Showing 129001 words to 132000 words out of 176330 words

Chapter 44 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

12

ya zaci maryam na bacci ne,dan tsayawa tayi tana kallonsu,take jikinta ya bata mahaifiyar abdullah ce saboda diban kama kadan da sukeyi

Dukkansu suna zaune kan tabarmar suna jimanta al'amarin,har yanzu maryam ta kasa ma

tsawa daga kusa da mamin ganin take kamar har yanzu mafarki take,don ranaku daidai ne bata mafarki da mamin cikin baccinta

kasa daurewa mamin tayi tace

''banga Abdallah ba,ina yayi ne



''

''ya fita tattaki shi da hashimu nan bayan gari bakin rafi,kinsan

an kwana biyu ba'a taka qafar ba''

cikin mamaki mamin tace

''hisham dai,dama hisham na tare da ku



''kai maryam kawai ta iya gyadawa

''Allah mai iko,shi yasa na rabu da ganinshi,babu irin cigiyar da ban ma hisham din ba ashe kuna tare''

kasa zama ma

ryam din ma tayi ta shiga dauki ta dauki hijabinta ta sulale ta fice

tun daga nesa ta hango su zaune su biyu shida hisham da alamu magana suke mai muhimmanci sosai,a hankali ta dinga takawa tana qarasawa inda suke dukka idanunta na kan kyakkyawar fuskar a

bdalla

''taqi ta gane hisham taqi ta fuskanta,basan ta yadda zan fasalta mata ba,bansan hanyar da zanbi ba hisham,am doing my best hisham,ka gaya min ya zanyi



''

abinda taji yana fada kenan ba tare da ta fuskanci kan me yake maganar ba,sai ta qara

sauri ta isa garesu data tuna maqaaudin zuwanta gurin,ji yayi kawai an kama hanninshi kana ta fara jansa,a mamakance ya dago yana kallonta,kasa tambayarta ma yayi sai ido da ya zuba mata,ganin yadda ta dage tana janshi ya sanya shi sauqaqa mata wahalar ta

hanyar tashi ya bita tamkar raqumi da akala

bata bar jan hannunshi ba har sai da suka isa ga tsakar gidan inna wuro kana ta kauce daga gabanshi,tashin farko idanunsa suka sauka kan maminshi,runtse idonsa yayi ya sake budewa don ya tabbatar shin da g

aske ne ko kuwa mafarki shina yake yi kamar yadda ya saba

''mami ce''hisham dake tsaye gefansa ya fada,ita din ma ajikinta ta ji zuwan nasa a hankali ta waiwayo suka hada ido da tilon dan nata,wani irin rauni abdallah yaji ya shigeshi,kewa qauna da soyayy

a irin ra da ya iyayensa ta taso masa,take jikinsa ya kama rawa yaji qafafunsa ba zasu iya daukarsa ba,yau maminsa ce a gabansa



durqushewa yayi a gun a kan gwiwoyinsa kansa na duqe a qasa,hawaye ne ya balle masa tamkar mace,jikin mamin a mace ta miqe

ta isa gabansa ta kira sunanshi

''abdallah,abdallah na ka yafewa maminka'' da sauri ya miqe ya kama hannayenra hawaye na sauka kan fuskar kowannensu,rawa bakinsa yake yama kasa magana,duk abinda yayi niyyar furtawa sai ya kasa,qaunar mahaifiyar yasa ke s

ake tosa masa,shaquwa da soyayya dake tsakaninsu ba qarami bane,yana jin bashi da kowa idan ba mamin ba,a lokacin data guje musu ji yayi kamar ya mutu,tawakkaki da imani da Allah ne yasa ya iya danne zuciyarsa yasa mata yadda da qaddara kafin daga bisani t

a gano cewa koma meye ta aikata musu ba bisa hankalinta bane

Qarshe fadawa yayi jikinta yana jin nauyin da zuciyarsa na dada raguwa,wani sauqi ma samuwa cikin zuciyarsa daga abinda ya cunkushe mafa a da

hagu da dama suke zaune sun sanya mamin a t

sakiya,ko qwaqwaqwaran motsi sunqi yi,ta dubesu cike da tausaya da qauna

''abdallah ku tafi ku kwanta hakanan,Allah ya kaimu gobe ko



''murmushi duka sukayi abdallah ya girgiza kansa

''yau mami komai iya satar baccin banjin zai iya saceni,ko na kwanta di

n bazan iya baccin ba,itama haka don babu ranar da bazata yi maganarki ba koda cikin zuciyarta ne,saidai idan ke kinajin sai mu qyaleki ki kwanta ko''

girgizq kantq take cikin zuciyarta tana sake jinjina qaunar dake tsakaninsu,tsanar nene ta qara ci

ka zuciyarta,tana jin mawuyacine ta iya yafe mata haqqinsu data dauka,raba qaunar data yi dake tsakaninsu na tsawon lokaci ba tare da sunji ko sun gani ba,haqiqa Allah ne ke saka soyayyar dan adam cikin zuciya

A taqaice kwanan zaune sukayi su duka uku

n don sai bayan sallar asuba kowanannsu ya kwanta

Qarfe uku na rana suna tare da ita maryam abdallah da hisham,mamin ta dubi Abdallah

''gobe nakeson mu koma gida abdallha,saboda haka ku fara hada iya abinda ke da muhimmanci,saura ku barwa mutan gid

an kafin komai ya qarasa daidaita ku sake waiwayarsu''

cikin shagwabar da ya jima baiyi wa mamin ba yace

''mami a daga min qafa zuwa jibi,akwai muhimmin abinda nakeson qarasawa kafin mu wuce din''

girgiza kanta tayi

''a'ah,gobe zamu tafi''cike da ladab

i yace

''shikenan mami,amma sai la'asar ko''

''Allah ya kaimu la'asar din''

wani abu ya darsu cikin zuciyar maryam,duk da zuwan mamin ya mantar da ita kaso sittin cikin dari na damuwar data shiga duk da cewa abun na manne cikin zuciyarta,ta bisu da kall

o lokacin da ya miqe yana cewa hisham yazo ya raka shi,wani dan banzan kishi ua lullubeta hakanan zuciyarta ke gaya mata gurin mero zashi

''sannu maryama''maganar mami ta dawo da hankalinta,murmushi maryam din tayi ta sunkuyar da kanta,kama duka hanna

yenta mami tayi

''na gode na gode na gode maryam,haqiqa bani da abinda zan iya biyanki da shi,halaccinki da alkhairinki mai tarin yawa ne a garemu,haske ce hakanan alkhairi ce ke a rayuwarmu ni da dana *ABADAN* ba zamu taba mantawa da ke ba maryamu,tabbas

babu wadda ta cancanci abdallah sai ke maryam,'yar halak ce kw gaba da baya,kin riqe amana da alqawarin da kika yimin tun washegarin ranar da aka kawowa abdallah ke,baka taba sanin masoyinka na asali sai wani abu ya sameka maras dadi a rayuwa,maryam ina s

onki kamar yadda nake son abdallah,hakanan ina sake baki amanar abdallah,ki kasance a gefansa *ABADAN* duka tsawon rayuwarsa,na tabbatar cewa matuqar kina tare da shi koda bani duniya bazai shiga mawuyacin hali ba,don Allah maryam kici gaba da riqe abdalla

h kamar yadda kika yi a yanzun''

Gaba daya maryam taji mami ta rikito mata wani qaton nauyi ta dora mata ne,kamar ta daureta ne da jijiyoyin jikinta,girman mamin na da yawa a idanunta,tana daukarta ne kamar mamanta data haifeta,ta rasa mai zata ce da

mamin

_kuyi haquri da wannan_

*mrs muhammad ce*

👑

📚📚📚



🏽



🏽



🏽

💖💖💖💖💖💖

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺

💖💖💖💖💖💖

🌺🌺🌺🌺🌺🌺



💖🌺💖🌺



💖🌺💖



🌺💖



💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

🌺💖

🌺💖🌺💖



🌺💖🌺💖



🌺💖🌺



💖🌺



💖

© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

*_home of expert and perfect writers_*





5



6



*_Daga abdullahi dan umar Allah ya yarda da shi yace:Manzan Allah S A W yace''mutum

bazai gushe ba yana tambayar muta ne(roqo) had sai yazo ranar qiyama fuskarsa babu tsoka daya ta nama(qwarangwal)'',ruwayar bukhari da muslim ce_*

*FANS NA ABDLLAH DA MARYAM,YA BANI SAQO YACE NA GAYA MUKU BA'A SHIGA TSAKANIN MIJI DA MATA FA

😎😎

,T

SAKANIN MIJI DA MATA SAI ALLAH,WANDA YA SHIGAVTSAKANIN MIJI DA MATA QARSHE SHI ZAIJI..........

🙈

*

😎😂

Itama kama hannun mamin tayi

''insha Allahu mami muna tare,babu abinda zai raba mu da ke tare zamu rayu''

giriza kanta tayi

''ko ba dade ko

ba jima dole wataran na tafi na barku maryam,baya ga haka ma duk musulmi na qwarai ana son ya dinga tunawa da mutuwa ko da yaushe,haka annabi muhammad S A W ya horemu yace mu yawaita tuna mai yanke jin dadi''

''haka ne mami amma don Allah kiyi shiru,k

ina tare da mu insha Allahu''

mirmushi kawai mamin ta sake yi

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Kayan sawarsu kadai suka diba amma komai sun barwa inna wuro

''bawan Allah ku cire wannan abar taku mai karbar hasken rana ku tafi da ita''daroya ta basu abdallah yace

''

a'a inna,ku barta ai kuma zata muku amfani,kudin shekara guda aka sanya mata kinga idan aka cire ai anyi asarar kudin ciki,tunda mu muna da inverter acan''bata fuskanci me yqce ba dai amma ta masa godiya

''mune da godiya inna,karamcin da kika mana bazai f

adu ba''

Kudi mamin ta ajjiyewa tsoho alhajin amma qeme me yaqi karba,yace shi abdallah jika ko da ya daukeshi,ba don a biya shi ya masa aiki ba,ko a hanya ya ganshi yana da buqata irin wannan shi mai taimaka masa ne

mamin tace itama ba biyansa tay

i ba Allah ne kadai zai iya biyansa amma sam tsoho alhaji yaqi karba bisa dole ta haqura,itama inna wuron qin amsa tayi,sai dabara mami tayi ta cusa mata qasan tabarmarta yadda bazata gani ba har sai sun tafi

Dukkaninsu suka rakosu har bakin mota cike

da kewa,maryam kam harda qwallanta don tasan zatayi kewar qauyan ba kadan ba

''ka shiga motar hisham kai da hisham din idan yaso ma taho a tawa ni da maryam''

cikin shagwaba irin wadda ya sabawa mamin yace

''gaskiya mami qafata qafarki,a zamu raba mota

ba''qememe yaqi yarda kuma ya kasa ya tsare maryam ba zata shiga kowacce mota ba

Dole hisham ya shige motarsa shi daya,maryam da abdallah na gaban motar mamin ita kuma mami na baya,gaba daya ta hade gabas da yamma na fuskarta don mami ce tace dole it

a zata shiga gaban,shi kam dadi ya kamashi ya dinga satar kallonta yana son ta kalleshi ya tsokaneta,kamar kuwa tasan da hakan taqi uarda ta dubeshin

Yana shirin tashin motar mero ta leqo daga soron gidansu da alamu tana labe ne tun dazun a nan,idanh

shabe shabe da hawaye,sai abdallahn ya kashe motar ya bude murfin ya fice yana fadin

''ina zuwa''

maryam na kallonshi ya qarasa inda meron take,sai ta rufe fuskarta da mayafi ta hau kuka sosai,tana iya hango yadda bakinsa ke motsi da alamu wani abun yake

gaya mata,daga qarshe dariya ta saka,yasa hannunshi cikinaljihu ya fiddo da dubu biyar cikin kudin da jiua hisham ya rakashi cikin gaya ya ciro a ATM machine

Sai sata shige gidansu sunan ya juyo ya dawo cikin motar,yana shirin daura belt mami da hank

alinta ke kan wayarta tace

''ita kuma waccan yarinyar fa wace



''

murmushi yq dan saki kana yace yana kunna motar

''zan miki bayani idan mukaje gida''

bata amsa masa ba ya tashi motar bayan yayi addu'a ta matafiyi ya soma tafiya

La'ilaha illa anta

subhanaka inni kuntu kinaz zalimin ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta sakamkon wani irin daci da take ji,yana tuqin shima yana

satar kallonta,so yake ta kalleshin kuma taqi kallonsa,ya juya ya dubi seat din baya mami ta kashingide abinta tana gyangyadi,ai

dole kam sam tunda tazo garin bata yi wani barcin kirki ba tana ta 'ya'yanta

Ya cire hannunshi guda daya daga kan sitiyarin ya saka cikin tafin hannunta

''baby,me ya faru



,naga kamar baki farinciki da dawowarmu gida''

zame hannun nata tayi cikin ha

de rai

''ka kula fa malam da kyau,tuqi kake,kada kaje ka zubar da mu''murmushi ya kuma yi yana qoqarin sake lalubar hannunta

''mutane biyu wadamda duk duniya babu wanda ke muhimmanci a gurina sama da su fa nake tuqawa,kinga ya zamarmin dole na kula iya k

ulawa''

bai qyaleta ba sai da ya kuma kamo hannun nata yana murzawa a hankali kuma atausashe yana lumshe ido,ta sake zamewa wannan karon tana fadin

''ada ka jimin ciwo bana bayan kai ka adana taka amaryar''

ba don ya daure ba saura kadan ya sheqe da

dariya,ya sami sarai abinda ke cin zuciyarta kenan

''anzo gurin kadan kika gani yarinya,nayi alqawari kuma sai ya cika,da bakinki zaki furtawa abdallah kina sonahi,sai kinsam ABDULLAHI ba kanwar lasa bane,a jininmu yake''ya fada cikin zuciyarsa,a fili k

uwa shima sai ya janyr hannunshi ya maida kam tuqinshi yana fadin

''au haka ne fa,am sorry''sauran qiris ta fashe amma bangaren zuciyarta ya tausheta

🍃🍂🍃🍂🍂🍃🍂

Dan qaramin biki suka je suka tadda anayi a gidan duk na taryar abdallah,duka 'yan

uwan mahaifi da mahaifiyarshi ne da sukasan halin da ake ciki,saidai babu wanda baiyi mamaki ba ganin abdallahn kamar ba wanda ya kwanta cuta ba,ya sani sarai hakan ya samu asali ne daga kyawun weather na garin ni'ima da kuma kyakkyawa kuma cikakkiyar kul

awa da ya samu daga maryam

Cikin mahalarta taron harda SALMA da JIDDA wadanda ke ta binshi da kallon sha'awa da kishi,kishi kuma na banza,eh na banza mana don tunda ya kwanta babu wadda ta tako qafarta da niyyar gaisheshi,a zatonsu abdallan ya gama ai

ki ne cutar data sameshi ba qaramar mummunar cuta bace babu ranar warkewa

to ko dama can shi ba yinsu yake ba ballanta na a yanzu da yasan ajin kowa

babu batun komawa bangarensa a yanzu don mami tace bata yarda da gidan ba ma baki daya balle bangaren

sa don haka cikin dakunan dake corridor din nan guda hudu tasa aka gyara biyu,abdallah ya dauki daya maryam ta dauki daya,tana sane ta raba musu dakin don tuni tayi magana da hajiya laila ta sudan next weak ta zata shigo nijeria zata yiwa diyar mr presdent

gyara jiki na bikinta da za'ayi so zata sauka gidan mamin don sabon gyara mamin tace tana so ayiwa maryam din,a cewarta ba zasu tare sabon gidansu da tun

asali a can aka yi jeren maryam ba sai ta gama gyara diyarta,daga maryam din har abdallan ba eanda ya

sani,ita dai maryam raba dakin da mamin ta yi musu da kanta ba qaramin dadi yayi mata ba don nata son ko yaya tayi wani abu da zai fallasata gurin mamin,s

hi kuwa abdallah ckkin tunani mamin ta sakashi da tunanin ko maryam ta gaya mata wani abu ne game da

yadda aurensu ya samo asali



🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Ita kanta tayi mamakin baccin da tayi,ta jima sosai rabon da tayi bacci irin wannan,don a qauyen ni'ima yawanci daga ta idar da sallar asuba bata komawa,zama take kan abun sallah tayi addu'o'inta da karatun q

ur'ani sabida lokaci ne mai falala da akeson yin addu'a a cikinsa,gari na yin shaa zata jiyo kwaramniyar inna wuro take zata fito su hau aikin kintsa gidan da hada abun kari,bata farka ba tunda ta kwanta sai shida,tayi sallar asubahi ta sake komawa,sau biy

u abdallah na leqota ba tare da ta sani ba tunda bata qulle dakin ba ta kwanta

sai sha daya na safe ta kuma tashi,kayan jikinta ta cire ta daura towel ta shiga wanka,bayan ta fito tayi tsaye gaban madubi tana goge ruwan jikinta kana ta ja dressing cha

ir ya zauna akai tana qoqarin fara shafa mai

''amma fa yau garin kamar da zafi zafi,ki shafa kadan kada ya saki gumi da yawa''taji an fada,a tsorace ta waiwayo,yana kwance abinsa daidai kan gadon nata hankalinsa kwance kamar a dakinsa yake,sanye yake da t

shirt fara qal mak gajeran annu sai three quater shima din fari ne tas,yayi saisaye da gyaran fuska ya sake yin kyau kmar wanda aka canza shi daren jiya

A hanzarce ta miqe da gudu ta koma cikin bandaki gqulli,tsaye tayi jikin qofar bandakin,takaici y

a sake cikata data bi jikinta da kallo,yanzun qila gwanin kallon mutane ya gama qare mata kallo,ta waiwaya ga babban madubin dake maqale a bangon bandakin ta kalli kanta,daga cinyarta ne kawai zuwa qirjinta a rufe amma ko ina na jikinta awaje yake,tuni qwa

lla ta cika mata ido,ta koma ta sake keqashi ta jikin qofar,yana kwance bashi da niyyar tashi,danne dannensa ma yake a waya abinsa

''idan zaki fito ki fito abinki,ni zuwa nayi mu gaisa kuma na tambayeki,ba abinda kike zata bane''yq fada yana sake gyara kw

anciyarshi

taja baya da sauri din gani take yana kuma hangota ne,idan banda rainin hankali irin na abdallah a haka zata sake fitowa



,kuma haka ake shiga dakin mutum ba neman izini bakasan ma ya shigo ba

tana tsakq da neman mafita taji ana knocking qo

farta,kafin ta kai ga amsawa taji muryar mami na fadin

''maryam,baki tashi bane



''

gyara muryarta tayi kana tace

''na tashi mami na farka tun dazun''

''ok to bude min''

rarraba ido ta fara yikamar wadda ta yiwa sarki qarya,gaba daya ta rude,abdallah s

o yake ya ja mata abin kunya,haka kawaj mami ta raba musu

daki ta gansu kuma tare,ita ga towel a jiki ta fito daga wanka,ta matso jikin qofar sosai yadda abdallah zai iya jinta cikin rawar murya tace

''kaga abinda ka jawo mana ko,yanzu meye haka don A

llah''

tana kallo shi yana dariya

''ni ban jawo komai ba,kwato ne ni balle kice idan an ganni a dakin za'a jefeni ko ayimin bulala,ki fito kawai ki canza kayanki ki bude mata''haushi ya qara kama ta ganin yadda ya maida abun ba seriouse ba,cikin qunan ra

i tace

''Allah ya sawwaqe wallahi na fito ka gani a haka''

yayi wani irin juyi yai ruf da ciki saman gadon yana fadin

''mu shekara a haka mana yammata''

''maryam,me kika ce



''inji mami,sai tsoro ya sake kamata kada dai ace taji muryoyinsu,ta dan da

ga muryarta tace

''am...am...cewa nayi...cewa nayi dama ina bandaki ne wanka nake''ta fada cikin tsoro

''ok,to shikenan nari na shiga gun abdallah dukkanku baku karya ba shima daga cemin zaije wanka shiru,idan kin fito ki samemu a dining''ajiyar zuciya t

a saki da taji alamun mamin ta tafi

Miqewa yayi ya sauka a gadon jin mamin ta soma qwaqwasa qofar dakin nashi,tana kallonshi ya murza key ya bude dakin,lallima *SAMUN WURI*(by maman farida),har ma wani key ya saka mata a daki kamar nashi dakin,bata ta

nka masa ba har ya fice don kada kulashi y sake dawowa ba qaramin dan neman magana bane kadan daga aikinshi

Yana fitowa suka hada ido da mami,duk sai ya dububurce,kunyarta yaji ta kamashi ganin yadda ta harde hannunta aqirji ta zuba masa ido,sai ya so

ma shafa qeyarsa,dariya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login