ
''
kai ya dan sosa don kada
ta gansu a rana su masu dariya ya sunkuya yana daukarta bisa kafadarsa yace
''haka ne fa,mama na tafi ta kowa ai''ya juya ya fita maryam na qyalqyala musu dariya,ganin yaaran na kallonta saboda dariya da suka ha tanayi da basu san dalilinta ba yasa ta da
idaita natsuwarta,ta kammala shirya abdus samad ya haura gadon da abdul ahad ke kai,ta dubi abdul ahad
''idan ka kammala addu'anka ka karanta masa shima kafin ya sake komawa baccin''
''to ummi''
gadon mami ta koma ta sake gyara mata gami da shimfida
mata abun sallah don ta riga ta saba bata kwanciya sai tayi sallah raka'a biyu,har ta koyawa maryam din ma,saida mamin ta fito sannan ta shiga itama ta daura alwalar
tana bisa abun sallan mami na zaune gefan gadon tana laranta azkar da bata samu dama
r yi ba,wayarta na hannun abdul ahad yana danne danne,bata fiye damuwa don ya dauki wayarta ba don ta san hakin yaron indai kaga wayar a hannunshi wani abu mai mihimmanci da zai qareshi yake dubawa,Allah ya zubawa yaron tsantsar basira,hankali da nutsuwa,u
wa uba ya samu ingantacciyar tarbiyya ta buga misali,ba qaramar tsaiwa maryam tayi kan tarbiyyan 'ya'yanta ba musamman abdul_ahad wanda dama danka na faro kusan shine tubalin sauran 'yan uwansa,irin tarbiyyar daka nashi to sauran ma idan ka haifesu zasu ta
ahi ne kan aninda suka ga na gaba da su nayi wato babban yayansu,saboda ko yaushe suna tare,suna ganin irin abubuwan da yakeyi suma zasuyi qoqarin yin koyi da shi,hakann idan gurbatacciyar tarbiyya ya samu,da sun fara girma zasu bi sahunsa
Ta shafa
addu'o'inta kana ta miqe ta ninke abun sallar,mami ta dubeta
''ya kamata kam ki tafi haka ki kwanta maryamu,kullum ace sai kin tayamu hira zaki tafi daki ko kwanta,banda abunki ai bani,kadai ce a dakin ba balle kice kewa zata dameni,ga mai gida na ma baiy
i bacci ba''
murmushi maryam din tayi cikin kunyarta din nan da har yau bata canza ba,har yau babu wani abu da ya ragu daga qaunar da mami ke mata sai ninkuwa ma da yayi
''kije ki,kwanta maryam kinji,Allah yayi miki albarka,haqiqa har *ABADAN* bazan dain
a alfahari da ke ba,kin cika uwa ta gari mai fidda kyakkyawar yabanya,fata na ubangiji ya cika rayuwarku da haske farinciki da kwanciyar hankali,kin haifa min jikoki maryam hudu ne amma inaji sunfi miliyan,sabida samun yara kamarsu wallahi ba don suna jiko
kina ba sai an tona,Allah ya miki albarka,Allah ya miki albarka''kanta na aqasa take amsawa da amin zuciyarta cike da farinciki da qaunar mami
Wayar tata dake hannun abdul ahad ta dauki tsuwwa wanda tun tana cikin yin sallah ta ji tanayi,abdul ahad ya
dubi umminsa
''ummi,abba ke kira tun dazun''yana saukowa daga gadon ya miqa mata wayar,ta riga da ta horesu,sam basa daga mata kira sai sun kawo mata ko sun sanar mata,ta daga kana ta kanga wayar a kunnenta
''please dear ki taho haka don Allah,i nedd yo
u''murmushi ya subuce mata,kunyar mami tasa ta kana magana sai kawai ta katse kiran,minti biyu tsakani saiga tex dinshi
''gaskiya fa ina alkunya da yawa,na baki minti biyar matuqar baki taho ba da kaina zanzo har,gaban mami na sungumeki,kin sani zan iya k
o
οΌ
''murmushi ta sake saki taci gaba da duba agogo
sai da ta minti biyar din sun cika daidai sanan ta miqe ta yiwa mami sallam,a bakin qofar dakinsu mamin taci karo da shi dauke da amatullah,dariya ta subuce mata
''gaskiya kun samu aikinyi,ta yadda ke
nan zata kwana cikin 'yan uwanta''
''me ruwanki da mu
οΌ
,kedai ki kuka da kanki,yau sai kin biya dukka bashin da kika ci''kai ta girgiza tana murmushi ta wucesu shi kuma ya shiga dakin
Bandaki ta fada kai tsaye bata zauna ba,sai data yi wanka mai kyau
kana tazo ta mulke jikinta da turaruka masu dadi wadanda ta siyosu dazu da rana da suka fita yawin miqe qafa,dukkansu na kamfanin alharamain ne masu dadi qamshi,daya daga cikin kayan baccin data siyo ta cira,doguwar riga ce har qasa mai hannun shimi mai az
abar yauqi da santsi tana da dan duhun kala kadan ta sanyata,ta feshe kanta da turaren gashi kana ta rage hasken fitilar dakin ta haura gadon ta kwanta,jin shiru bai dawo,ba ya tabbatar mata yana can ana tataburza wata qila da amatullah,kiran da ya ahigo w
ayarta ne ya katse mata zancan zucin da take yi,lubabatu ce da hanzarinta ta daga don tana sa ran jin daddadan labari saboda sun baro nijeria hindatun nada tsohon cikin haihuwarta