Showing 87001 words to 90000 words out of 176330 words

Chapter 30 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

29

ya wuce ta bishi da godiya

gefanshi ta dawo ta zauna ta fara matso cream din,a hankali take shafa masa a gefe da gefan fuskarshi,idanunahi qyar cikin n

ata,nauyi takeji da kunyarsa duk lokacin da ya zuba mata idanunshi,a hankali ta janye qwayar idonta tana ci gaba da shafa masa din,ta kammala ta dauko shever ta fara masa askin,ajiyar zuciyan da ya saki ya sata saurin kallonshi cikin tsoro,cikin sassanyar

muryarta tace

''ko na yanke ka

?

''murmushi ya mata ba tare da ya nuna alamun a'a ba,kusan sakanni uku sannan taci gaba,a hankali taji ya riqe hannun nata da take shaving di dashi,ta sake waiwayo ta kalleshi shima din ita yake kallo

ta langabe kai

''da za

fi ko

?

,dama na ce masa ban iya ba.....''bata qarasa ba taji ta kan qirjinsa sakamkon janyota da yayi ya rungumeta tsam

dukan uku uku qirjinta ya shiga yi,tayi yunqurin tashi taji ya sake maidata,idanunshi a lumshe kamar yadda nata yake,dukkansu suna jin

bugun zuciyar junansu da ta qara gudu fiyeda yada take bugawa,sannu a hankali taji kasala na kashe mata duk wata gaba ta jikinta,jikinta ta saki batasan yadda akayi bacci yayi awon gaba da ita kan qirjin nasa ba,shi din ma yanayin ya masa,ji yake amar ya

tsaida lokaci don su dawwama a haka,tun yana jin saukar numfashinta har shima baccin yayi gaba da shi

πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒ

kusan lokaci daya suka farka,da hanzarita ta miqe daga jikinsa don tunawa da cream da ta bar masa a fuska,idanunshi a lumshe yake kallont

a,sai taga ya kai hannunshi gefan kunnenta ya ciro wani abu ya nuna mata,cream dinne da sauri ta dauki madubin dake hade set da shaver din ta haska,ai kuwa gashi nan ta kwaaheshi ya bata mata fuska ta dubeshi suka hada ido sai suka saki murmushi tare,dan t

owel din askin a janyo ta goge fuskarta ta matsa ta dauki shaver zata ci gaba da askin,dora hannunshi yayi saman nata hannun da sauri ta janye hannun nata saboda tsigar jikinta da taji ta tashi,ya karbe abun askin ta fuskanci me yake nufi don haka ta dinga

haska masa yana askin da kansa,idan ya gaji ya tsaida hannun nashi ya huta tunda har yanzun ba wani qwari ne da shi ba

towel tasa mai mai kyau ta goge masa fuskan bayan ya gama,tana shirin miqewa taji ya riqo hannun nata ya sanya tafin hannunshi cikin na

tan ya matsa su sannna ya gyada kai ta fuskanci godiya yake mata,murmushi kawai ta saki ta sunkuyar da kanta kana ta zame hannun nata ta sauka daga kan gadon tana tattara kayayyakin da sukayi amfanin da su har yanzu idonshi a kanta yake,yanayinta kadai bur

geshi yake,kominta anutse cike da tsafta tausayi da kulawa,ya maida idonsa ya lumshe bayan yaga fitarsa yana addu'ar Allah ya bashi damar da zai nuna mata nashi kalan halaccin koda bata sonshi

da uammain mubarak ya kawo wheelchair da hisham yace ya kama

ta a fara dora abdalla atleast zai dinga jin dadi idan an fita dashi daga bedroom zuwa parlour zuwa balcony din saman tunda ba zata iya saukowa da shi ba falon qasa,yaji dadi kuwa don alamu sun nuna afuskarshi,yawanci idan la'asar tayi aka dorashi zata yit

a shawagai da ahi daga parlou zuwa kitchen zuwa balcony din wani sa'ilin ma ya mata alaman su zauna cikin kitchen musamman idan tana girki,ganin zaman shiru suke yi yasa tana girkin tana bashi labaraimasu debe kewa,hakan kuwa na matuqar sa farinciki a zuci

yarshi,don zata ga fuskarsa ta fadada sosai da murmushi alamun yana jin dadi

saidai kallon qurillar da abdallah ya koya tilas yasa take zama da hijabi,don ba qaramin kunya yake bata ba,ko ina yaso kalla kallonsa yake kanshi tsaye,da sun hada ido kuma ya

wani lumshe ido ya basar kamar bashi ba,wani lokacin murmushi take cikin zuciyarta tace

''hali zanen dutse,babu abinda ke saiyawa dan adam halinshi,har yau halin abdallah na basarwa da waskewa na nan cikin jininshi''

*mrs muhammad ce*

πŸ“šπŸ“šπŸ“š

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺



πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–



πŸ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–

Β© *HA

SKE WRITERS ASSOCIATION*

πŸ’‘

*_home of expert and perfect writers_*



β–Ά

4

⃣

3

⃣

*_An karbo daga nana Aisha Allah ya qara yarda a gareta tace:naji manzan Allah S A W yana cewa ''ya Ubangiji duk wanda aka dora mishi wani shugabancin na al'umata

,ya tsananta musu Allah ka tsananta masa shima,wanda aka dora mishi wani shugabanci na al'ummata ya tausasa ya sassauta musu Alla ka tausasa masa ka sassauta masa shima_*

Qarfe biyar da rabi ne na yammaci mai cike da ni'ima da dadi kasancewar

ko kusa garin babu rana sai lullumin hadari da ya lullube sama,su biyu ne zaune cikin falon yana kan wheel chair tana kan kan kujera saidai suna facing juna ne

novel ne a hannunta take karanta mishi sannu sannu cikin daddadar muryarta,tunda ta kifa fuskar

ta alittafin data kare fuskarta da shi bata dago ba saboda nauyin da kunyar kallon da abdallahn yake mata,gashi hakanan yaqi yarda yau a saka mashi kaya complete,duk wanda hisham ya ciro sai ya wurgar shi daminshi suke,wando three quater ne ajikinshi da ri

ga armless duk wata qirar jikinsa ta bayyana

A hankali yasa hannunshi ya riqe littafin yayi qasa da shi tavdago kanta suka hada idanu,ido daya ya kashe mata yana murmushi don ya fuskanci abinda ya sata qin sakewar,littafin ta sakar mishi ta dora fuska

rta saman cinyarta cike da jin kunya,taba kanta taki yayi sai taqi dagowa,ya daga littafin ya dan buga mata kadana akanta tare da cusa mata shi.

A hankali ta dago da zummar dauke littafin taci gaba da kare fuskarta,rubutu ne baro baro a bangon littafi

n I LOVE U,wani feeling ta dinga ji tana sake maimaita rubutun tamkar yau ta fara ganin kalmar,a dan sace ta rage tsawon littafin idanunta suka fito,karaf suka hada idanu da abdallahn daya zubawa cover littafin ido,tayi azamar maida littafin saidai tuni ha

riqe da hannunshi daya yana ci gaba da kallonta,ji tayi bazata iya hada qwayar idanunsu ba saita sauke qwayar idanun nata kan cinyarta tana kallon yatsun hannayenta.

Qarar bugun da akayiwa qofar dukkansu sai data basu tsoro,kusan a tare suka kalli qo

fan,mami ce ke shigowa a burkice idanunta a kansu, qaraso gabansu ta ja burki

''sannunku qananun 'yan ta'adda,wato har kisa kuka so yimin cikin gida na ko

?

,to wallahi baku isa ba matuqar kuka ci gaba da yunqurin taba lafiyar wani cikin gidan nan zan iya

tattarku kubar min gida tunda dai ba naku bane,kada ku kiskura ku sake aikata wani abu mai kama da haka don ba gidan 'yan ta'adda bane nan''duk maganar da take kan maruam na duqe a qasa,yayin da abdallah ya zuba mata ido cikin qunar zuciya da tashin hankal

i,me ya sami maminshi haka

?

me ya canza masa mami

?

,mamin da bata

qaunar taa ko sauyawa fuskarshi tayi,mami mai tattali da qaunar farincikinsa,mami dake qauqnr maryam ta dauketa tamkar diyarta ta cikinta

ta kalli maryam''kuma ki gaggauta zuwa ki nemi ya

fiyar nene da danan idan ba haka ba wallahi sai na wulaqantaki,idan banda ma ke butu ce shegiya mara mutunci daga zuwa ya duba lafiyar mijinki sai ki masa irin wann mummunar sakayyar,na baki nan da minti talatin kije ki basu haquri''ta juya zata fota suka

hada ido da abdallqh,hara ra ta wurga masa saboda jin wani abu na son taba zuciyarta,sai kuma wani abu daga can daban ya taso ya danneshi

shiru ne ya ratsa falon bayan fitarta,dukkansu kansu na sunkuye zuciyoyinsu na saqa musu abubuwa mabanbanta,ganin

ya kusa gota mibti talatin din da mami ta bata ya sanyata miqewa da sauri,hannunta taji an damqo,ta waiwayo sai taga abdallah ne,a hankali ya dao idonsa suka hada ido,da sauri ta kawar da kanta saboda tashin hankalin da ta gani cikin qwayar idanunshi basu

musaltuwa,fararen qwayar idanunshi sun juye sun koma ja baya ga jijiyar kanshi da ke tashi,kai ya girgiza mata alamar ba zata je ba,itama kan ta girgiza kana ta dawo gabanshi ta durqusa tace

''kayi haquri ka bari inje din,umarnin mami nake qoqarin cikawa

ba donsu zani ba,kada ka manta har yau mami na matsayin uwa ne a garemu kaga ya zama dole mu bi umarninta don gamawa da duniya lafiya indai ba ya sabawa addini ba''

shiru yayi ma wasu 'yan daqiqu kana ya daga mata yatsunshi guda biyar alamun minti bi

yar ya bata,guada kanta tayi sanan ra miqe ya bita da kallo har da fice

tana gab da shiga waitin falo inda anan qofofin bangaren nau yake ta hango adnan,muta ne uku ne zabga zabga baqaqe,cikin baqin kaya masu qirar samudawa biye da shi,kallo daya zaka

musu ka tabbatar cewa babu masaukin imani cikin zuciyarsu,mamaki ya cikata duk da tasan cewa lokaci lokaci zaka ganahi da ire iren mutanen a matsayin abokanshi,sai ta kasa wucewa ta rakube har suka wuce,tazarar minti biyar ta bada tasan zywa lokacin sun s

higa koma ina zasu ahiga sannn tabi bayansu,a qofar waiting parlour din suka kusa karo da mami wadda ke sanye da kayan aiki da alama asibiti zata fita taja da baya ta bata hanya,harara ta watsa mata mamin kana ta fice,girgiza kanta tayi kawai tabi ta da ka

llo,kallo daya zaka mata ga wanda ya santa yasan cewa ta canza,tsaftarta har yanzu tana nan saidai duka gayun nan babu shi,bata mantawa shekaran kiya doctor safara'u abokiyar aikin mamin ta kira maryam take tambayarta me yake damin mamin ne,kullum tazo off

ice bata da aiki sai kuka,tambayar duniya kuma ba zara gaya maka abinda ke damunta ba,magana daya zata gaya maka shine babu komai

Ganin babu kowa cikin falon qasan ya sanyata nufar sama,tana atep din qarahe na matattakalar ta soma jiyo maganganu,tamka

r an dasata agun ta kasa gaba ta kasa baya

''yace saidai mu mu qarasa aikinmu,dalili kenan da yasa nace ka nemo min su mugu,wanna karon zamuyi aikin qarshe kan abdullahi,jibi da daddare nake so ku kashemin abdullahi,kafin ranar zansan duk abinda zanyi na

kori yarinyar daga gidan nan,idan kuma tayi taurin kan qin tafiya na baku dama ku hada harda ita....''

''haba nene haba nene,ya zaki ce a kasheta bayan kinsan qudirina akanta...''adnan ya katseta

''dakata min adnan,wanna karon bana son matsala kowacce ir

i ce,mata gasunan bila haddin,koda an kasheta da zarar ka samu 'ya'yan banki kana iya samun dubunta ka huta da su ko ka auresu,mubar wannan maganar''

bibbiyi ta dinga hada matattakalar benan tana saukowa,badon nutsawa da sukayi kan maganr ba da babu a

binda zai sanyasu jin takun saukarta,saidai ina dukkansu hankalin yayi gaba,a inda ta bar abdallah ta tarar da shi,a hankali ya dago kai yana dubanta,gqnin irin birkicewar da tay ya zuba mata ido kamar mai tambayarta,cikin rawar jiki ta tura whewl chair di

n suka ahige brdroom ta maida muqulli ta rufesu,jikinta na rawa ta dauki wayarta,ta fara qoqarin neman numbers dib hisham saidai bata yi sa'a ba ta samesu a kashe,bakin gadon ta koma ta dafe kanta ta fashe da matsanancin kuka,tana kallon abdallah na daga m

ata hannu saidai ta kasa ce masaa komai,tausayinsu su duka biyin ya lullubeta

Misalin goma na dare ta samu wayar tashi ta shiga,da sauri ta fita adakin ta canza daki don bata son abdallah yaji komai,shi,kansa da baisan meke faruwa ba hankalinshi a tas

he yake tun dazun fuskarsa ta nuna,bata jira jin komai daga bakinsa ta fara fada masa abinda ke faruwa

innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa,tabbas zarginsa ya zama gaskiya

''ki saka nutsuwa afuskarki maruqm,kada ki sake ki nuna musu kiji

wani abu,yanzun haka ina kaduna amma gobe qarfe biyar da rabi na asuba zan taho,insha Allahu duk inda goma na safe yake ko tara na iso kano,na miki alqawarin babu abinda zai sameku,a gobe zan fiddaku daga cikin gidan insha Allahu''

Yadda ta kwana tan

a sallah haka ya kwana akan whellchair yana kallonta,cikin jikinshi yake jin wani mummunan abu na tunkaro su,yanayin data shiga kadai ya isheshi amsa,sam yaqi yarda ma akwantar dashi,da safe saiga nenwn zahariyya harda danna wai sunzo duba abdallahn,yanayi

n fuskarta idan ka kalleta dik qwaqwarka ba zaka tsammaci gana cikin mummunan tashin hankali ba,ba qaramar jarumta ta nuna ba,haka suka qaraci kallonau suka fice maryam ta bisu da ido cike da mamakin qarfin hali irin nasu

mubarak ma da yazo sam qin ya

dda abdallah yaui ayi masa wanka,abincin ma da qyar ta samu yaci,ya fahimci manufarsa yana son jin abinda ke faruwa ne a ganinta kuma bai kamata yaji din yanzu ba

πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚

yana kan wheelchair din yatsunsa soke cikin na juna yana kallon su

tsaf h

isham ya gama hada duka wani atm card takardun companies filaye gidan gonaki da na duk wani estate da plaza na abdallan ya sanya cikin wata jaka baqa ua zuge zif din,maryam yasa ta ciro babban bargunan dake ninke gefe daya kan gadon,ya jera dukkan filalluk

an dake kan gadob ya lullubesu da bargon take suka tashi kamar mutum kana ya qarasa inda abdallah yake da niyyar sauko da shi daga kan wheel chair din

qememe abdallah yaqi yarda ya sauko da shi din,idanunahi sun kada sun koma tamkar gauta saboda tsana

nin fushi da masifa,jijiyoyin kanshi dana wuyanshi sin fito rada rada,ua fahimci abinda abdallan ke nufi saidai bazaiyiwu suyi masa abinda yake so ba,a tausaahe ya dubeshi

''abdallah na sani sarai tun ba yau ba kai din jarumin namiji ne ba rago ba,kaga ab

ubuwan masu hadarin gasje ka shiga wasu da dama daga cikinsu,amma a yanzun abdallah bazai yiwu mubarka ba rayuwarka na cikin hadari,da ace yau lafiya qalau kake abdallah bazqn maka ahishshigo ba saisai na taya ka da ddu'a ko kima idan ka buqaci taimakona,n

ayi imanin da lafiyarka qalau ka fini experience na yadda zakqyi aolving case din,amma ayanzun haquri zakayi abdqllah dole kana buqatar taimako''

A nutse kuma ahankali ta tako gabanshi ta taugunna,hannunta ta sanya cikin tafin hannunshi ta mannesu tar

e hisham na gefe yana kallonsu,lumshe idonsa yayi,kimanin minti goma suna a haka sanna tace cikin tattausan muryarta

''kabi hisham mu fita daga gidan nan abdallah,ni maminka hisham dama qasarka baki daya duka muna buqatar rayuwarka,bama so mu tasa ka bama

son muyi asararka abdallah don Allah''

cikin jikinshi babu inda maganarta bata shiga ta tsinka masa jijiya ba,ina ma ace zaya iya hude baki yayi magana,da banu shakka zai tambayeta ne daga zuciyarta kalaman suka fito ko ko iya labbanta ne,koma dai y

aya ne ta sanya zuciyarsa cikin wani kundi mai wuyar karantawa lokaci guda,bai taba jin kalamai makamanta wadannan daga bakinta sai a wannan karon,a nutse hisham ya sauke abdallah daga kujerar ua ahimfidar da shi cikin bargon har a lokacin idanunshi na kan

maryam dake tsaye tana kallonsu cikin raunin zuciya,yana shirin nanndeahi ya kanye idanunshi daga kanta ya maida kan hisham,alama yayi masa da maryam,ya fuskanci me yake nufi duk da yanayin da suke ciki sai da murmushi ya subucewa hisham din.

''ka kw

antar da hankainka ba'a gidan zamu barta ba itama zata fice amma ba lokaci daya tare da mu ba don kada afuskanci me muke ciki alright

?

''kai ya gyada masa sanan ya lumshe idanunahi kamar mai bacci

tsaf ya gama nade abdallan kamqr kayan wanki cikin bargon,q

ofar shan numfaahi kawai ya bar miahi,yana nishi da qyar ya saba shi kan kafadarshi

maryam ce ta fara yin gaba,ta fita tana dube dube kamar mai neman wani abu,saida ta tabbata babu idon kowa sannata dawo ta yiwa hisham magana,ya

qaraso bakin motarahi

ya bude gidan baya ya shimfidar da Abdallah ya rufe cikin sassarfa ya zagayo

''mintina hamsin sun isa naje gida na dawo,kafin cikar minti hamsin din ki fita kamar zaki wani abu ne awaje ki dawo ki sameni a bakin titi sai na daukeki mu wuce''cikin gamauwa

ta gyada masa kai,ta juya da sauri ta koma bqngqren naau shi kuma ya tada motar cikin sauri,mai gadi ya dage masa get ya wuce

qurar motar nene kawai ta gani ta iso gin tana tambayarsu wanda ya fita daga gidan,daya dagq cikin security din daya fusu jin hau

sa yace

''abokin oga ne,oga hisham''tayi qaramin mirmushi hadi da cije lebanta,cikin salon mugunta kana ta hade ranta

''dagq yau kada ku sake barinshi ya shigo cikin gidan nan,duk wanda ya kuma kuskura ya barshi ya sake shigowa to ya tabbatar ranar a bak

in aikinshi''

cike da biyayya suka qameta tare da cewa''yes madam''

bedroom din nasu ta koma ta tattara 'yan qananun abubuwan da tasan zasu mata amfani ta dauki 'yar jaka qarama ta zuba aciki,ta koma kan sofa ta zauna lokaci lokaci tana duba agogo,ci

kar mintina arba'in da biyar da fitarsu kenan don haka ta miqe ta rurrufe duka dakunan baccin da saman ma baki daya ta fito zuwa harabar gidan

A nutse tazo fitar tata bata samu wata matsala ba don sukkansu sun ruga da sun san wace ita cikin gidan tana

sake taku na fita daga gidan zuciyarta na kuma bugawa,sai data tqbbatar ya fice daga gidan baki daya kana ta qara wani irin saurin kamar zata tashi sama,ji take kamar za'ace da ita ke dawo,ajiyar zuciya ta saki da taga motar hisham na jiranta,ba bata loka

ci ta hude ta fada kana ta maida murfin ta rufe,idanunta na rufe suka hau kan titi kana ta saki wata ajiyar zuciya,hawaye ne ya balle mata ta kalli hisham

''amma hisham mami fa

?

''

kanshi ya girgiza

''sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login