Showing 33001 words to 36000 words out of 176330 words
kwatoci da suke da su budaddu wadanda ke wa ababan hawa cikas gurin wucewa,sannu a ankali take takwa har ta isa qofar gidansu
Ba laifi akwai ahige da ficen al'umma wanda baka rasa gidan da shi sakamakon yaw
an 'ya'ya da sana'a da auke da shi,musamman a irin wanna lokaci da ake shirin tada sallar azahar masu neman abincin rana nata hada hadar siya,wanda ayanzun huwaila ce kadai keyi don inna hadiza na ganin yanzun ta girmewa haka
da ''zan wuce zan wuce''t
a samu shiga cikin gidan saboda yawan mazan dake soron suna dakon a miqo musu abincinsu,can tsakiyar yara ta hango lubabatu da daurin qirji tana zuzzuba abincin a kwano tana mita,alamu dake nuna cewa inna huwaila bata nan kenan ita aka bari da aikin abinci
n,qofar dakin inna hadiza kuwa labule ne asake qarar music na fita,kada kanta tayi cikin zuciyarta tana fadin''fidan mu,gidan mu
kenan,ya Allah ka daidaita shi kamar kowanne gida''ta cire takalmanta tashige dakin mamanta
daidai lokacin da maman ta fit
o daga dakin da suka maida kitchen dauke da farar roba da ta zuba shinkafa danya aciki,da alama girki take wato yau baban nasu yayi tsiyar kenan kowa kansa yau zai ciyar
murmushi ya subucewa maman kamar yadda ya bayyana fuskar maryamu,wani farinciki dukka
nsu suke ji wato da da uwa ba wasa ba,ta isa gaban maman tana niyyar amsar robar hannunta yayin da mamar ke cewa
''maraba,yau kece atafe,a'ah barmin kayana yanu zan kammala ai,daga ahigowarki ko hutawa baki yi ba''dole ta qyale maman ta fita waje ta wanko
shinkafar ta ta zuba sanna ta dawo ta zauna
hira sosai suke da mamar nata har ta kammala shinkafa da wake da an quli hade da salad tumatir albasa da cocumber,zasu tada sallar kenan hindatu ta shigo,murna kamar ta cinye maryam,cewa tayi itama ba zata
zauna ba bari ta fara sallar,ta yada takardun jarrabawarta saman kujera ta fita ta yo alwala
Dari biyar maryam ta fitar ta bawa hindatu da kanta taje ta aiyo musu serdine soyayye suka zauna hankali kwance suna cin abincinsu suna hira,hindatu sai santi
n maryam take
''wallahi adda maryam kada kiso kiga yadda kika koma,kin zama wata hajiya skin dinki tayi wani freah,qiba ce kawai baki qara ba,kinga kiwa da kin dada qiba tsawon nan naki raguwa ziyi''
dariya ma ta basu mama tace
''to sarkin zance,kiyi a
hankali dai kada ki qware''cikin nishadi auka kammala hindatu ta guara gurin ta dawo suka sake bude sabon babin hira,da daidai da daidai take jin matsalolinsu,sai taji dadi jin cewa basu da wata matsala mai yawa,mama tana cikin lemonta sosai don haka sai d
an abunda ba'a rasa ba,wanda shina mafi yawa kan karatun hindatu ne
duka albaahinta ta fidso ta damqawa maman tana fadin ta fadi abunda ya dace ayi da su
''um um maryamu,ke din mai hankali ce,na tabbata ko bance komai ba zaki yi duka bunda ya dace di
n''
tana lissafawa mama abunda takeso tayi din maman na sa mata albarka,ciki harda aiyqn kayan abinci ta ajjiye agidan nasu tunda albaagin nata ya tasamma dubu dari
''hmmm um''hindatu ta fadactana turo baki,maryam ta juya ta dubeta
''ya akayi bakin
ki da magana kenan''
''wlh akwai,haka kawai zaki narka albashinki ki siyi abincin gida wanda har wadancan mutanen za'aci,jamila ma da suke qaryar arziqi bata taba siyan gallon din mai ta ajjiye tace kowa yayi amfani da shi ba sai ke da kike nema da gumink
i,a jikinta kawai zaki ga samunta ita babarta da 'yan dakinsu''
_kumin afuwa kuyo maleji da wannan,a bini bashi_
*mrs muhammad ce
π
*
πππ
β
π»
β
π»
β
π»
β
π»
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*22
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
mu
rmushi maryam tayi
''akwai bambanci tsakanin jamila da maryama,mama ce mu ta haifemu uwa ta gari,mai nuna mana hanyoyin alkhairai da samun dacewa duniya da lahira,yayin da su kuma inna hadiza ce ta haifesu,kowanne mutum da kika gani yana kyauta ne da abun
da yake hannunshi yake kuma da shi na alkahairinsa ko sharri,ma'ana duk abunda mutum yayi miki na sharri to abunda ke hannunsa kenan sharrin,ke kuma kada kice za kiyi amfani da abunda yake hannunki na sharri ki maida masa da martani,nuna masa ke alkhairi n
e da ke,kada ki damu da sai wani yayi abu zakiyi,idan kina da dama kiyi din,kuma ki qudurce cewa kinyi ne saboda Allah,to sai kiga koda wanda kika yiwa din bai gani ba baki da haufi don kinyi ne domin Allah kuma ahike bada lada da sakamako''
cikin hikima
maruam ta ragewa hindatu haushin da take ji na abunda tayi shirin yi a gidan nasu,har ta rakata super market din dake bayan layinsu ta siyi cartoon na macaroni taliya da couse couse,galoon na manja da man quli,dan madaidaicin buhun shinkafa,ta siyawa maman
ta kayan tea complete,har da su cornflakes saboda hindatun
ledar da mami ta bata ta atamfofine guda biyar ciki da sabulai masu tsada sinqi biyu mamanta bawa guda biyu hindatu daya ta ware biyu zata bawa huwaila da hadiza,yara suka samu suka dauko musu kay
an hindati na biye da su yayin da maryam tayi gaba
sallamarta atsakar gidan tayi arba da baban nata,cikin fara'a ta nufeshi tana shirin tsugunawa tace
''baba,barka da warhaka''yayin da shi kuma ya tareta cikin hade fuska ba kuma tare da amsa gaisuwar ta
ba yana fadin fadi
''lafiya ,ya akayi me kika zo yi
οΌ
''
''ya salam,taya za'a raba mjtum da gidan mahaifinshi koda kuwa aure yayi ballantana ita da bata yi aurenba
οΌ
''take zantawa ita da zuciyarta
''zuwa nayi na gaidaku baba,kusan wata guda ban ganku ba''
''amma dai maryamu ina cewa.....''maganar tasa ta katse lokacin da yara suka soma ahigo da kayan suna ajjiyewa
''yaya,kai,wannan kuma daga ina
οΌ
''
''siyayyar adda maryam ce''hindatu ta bashi amsa lokacin da take sallamar yaran da naira goma goma ladan da
ko
''uwarta ta siyowa kenan
οΌ
''baban ya fada yana duban kayan
''a'ah baba,na dukka gida ne,ga wannan baba a sa mana albarka''ta ce tana ciro naira dubu biyar ta miqa masa
washe baki ya shiga yi
''ah,lallai haihuwa mai rana,maryamu dukka haka,basuyi yawa
ba
οΌ
''
mirmushi ta danyi zuciyarta fal mamaki
''basuyi ba baba''
''ah lallai wannan gidan aiki ya karbeki,to Allah yayi albarka ya bada miji na gari''ya fada yana irga kudin fuska qunshe da fara'a
ko banza taji dadin addu'ar da yayi mata,tunda dai uba
uba ne ba'a canzawa tuwo suna,sai take jin ranta yana mata dadi
ina wuta inna hadiza ta saka maryam,qememe taqi karbar atamfar da ta bata din ai ita tafi qarfin atamfa wallahi,su yanzu atamfa saidai su bayar,ita kuwa huwaila hannu ta saka ta amshe kayarta
tana tunanin gobe idan Allah ya kaimu taje kasuwar bakin rimi ta saida barta ko dubu biyar suka bata ta rage son tuni bokan uwani suka soma tatsarta,ita kuwa hindatu ta kalmashe tace gaba ta kaita,
''aikin banza aikin wofi,wa ma yasan daga inda kudin suk
a fito,an tura yarinya yawon karuwanci tana samo kudi tana kawo muku kuna karbewa an fake da gidan aiki aka kaita,a dai juri zuwa rafi da tulu diban ruwa wata rana zai fashe,ke kuma na dawo gareki munafuka makwadaiciya,an baki abu kinsa hannu kin karbe,to
ni nafi qarfin atamfa wlh ehe''
''Allah ko
οΌ
,Allah sarki,mu gani a qasa mana wai inji kare ance ana suna a gidansu,idan akwai uwar makwadaita ta duniya to kece kakarta,kwadayin ne ya sakk cusa 'yarki inda bata da gurin zama,kuma da sannu unguli zata koma g
idanta na tsamiya''ta yaue labulen dakibta ta shige tabar inna hadiza na ci gaba da babatu da sharrence sharrance kala kala
lokacin da maryam ke sallama da mama tana shirin ficewa daga tsakar gidansu zuwa soron jamila ta danno kai zuwa,ta cake ado cikin w
ata yar ubansun shadda dinkin riga da skert na rashib arziqi,qam rigar ta kamata har boobs dinta na yowa sama,babu zancan mayafi sam atattare da ita sai daurin zamanin nan da ake kira ture kaga tsiya,waya take tana taku cikin isa da qasaita tamkar wata diy
ar qaruna
''yanzun nan na fito daga gidan mu hadu kawai a ni'ima guest palace din,amma fa gaskiya wannan karon bazan kuna ba gida zan koma,ok sai na iso''daidai lokacib da ta kammala wayar,bangazar kafadar maryam din tayi sannan ta juyo a wulaqance ta qar
e mata kallo,wata mahaukaciyar dariya ta saki tana ci gaba da kallonta
''sannu adda maryam,ana nan ana fama ko,ko da yake dai....''ta fada tana kuma kallonta daga sama har qasa
''ba laifi naga kin dan canza,ko an fara bin kwalta ne
οΌ
''
waniabu ne ya toka
rewa maryam dim maqoshi,rainin hankalin ya fara isarta dukan ya mata yawa,tayi mata uwarta ta mata,batasan lokacin da ta daga hannu ta zabga mata mari ba,ba ita kadai ba hatta da hindatu tayi mamaki,tsawon shekarun da suka dauka bata taba gwada yiwa wata c
ikin maraina wayon ta haka ba
''kan can uba,kut,me nayi miki,ko ko tsabar baqin ciki da qyashi ne...''
''kika ci gaba da magana ina mai tabbatar miki zaki kwashi haqoranki a qasa,banza jahila dabba wadda batasan inda yake mata ciwo ba''
tsit tayi da bak
inta don taga irin bacin ran da bata taba gani cikin idanun maryama ba,gaskiyar hausawa dake cewa wargi ma guri shika samu
daga haka bata dada ba ta mewayeta tayi wucewarta,dadi kam tamkar maryama ta taka rawa saboda farinciki,mama ma wannan karon bata ce
uffan ba,don tsan yau da gobe tafi qarfin wasa,fitarta waje babu inda idanunta suka kai sai kan jabir dake zaune mazaunin direba,idanunshi qur bisa qofar gidan tamkar dama an sanar da shi maryam din na fitowa,mamaki da tausayi suka cika maryam,jabir ne wa
nnan,jabir ne ya koma haka,ina gayu davtsaftar jabir suka tafi
οΌ
,me yake faruwa da jabir me ya sameshi
οΌ
,mamakinta bai sake daduwa ba sai da taga ya dauke kansa daga gareta tamkar ma bai taba saninta ba
cikin matuqar sanyin jiki take takawa har ta isa bakin
titi ta tari napep tayi gida
lokacin da ta isa gidan tuni anyi sallar magariba duhu ya riga ya shigo,ba haka taso ba taso ne ta koma da wuri ta dora musu dinner din,saidai lokacin ya riga ya qwace mata,kitchen din ta nufa kai ysaye bata ko doshi dakinta
ba,mami,ce gaban gas din tana ta hidimar hada abincin,yayin da kuna dan shagwabar nata ke tayata da dauko wannan dauko wancan
''idan banda rigimar abdallah don Allah ina kai ina girki
οΌ
,nace ka...''sallamar maryam ta katseta
''sannu mami da gida,har kin d
awo
οΌ
''ta fada tana ahirin amsar aikin daga hannunta
''yauwa maryamu ya kika barosu
οΌ
''
lafiya mami suna gaidaki
οΌ
''
''kinga maruamu barmin nayi yau dai daya ki huta kema,nima na wasa qwaqwalwata ko
οΌ
''mami ta fada tana hanata aikin da take qoqarib karba
'
'ayyah,mami da wuri ma naso na dawo lokaci ne ya qwace min''
tsaki abdallah ya ja hadi da barin miqo albasar da yakewa mami ya koma ya zauna
''ki bata mami aikinta ne,idan baki bata ba ma acikin albashinta na wani watan''
yau ranta abace yake tana jinta
daidai da duk wanda ya taba tane,hakan ne yasa ta maida masa raddi
''babu damuwa,mami ina jinta ne tamkar mama na ne saboda haka babu ciniki tsakaninmu,ko ba kudi qimar shekarunta sun biya in mata aiki''
baki ya tabe kamar mace
''gaskiya ne naga kina a
msar albashinki,ai da,sai kice kin yafe''
murmushi tayi cikin gatse,sanann cikin qasa da murya ta yadda mami da ta tafi sink wanke albasa ba zata ji ba
''kada ka manta haifata akayi yadda akayi yadda aka haifeka,aiki nake kamar yadda kake wa qasarka aiki
da albashi ake biyanka,am not a servant,ciniki kuma ko tsakanin da,da uwa halas ne''
tofa baki yasan me zai fada tuni fuskar 'yan maza ta sake hadewa
a zafafe yayi niyyar maida raddi saidai isowar mami gun ya katse masa hanzarinsa,tilas ya hadiye abunda
ya qunso
''zan zuba miki albasar maryamu kafin nan ki shiga daki kin ajjiye kayan hannunki kin sauya kaya ko
οΌ
''
''to,mami na gode''maryam ta fadi gami da juyawa ta bar kitchen din,abdallah ya bita da kallon zaki san koni waye,yayin da ta daga kafadu ala
mun dake nuna masa am ready
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:52 PM] 80k:
πππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ
*ABADAN*
πΊπΊ
πΊππΊππΊ
πΊππΊπ
πΊππΊ
πΊπ
π
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πππππππ
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
ππΊππΊππΊ
ππΊππΊπ
ππΊππΊ
πΊππΊ
πΊπ
πΊ
βΆ
2
β£
3
β£
*_an karbo daga abu hurairah Allah ya qara yadda da shi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace: kalmomi guda biyu,masu
sauqi akan harshe,mafiya soyuwa agurin ubangij,masu nauyi akan mizanin auna ayyuka SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI,SUBHANALLAHIL AZIM_*
su biyu cikin falon misalin qarfe goma na dare,mami na bisa computer dinta tana tsara wata saminer da zasu gabat
ar yayin da maryam ke zaune gefanta tana tayata hira
''abdallah shiru bai dawo ba,halan yau aiki ne ya tasaahi gaba''cewar mami lokacin da take ci gaba da typing
''da alama''maryam tace
mami tadan bar abunda take ta juyo da hanklainta ga maryam
''wai
ni kam maryam meye matakin karatunki ne
οΌ
''
murmushi ta danyi
''degre ce''
''ta daya ko ta biyu
οΌ
''
dan bude baki tayi alamun mamaki
''a'ah mami,ta dayan dai''
''mai zai hana in maida ke makaranta ki samu wata degree din kan fannin kasuwanci
οΌ
,na fuskan
ci kina da amfani matuqa atattare da mu,sa'annan ina buqatar mai kula da kamfanonin abdallah mai amana kamar ke,kamfanoni wadanda ya gada da kuma wadanda ya bude daga baya,ya kike gani maryam zaki iya
οΌ
''
shiru ta danyi cikin shakku,bata son ta fiya zu
ra kanta cikin harkokin masu hannu da shuni, tana gudun wulaqanci,duk da tayi amanna cewa mami sam ba haka take ba,ta yarda da karamci da kuma son jama'a irin nata,to amma shi uban tafiyar fa wanda sam tasu batazo daya ba
οΌ
''yaya ne maryam naji kinyi shir
u ko baki da sha'awa
οΌ
''
girgiza kanta tayi
''a'ah mami,duka abunda kika yanke mami dai dai ne,amma zanso na fara sanar da baba da mama naji me zasu ce akai''
''gaskiyarki,wannan dai dai ne,amma duk da haka ki fara hada min takardunki nasan bazasu qi ba,
babu wanda zaiqi ilimi wa dansa,ina da qawa a jami'ar b u k sanate ce so insha Allau babu matsala''
''to mami na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma''
''no maryam,diya ta nayiwa kinga babu buqatar godiya''gyada kai tayi fuskarta qunshe da mu
rmushi
sallamar nene ce ta maida hankalinsu bakin qofar,nenen ce kiwa cikin doguwar riga mai zubin buba mai taushi saidai wannan nada hannaye gajeru da alamu shigar barci ce tayi
''maraba da nene''
''yauwa...mami''ta fada tana zama cikin daya daga cikin
kujerun falon dake,daura da inda mami da maryam din ke zaune,a mutunce suka gaisa
''zuwa nayi na diba yarona abdallah kwana biyu banjin duriyarsa''nene ta fada tana murmushi
mami ta rufe computer tana cewa
''abdallah na nan qalau aiki ne ya sashi g
aba,da wuri yake fita kuma bai shigowa da wuri,yanzun na zancanshi muka gama da maryam''
ta juya ta dubi maryam sai a lokacin ta gaidatakanta na sunkuye a qasa,sam batason kallon idanun natar,haka nan sai taji fargaba ta kamata,second talatin idanunta na
kan maryam din tana saqa a kanta kafin ta dauke kabta ta maida ga mami
''lafiyanshi dai qalau ko
οΌ
''
''lafiya qalau yake''mami ta bata amsa cikin jin dadin tambayar tata,wadda har ga Allah tayi tsammanin ta mata ita ne da zuciya daya
ta miqe tsaye ta
na cewa
''tiw,ni zan wuce dama abunda na shigo naki kenan,sai da safenku''
''Allah ya bamu alkhairi nene an gode ki gaidamin su zubaidan kwana biyu ma bata leqo min ba,zahariyya dama sai wani abun ya kawota''murmushin yaqe nenen tayi cijin zuciyarta tana
cewa
''bintu ki guji ranar gamuwar mu dake,gamon mu dake bazai ma rayuwarki daidai ba''
''abdallah na bani kunya wlh,dubi yadda baiwar Allahn nan ke sonshi take damuwa da shi,amma shi bashi da abun wulaqantawa sai diyarta,idan baiyi wasa ba na kusa
masa auren dole''
'yar qaramar dariya ce ta subucewa maryam
''ai mami ba'a yiwa namiji auren dole''
itama dariyar ta tayata
''to za'a fara kan abdallah''
mintina ashirin basu cika da fitar nene ba abdallan ya shigo,ya sauya shiga ba wadda ya fita
da ita bace,indai mami taga hakan to a gajiye ya dawo ya fara shiga sashensa yayi wanka ne
kan table maryam ke serving nashi yayin da shi da mami ke hira jifa jifa,ta kammala tana shirin sauka ta basu guri taji yace
''ke...mene wannan din
οΌ
''ya fada yana
nuna abincin da ido,kafin ta bashi amsa mami ta karbe zancan
''dambun shinkafa ne mana''
ya bata fuska kamar yadda yara keyi ya dubi mami
''gaskiya mami ni bazanci wani abu dambu ba''maryam ta kalli farantin don sake gano aibun dake tattare da dambun d
a ta bata lokaci a kitchen tana girkawa,dambun shinkafa ne da aka masa hadin vegtables sosai saboda ta sonshi da son gayayyaki,cabbage ne carrot zogale green beans harda gyada da wadatacciyar albasa sai dafaffen nama data yankashi qananu ta zuba a ciki,mam
aki tayi cikin zuciyarta duk da bata nuna ba kan fuskarta,ta lura tsirfar da ya tsuro da ita kenan cikin yan kwanakin nan
''amma kaifa dazun kace shi kake sha'awar ci ayi maka
οΌ
''
''am sorry mami na,dambu ayanzu is too heavy na cishi na kwanta ai sai
ya kashe miki ni''
dariya ma ya bata,bata zaci konai ba don yaune ya fara