Showing 153001 words to 156000 words out of 176330 words
gami da dage gira.
Sai kawai taga ya
dangwalo ya tsotsa
''hmmmm,gaskiya da dadi''ya fada yana kaiwa bakinsa,kafin ta qwace har ya kurba,ta karbe kana ta zubar
''na gaya maka mazq baku sha,idan poising ne kuma fa
?
''
sai taga ya saki murmushi mai fidda sauti kana ya harde hannunsa a qirji
'
'sai abun ya zama abun alfahari a gareni,masoyiya ta bawa masoyinta guba sabida tsabar qauna,kuma zaqinta zanji dear na,ballantana ma na sani ke din ba zaki iya ba,saboda wasu ma da suka yi yunqurin bani naci kin kawar da hakan,ko kin manta har asibiti kik
a je aka tabbatar miki da irin nau'inta da kuma qarfinta
?
''
ido ta zaro,wai abdallah aljanine ko kuwa yana da su ne
?
murmushi ya kuma yi,ta bude bakinta da niyyar yin magana,sai yayi azamar qarasowa gabanta,yasanya tafin hannunshi ya rufe labbanta yana k
allon qwayar idonta tare da cewa
''yi shiru da bakinki,ki adana duk wasu tqmbayoyi da kike da,su,wannan hiran na daya dagq cikin hirarrakin da na tsara mana,cikin gidan mu na qauna,a kan gadon soyayya,a kuma qirjin masoyi''ya qaraahe maganar yana kashe ma
ta ido.
kunya ta kamata sai ta zame bakinta tana murmushi ya sake matsowa kusa da ita yana yin qasa da murya saitin kunnenta
''ina fata kin tanadarmin salo salo na soyayya da,qauna wadda zaki shayar da ni,kinsan abdallah dan soyayya ne,yana son soyay
ya musamman ga matarsa''ya fada yana qoqarin janta jikinsa,gabanta ya shiga faduwa,ta faki idonsa ta zille tayi hanyar fita,baiyi yinqurin binta ba don ya tabbatqr da mutane a wajen amma sai ya matso uadda zata iya jinsa ya biyo bayanta
''ki gama zulle zu
llenki yarinya,awa,nawa,ne ya rage
?
''hakan da ya fada sai ua sata tsayawa ta juyo ta dubeshi idonta har ya cika da qwalla,dariya ya sa mata tayi hanzarin ficewa daga gun.
Zuwa la'asar gaba daya hajja laila ta gama da kyawunta,tamkar buga qunshin aka
yi aka dayeshi,banu kuskure ko daya aciki,ja ne amma har saman hannu da saman qafa,abinka da fara ya fito kuwa yayi marun,kyau kam basai an fadeshi ba ya gama yi,tuni yan kawo mero sun tafi don yaci ace ma zuwa la'asar din sun kai gida,saukowarta kenan dag
a saman mami dauke da wata leda wadda wani arnen codenet ne a ciki da aka fidda wa dinki na garari,kudadr mamin ta saka masu yawa ta siyawa maryam din sabida wannan rana,sallama akayi aka shigo falon qasan,raliya ce janye da hannun fadil(yaronta)sai hindat
u da lubabatu da kulu,baaba huwaila da hajiya atika.
Cikin dakinta suka shiga ita da raaliya hindatu lubabatu da kulu,baaba hadiza da hajiya atika kuwa suna sama gun mami,mami ce tasa duka suka zo don yi mata rakiya,hira suka dinga yi wanda zuwansun y
a rage mata fargaba sosai,lubabatu da kulu nata kallen kallen gidan mami don yau ne zuwansu na farko,sun tabbatar cewa Allah ya yiwa adda maryam din baiwa ba qarama ba.
Raaliya ce ta shiryata tsaf cikin codenet din orange da yellow,kana ta dora mata a
lkyabba da mamin ta hadota cikin kayan,yellow ce mai ratsin fari,fadar irin kyawun da tayi ma bata baki ne,su kansu tsayawa sukayi kallonta,kai tsaye gin mami suka fara zuwa kana suka fice suka barta ita da ita,kallonta mamin take cike da farinciki,burinta
kam ya gama cika a yau,hannu ta miqawa maryam din ba musu ta bata,gefeanta ta zaunar da ita kana tace
''maryam,da farko abinda zan fara cewa dake shine kiyi haquri,don babu wani abu da ya wuce haquri da mace zata riqe wanda zai,zame mata jagora kuma mado
garar gidan aure,haquri maryam shine komai a rayuwa,kiyi haquri a duk yanayin da zaki tsinci kanki a gidan aurenki,duk wata mace da kika
gani zaune gidan aurenta wallahi ba za'a rasa wata matsala da take fuskanta ba komai qanqantarta,ta wata ne tafi ta wat
a,qila wadda kikewa hangen ta haye ta huta da zata buda miki cikinta wallahi saikin tayata kokawa,komai dadinki da mimi wataran sai kun samu sabani,donko tsakanin harahe da haqori ma ana sabawa,na biyu riqe sirri ki riqe sirrinki ke da maigidanki maryam,ko
ni idan bai zama dole ba bana buqatar jin sirrinku ke da abadallah,ku riqe amanar juna,ku riqe sirrin juna,ku zauna da juna cikin amana''nasiha ta dinga mata irinta tsakanin da da uwa,kuka sosai ta dinga yi har sai da mamin tace
''a'ah,ai kuma zaki batawa
abdallahn kwalliyar me akayi kenan kuma uhm.....maza share hawayenki,duk da haka kowacce mace ta saba yau hashi kowa na zaune agidanta''.
Da kanta ta kama hannun maryamun har harabar gidan ta sanyata cikin sabuwar range robber baqa wul wadda kyauta c
e mamin ta yi mata,tukuici ne ta bata,kadan daga cikin irin abubuwan da take ji zata iya yiwa maryamu,yadda ta kama hannun mamin itama sai ta karya mata zuciya har sai da ta share qwalla,motocine kusan shida don akwai yayar mami da qanwarta,sai yayar marig
ayi alhj abdulkareem mai nasara da qanwarsa,tana nan tsaye mamin har motar ta daga suka fice daga gidan kana ta juya ta koma ciki,tun daga lokacin ta soma jin kewar maryamun,bangare daya ga abdallah dake shirin tafiya shima,babu shakka kewarsu zatayi ba ka
dan ba,don ma ga mero nan,amma kafin su saba su maye mata gurbin maryamunta ai ba nan kusa bane
Sai da suka fara zuwa gidansu suka kaita gun mama da malam mamuda mahaifinta kafin su wuce da ita gidanta.
Wani irin yadine ajikinsa orange colour m
ai bala'in kyau da taushi,dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,fuskar nan tashi tayi wani irin kyau na musamman,hisham ke riqe da wata iriyar jaka da aka qawata ta da rubutu mai kyau suna tafe yana masa tsiya har suja qarasa gun mami,tana falon nata tana
sallah ya tura qofar suka shiga,kujera suka samu suka zauna suka jirayeta har ta idar,sai data shafa addu'a kana ta tashi ta dawo kan daya daga cikin kujerun itama ta zauna,hisham ne ya fara magana
''mami gashi na kawo miki shi,ayi masa nasihar zaman aure
''mirmushi mamin tayi tace''ka kyauta kuwa,shi yasa nake sonka hisham badai hankali ba''
harararsa abdallah yayi''jimin dan rqimin wayo,kana nufin zan iya tafiya banzo ga mami na ba
?
''
dariya ya masa don ya fuskamci yanayin fuskarshi har ya canza ya kuma
san ba wani abu ne ya tabashi ba sai barin mamin da zaiyi.
''abdullahi''ta kira sunanshi da salon da bata taba ba,take ya dago idonsa ya kalleta,sai ya kasa civgaba da kallon nata ya duqar da kanshi,son ya hango magana zata masa bata wasa ba
''shi a
ure da kake gani girma ne da shi,daraja da shi qima gareshi,sunna ce guda ta wanda akayi duniua da lahita dominsa wato annabi muhammad S A W duk wanda ya wulaqantashi baya tare da annabi na tabbatar kuma bazaka so haka ba,a duk sanda ka dauki yarinya,aka r
qbata da uwa da ubanta da
inda ta taso tavgirma,aka rabata da danginta aka rabata da duk wani wanda ta saba da shi aka baka to ka tabbatar da xewa amana ce aka baka mai girma,kasan sarai hikuncin wanda ya tozaratar da amana ko yaci amana ko
?
,ka tuna ko yau
ahe cewa matarka ba siyanta kayi ba,ba baiwarka bace 'yace 'yantacci ya mai yanci,kada ka dinga mu'amala da ita irin mu'amalar bawa da ubangidansa,a'ah,ka mu'amalance ta wani lokaci kamar 'yarka,ka tsawatar mata ka bata shawaea ka tausasa mata kaja girmank
a,ka mu'amalanceta wani lokaci kmar mahaifiyarka,ka tausasa mata,ka kyautata mata,ka girmamata,ka mu'amalanceta wani lokaci kamar qanwarak,ka qaunaceta ka kauda duk wani abu da zai cutar da ita ko ya,bata nasabarta,ka dorata kan hanya madaidaiciya,ka mu'am
alanceta kamar qawarka,ka gaya mata damuwarka,kayi shawara da ita,kuyi wasa kuyi dariya,matarka duka tana da wannan mtsayin a gareka''.
Ta dora da cewa''na tabbata har yau kana iya tuna mu'amalata tsakanina da mahaifinka wanan kawai ya isheka madubi,y
a iaheka littafin da zaka dinga karantawa ko yaushe koda ban ce maka komai ba game da zamantakewa da iyali,abdallah ka guji zalunci,Allah da kansa ya fada cewa ya haramta zalunci abinsa kansa,kuma ya haramtashi a tsakaninmu,ka kyautatawa matarka,ka sauke d
uk wani nauyi da Allah ya dora maka,yadda kake da haqqi a kanta haka itama take da haqqi a kanka,ban yarda ka take mata haqqinta ba abdallah,iya wannan nasan ya,isheka nasanka nasan tarbiyyar da na maka,don Allah abdallah kada ka watsamin qasa a ido,kayi z
ama zama na haqiqa da matarka,Allah zai tsadaku ranar gibe kan yadda kuka sauke haqqin jilunanku,wallahi wannan gaskiya ne babu ko tantama aciki''
idanunshi tuni sun hama hada ja,zuciyatsji zafi take masa,karo na farko da zai rana gidan kwana shi da mamin
sa,a hankaki ya miqe daga mazauninsa ya isa gabanta ya durqusa kangwiwoyinshi,kana ya cire hular kansa
''mami kisa kin albarka,kici gaba da yi mana addu'a,insha Allahu zanci gaba da zama abun alfahari a gurinki''
hannunta ta dira saman kanshi kana tace
'' *BARAKALLHU LAKA,WA BARIK ALAIKA,WAJAMA'A BAINAKUMA FILKHAIR*'',ta amshi ukar da kanta ta maida masa ita saman kansa,sai ya kasa jurewa ya dora kansa saman cinyar mamin yana ajiyar zuciya,tausayinsu ya kama jisham,babu shakka ba qaramar qauna nace tsaka
nin wannan da da uwar ba,sai ya,kasa zama shima ya tashi a hankali ya fice,uwa ba wasa ba.
Mamin bata masa magana ba don ta saba da irin hakan,majority tun yana yaro idan zuciyarsa na quna haka yake ya dira kansa saman cinyarta har sai ya huce,don bas
hi da qawa a lokacin ko aboki da ya wuce maminsa(yana da kyau iyaye ku zama kune abokai ko qawa na farko wanda suka matuqar shaquwa da 'ya'yansu kafin kowa,ta hakane zaki samu damar yiwa diyanki kalar tarbiyyar da kikeso mai kyau ba tqre da wasu sin samu d
amar ruguje miki ba,bawa yara damar shaquwa da aboki fiyr da iyaye da rashin jansu a jiki babbar illace,da abokin nan ko qawarnan zwta dinga shawara,ita zata dinga gayawa damuwarsa bake ba,kinga kenan zai iya dorashi kan irin tasa tarbiyyar,amma idan akwai
shaquwa tsakaninku kece mutum ta farko da zai fara dinga gayawa matsalolinsa da damuwarsa kafin kowa,saidai idan kuma yayi aure Allah ya bashi mace ta gari sai ki koya masa neman shawara daga matarsa,saidai idan duka su biyun tunaninsu baikai nan ba ko ma
s'alar tafi qarfinsu,a kuka don Allah iyaye,tarbiyya abace mai tsada da
wuya,amma a qarshenta kuma ke uwa ke zaki fi kowa mora da jin dadinta koda baki duniya kuwa).
Ita ta riqo hannunshi suka sauko qasa,ya zama kamar ba abdallah ba,qwarin rai da qarf
in zuciyar nan duka babu,har dariya ta dinga masa kan cewa ya girma fa,ya kamata ya koma abdallahn sa,nan da ten months yana iya zama daddy,abinda ya sashi dariya ya kuma bashi kunya kenan,bakin freezeer suka isa ta bude ta ciro wata qatuwar leda ta sake j
ansa har suka fito harabar gidan inda motocin security dinsa guda uku data abokansa guda uku ke jiransa,cikin motar da za'a kaishi ta bude masa da kanta ta sanyashi kana ta miqa masa ledar''Allah ya tsare hanya,a sauka lafiya''ta fada kana ta rufe musu qof
ar ta koma ciki,a varanda ta tsaya har sai da taga ficewar motocin duka.
Mus'ab abokinsu ke tuqa motar,usman na gefansa baya kuma hisham ne da abdallahn,cikin salonvtsokana hisham din yace
''idan bakason rabiwa da mamin kawai mu maidaka gida sai a yi
wa maryam waya ta haqura kawai''harar ya galla masa bayn ya sauke ajiyar zuciya
''mami da maryam duka rayuwata ne hisham,ka sani,ba sai na maka dogon bayani ba''tsokanarsa suka ci gaba da yi tare da yi masa shaqiyanci kala kala irin na abokan ango har suk
a iso unguwar.
*mrs muhamma ce*
👑
📚📚📚
✍
🏽
✍
🏽
✍
🏽
✍
🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺
*ABADAN*
🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶
6
⃣
4
⃣
*An karbo daga Abdullahi dan salaamin Allah ya yarda da shi yace:naji manzan Allah S A W yana cewa:(
(ya ku mutane,ku yada sallama,ku ciyar da abinci,ku sada zumunci,kuyi salla cikin dare lokacin da mutane suke bacci zaku shiga aljanna cikin aminci))*
_imamut turmuzi yace hadisi ne ingantacce_
*gaisuwa ta musamman gareku tare da dimbin godiya da
jinjina*
*mom hanee*
*fatimah zahra haske asso*
*zainab idris makawa(takari)*
*maman farida(samun wuri)*
*maman rufaida (manal)*
*hafsat mai sharif(rayuwar aure na)*
*Billy galadanchi(hanjin jimina)*
*khairat*
*mrs ibrahim*
*maman aysha(gadar
zare)*
*ummu zainab*
*rabi'ah haroun*
*maryam gital(ba halul kitabi bace)*
*KAI
!
KAI
!!
, INA KUKE MASOYAN ABDAN,TO KU MATSO NA GAYA MUKU
👂🏾
*
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*wannan page dinfa naku ne,duk inda kuke na sadaukar muku da shi kyauta,wa
nda na sani da wanda ban sansu ba,na kusa da na nesa*
🏆🏆🏆
*NAGA SAQONKI AISHA GARKUWA
😂😂😂
,NI DAKE AI DUKA DAYA NE MUSULMI DAN UWAN MUSULMI NE
😜😂
,KICI GABA DA KARBAR SU AI DAMA NANA AISHA AI UWAR KOWA CE,UWAR MUMINAI R.A,NA GODE DA KIKA MIN KARAR
KARBAR FANS DINA DA MUTUNTAWA KIKA BASU FURA DA NONO,ALLAH YAYI MANA JAGORA*
😂😂🙏🏽🙏🏽
😍😍😍😍😍
Gida ne gini na alfarma,gini irin na gata,gini ne mai cike da tsari kyau da fasaha a cikinsa,kana shiga gifan kawai zaka tabbatarwa kanka c
ewa gida ne da ni'ima da kwanciyar hankali tayi kaka gida acikinsa,sanyi da iskarsa ma daban take albarkacin tsirrai daya wadatu da su,duk inda zai kasance ansa tiles cikin harabar gidan baki daya an maye gurbinsa ne da grass carfet mai ban sha'awa,duk cik
in abokan nasa babu wanda ya iya
tsuke bakinsa ba tare da ya yaba ba,a haka suka ajjiye motocinsu suka dunguma zuwa,cikin gidan
parlour na farko anan suka ci burki,ya dubesu baki daya babu ko kunya yace da su
''daga parlour na farko fa banjin zan iya
barin wani ya shiga parlour na biyu bare na uku,saboda haka anan zamuyi sallama da ku''
mus'ab yace
''dan iska,zakayi abinda yafi haka ma,kamar a kanka aka saukar da wahayin kishi,mun gama maka amfani ai tunda mun rakoka''
dage gira hade da kafadusahi
yayi
''eh da gaskiyata fa,haka kawai na kwasheku har bedroom din matata,ina da kishi gaskiya''
''muma bamu ce zamu shiga ba malam,tunda munyi na Allah ai shikenan''inji usman yana ajjiye ledar hannunshi,yana dariya qasa qaa ya dafa kafadarsa''yauwa mutum
ina,dadi na da kai sauqin kai''
Tsokana dai irin ta abokan ango haka sula yo masa yana ramawa,barkwanci sosai suka dinga yo kama suka juya suka fito ya rakasu,har sunyo gaba hisham ya dawo
''yauwa,inason ganinka fa''
''zaka batan lokaci kenan,na bar
gimbiya fa batasan na shgo ba ma fa''murmushi hisham din yyi mai hade da dariya
''me kake ci na baka na zuba,kunnenka na tsaya na ja don naga yadda kamka ke rawar nan,wlh kayi a hankali kada ka cutar musu da diya,na sanka sarao idan kana som abu baka dau
kar lamarinsa da wasa''
kunnen abdallah ya turo masa yana fadim
''to daddy,ga kunnen,fadi da kyau,ko daki zan baka ne ma kusa da namu kayi sa idon da kyau''tare suka sheqe da dariya kana suka tafa
''Allah ai kaine da iua shege,kai wa yasan me zakayi ran
ar da aziza ta zama taka''har wani sosa kai hisham yayi kana yace
''wlh fa,na barku lafiya to''ya fada ya juya yabi sahun yan uwansa dake zaune cikin mota suna kiransa aballah ya bishi da kallo,yana son hisham mutum ne mai amana wanda samun kamarsa sai an
tona,ba duka mutum bane a wannan zamanin zakamasa alkhairi ya saka maka da alkhairi,mafi yawancinsu da sharri suke saka maka sai yan kadan
Sai da ya tabbatar sun fice sannan ya isa ya rufe gate din gidan don bai kawo mai gadi ba tukun,bai koma ciki
ba sai da ya tabbatar ya rufe ko ina
A hankali yake takawa yana nufar cikin gidan,iskar damina na kadashi,wani irin ni'ima ce yau lullube da sararin subhana,iska ake mai dadi da shiga jiki,gefe guda wani tawagar farinciki ne ke shawagi cikin zuciyars
a,jinsa yake cikin wata duniya ta musamman,yau gashi ga maryamunsa,cikar muradinsa cikar burinsa,sashensa ya bude ya ciro kayan bacci farare tas da towel dan qarami kana ya rufe ya dawo sashenta ta cikin parlour din gidan na biyu,a hankali ya,keta har falo
na uku wanda daga shi sai wani dogon corridor wanda kana shiga zaka tadda dakunan bacci uku,sai matattakalar bene wadda saman shima ke dauke da dakunan bacci parlour
toilets da kitchen,a hankali ya,haura saman kansa tsaye ya tura qofar daya daga cikin dak
unan da ya gani a bude wanda hakan ya tabbatar masa a ciki maryam din take
''assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatu''ya shiga da sallama wanda hakan ba qaramin rage mata fargaba yayi ba,gefan kujerar dakin take zaune,kanta na duqe lullube da alkhy
abbar jikinta,tsayawa yayi cak kana ya kingina da bangon dakin yana qare mata kallo duk da bai ganin fuskarta,ya kashe a qalla mintina biyar a haka zuciyarta na bugawa a hankali kanta na a qasa,ta tabbatar har yanzu yana cikin dakin saboda qamshin turarans
a da ya cakude da nata ya lullube dakin,haka nan ya sake haifarwa da dakin wani irin ni'imtaccen yanayi,sannu a hankali ya dinga takowa gareta bayan ya ajjiye kayan hannunshi duka saman dan qaramin table na glass dake a gaban gadon,ya isa gabanta ya zube d
uka kan gwiwoyinshi,hannayenta ya kama ya sanya cikin nasa yana qarewa qunshinta kallo,tamkar yasa harshensa ya lashe haka yaji,sai da ya more kallonsa sannan ya dora kansa saman cinyanta yana leqen fuskarta,bai ga fuskar sosai ba sakamakon hular alkyabbar
ta sanya ta yin duhu,a hankali ya sanya hannunshi ya janye hular take fuskarta ta bayyana