Showing 51001 words to 54000 words out of 176330 words
aikata ya mamayeta,ita so tayi aci mutuncin maryam ita kadai a kuma koreta ta bar gidan,kasa daukar irin kallon da yake matq tqyi tqyi qasa da
idanunta
muryarsa a kausaahe cike da sautin fushi yace''wanne la'a nannen Allahn ne ya mana wanna qazafin,ko da yake mami kince salma ce,amma nayi mamki mami,kin san halina ciki da bai,kinsan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba,me yasa lokaci g
uda wata can zato ta rushe kyakkyawar fahimtar da mukayi shekara da shekaru da gina ta,kai cina da har yau,ban kubuta daga zarin zan aikata zina ba daga gun mahaifiyata''ya fada yqnq girgiza kai jijiyoyin kansa na tashi,sai jikin mqminyayi sanyi,tabbas bab
u kyau gaggawar yarda da abunda baka da yaqini,balle abdallah da maryam,babu wana bata san halinsa ba,dukkansu tasan ne zasu aikata da wanda,ba zasu aikata din ba
ganin da salma tayi mami na shirin yarda da abdallan ita ta tashi a tutar kunya ya sanyata s
ake,zaqalqalewa
''ni ba la'a nanniyar Allah bace,kuma na gani din ne da ban gqni ba ai da bazan......''
bata qaraahe maganar ba taji quma abakinta,abdallah ya jefeta da ruwan robar dake hanjunahi wanda ko rabi bai sha ba,aka kuma yi sa'a ya sauka a bakin
nata,ta dafe lebunan nata wani azabar zugi na ratsata,take lebunan suka fashe,bayan sun kumbura sunyi suntum cikin daqiqar da bata wuce talatin ba
hakan baiwa Abdalla ba ciki fushi ya yo gunta,da sauri mami ta shiga tsakaninsu tasa hannunta tana tokare q
irjinsa don iya inda tsawonta yake kenan tana turashi da baya
''ki barni mami na lalata shashan bakin da bai iya komai ba face sharri da qazafi wa mutane''
''ka dakata abdallah,nutsu don Alla banason shashanci''mamin ke cewa,tasan halinshi sarai,bai fiya
sairin fuahi ba amma idan ya fusata din komawa yake kamar mahaukacin zaki
kusan minti biyar mamin na artabu da shi
''na nutsu mami,amma na bata minti goma ta tattara dukkan wani abu nata tabar gidan nan,wallahi wallahi ta sake muka sake haduwa da ita sa
i na
nakasta ta,banza shasha sha kawai,don ina rufa asirinki,sau nawa nake kamaki da syrup da capsule cikin jaka,shine har kike da bakin yiwa wani qazafin zina,to idan baki bar gidan nan ba nan da minti goma ba nine zan zamo mutum na qarahe da zaki tiwa qa
zafi a rayuwarki,bindigata zansa na harbeki ki mutu kowa ya huta''
cikin huci ya juya a sukwane ya fice,da sauri maryam tayi gaggawar jaye qafafunta badon tayi hakan ba kadan ya rage ya take mata dogayen yatsunta
bibbiyu ya dinga hada matattakalar har ya
gama sauka daga benan,abida ce da saddiqa tsaye kowacce cikin sleeping dress tayi tsuru tana sauraron abinda ke wakana a saman,zuciyar kowaccensu tayi fari jin an kori salma suna ganin tamkar aiki aka rage musu
wani banzan kallo ya bisu da shi ba tare da
ya furta komai ba ma suka watse
cikin mintina qasa da goma salma ta hada komatsanta tana kuka wiwi mami na lalkabrta ta shiga motarta ta fice agidan,ranar sai gidan ya wuni shiru kowa na dakinsa,mamin ma haqura tayi da fita asibitin ranar don tsoron kada
ta tafi wata fitinar ta taso,jin shirun yayi yawa abdallah bai sake shigowa ba ya sanyata tattaki da kanta zuwa bangatenshi,don ta san cewa ba lafiya,don komqi akayi bazai iya fita bai gqyq mtq ba,to tabbas yana cikin dakinshi ne
A qurya ta sameahi kwanc
e daidai yayi rigingine kan gadonshi,shigowartaya sanya shi miqewa ya zauna
''me kake haka har yanzu baka fito ba ko karyawa baka yi ba ga azahar ta gota biyu da rabi fa yanzu''
''bana jin yunwa mami''ya fada cikin rashin walwala,sai kuna ya dago ya dube
ta
''mami ina fatan bakiyi fushi da ni ba,na kasa sukuni tun dazun''
dama ta sani a runa,yanzun haka bacin ran da ya gqni kan fuskarta ne ya sashi kasa fita,tun yana qarami haka yake,baya juriyar ganin bacin ranta
''zan iya yin fushin da kai dai na haqi
qa matuqar baka gayan gaskiyar abunda ke faruwa ba''
''zan gaya miki mana mami,mami kiss ne kawai,wallahi bayan haka babu komai,kuma ko shi din ma haushi ta bani,kallon dan iska take min''ya fada bayan ya riqe hannayen ta cikin marairaicewa
dariya yaso b
awa mamin amma sai ta gimtse don ba muhallinta bane
''don tana maka wanna kallon idan banda rashin dabara da wayo ta hakan zaka wanke kanka ta fahimci na gari ne kai
οΌ
''
''am sorry may mami,nayi kuskure''
a nutse ta dinga masa fada sanna ta rufe da fadin
''idan irin hakan ta sake faruwa raina zai baci fiye da bacin ran daka gani yanzu,don ban yarda asabi Allah ba,duk son da nake maka zan iya ajjiyeshi gefe na hukuntaka hukunci mai tsanani,kada makamancin hakan ya sake faruwa akan ko wace ma indai ba mata
rka bace''sai maganarta ta qarshe ta bashi kunya ya dan sunne kai
dariya ta danyi
''da nema yau kuma nice akejin kunya''dariyar shima ya tayata
sai kuma ta hade cikin seriouse tone
''sannan abdallah,lallai lallai ya kamata kayi aure indai kana son hank
ali na ya kwanta yadda ya kamata,ka fidda mata cikin masu qaunarka''
qasaitaccen murmushin nan nashi ya saki
''relax mami na,insha Allahu kwanan nan zan sanyaki farincikin da kika dade kina fata,zan kawo miki mata ta har gida nan kusa,amma fa abida da sa
ddiqa kowacce ta wuce gidansu,don wlh mami bazan iya auran kowaccansu ba''
''naji,saddiqa dama gobe tace zata tafi,abida kuwa dole ayi haquri sai an samu visa,zata sake ko sati uku ne tare da mu''
''shikenan mami,zan wa abokina magana harkarsu ce''
qeme
me yaqi fita yace zai je ko ina ba sai ya tabbatar ta gama hucewa haka suka wuni a gida gaba dayansu
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:53 PM] 80k:
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ
*ABADAN*
πΊ
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
ππΊππΊ
ππΊπ
πΊπ
π
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊπ
πΊππΊπ
πΊππΊ
ππΊ
π
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
π‘
*_home of expert and perfect writers_*
βΆ
3
β£
2
β£
*Allahumma ya i
mada man la imada lahu,ya sanada man la sanada lahu,ya giyasa man la giyasa lah,ya karimal afwu,ya hasanat tajawuz,ya khaahifal bala'a,ya azimar raja'a,ya aunaddu'afa'ah,ya munqizal garqa,ya munjiyal halka,ya muhsin,ya mujmil ya mun'im,ya mifdil,antal lazi
sajada laka sawadul laili wa nurun nahaar,wa dau'ul qamar wa shu'a ushshams,wa da wiyyul ma'i wa hafifushshajar,ya Allahu la sharika lak,ya rabbi ya rabbi ya rabbi,Allah ka shiga lamarin mutanen qasar burma,Allah ka shiga lamarin jama'ar musulmin duniya b
aki daya don sayyadis saqalain*
ππ½ππ½ππ
Qarfe goma saura na dare mami ta shiga dakin nata,har ta gama shirin bacci tana kwance tana jiran wayar abdur rahim da yace ta jirashi kada tayi bacci zai kira ta,da sauri ta miqe tana maida hulart
a da santsin gashinta ya sa ta sabule,mamin ta dan bita da kallo qauna da tausat
yinta suka lullubeta ganin ta takure ta kasa hada ido da ita
gefan gadon ta qaraso ta zauna kusa damaryam don ta dafa gadon bayanta
'.dago ki kalleni maryamu,mamanki ce
fa''sai taji qwalla na shirin zubo mata nauyi da kunyar mamin takeji,gefe daya hauhi da tsanar abdallah na takura zuciyarta
''ki kwantar da hankalinki abdallah ya yimin bayanin gaskiya,ba laifinki bane laifinsa ne,kuma nayi masa gargadi insha Allah bazai
sake faruwa ba kinji,ki i gaba da kame kanki maryam kamar yadda kike,daraja mace da mutuncinta yana tqfin hannunta,ruwanta ne ta riqesu su zame mata abun alfahar ruwanta ne ta wargaza,bazan so wani abu ya shafi mutuncinki ba maryamu don tamkar amana kike
a hannu na,ko bayan haka ma unajinki har cikin zuciyata,haka za bazan iya yafewa abdallah ba idan ya maki wani abu da ya sabawa shari'a da mutuncinki,duk abinda kuma nayi nayi ne saboda kare martabarki,ina fata kin fahimce ni
οΌ
''
gayada kai tayi tana share
hawaye
''na gane mami,na kuma gode Allah ya qyara girma da lafiya''
wayar abdur rahim ta katse 'yar hirar da mamin ta fara janta da shi don ta saki jikinta,ganin maryam din taqi dauka yasa mamin ta dago wanda ke kiran
''bari in abku waje kinga ma
shikenan ya fanshe ni sai ya qarasa lallashin,ki gaisheshi sai da safe''ta fadi tana miqewa cikin dariyar zolaya,kasa amsawa tayi ta sunne kanta saboda kunya mamin na dariya ta fice
hira suke abinsu sosai irn ta masoya kamar sun shekara da sanin juna
''maryam ya kukayi da abban,nasan dai an bani dama ko
οΌ
''
ta dan zaro ido tana fadin
''wa ya gaya maka,abdul irin wannan zumudi haka''ya marairaice murya
''maryam bani so in rasaki ne inaso a bani dama koda kudine a kawo''
ajiyar zuciya ta saki
''abdu
l dole dai ai mu danyi haquri ko,tunda yanzun dai kaga azumi saura kwana bakwai,mu bari bayan sallah idan Allah ya kaimu sai ayi dukka abinda za'ayi''
''wa ya gaya miki azumi na hana kai kudi,akwai cousing dina safiyya hudu ga azumi aka kai kudin aurenta,
so pls maryam ki barni na kawo kudin idan yaso bayan azumi asa mana ranar aure na qagu ki zama tawa,baki san ya nake ji ba duk lokacin da na kalleki ko naga kin fita a matsayin budurwa ba mata ta ba,bani da wani iko a kanki''
dariya ta saka
''yaushe
ma kake ganin nawa ne abdul''
''ina iya ganinki mana da idon zuciya''
''shikenan yanzu mu bari zan sanar da mami na,duk yadda ta kama zaka ji''
da qyar abdur rahim ya barta bayan ya cikata da dad'ad'an kalmomin qauna
ππππππ
Su hudu ne cikin
lafiyayyar motar da idan ka shiga ba zakayi tsammani tafiya akeyi ba sai idan kaga kuna wulga gurare,mami ce da maryam a baya sai Abdallah da driver a gaba
mami cikin shigar leshi dinkin buba orange wanda yasha adon lemin hreen,takalmi jaka da mayafi duk
ka toomatch masu dan karen tsada da kyau,ba qarya mami gwanar iya ado ce,ko cikin mata masu shekarunta da wuya ka samu irinta goma,shi yasa sam sai ka rantse bata haifi abdallah ba,zakayi tsammani yayarsa ce kawai
maryam ma cikin cikin kwalliyar take amma
zamu iya cea kwalliyar jiki don babu wani make up a fuskarta,material ne pich da kwalliyar sea green,tayi adon takalmi mayafi da fashion na dan kunne duka kalan sea green,ba gwanar jaka bace hakan ya sa wayarta ce kawai riqe a hannunta,abdallah dake gaban
mota yake ta faman zuba mitar shi kam da an barshi bazaya je ba,ba gun zuwanshi bane idan ba kamawa tayi ba,sanye yake da shadda light blue dinkin tazarce da yaji aikin hannu na maza dan ubansu da baqar hula,takalmi sau ciki baqi da agogo,kallo daya zaka
masa ka tabbatar kudin da jikin nashi ya lanqwame ya ishi mai qaramin qarfi jari
''ayita aure gab da azimi barna tayi ta afkuwa''ya fada yana yarfar da hannunshi wanda ke daure da agogon ruwan gold''nikam dai wallahi kam duk wanda yamin aure a irin wa
nnan lokacin alhakin a kansa''
''baka da kunya ka maidani kakarka,yaro duka ka gama mitarka,dinner ce dai si kaje,minti nawa anyi an gama,hajiya mai gado idan da halacci ba zaka mata haka ba,ita tayi yayenka abdallah,ba qaramib sonka take ba''
ya dan
waigo yq dubi mamin
''ayyah mami me ya kawo maganar yaye na''ta dago shi qwarai wai shi baya son raini,dariya ta saka
''to meye kowa ma an masa yaye har ni kaina''kadan kadan take bashi labarin quriciyarsa gidan hajiya mai gadon,yana son ji amma baiso w
ani ya ji masa ya raina shi don haka ya canza topic din
''mami,cikin kwankin nan nake son kawo miki dear ta gaidaki,so kuma bata nan sunje umarar azumi,ni kuma na qagu mami in yi wani motsi''
murmushi ne ya subucewa mami
''ummm,abdallahhh......,yaus
he ka zama haka
οΌ
yaushe sonta ya maka irin wannan kamun
οΌ
kai har naji ina sonta data iya sato zuciyar birkitaccen yarona haka ta farat daya''
murmushi yayi hadi da lumshe idonsa,ya jinginar da kansa jikin seat din motar yana tunata yana jin wani yanayi na s
higarsa,mami ta sosa masa inda yake masa qaiqayi
''dis luv inside of me is strong mami,there ar no boundaries that it can hide''
Kasa daurewa mamin tayi har sai da ta dan daki kafadanshi ta baya dariya ta kamata,ringin din wayar maryam ya katsesu,abd
ur rahim ne,kamar ko yausheta kasa dagawa saboda kunyar mami shi kuma bai fasa kira
tsaki abdallah yaja yana fadin
''du Alla a kaahe wannan culculator din ya damemu haka nan''
mami ta kalli maryam
''daga kiranki maryam,ba mai jinki hirar mu muke''
tsa
ki ya kuma j''idan ba zata daga ba asauketa ta kammala wayar ta biyo mu daga baya kota koma gida''
''shut ur mouth,oya ina jinka,muyi maganar dake gaban mu''cewar mami
Minti ashirin tsakani suk iso gun dinner din,ita dai maryam rava idanu kawai take
don bata saba zuwa ire iren guraren ba,bata da wannan rawar qafar sam,da dai su jamila ne su lubabatu tof babu na biyunsu
uwar taron dakanta ta fito ta taresu
''masha Allah hajja bintu ina kika samu kyakkyawar diya haka,ko surukar taki ce''
murmushi tay
i ta wauwaya ta kalli maryam da abdallah dake bayanta,sai taga sun mata kyau din kuwa tamkar wasu couples,abinda bata taba kawowa a ranta ba ta jishi lokacin,sai taji tana fadi cikin zuciyarta ina ma da gaske ne haka dinne,ya waiwaya ya danqarawa maryam ha
rara sai akayi sa'a suka hada ido,ya dan matso gab da ita har tana sheqar qamshinsa kana yayi qasa da murya kamar mai fada mata abun arziqi
''yi gaba mamalama,kin wani jera da muta ne kamar sa'anninki,salon 'yan jarida su ganmu tare ki samu daukaka ni kun
a ki bani kunya'',itakam tsoronshi take don neman tsari take da shi hakan ya sanya batare ce masa komai ba tadan ja da baya da yake ya fita sauri tuni ya dan zar tata
mami ta kalli hajiya mai gado
''diyata ce ita din ma,amma surukar naku na zuwa insh
a Allahu,don shekaran jiya yaron naki ya min albishir,ya gama ruwan idon nashi da bani kunyar gun iyayen yara''
''a'ah,a qyale yaro na,ai lokacinshi ne a barshi ya zaba ya darje,ai ya cancanci yin hakan''
''um um kada ka ki fasa masa kai''
''ba zancan f
asa kai sai tsabar gaskiya''da daddan hirarsu irinta qawaye suka iso gurin da ka tanada don baqi na musamman irinsu
anyi kiran iyayen amarya suzo su nuna tasu karar don haka mami ta miqe,ta dubi abdallah dake ta faman shan qamshi idanunshi na kan waya
tunda sukazo
''bari muje nida martmyam liqi yanzun zamu dawo,kaima ya kamata ka qarasa ku gaisa da amaryar''
''ina zan iya tashi an cika guri da sakarkarun 'yammata marasa kamun kai,duk inda ka motsa suna kallinka kamar wasu mayu''
''kaji da shi dai,ka
llo kuma kayi abun kallin ne dole a kalleka,dukka abokan ango na gun stage suna liqi kaja ka zauna bayan kaima abokinka ne''mamaki ya cika maryam,yadda taji ana tababa da shi kan bazai je ba tayi zaton ma bai sanshi bane
''mami ni bazanje in kalli mat
ar wani ba don nima babu mai kallarmin tawa''
''haka za'ayi naka bikin kenan kana nufin''
''ko za'ayi mami ba zata zo min da irin shigar da amaren yanzun suke ba,sai babballata in zubar''
hade rai mami tayi
''to ni kuwa bazaka balla 'yar muta ne ba ka
barmu da jidali ba ka canza tunani''
murmushi ya subuce masa ganin yadda mamin ta hade rai kamr ma ya riga da ya aikata
miqewa yayi ya karbi jakar hannunta yana dariya
''Allah ya barmin ke mamata ni daya,muje in rakaki,Allah ya huci zuciyar hajiyata
''
''hutsu ne abdallah''maryama ta fada cikin zuciyarta,suna hada ido ya daka mata harara ya kuma hade rai qyam tamkar bashi yake murmushi yanzun ba
a baya suke binta har suka isa atge din,ya miqawa mami jakar yana fadin
''gashi mami,ayi liqi a hank
ali''
''haba handsome,girman mami ne ai ta liqa ko nawa take so,babu ji tunda tana da kai''maryam da abdallah suka kalleta lokaci guda don mami bata ji ba tuni da kutsa ciki,wani sakaran kallo yayi mata gami da jan tsaki,ita dai maryam gaba tayi tana qoqa
rin bin sahun mami tana fadin cikin zuciyarta
''kin debo ruwan dafa kanki''
ji tayi an riqo tsintsiyar hannunta gam ana janta,babu shiri ta waiwayo abdallah ne tuni har ya fara tafiya,tilas ta saita wa kanta hanya ta bishi a baya tamkar raqumi da kal
a,don idan tayi tirjiyar bin nasa zata iya zubewa a qasa don da sauri yake jan nata
bai saketa ba sai da suka iao teburin na su kana ya sakar mata hannu hadi da yi mata nuni da kujerar data tashi dazu a kai,tsareta yayi da idanunshin nan masu kaifi
''sit
,dake aka hada kutingwilar zuwa na nan,shine kuma duka zaku fashe ku barni zaune ji daya kamar yaron mayu,ki zauna ki kula da ni har mamin ta dawo ta karbeki,daga nan ma idan club zaki wuce ke ya shafa''
Tuni hawaye sun cika idanunta,bata ce masa komi
ba ta zame ta zauna,shi kuma yayi tsaye hannayenshi harde bisa qirjinsa yana qarewa gun kallo tamkar mai neman wani
matashin saurayi ne yake dosowa gurin,kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewa ya gogu cikin duniyanci,sannu a hankali yake qarasowa
har inda maryam din take,shigowarsa gurin kenan idanunahi sukayi tozali da ita,totally ta gama yi masa fatanshi daya 'yar hannu ce,zai iya kashe mata ko nawa ne matuqar zai samu hadin kanta,ta bayan kujerarta ya zagayo yasa dukka hannayenshi ya dafe makar
in kujerar
''hello babe...''
gabanta ne ya yanke ya fadi,har ta kasa jiyowa taga