Showing 126001 words to 129000 words out of 176330 words

Chapter 43 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

41



wa,wani kyau yaga ta yi masa cikin baqi da ja din pakistan riga da wando,duk da rigar har gwiwa take amma gefe da gefe an tsaga shi wanda hakan ya sake taimakawa wajen fidda sharp dinta,ta nanade kanta da baqin dankwali da ya sake fidda hasken fatarta mura

ran,sau tari yakan raya cikin zuciyarsa kodai ta hada jini da larabawa ko indiyawa

Darensu na shekaran jiya yake tunawa har yau daren yaqi fita daga tunaninsa,wani babban matsayi ya bashi don bai taba samun dama kamar ta ranar ba,har hanzu idan ya tun

a yadda take shafa masa maganin sai yaji taikar jikinsa ta zuba,taushi ta laushin tafin hannunta kamar auduga,itakam ta bada hankalinta ne kan girkinta saboda haka bata lura da kallon da yake mata ba,saidai lokaci lokaci tana jin gabanta na faduwa ko taji

tafiyarta na hardewa

ta fito daga kitchen zata ja ruwa a rijiya,a wannan karon kam ta kamashi dumu dumu yana kallon nata,saboda wani tsabar qarfin hali irin na abdallah tare suka hade rai hakanan kowa ya janye idonsa daga kan dan uwansa ta ita ta wuce

bakin rijiya shi kuma ya bude shafin gaba na qur'anin hannunsa ya shiga sabuwar sura suratul jinni bayan ya gama suratu nuh daga sama yaje gangarowa qasa surori kadan suka rage masa ya hada saukarsa don yau yake son kammalata gobe juma'a za'ayi sadaka wa

mabuqata

ta debi na farko cikin rijiyar mara katanga don kowa yasan yadda bakin rijiyar qauye yake a bude take kuma daf da qasa ta kai rumfar girki ta sake dawowa ta zuba cikin botiki duk yana satar kallonta ta gefan ido don baiso ta kuma kama shin ku

ma gashi bai gajiya da kallon nata,ta daga botiki kenan santsin lakar dake bakin rijiyar wadda ta jiqu da rya ya debeta,luuu gaba daya ta tafi tayi kan rijiyar

''maryam''ya fada cikin wata iriyar gigitacciyar murya idanunta a rufe tana ambaton sunan Allah

,zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje da kanta,ta gama saddaqarwa yau kam sai yanda Allah yayi da ita don ba makawa cikin rijiyar zata yiwa masauki don

qafarta ce ta fara gjrdewa wani zafi ya kuma ratsata ta saki qara,jikin mutum taji ya fada gab

a dayanta kana aka janyeta gefe,a mamakance ta bude idonta saboda ta gama bayarwa zata jita tsamo tsamo cikin ruwan rijiyar ne,sai kuma ta sake haduwa da wani abun mamaki da yaso sandarar mata da jinin jikinta

Abdallah ne tsaye bisa duga dugansa kan q

afafunshi kamar yadda yake a da,ta dan janye jikinta daga gareshi da fuska mai dauke fal da mamaki tabi tsawonsa da kallo,tabbas shine abdallah ne,the gentle giant man din nan,abdallah dai abdallah mami,kasa daina kallonsa tayi don har yau tana jin kodai m

afarki ne daga irin mafarkan da saba yi,baya dai ta sake ja saidai wani zafi daya ratsa qafarta ya sata durqusaqa tana fadin''wash''wasu hawayen farinciki suka aulmiyo daga idanunta

Cak taji ya dauketa baki daya bai direta ko ina ba sai kan kujerarsa

da ya tashi ya ajjiye ta a kai bayab ya dauke alqur'anin dake kai ya maida man window din dakin inna wuro,reshe sai ya juye sa mujiya a maimakon abdallah dake kallonta a sace dazun,yanzun ita ke binshi da kallo baki sake kuma kai tsaye

Gabanta ya dawo

ya durqusa baiko damu da rairayin dake gurin kada ya bata masa kaya ba,ya kama kyakkyawar qafarta da yake tunani anan ta gurde din

matsawa wani guri yayi sannan yace

''nan ne



''bata fahimci ma da ita yake ba don ta tafi cikin duniyar mamaki,saida yasa b

akinsa ya hure mata brown oily eyes dinta da suka qara sheqi sakamakon sabuwar qwallar dake ciki tana yawo,bata kai ga fitowa ba

''kada ki cinyewa mero ni mana,ina ne gun ciwon



''ya tambayeta yana sake duban qafar tata

''abdallah ka warke



ka fara taf

iya fa abdallah ko baka gani ba



''kyakkyawan murmushi ya saki kana ya dago ya dubeta kana ya sake maida kansa ga qafarta

''na sani kuma na gani,tun shekaran jiya na warke maryam,ranar da kika kwana a qijina,ranar da tsoho alhaji ya baki magani kika shafan

da hannayenki masu albarka''

qwallar ta subuce ta zubo ta ido daya,muryarta so cool tace

''amma abdallah kaci gaba da zama a maysayin mai lalura



me yasa ka boye samuwar....''

''shshsh



''ya fada bayan ya sa qwayar idonshi cikin nata

''akwai dalili,

sannan yanzun ba muhallin nganar bane''

kai ta girgixa ya gane so take ta fake ne ta masa borin nan nata,don haka ya rigata ta hanyar matse inda ta gurde din,ai kuwa tuni ta saki abinda takeso ta fada din ta maida gurbinsa da fadin

''wayyo qafata''tare d

a runtse ido ta kuma damqe hannun abdallahn,sake surarta yayi daga kan kujerar ya maida ta kan rabarmar kabar dake

shimfide kusa da kujerar ya ajjiyeta,zama yayi ya miqe qafafunshi ya jawo qafar tata kan cinyarsa,idanu a warwaje tace

''me zaka yimin haka

abdallah,kada ka fama min ciwo''ta fada a tsorace don tasan irin wannan gurdewar ta taba irinta taja bakinta tayi shiru taqi gayawa mama,sai data yi kwana uku maman ta lura,ta takura mata sai taje an duba mata,da taje ashe targade ne,taqi yarda a gyara mat

a qarshe sai da maman ta kaita da kanta,ai kuwa har suma tayi kafin a gama gyaran din qafar ta gama yin tsami,shi yasa yanzun ma ta tsorata kada taje irin wancan ne

Bai tanka mata ba kamar yadda bai kalleta ba ya kama gurin,kamawar farko ra saki qara

tayo jikinsa baki daya ta nanade shi saboda azaba,kasa ci gaba yayi saboda irin riqon da tayi masa ma baki daya ua zare masa lakar jikinsa,tuni ta fara hawaye tana roqonsa kada ya sake taba mata wlh zafi

shiru yayi yana kallonta yadda taje faman kuka kama

r yar baby,sai kukan ya bashi sha'awa saboda duka eye lashes dinta sun jiqe sa hawaye sun sake zara zara

Tazara ya sake bata ya faki idonta ya kuma damqar ciwon,ta qara shigewa jikinsa gumi yana karyo mata tare da wani sabon kukan,har cikin xuciyarsa

yake jin kukan amma yasan idan ya qyale mata gaba zafin da zatajin sai yafi haka don ya gane targade ne a qafarta,qarfinsa yasa bai qyaleta ba sai da ya gyara,tuni ta jiqe sharkaf da gumi da hawaye harda majina,ya kalli fuskarta sai yaji dariya tazo masa d

uk fuskar ta hada ja,miqewa yayi ya nufi daki ta bishi da kallo don har yau mamakin takawarsa bata saketa ba,ya fito da handkherchief mai kyau da kansa ya dinga goge mata fuskar har sai da tayi tsaf kana ya gyara mata zaman ya miqar mata da qafarta ya jing

inata da bango

gabanta ya dawo ya zauna dirshan,ganin yadda take jefa masa harara ya sashi daukar qur'aninsa ya bude yaci gaba da tilawarsa a zuciya

sai ta tsinci kanta itama tana qare masa kallo,ko ta ina abdallah cikakken namiji da samun irinsa sai

an tona,kyau zubi da tsarinsa kadai ya isheshi ya godewa ubangijin daya qerashi

Komai nashi daidai yake,babu abunda yayi kodan ko yawa a tare da shi

''ya dai yammata akwai magana ne



''taji ya fada,kunya ta kamata ta rasa na cewa sai kawai ta soma

qoqarin tashi,hannunta ya riqe yana fadin

''take it easy''sannan ya maidata ya zaunar

''idan kin tashin me zakiyi,ina kuma zaki je



''

''girki na dora kuma ban kammala ba,gashi yamma na dada yi''

sai ua dinke girar sama da ta qasa kana yace

''tab,ai ku

wa yai saidai kada kowa yaci abinci cikin gidan nan,babu girkin da zakiyi''baki ta saki tana kallonsa yadda yabi ua hade rai tamkar wanda ta zaga,sai taga ya ajjiye qur'anin bayan ya saka alama ta inda zai tashi ya nufi rumfar girkin,kallo ta bishi da shi,

sai ta tsinci bakinta yana furta

''ahamdulillahil lazi bini'imatihi ta timmus saalihaat kana ta limshe idonta tana sake gaskgatawa da miqa dukkan imaninta ga Allah,shine mai kun fa ya kun,yadda duk yakeso haka yakeyi haka kuma za'ayin''

Tana kallonsh

i yana tura wutar iccen tuni hayaqi ya bulbuleshi sai gashi ya fito da sauri daga rumfar idanu jajur hawaye na diga,dariya taso kamata,dama idan banda rigimar sa ina shi ina wutar icce,wataqila ma tunda gake bai taba zuwa gaban murhu ba balle ayi batun gir

ki,yana goge qwallan yana fadin

''kai kai kai,yanzu baby haka kike shaqar wannan abun kamar kanka zai juye,gaskiya daga yau kin gama''dauke kanta tayi kamar bata jishi ba bayan kuma ta gefab ido take satar kallonshi

Baikai ga zama ba nero tayi sallam

a ta shigo gidan,turus tayi ta tsaya tana kallon abdallah,gani take kamar ba shi ba,sam ta kasa dauke idonta daga kanshi

''wannan kallon fa



''yace da ita sai ta sunne kai wai ita kunya,qarasowa tayi tana fadin

''yaushe ka warka abdullahi



''

''kinga ga g

irki can inna ta bari jeki qarasa tukunna kya zo muyi hirar''

miqewa tayi ta isa nufi cikin rumfar tana sake mamakin warkewar tasa har ta gaza boyewa tana zaune a rumfar girkin tana waiwayensa

hakanan maryam taji wani abu ya takoreta,ta dade tana qar

yata kanta akan irin abunda takeji idan mairo ta rabi kanta da sunan kishi ne saidai a yanzu a yadda abun yaqi barinta ta tabbatar cewa kishin ne

baifi saura awa daya a kira magariba ba inna wuro ta dawo gaggauce don bata kaiwa magariba a unguwa

itam

a dai da mamakin take kallona abdallah dake tsaye kan maryam ya harde hannayensa a qirji yana kallonta kamar wanda aka baiwa gadinta

''bawan Allah



,Allah mai iko,kaine a tsaye da qafafunka



''

kyakkyawan murmushin nan nasa ya saki kana ya qarasa ga innar

yana karban daurin buhu dake hannunta ya sa mata shi daga gefe

''ni ne inna wuro''

tana kame da bakinta tace

''bari malam yazo yaga ikon Allah,Allah gwanin iyawa ya amshi addu'ar bayinsa,kai Allah mun gode maka,sannu bawan Allah,Allah ya qara lafiya''

''ameen ameen inna''

ta dubi maryam dake zaune

''ita kuma wannan fa,meron ta barwa girkin kuma



''

Ya juya ya dubi maryam da ta dan hade rai don tasan yanzun innar zata sako wani abu kuma daban,ita kam gani take sam bata sonta yanzun tafi son abdalla

h da mero kawai

dariya ta tasowa abdallah,bai iya hadiyeta ba sai da ya dan dara

''inna targade tayi,Allah ma ya soni ya rufan asiri saura kadan tayi iyo cikin rijiya''

cikin tsoro innar ta zaro ido

''rjiya



,garin yaya ni 'yasu mairamu



''sai ta sake yi

n fuskar shanu ita ala dole sai ta nuna haushi take ji,sai abdallah ne ya bata amsa

''ina tsammani santsin lakar can ne,ba shiri inna na qarasawarkewa naje na tarota''

''to Allah ya rufa asiri''ta fada tana dan masa magana da ido,shi ma ya maida nata ams

a ta hanyar langabe kansa da daga hannunshi alamun ban haquri

mairo ko dake bakin wuta cikin zuciyarta take cewa

''shi kuma baya tashi warkewa sai ranar da wani abun zai sameta,haka ma fa bakinsa yayi''

(hmmm,abdallah na maryam)

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Washegari da hisham suka wayi gari cikin garin ni'ima cikin kuma gidan inna wuro,dukkansu tare suka zauna karin safe,kowanne ka dubi fuskarsa zuwa zuciyarsa cike take da farinciki mara misali,hira suke a tsakaninsu har suka kammala,maryam ta kwashe kayan

ta gyara gurin

tsoho alhaji yace

''to alhmdlh abdullahi,kaga dai yadda ubangiji ya karbi addu'armu cikin lokaci qanqani''

kanshi a qasa yace

''hakane,malam naga darasi cikin rayuwa sosai,naga abunda da can bansan da shi na sai da Allah ya jarrabace

ni da lalura,rayuwa abar tsoro ce haka duniya ma abar tsoro ce,darasi ne babba na koya cikin lalurar da Allah ya jarabceni da ita''

''gaskiya ne,dama wani abun baka saninsa ko gane shi sai ka shiga wata jarabtar,Allah ka bamu ikon cinye jarrabawarsa''

dukkaninsu suka amsa da ameen

tsoho alhaji ya dubeshi

''yanzu sai shirye shiryen tafiya gida kenan''

murmushi ya saki kana yace

''banjin barin garin nan da wurwuri haka,garinku ya yimin malam sosai,yaci sunanshi ni'ima,bazan taba mance wa da garin na

n cikin tarihin rayuwata har abada,baya ga haka neman aure nake malam cikin garin naku''

dum kunnenta taji gaba daya yayi tamkar ba zata iya ci gaba da sauraren komai ba,sai ta rasa gane a wanne bigire take a zaune



,duk wata laka ta jikinta ta daina a

iki,so take ta tashi ta bar dakin amma haka ya gagara

''a cikin karkaran nan tamu kuwa



''tsoho alhaji ua fada cikin mamaki,cike da tabbatarwa ya gyada kansa

''eh malam''

*mrs muhammad ce*

👑

📚📚📚



🏽



🏽



🏽

[5:05pm, 10/4/2017] Huguma

👑

:

💖

💖

💖💖💖💖

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺

💖💖💖💖💖💖

🌺🌺🌺🌺🌺🌺



💖🌺💖🌺



💖🌺💖



🌺💖



💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

🌺💖🌺💖🌺💖



🌺💖🌺💖



🌺💖🌺



💖🌺



💖

© *HASKE WRI

TERS ASSOCIATION*

💡

*_home of expert and perfect writers_*





5



5



*Daga abdullahi dan mas'ud Allah ya yarda da shi yace:Manzan Allah S A W yace ''duk wanda yayi nuni(fara aikatawa) akan wani aiki na alkhairi yana da kwatankwacin ladan w

anda ya ya kwaikwayeshi(ba tare da an tauyewa kowa cikinsu daga ladansa ba''(haka yake ga wanda ya qirqiri wani aiki na sharri kuma wani koyi da shi shima yana da zunubi kan duk mutum daya daya aikata irin aikin kwatankwacin zunubin wanda ya aikata aikin)*

*An karbo daga abu ayyubal ansari Allah ya yarda da shi yace:naji Manzan Allah S A W yana cewa''duk wanda ya raba tsakanin uwa da danta,Allah sai ya raba tsakaninsa da masoyansa ranar qiyama'',a wata ruwayar ta abi musa yazo da lafazin ''Allah ya la'

anci wanda ya raba tsakanin uba da dansa,da dan uwa da dan uwansa''*

tuni ta miqe sabida kunnuwanta ba zasu juri jin abinda zai fada ba,saidai kafin ta kai ga ficewar har tsoho alhaji ya sake tambayarsa

''wacce yarinya ce abdullahi ka gani d

in,yar wajen wace



''

''ba wata bace ba malam,ta gida ce,mar........''

cike da gaggawa ra qarasa ficewa daga dakin don tuni zuciyarta ta riga ta bata sunan wadda zai kira din,dakin inna wuro ta wuce ta haye can quryar gadonta gami da cusa kanta tsakanin f

ilalluka

''me abdallah yake so na masa ne da zai fahimceni,wacce hanya zan biyo masa da zai fahimce ni



ta yaya abdallah zai nemi auren wata



watan ma mero



eh tasan bazai wuce ita din ba don duka take takensa ya gama nuna mata haka''tambayar data ringa nana

tawa kanta kenan

tana nan kwancen kimanin minti talatin da wani abu ta jiyo maganarsu,muryar inna wuro ta fara jin

''Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku,ni dama tuwo na maina ne,da kai da itan duka daya ne a guna''

wani irin abu taji ya tsirg

a mata da bata taba jin makamamcinsa ba,babu shakka kishi bala'i ne,bata sake gasgata kanta cewa tana kishin abdallah mai tsananin zafi ba kamar ranar,take ta yankewa kanta daga yau bata sake kwana a garin tunda ta gama iya abunda zata yi din,cikin qanqani

n lokaci zazzabi mai zafi ya rufeta

Duk yadda inna wuro ta so fa fito ta qiya,gani take duka basu sonta,har,hisham wani irin haushinsa take ji,ko kowa zai goyawa abdallah baya ai bai kamata shima yabi yarima yasha kida ba,kwanciyarta tayi kan gadon ta

na jin yadda jikinta ke fudda hucin zazzabi ta kuma qi yarda ta gayawa kowa,sallar magariba da isha ne kawai ya tasheta daga gadon shima din sai taga innan ta fita a dakin

🍂🍂🍃🍂🍃🍂

Daga alwalar sallar asuba ta hada da wankanta baki daya ta dawo d

akin inna ta canzq kayan tunda ta debo kayanta ganin hisham yazo tasan dole tare da abdallah suke kwana bazaiyiwu kuma tayi ta ziryar dauko kaya ba shi yasa ta debo duk abinda take da buqata

abin sallah ta saka tayi raka'atanil fajr wadda falalarta Ma

nzan Allah S A W yace tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi,bata ko jira tayi azkar ba ta koma gadon ta sake nadewa,tanajin inna wuron na tada ta tayi banza da ita duk da idanunta biyu,ta baza kunnuwanta ne a tsakar gida ko zataji fitarsu abdallah ta

shiga dakin ta dauki abinda ya mata saura

Tun tana azkar tare da tsumayin fitowarsu har wani dan qaramin bacci ya sacera sabida rashin isashshen bacci da bata samu ba jiya

Da addu'a ta tashi,ta zabura ta zauna kan gadon ganin rana ra gama fitowa

sosai,ta,duba agogon dakin qarfe sha daya har da rabi na safe,takaici ya lullubeta,duka lissafinta iwar haka ta tsufa a kano,ta soma yaye bargon jikinta cike da takaici

sallama aka yo cikin tsakar gidan,kunnenta ta kasa sosai don tantance da gaske ne ko

irin mafarkan da ta saba yi ne,kamar kuwa ansan tantamar da take yi aka sake rangada wata sallamar

Habawa ai duk tsawon gadon inna wuro mai rumfa batasan lokacin data dirgo daga kai ba kana ta kwasa a guje,bata dire a ko ina ba sai tsakar gidan,saura

kadan suci karo da MAMI wadda ke tsaye tana son sake yin wata sallamar ga zatonta masu gidan basu jita ba

Zubewa tayi gaba daya a gaban mamin ta saki wani kuka mai cin rai,bata taba tunanin ganin mamin na a irin wannan lokaci ba dama zuciya kuma a kus

a,ita ma mamin kasa daurewa tayi ta durqusawa ta dago maryam din hawaye na fita daga idanunta,rugume maryaman gaba daya tayi a jikinta cikin wani irin yanayi,daidai lokacin da inna wuro ke fitowa daga bayi dauke da buta a hannunta tana mai amsa sallamar do

n tana cikin bayin yake jiyo ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login