Showing 42001 words to 45000 words out of 176330 words

Chapter 15 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

57

tsaidata,har ta iso gabanta ta kasa motsawa,cikin huci take dubanta

''rashin karbar tayi na yarinya daidai yake da tangal tangal da rayuwarki,arziqi na bi

nki tsiya ta hanaki ki ganewa,kije....ko babu ke sai na cika burina,hanyoyin nada yawa,amma ki tabbata rayuwarki na cikin hadari,kuma wallahil azeem kika bari maganar nan ta fita sai na batar dake''

a sukwane ta bar sashen,da qyar ta kai kanta dakinta

cikin mawuyacin hali,fadar irin halin data tsinci kanta bata baki ne

tabbas ta kuma gasgata cewa nene na iya aiwatar da duk abinda ta fada din,ta gani,cikin qwayar idonta

mafita daya take hangowa a gareta shine ta nemi miji tayi aure,ba zata iya kallon

qwayar idanun mami ba tace tabar aiki,wata fuskar tafi gaban mari,aure shine zai rabasu salin alin

*_dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki_*

*_ina taya daukacin al'ummar annabi murnar zagayowar babbar sallah da fatan za'a gudanar d

a bukukuwan sallah lafiya_*

*_insha Allahu daga yau zamu je hutun sallah,littafin abadan zaici gaba da izinin Allah bayan qare hidindimun sallah_*

*_subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika_*

*mrs muhammad ce*

πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“š

✍

🏻

✍

🏻

✍

🏻

✍

🏻

[9/17, 12:53 PM] 80k:

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺🌺



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸŒΊπŸ’–



πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

*WRITTEN BY*

*

SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ

πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–

πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ

πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ

πŸŒΊπŸ’–

🌺



β–Ά

2

⃣

8

⃣

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*

πŸ’‘

*_wannan page din naku ne,wato mata iyayen gida,ku huce gajiyar sallah,Allah ya qara mana himma da lafiya,ya bamu ladan

kula da iyali_*

material ne a jikinta mai baqi da fari,skert din baqine sol babu digon komai,rigar kuma fara ce mai adon baqaqen fulawoyi,irin dinkin nan ne da muke kira three quater iya gwiwa,skert din simple ne mai tsaga a baya,baqin mayafi ne

tayi rolling da shi sai farin plate shoes mai igiya data sanya

a kasalance take nunawa ma'aikatan irin kayan da suke so su kuma suna cirowa suna sanyawa cikin keken tura kayan,qarfin hali kawai take,batason nunawa mami wani abun na damunta,duk da tan

a jin kamar zazzabi na shirin kamata

sannu a hankali suka qurewa bangarwn electronics dake cikin makeken shagon zamanin nan na shoprite dake ado bayero mall,suka juya bangaren warmers da plates cups da sauransu,daya bayan daya take bi tana zaban sabab

bin design

''subhanallah''suka fadi a kusan tare suka kuma ja da baya,tuni cups din da ta dauko sukayi nasu guri a qasa sakamakon karon da sukayi,a tare suka duqa suka soma kwashewa

''kiyi haquri madam don Allah ban kula bane''ya fada yana miqa

mata guda ukun da yayi nasarar kwashewa,sai a lokacin ta dubeshi,baqi ne ba can ba zaka iya kiranshi da chaculet,dogo ne maras qiba,ya mata kama sosai da mutanen qasar habasha ko kuma baqaqen fulani

''ba komai'' ta fada tana amsar kofunan,kana ta rabeshi

ta wuce

''ko am min izini na taya madam din zabar kayan duk da ba bangare na bane

?

''taji an fada daga bayanta,da sauri ta waigo mutumin dazun ne,tamkar tace a'a sai kuma taga babu buqatar ta fadi hakan

''bismillah''tace da shi

cikin hikima da dabara

yake bayyana mata ko shi waye

''ni sunana abdur rahim tasi'u alhasan,ina zaune a unguwar qoqi dake tsakiyan birnin,ni dan kasuwa ne kamar yadda mahaifina yake,ina fata kin gamsu da dan taqaitaccen bayanin da na miki''ya qarashe magana lokacin da ya

ke tura kwandon yana kuma kallon fuskarta

dan qaramin murmushi ne ya subuce mata

''to ni kuma meye nawa da sanin kai waye,daga taya ni siyayya

?

''

murmushin shima yayi bayan ya tsaida basket din

''ke kuwa kike da ruwa,saboda ina sa ran zamowarki uwa

r gida na,bazan boye miki ba tunda na ganki naji kin kwanta min,da gaske nake sonki *maryam*aurenki kuma nake so inyi anan kusa''

a mamakance take kallonshi,to ko addu'ar da ta kwana yi jiya ne Allah ya amshi roqonta

?

,babu shakka Alkah maji roqon bayinshi

a kurkusa ko a nesa

''yaya akayi kasan sunana,bayan a iya sanina ban gaya maka ba baka kuma ji wani ya ambata ba

?

''

murmushi ya sakeyi

''maso dan tsuntsu shike binsq da jifa,sonki nake bada wasa ba hakan yasa nasan komai game dake kafin na iso gareki''

cikin wani mamakin ta kuma dubanshi

''kana nufin ba yau ka fara sani na ba

?

''

ya dage girarsa sama

''eh,kusan haka dinne''cike da mamakin shigowar abdur rahim cikin rayuwarta lokaci guda suka kammala dukkan siyayyrsu ita da abokan tafiyar tata,har

lokacin abdur rahim din na biye da su hqr suka kammala,a bakin motarsu ya dubeta

''yaushe zanzo mu tattuna a nutse''ya tambayeta yana murmushi,dan jim tayi tana tunani a lokacin taji wayarta na ringin,da sauri ta cirota,ta duba,atsammaninta hindatu ce do

n tace zasuyi waya sai kuma taga baquwar number

''ga number dina nan kiyi serving zan kiraki naji lokacin da zanzo din''

da mamakin karona uku ta sake dubanshi,mamakin ina ya samu num dinta,kamar yasan me take tunani yace

''nasan mamkin inda na sami

number dinki nake ko,kada ki manta na gaya miki dazu,na shigo sonki ne bada wasa ba hakan ya sanyani sanin komai game da ke tun kafin na iso gareki''murmushi ta sakar masa,sai taji abdur rahim din ya burgeta karo na farko,wannan wane irin so ne haka

?

ko cikin motarma tunani abdur rahim din ta fada,tana gaya wa kanta ta samu mijin aure tabbas,tana kuma qarfafawa kanta gwiwar wannan karon zata shiga dakin aure kamar kowacce mace

bayan mami ta gama ganin kayan ta yaba sosai,don tace basu taba siyan

kaya new fashioned and durable haka ba kamar wannan shekarar,kai tsaye dakinta ta wuce don tayi sallar la'asar su fara rage koda gyaran kitchen ne tunda taga da time,biyu daga cikin daki hudun dake rufe ta sake gani a bude,bata ce komai ba don ga tsammanin

ta baqi mamin ta sakeyi

da taimakon ma'aikatan harda baaba uwani cikin qanqanin lokaci suka fidda tsoffin kayan kitchen din suka fara shirya sababbi,aiki na yiwa maryam dadi sakamakon yadda yake tqfiya cikin tsari,sunayi kuna suna hiransu abinsu,kad

a ma baaba uwani taji labari,akwai abun dariya

''lamarinku na yaran zamani na bani mamaki''baba uwani ke fadawa maryam qasa qasa

''me mukayi baaba uwani

?

''maryam ta tambayeta tana fiddo da wani foodflask daga cikin kwalinshi

''mata su dinga biyo maza g

ida suna neman aurensu

?

''

''kamar yaya baaba

?

''

''hmmm,yaran nan mana dake son yaron gurin hajiya abdullahi,dazu daya yarinyar nan itama tazo da kayanta na satittika,ummm.......salamatu,mu a da ba sai an kaiki daki ba ma kike sanin waye mijin

?

,idan ma ku

wa har kinsan waye shi din kafin a daura aurenku to ko hanyar da yabi baki iya bi saboda kunya,idan kuwa tsautsayi ysda kuka hada hanya to sai kinkusa qamewa a tsaye vaki iya motsi har sai ya wuce''

dariya ce ta kubcewa maryam

''baaba kin iya bata su

na,salma ake cewa ba salamatu ba''

''kome me take ne barta,abun nasu sai addu'a,ko kunyar hajiya basa ji,ko fada ne ya kama yi suke a gabanta,abunda mu ko abinci baka iya ci gaban suruka,wannan zamani wannan zamani yazo qarshe,fatan Allah yasa mu gama laf

iya''

''ameen''maryam din ta amsa mata da shi,daga haka bata ce komai ba,ita kanta mamaki take,saidai babu ruwanta don bata shiga shirgin da ba nata ba

ana kiran sallar magariba suka kammala aikin duk girman kitchen din yayi kyau ya sake haske,lallai

sabon abu akwai kyau inji baaba uwani,ita kanta mamin ba qaramin mamaki tayi ba,ta sallami sauran ma'aikatan tana yabawa qoqarinsu

dakinta ta kuma komawa sanda tafito daga kitchen din abida ce zaune gaban makekiyar t.v plasma tana kallo sanye da mats

attsun riga da wando,kusan duka shigarta kenan ta fidda tiraici ko doguwar riga zata sanya sai ta samu mai tighting jiki,wanka tayi ta sauya kayan jikinta,ta daura alwala tayi sallah,tana saman dadsuma tana lazumi ta tuna zata kira fa hindatu,ta laluba way

ar bata jita ba hakan ya bata tabbacin ta manto ta a kitchen,ta gyara zaman ijabin jikinta ta fice ta nufi kitchen

su uku ta tadda yanzu a falon abida salma da abdallah da suka saka atsakiya,kallo daya zaka musu ka tabbatar daga abidan har salman ba j

in dadin zaman suke ba,shi kuwa hakimin na tsakiya zaune yana ta aikin amsa waya,bisa dukan alamu wani aiki yake shiryawa don taji bada order din yayi yawa cikin fada da fushi

ilai kuwa cikin sabuwan kitchen wear din ta ganta,missed call goma ta taras

,hudu na hindatu hudu na abdur rahim daya na raliya,murmushi tayi don dama ta sani bata da masu kiran nata sai su,sai ta rasa wanda zata soma kira a cikinsun,cikin haka kiran mami ya shigo

''kina ina ne maryamu,na shiga dakinki ban tadda ki ba''

''mami i

na kitchen''

''baki gajiya ne maryam aiki sai kace inji,already baaba uwani tayi abinci ki huta haka nan don Allah''

tana jin dadin qaunar da mami ke nuna mata qwarai da gaske

''wayata na manta ma nazo in dauka''

''ok,ki sameni a parlour na''

''to''ta

amsa mata ta cire wayar daga kunnenta ta fita daga kitchin din

''ke mero''taji an fada lokacin da take qoqarin hawa matattakalar benan

kamar kada ta juyo sai kuma ta waiwayo din don ganin mai mata kiran,abida ce

''meye kika tsatstsareni da idanuwan

kin nan kamar na

?

,shawarma nake sonci,ki shiga kitchen yanzun kimin idan kin iya''

rausayar da kai maryam tayi

''batun iyawa na dade da wuce babinshi,saidai lokacin aiki ya qare,zaki iya barwa gobw idan Allah ya kaimu,tunda majority utensils din duka sab

bi ne bamu bude su ba''

cikin izza isa da gadara tace

''ke,wai mai kike taqama da shi ne,ki fadi nawa ne albashinki duka a nunka miki bama iya kudin aikin yau ba,ban mance ba rannan haka kika mana wani abu tuwo sunanshi ko me

?

nace kimin wani kalar gi

rkin kika ban banzan answear irin wannan,kinsan wace ni kuwa

?

''

sakin makarin silver din da maryam din ta riqe tayi ta juyo ga abidan sosai

''ni ba kowa bace kuma bana taqama da kowa face Allah,kudi kuma ba zaki bani yanke talauci ba har abada,matsay

in da Allah ya ajjiyeni ya gamsar da ni sosai na kuma gode masa,gaskiyata na fada tsarin siki na kenan cikin gidan nan,baquwa ce ke ina zato shi yssa kike mantawa,sannan ke din ma ba kowa bace face baiwar ubangiji kamar yadda nike kowa kuma yake''

a h

ankali abdallah ya dago kanshi daga kallon wrestling a tashar mbc action da yake ya dubeta,sai yaji amsarta ta burgeshi,babu hayaniya cikin raddinta,cikin calmnesses and cool voice,sai ya dan tsaida abunda yake yaga yadda za'a qare

tuni fuskar abida ta ca

nza,cikin bacin rai ta dubi abdallah

''mu sugar kana gani da jin abunda yarinyar nan ke gaya min ko''ta fadatana nuna maryam wadda tuni har ta kusa kaiwa qarshen benan

murmushi ya saki mai hade da yar dariya

''duk bakery din dake garin kano kin rain

a,kin rasa inda zaki ci shawarma ne

?

''

''zaka iya kaini ne

?

'

''a lissafin lukuta na babu wannan,idan kina so akwai direbobi sai wani daga ciki ya kaiki ya dauko''sai ta sake tunzura,ya yrfata gaban salma kenan

?

,abunda madyam din ta mata ya hadu da wanda

abdallah ya mata ya zamar mata zafi biyu

a zafafe ta miqe tana cewa

''tunda kai bazaka iya daukan matakin komai ba to ni zan daukarwa kaina,bazan zauna talaka 'yar talaka wulaqantacciya ta dinga taba mutuncina ba''

wani murmushin ya kuma saki ya kim

a kashingida

''eh kuma fa,gaskiyarki nima na goyi bayanki,kamarki diyar ambassador guda bai kamata a dinga samun iein haka ba,jeki dauki mataki''

sai ya kuma tunzurata don ta fuskanci kamar gatse yake mata ko kuma jirwaye mai kamar wanka,a haukace ta hay

e saman

kujera ta samu ta zauna tana fadin

''gani mami''

''yauwa maryam....cewa nayi''maganar mamin ta katse sakamon kiran da ya shigo wayar maryam din,screen din ta duba,sunan abdur rahim ya bayyana,sai ta maidata silent taqi dagawa

''ki daga mana

maryamu''inji mami

murmushi tayi ta dan sadda kanta

''um um mami,ina jinki''

cikin murmushin da salon zolaya tace

''kodai suruki na ne maryam

?

''

sai kunya duk ta kamata tayi qasa da kanta tana murmushi

,ganin tayi shiru yasa mami cewa

''Allah y

a tabbatar mana da alkhairinsa,shawarata gareki ki riqe mutuncinki,ka kame kanki,mutuncin mace kunya da kamun kai,duk da nasan duka halayenki ne,idan na samu lokaci zan miki magana yazo inganshi mu gaisa''cikin jin dadi da gamsuwa da maganganun mamin take

gyada kai,sai ta kuma tsokanarta

''bari nayi sauri na sallameki kada surukin nawa ya qosa da jirankin ko''sai ta sake bawa maryam din kunya

''kaya ne wadanda aka fitar da kayan firniture da za'a fitar gobe nake son ki zazzabi dukka abunda kike so ki

kaiwa mamnki ko zatayi amfani da wasu wadanda bata so ta bada''

tayi mamakin yadda mamin ta bada kayqn,don kaya ne da babu abunda aukayi tamkar yau aka zuba su espicially kayan furniture din,ta wani fannin kuma ba abun mamaki bane saboda halayen mamin ne

*karamci* da *kyauta*

sabanin wasu masu hannu da shunin da sun gwammace su saida kayan maimakon 'yan uwanau su amfana furniture ne ko kayan sawa,ko me zasuyi da kudin oho,bayan Allah ya wadata su ya basu arziqin amma suna maida kansu baya

''na gode m

ami qwarai,Allah ya qara girma''

murmushi mamin tayi

''bakin maryamu ya saba da godiya,nasha fadi miki ba haka tsakani na da ke''

kafin tace wani abu an banko qofar an shigo,abida ce kanta tsaye ta tafi gurin mami

''mami,ki shiga tsakanina da house gir

l din nan,hala bata san koni wace ba,ta raina ni matuqa,wallahi idan bata kama kanta ba zanyi sanadiyyar

qulle danginta kaf babu wanda ya isa ya fito da su,batasan ba'a raina ni ba,bana daukar raini

?

''

kama kai mami tayi tana kallon abida

''qara kika kaw

omin ko mataki kika zo dauka

?

''cikin rashin iya magana tace

''duka mami''

ta riga da tasan abida rainon tabara ce,ta san ita har zuciyarta magana ta fada mai kyau,ta bar ta tata ta juya ga maryam ta tambayeta mai ya faru,a nutse ta gaya mata

''tashi kij

e maryam,sai da safe Allah ya bamu alkahairi''

''ameen mami''ta fada tana ficewa,yunqurowa abida tayi gurin maryam mami ta dakatar da ita

mamaki ne ya ishi maryam,tana shiga daki kiran abdur rahim ya shigo wayarta,murmushi ta saki ta isa gefan gadont

a ta zauna sannan ta daga

*mrs muhammad ce*

πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“š

✍

🏻

✍

🏻

✍

🏻

✍

🏻

[9/17, 12:53 PM] 80k:

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺🌺



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸŒΊπŸ’–



πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺

🌺🌺

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

*WRITTEN BY*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ

πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–

πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ

πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ

πŸŒΊπŸ’–

🌺



β–Ά

2

⃣

9

⃣

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*

πŸ’‘

*_home of expert and perfect writers_*

Kimanin awanni biyu suka shafe ka

n layi ita da abdur rahim din,ta fuskanci ya dan san wasu abubuwa game da ita wanda hakan ke qara mata amanna da qaunar da yake iqirarin yana mata din,tuni ta yanke ma ranta abdur rahim na daya daga cikin batutuwan da zasu tattauna a gobe ita da mamanta,ba

i barta ba har sai da ya fuskanci ta soma jin bacci tukunna ya mata sallama cike da qauna da bege mai yawa

πŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒ

Abu na farko da ta fara cin karo da ahi cikin gidan nasu bayan yin sallamarta shine dambe tsakanin huwaila da haduza abinda zata i

ya cewa bata taba gani ba,daga gefan huwaila lubabatu ce da binta ke zuga uwarsu,yayin da kuna gefan hadizar kuma shamsiyya da yasira ne suma ke nasu aikin sai jamila dake zaune bisa dakalin qofar dakin mahaifiyar tata da uban akwati a gaba,idanu jajir wan

da ke nuna bisa dukkan alamu kuka take sharba ko kuma take kan sharba din,mamanta ta hango na shirin fitowa daga dakinta hannunta ruqe da dankwalinta tana mai qoqarin daurawa hindatu na biye da ita tana fadin

''don Allah mama ki barsu''

Da sauri mary

am ta taya hindatu tarar maman nata

''mama wanna ba sabgarki bace,kin taba ganin suna dambe

?

,to ki qyalesun kamar yadda hindatu tace Allah ne yasan me ya hadosu,babu ruwanki mamana tunda koma mene lokacin da zasu qulla basu nemi shawararki ba,kiyi addu'a

kawai Allah ya warware musu ita ta ruwan sanyi''

da dadin baki suka sanyata a tsakiya suka koma cikin dakin abinsu,har aka gama shigowa da kayan suna bala'i basu sani ba

''amma maryama gini irin wannan namun ai bai cancanci kayan gado na alfarma irin

wannan ba''

dariya ma maman ta baiwa maryam

''haba mama,tunda Allah ya baki sun cancanta din kenan,yanzu aikin kawai zamu shiga yi har kitchen din''

hindatu dake tsaye wadda farinciki duka yabi ya cikata tace

''yauwa adda maryam,kinga zuwa gobe mun ga

ma zama 'yan gayu,babu raini wallahi,don duk cikin gidannan babu mai arziqin siyan irin wadan nsn kayan''

dadiya duka ta basu don har yau hindatu shirmen auta bai saketa ba

sai da suka soma fidda na dakin maman suna shigar da wadancan sannan suka ank

ara,lubabatu ce ta fara gani ta zunguri uwarta dake riqe da habar zaninta daketa kwancewa saboda azabar bala'i tana qoqarin daurawa

''huwaila tayani gani,kinga su kuma wadan nan ina suka samo kayan alfarma haka''

da sauri ta juyo don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login