Showing 81001 words to 84000 words out of 176330 words

Chapter 28 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

20

zaune a muhallinta suka mutane suka dinga zuwa suna gaisawa da taya su murna,saidai babu daya cikin yammatan da suke son Abdallah data gani a gun,da al

amu kuwa hansu zuwa gun akayi,kodai iyaye ko yan uwansu,qarfe aha daya aka taahi kai tsaye mami tace su quce bangarensu maryam taje ta kwanta ta huta.

Yana iya hangota cikin dan qaramin hasken fitilar barci takure saman gadon yayin da shi kuma ke kwance

saman sofa din dake cikin bedroom din,a haka sai kayi tsammanin bacci suke saidai ko kadan kowannansu da duniyar daya shiga ita nata tunanin har yau kan amsar tambayoyinne da takeson bada su a gobe batasan ta samu failure,ya miqe ya ciro paper cikin ma'aj

iyar da yake ajjiye takardu yar qarama dake can qasan gadon wanda sai ka danna wani abu take iya bullowa ya hada da biro ya dawo yayi kwanciyar rigin gine ya soma rubutu ajiki.

a qalla mintina goma ya samu kyawawa yana ruutun,a hankali yaji jikinsa ya s

oma masa nauyi tamkar an dora masa dutsen dala,ya sake yunqurawa da nufin daga hannun nashi a karo na biyar saidai ko alamar motsawa baiyi ba,wasa wasa sai magana ta zama babba,ya bude bakinsa da niyyar yin magan amma sai yaji kamar super glue aka saka aka

manne fatar lebansa ta sama da qasa saidai.

Cikin mintina da basu gaza ashirin ba komai nasa ya daina motsi face idanunshi da kunnuwansa dake iya jin abinda ke motsi da qara baya ga haka babu wani abu dake moruwa,tuni takarda da biron hannunshi suka su

lale suka fadi qasa,hannayen suka zube gefe guda,gasu a jikinsa amma ji yake kamar an cire masa su su da qafafunsa.

*mrs muhammad ce*

πŸ‘‘

πŸ“šπŸ“šπŸ“š

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺



πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–πŸŒΊπŸ’–





πŸŒΊπŸ’–



πŸ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–

Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

πŸ’‘

*_home of expert and perfect writers_*



β–Ά

4

⃣

1

⃣

πŸ‘‚πŸΎπŸ‘‚πŸΎπŸ‘‚πŸΎ

πŸ‘‚πŸΎ

*shin ka/kina da labarin mutune guda bakwai da zasu shiga inuwar al'arshin ubangiji ranar da babu wata inuwa sai tasa

?

,ranar da rana zata matso daf da kawunun al'umma ta dinga tafasa qwaqwalwansu

?

,to ku matso kuji daga bakin da baya qarya*

*_An

karbo hadisi daga abu hurairah R A yace:Manzan Allah S A W yace: mutane guda bakwai Allah zai saka su cikin inuwarshi,ranar da babu wata inuwa sai tasa_*

1

⃣

*_shugaba adali_*

2

⃣

*_da saurayi matashi ko matashiya da suka rayu cikin bautawa Allah mai girma

da daukaka_*

3

⃣

*_da mutumin da zuciyarsa ke rataye da masallaci,ma'ana wanda ko yaushe jira yake yaji anyi kira zuwa sallah ya tafi masallaci_*

4

⃣

*_da mutane guda biyu da suka so junansu saboda Allah,don Allah suka hadu kuma suka rabu donshi ma'ana ba

don wani harkar banza ba ko duniya_*

5

⃣

*_da mutumin da mace ma'abociyar kyawun sura tayi kiransa zuwa yin zina ko aikata wani fasiqanci yaqi yace mata ni ina tsoron Allah_*

6

⃣

*_da mutumin da yayi sadaka ya boye yin sadakar da yayi har hannun hagunsa ba

isan me damansa ta ciyad kota bayar ba_*

7

⃣

*_da mutumin da ya tunq girma Allah a kebe shi kadai idanunsa suka zubda hawaye saboda tsananin girma da tsoro Allahn_*

Duk yadda abdallah ya kai ga son motsa sassan jikin nasa bun ya faskara,ya yarda ya kima

saddaqar da cewa wani mummunan abu ya gama faruwa da shi,tamkar wanda dannu ya danneshi haka yake ji

babu tsumi babu dabara sai Allah haka yake ta faman ambata

sam bata san halin da ake ciki ba,saidai gaba daya ta nemi bacci a idonta ta rasa wanda ta

alaqanta hakan da damuwar dake cunkushe cikin ranta,tayi juyi kan gadon yafi a qirga,ba zata iya tantance lokacin da bacci yayi gaba da ita ba

πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚

qarfe biyar da rabi na asuba ta farka daidai lokacin da wasu masallatan suka kai tsakiya a sal

larasu,da ddu'ar tashi a bacci ta farka a bakinta kamar yadda ta saba sannan ta lalubi wayarta don jaska dakin da babu wadatar haske a ckinsa sakamakon kashe qawayen da akayi,sai data lalubi makunnin ta kunna sanna ta sauko daga gadon,a hankali idanunta su

ka sauka kan abdallah wanda zuwa lokacin ya rufe idanunsa gam zuciyarshi kawai ke aiki,ya gama amanna cewa tashi ce ta zo qarshe abinda yake jira kadai shine fitar ruhinsa daga gangar jikinsa,kamar ta wuceshi sai kuma taga bai kamata ba tunda dole dai ya t

ashi yayi sallah.

ta tsaya saitin kanahi cikin muryar dake nuna alamun yanzu aka tashi daga barci tace

''ka tashi kayi sallah lokacin sallah yayi,anyi asuba''jin ahiru ya sanya tayi zaton ko bai farka bane,amma wannan wace idiyar kwanciya ce haka

yayi

ya yada hannun

?

,sai ta dan duqa tana bubbugar filon da ya dora kanshi tana sake fadin

''anyi sallar asuba an kusa idarwa''

jin muryarta ya sanyashi bude idabun nashi a hankali tamkar mai tsoron ganin wani abun,sai ta dan zuba masa ido ganin yadda qwaya

r idanun tayi jazur,a sanyaye ta juya ta ahige toilet ta daura alwala ta fito ta tada sallah,ganin har ta idar bai tashi ba ya sanyata tayi zatob ko komawa ya sakeyi ne

kanshin ta kuma komawa ga mamakinta sai taga idanuwanshi biyu

''lokacin ta zaya fit

a alfijir na ahirin ketowa''

''bazan iya taahi ba maryam duk yadda naso hakan,ji nake kamar an daddaureni,ki taimakamin in tashi''abinda yake aon fada kenan saidai ina bakin yayi nauyi,ci gaba kawai yayi da kallonta,saita tsinci kanta itama da kallon nash

i,lokaci guda kuma taji jikinta ya mutu murus,komawa tayi bakin gadon ta zauna ta inda take iya fuskantarsa suna ci gaba da kallon juna

kusan mintina talatin suna a haka har shida da rabi

''rana fa ta fito ba zakayi sallar bane

?

''sai taga ya maida idan

un nashi ya lumshe,hakanan gabanta taji yayi wata mummunan faduwa,sai ta kasa zaman ta qarasa inda yake,abu na farko data fara lura da shi shine hannunshi da ya zamo qasa tunda ya farka bata ga ya gyara kwanciyarshi,ta sanya hannunta tadaga hannun taga ko

zai gyara saidai tan sakinshi ya biyo ta,ta sake gwadawa har sau biyu babu banbanci

batasan lokacin data furta

''abdallah lafiya kuwa kake

!

''cikin tsorata da rudani

idanun nasa dai taga ya kuma zuba mata tamkar zai hadiyeta,sai ta shiga kiran sunansa a

jejjere saidai ko guda bai amsa mata da shi ba

Lokacin da zuciyarta tayi mata hasashen abinda ya samu abdallahn jiri ne ya debeta ta zube a nan tana fadin

''me ya sameka

?

,me ya sameka don Allah abdalkah,ka bude baki ka gaya min''

inda zai iya da ya ma

ta maganar amma babu iko

sai kuma ta zabura ta miqe da gudu ta fice a sashen nasu tayi bangaren mami

da sauri nene ta toshe bakin zahariyya da ta dan saki ihun farinciki ganin shigewae maryam bangaren mamin a hargitse

''nene Allah yasa ya sambade la

hira''

''ko bai mutu ba to yana kan hanyarshi ta mutuwar''ta fada tana duban zahariyya

''don da ya kammla wucewar da ihun kururuwatsu kadai ta ishemu albishir''

saman mamin ta haura kai tsaye ta fara bubbuga qofar dakin nata ba qaqqautawa,tunda taji b

ugun ta tabbatar ba lafiya ba,ga zatonta ma abdallah dinne,tunda ta tashi dama takejin jikinta ba normal ba yadda ta saba jinsa,da hanzarinta ta murza muqullin ta bude qofan,kama hannun maryam tayi wadda taga tsagwaron rashin hankali kwance kan fuskarta

'

'lafiya maryam ne ya faru

?

''

fara jan mamin tayi

''mami zo kiga abdalkah,zo ki ganshi mami...''ta qarashe cikin rushewa da kuka

''Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alil hazna iza shi'it sahla''addu'ar da mami keta maimaitawa kenan

fili da zuciyarya cikin sassarfa take biye da maryam suka gifta su nene dake labe jikin window dinsu suna jiran jin abinda zai biyo baya

Yadda ta barshib hakan suka sameshi,a raunace mamin ta isa gaban kujerar ta zube,gaba daya rungumoshi tayo tana kir

an sunanshi,ita din ma saidai kallo da ido daga bisani ne hawaye ya gangaro daga ianunshi saboda ganin mamin nashi na kuka haiqan babu kuma baki ko hannun lallashinta,kjran sunan Allah kawai sike daidai lokacin da nene ta shigo dakin a rude kamar gaske

kallon da abdallahn yake mata ya sata tasha jinin jikinta,saidai ta nasar kawai don babu baki ko qarfin yin wani abu a kanta,tana ma sa masa tsammanin wuta zai qara zuwa lahira,

wani kallo ta jefi maryam da shi tare da zabura ta kai mata duka''me kika yi

masa muguwa azzaluma''

mami ce ta tare dukan

''haba nene''cike da haqiqancewa tace

''wlh ban yarda da yarinyar nan ba bintu,daga aure jiya jiyan nan ace mutum ya kamu da irin wanna lalurar

?

,anya ba mayya ya aura ba bintu

?

''

''me ya kawo duka wannan zan

can nene,muyi ta lafiyarsa ma mana''

kuka ta dinga yi haiqan tana fadin duk daren dadewa asirinki sai ya tonu shegiya mayya daga jiya zuwa yau kin lashe kurwar yaro saboda tsabar shahara a maitadaga bisani saiga zahariya da adnan,abun nasu ma sai ya zama

over acting,don mamin ce ke masu suyi shiru

πŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒ

Ranar basu kwana gidan ba cikin asibitin amalam aminu kano suka kwana,cikin kwana biyar babu irin gwajin da basuyi masa ba,saidai komai ya nuna normal yake qwaqwalwarsa spinal code dinsa da zuc

iyarsa kai har hanta da qoda duka sai da suka duba saidai result sai yazo komai normal

A lokacin zaka tausaya wamami da maryam idan kaga yadda suka koma,duk da qoqarin boye cutan da ake saboda yanayin aikin abdallan,shi kanshi ya rame saboda tashin hank

alin da yake gani cikin qwayar idanun maminshi da maryamu

cikar shi sati guda suka koma gida mami ta bada umarni ayi musu visa cikin satin zata fita da shi,kafin nan daya daga cikin manyan security dinsa mubarak wanda yake babba ne cikin masu tsaron laf

iyanshi da hisham amininshi ke taimaka su mamin gun kula da abdallah,kamar daga shi zuwa toilet da sauransu,mutum ne mai matuqar kirki mubarak kamar hisham,har albashinmubarak din mami tace zata dada yace baya buqata,babu irin alkahirin da abdallah baya mu

su don haka bashi da abunda zai sakq masa da shi sai ta wannan hanyar,haka hisham babu komai tsakaninsa da mamin sai fatan alkhairi da sa masa albarka.

Batun fitar da abdallahn da za'ayi yayi masifar daga hankalin nene ta soma zaton kada fa a kaishi waj

en ya samu sauqi haj bintu ta dawo musu da hannun agogo baya,don nene ta gama tsorata da irin kallon da abdallan ke binsu da shi duk lokacin da suka shigo duba shi

bata bata lokaci ba ta koma gun malam na hayi ta zazzage masa bakin jaka tare da qarin buqa

tunta

πŸŒ²πŸŽ„πŸŒ²πŸŽ„πŸŒ²πŸŽ„

Misalin qarfe sha daya ne na safiya suka gama waya da mama ta kirata don jin jikin abdallahn,tana shirin ajjiye wayar taga har sha daya da minti goma,mamaki da fatan Allah ya sa lafiya maryam din ke tayi jin shiruchar yanzu mami ba

ta leqosu ba

mawuya cine qarfe takwas ta gita bata shigo ta dubasu ba,haka nan ba zata tafi ba sai mubarak da hisha amininshi sunzo sun gyara abdallah ita kuma maryam din ta shirya breakfasy ta gyara bangaren nasu ta miqawa mamin break din ta bawa abdal

lan da kanta sannan taje tayi wanka,to yau kam duka mubarak ne yayi hidimomin shi kadai ita kuma tayi saura,da taga shabiyun rana ta kusa sai ta sanya hijabinta taga gwara taje ta duba mamin,don ta tabata ko bata da lafiya ba zata iya zama ba sai tazo ta g

ansu

sai da ta sake leqawa bedroom din abdallah ta taddashi har yanzun baccinsa yake don ko break baiyi ba,a haka fes da shi sakamakon kyakkyawar kulawa da yake samu,sai ka rantse lafiyanshi lau,kyau dac kwarjininsa duk suna nan sai 'yar rama da yayi,ta

usayi yake bata sosai,ta sake girmama kadaitar zatin Allah,dan adam ba'a bakin komai yake ba,yanzu kake mutum yanzu kake ba mutum ba,duk kuwa kyau asali dukiya da kake da shi idan yaso sai ya maidaka abun Allah sarki

ta share hawayenta sannan ta fito daga

sashen,sai data tsaya ta tabbatar ta qulle ko ina don yanzun bata yadda da kowa ta barshi daga shi sai abdallah idan ba mami ko mubarak ba

Ba zato taji ansha gabanta,da sauri taci burki tana dubanshi,adnan ne ya tsaya yana qare mata kallo kamar wani ts

ohon maye

''babe ina zaki haka

?

''duk wanda ya fito daga tsatson nene yanzu haka ta tsaneshi bata qaunar ganinsa,hakanan taji bata qaunar koda hada inuwa guda da su,tsaki ta ja kana tabi ta gefansa da niyyar rabeshi ta shige,sai ya sake binta ya tare hanya

r yana fadin

''haba baby ki tsaya ki saurareni mana,nifq sonki wallahi nake ki bani dama mu huta abinmu,da kyaunki da komai kin tattare kanki guri daya kin batawa kanki lokaci wajen jiyyar wancan nakasashen,kada ki cuci quruciyarki mana baby,ki bani hadin

kai ni kuma na miki alqawarin biya miki kowacce iriyar buqata kike da ita''.

dan ya tsanta ta nuna shi da shi

''ka bani hanya na wuce malam ko baka ji ba''

''common baby ki.....''

batasan lokacin da ta daga hannu ta tsinka masa mari ba cikin zafi da

huci tace

''ni ba irin matan da kake tnani bace,hakanqn ni ba butulu bace irinku,nakasashen mijina ya fiye min kai da yan uwanka kai da duka ma

danginka,daga rana irin ta yau kada ka kuma kuskuren tarata da banzayen magnganu irin wadan nan,banza shashaah

a bani hanya na wuce''

''ni kika mara,wallahi zaki san ba'a ja da ire irenmu,zaki san kin sanya hannunki kin mari adnan''

''na marekan,sai me,na mari banza na mari wofi

?

''ta fada bayan ta masa wani kallon banza ta kewayeshi ta shige gun mamin

Baaba uw

ani kawai ta taras itama tana qoqarin fitowa akitchen da alamu wanke wanke ta gama,suka gaisa a mutunce tana tambayarta mai jiki,ta amsa mata da sauqi kana ta tambayeta mamin

''hajiya tana sama,nima tun jiya da yamma rabina da ganinta,tace dqi da yammaci

n jiya kanra na mata ciwo zata ta kwanta,to tunda ta hau kuma har yanzu bata sauko ba''

''bari na dubata to,Allah yasa lafiya''inji maryam wadda ta fara taka benan

''ameen,kice ina mata sannu''inji baaba uwani dake ficewa daga sashen

''zata ji''

knoc

king tayi ya kusa goma kafin taji cikin murya kamar ta fada fada ance waye ne

?

''a sanyaye tace maryam ce''

ta kusa minti talatin kafin ta bude qofar bedroom din

mamin ce fes da ita ikin lace da alama bata dade da gama wanka ba saidai babu make up a fuska

rta kamar yadda taje a hade kamar wadda aka aikowa da labarin mutuwa ,kusan zata iya cewa bata taba ganin kwatankwaci yanayin a gun mami ba,kullum cikin fara'a take.

fuskar maryam qunshe da murmushi ta dan rusuna tana gaida mamin,duk da adaqile take amsa

mata bata kawo komai cikin ranta ba,tayi tsammanin ciwon kan ne ke damunta

Shiru ne ya ratsa tsakani bayan ta gama gaishetan

''wai lafiya malam kin min tseye a gaba na

?

''ta fada cikin sautin fushi

a tausashe tace

''ah.....dama ji nayi shiru baki shig

o ba,shine nae bari inzo in duba ko lafiya,ga abdallah ma baici abinci ba saboda rashin shigowarkin''

''banga damar shigowar bane,ni baiwar idan ubanku ce,siyata kukayi da zanta muku bauta,ok....na ganoki ma,wato bani da lokaci sai naku ko

?

,to kada Allah

yasa ahima yaci abincin kinibabbe,ruwansa ne daga yau kada ya kuma cin abinci a duniya,ni da zaya mutu ma da bai hutar da muta ne ba,mtswee aikin banza shine kika zo kika taahi mutane suna cikin hutawatsu,to wannna ya zame miki na qarshe da zaki sake takom

in saman ma,duk abinda kuke buqata ki tsaya daga qasa har sai na sauko,kinji na gaya miki''

daga haka ta ja qofarta ta bame ta bar ta anan

tamkar gini haka maryam ta koma,mafarki ne koko gaske,almara ce ko tatsuniya ce,ji tayi wasu hawaye masu dumi na

sauko mata,batasan sanda ta tsinci bakinta na furta

''ya Allah kada ka jarrabemu da wata jarabtar ta daban bayan wadda muke ciki,ubangiji idan ka saka mana wannan cikin sabuwar karrabar da zaka mana ba zamu iya jurewa ba nida abdallah,ya Allah sassaucinka

muke nema''bibbiyu ta dinga gani a haka ta bar bangaren zuwa nasu,tafi qarfin minti talatin zaune afalonsu tana rasgar kuka

wanna wace iriyar jarrabar rayuwa ce da suka wayi gari da ita da safen nan,anya ma kuwa da mami tayi magana

?

,mamin abdallah fa,mai

tattali da qaunarshi akoda yaushe,mai son ganin farinciki da walwalarsa,mamin da tasha bata amanar abdallah,tasha gaya mata bata da kowa sai shi ta kula mata da shi bata so ta rasashi yadda ta rasa mahaifinsa

cike da tantamar ba mamin bace ta dauki way

arta ta kira number dinta don ta tabbatar,saidai dagawar farko ta kuma cin karo da muryarta tana fadin

''wai nikam sa'arki ce maryam

?

,lallai na sakar miki da yawa kinga gadon barcina,sai na dauki tsatstsauran mataki a kanki kamar yadda nene tace''jin suna

n nene kawai data ambata ya sata dauke wayar daga kunnenta tana kiran sunan Allah,tabbas akwai wani abu na daban dakeaon kunmo kai

''Allah na roqekakoma meye ka kawoshi da sauqi ya arhamar rahimeen''ta qarasa fada tana rufe fuskarta da tafin hanunta hadi

da rushewa da kuka

kiran sallar la'asar ya fargar da ita abdallah data bari,da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login