Showing 168001 words to 171000 words out of 176330 words

Chapter 57 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

46

kanta,bata damu ba hasalima jin dadin hakan takeyi don ya sanshi farin sani,ba macen data isa ya tsaya yana kallo

nta to din me ita din halaliyarsa zata hanashi more kallonta,bayan ya gaya mata ba sau daya ba basau biyu ba kallonta ba qaramin jefashi yake cikin nishadi da sabuwar duniya yake ba

Sai data lakuce masa hanci sannan tace ''mr kallo''

''na amince''ya

fada yana murmushi,ta tura masa plate din abincin wanda ta cika da lafiyayyen alkubus da yayi kyau ya taahi yayi shar,da kwanon tangaran mai kyau dauke da miyar taushe wadda tasha tantaqwashi da naman kasuwa da manshanu ita kuma ta jawo wani jug na plastic

tare da wani kwanon tangaran da abun zuba sugar ta bude ta fara hada garin kwaki da suger da soyayyar gyada,cak ya tsaya yana dubanta ita kam batasan yana yi ba har wani tsinkewa yawunta yake kamar wadda taga wani abin dadi,sai da ya kira sunanta sannan t

a dago kai tana amsawa,ganin yadda fuskarsa tayi kicin kicin ya sanya jikinta yin sanyi,don ko kusa bata qaunar ta zama sanadin bacin ransa

''amma yaya mukayi da ke kwana ukun da suka wuce a jere.....ranar farko kika cemin sha'awarsa kike na barki k

ika ci kayanki,rana ta biyu kika ce min bakinki ba dadi da kika ci na jiya kinji dadi bana so amma sabida farincikinki na barki,shekaran jiya harda magiyarki da qwallarki na barki kici,jiya kuwa da kika tashi sai kika shaqeshi kika cika cikinki taf da shi

kafin ma na dawo,da na dawo saboda tsabar qoshin da kikayi loma daya na abinci kika ci kika fara amai,sanann yauma dai a gain kice min shi zakici

?

''sai ya girgiza kai

''bazai yiwu ba maryam,sai kace wanda ake ciwon yunwa a gidansa,aiko wani ke neman taima

ko a guna bazan bashi garin kwaki ba bare iyalina''tuni qwalla ta cika idonta,ga qoshi ga kwanan yunwa,tana son ta kyautatawa abdallah amma wlh idan taci abincin ji take kamar numfaahinta zai dauke,ba bata lokaci hawaye suka fara silmiyo mata,idonshi ya ru

ntse don babu abinda yaqi jinin gani irin hawayenta

''ya salamullahi,daga magana sai kuka

?

''

''Kinga matsonan muci abincin ko yaya ne,idan muka gama sai ki gayan meye damuwarki,idan ma duka nau'ikan abincin ne baki so ki lissafa irin wadanda kike so kona

wacce qasa ne in sha Allahu ni abdallah mai nemo miki ne kinji dear,amma wanann hawayen qona min zuciya yake''ya fada yana daga mata hannu alamum ta taho,ba musu ta matso jikinsa tana goge hawayen kanta a qasa,cike da son ta faranta ransa tasa cokali ta f

ara ci,loma biyu kadai tayi taji wani abu ya dunqule mata sai amai tun tana yinsa tana fidda abincin da taci,da garin kwakin da tasha dazun har ya koma bata iya harar da komai,gaba daya hankalinshi a tashe yake gani yake shine sila da ya takura ta,haka ya

dauketa cak yagyarata ya gyara gurin,bai samu nutsuwa ba sai da yaga bacci yayi awon gaba da ita,duk son da yakewa alkubus din da qyar ya iya cin yanka uku

πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚

cikin baccinsa ya dinga jin qamshin girki,da sauri ya farka ya mutstsuka ido,ya d

uba gefansa bata nan,kenan ita ke aikin girki a kitchen qarfe tara na safe

?

,da azama ya diro daga gadon ya doshi kitchen din

tsayawa kawai yayi yana kallonta tamkar ba ita ta gama sheqa amai jiya ba

?

,tayi kwalliayarta tayi kyau kamar ka saceta ka gudu

,ta matse cikin wata riga mai roba wadda iya qibarka iya yadda zata kamaka iya kacinta qauri an mata tsaga daga gabanta daga qaurin qasa zuwa gwiwa,ta gyara gashinta yayi kyau sosai,ji tayi kawai an rungumeta ta baya sai ta saki yar qaramar dariya

''kasan

kuwa irin tsoron daka bani

?

''

''nima ai kin bani tsoro baby,ke da baki da lafiya ina ke ina kitchen fisabilillahi''waigowa tayi suna fuskantar fuskarta qunshe da murmushi juna yana zagaye da qugunta,ta shafi sajensa kana tace

''ras nake jina shariky,ina

mai tabbatar maka idan za'a saka tsere sai na wuceka''dariya ya saka ya sumbaci kumatunta

''babu musu don naga alama,wai baby meye sirrin ne

?

''ya fada yana kashe mata ido,itama maida masa martani tayi

''name fa

?

''

sai da ya jujjuyata ya sake kallonta s

annan yace''gani nayi sai wani kyau kike qarawa,fatankin nan har tafi tawa laushi,kumatunki kamar kin boye qwai,brown oily eyes dinki kamar an kuma diga musu zaiba da oil,ke tsaho ne kawai har yau na fiki ba.....''kasa qarasa maganar yayi saboda manna baki

nta da tayi cikin nashi,sai da ta dan birkitashi sanann ta cire tana duban bakin nasa

''wannan bakin nawa kada ya cinyeni''sake janta,jikinsa yayi yana dariya

''Allah am seriouse,meye sirrin''

''matso na gaya maka''sai tayi dage don duk tsahonta abdalla

n ya fita ta kai bakinta kunnensa ta shiga jero masa

lumshe ido ya dinga yi yana saurarenta tare da sake shigewa jikinta,banji komai ba face kalmarta ta qarshe

''kaga kuwa kaine sirrin''dukkansu murmushi suka saki mai,hade da dariya dariya,ya kamo fuska

rta ya hada goshinsa da nata shima yana mayar mata da martanin kalmomin,sun kusa kwashe a qalla minti goma a haka har ruwan shayin da ta dora ya fara qonewa sannan ta ankara ta zame jikinta da sauri tana cewa

''you see,shi yasa idan ina abu mai muhimmanc

i banso kazo ka riskeni,don sawa kake ina mantawa da kowa da komai ciki harda kaina''shi ya qarasa hada kayan karin tana tayashi da wasu abubuwan kana suka,yi wanka suka shirya don yaune ranar da abdallahn ke raba tallafi gidan gajiyayyu da asibitoci wanan

n karon kuma tare zasu shi da mami,maryam ma ta kafe itama sai taje don baza'a samu ladan babu ita ba

*********

tafe suke cikin motar gwanin sha 'awa don baka banbance waye danta,tsakanin abdallah da maryam,shike jan motar maryam na gefansa,yayin da

motar security dinsa biyu ke gabansu biyu ke bayansu,yawanci indai tare da maryam ne cikin fitarsa bai yarda driver yayi tuqi wai don kada a gane masa ita,mami na baya tana duba wasu takardu jefi jefi suna hira da abdallah

''yauwa mami''

''uhmmm''taj

e dashi kanta na kan takardunta ,tasan tunda ya fadi haka tambaya gareshi

''dama wani lokaci mata na daina cin abinci sai wani abun daban

?

''bata bawa tambayar tasa muhimmanci ba,don a zatonta shirmene kawai irin na abdallah din haka tace da shi

''kamar y

aya kenan

?

''

''mami maryam,na rasa meke damunta,safe rana dare garin kwaki mai tsamin nan,abinci saidai ta dafa min kawai ni nayita narka,jiya da na matsa mata sai taci amai tayi mami,ni tausayinta ma nake ji''

wannan karom saida ta dago ta dubeta,kunya

kamar tayi me ta kama hannun abdallahn a sace ta matse cikin nata

''wayyo hannu na diyana''ya fada yana yamutsa fuska kamar qaramin yaro,da sauri ta sako hannun nasa taja hijabinta ta lullube fuskarta

''kada ka sake matsa mata kan cin abinda bataso,ka ba

rta''cikin damuwa yace

''amma mami gari fa

?

,bazai mata komai ba

?

''

''eh yana yi ne zata daina nan kusa''ta fada zuciyarta tamkar qanqara,addu'a take cikin ranta Allah yasa hasashenta ne zai tabbata

Ya sake rausayar da kai

''amma mami ni gani nake

kamar yana tsotse jinin mutum ko ruwa jikinsa''

''ba daya,nace maka zata daina ne fa''

''to Allah yasa''ya fada cike da hope,donshi har ga Allah abun na damunsa,gani yake wata cutar ce ta samu maryam dinsa,shi yasa ya sanar da mamin nufinsa idan ya gaya

mata akwai wani maganin ta bata,kasa cewa komai maryam tayi,lallai ta yarda Abdallah gabuntar dan fari da tabarar auta na tabashi sosai,a hankali mamin tace

''ki kula kawai da kanki maryam,duk lokacin da kika ji wani sauyi a tattare da ke kumin magana,ka

da kuce zakuji kunyata,ni mamarku ce baku da kamata''kanta aqasa ta amsa da to,shi kuwa gogan cewa yayi

''ni dama maganin kawai kika rubuta mata mami Allah na tsani naga tana shan garin kwakin nan''murmushi ta dan saki

''bakasan komai nada qa'ida ba,ba'a

rubutawa mutum magani kai tsaye,indai kawai kuka ga alamun canjin wani abu ko matsala to ku sanar da ni''

''to mami''ya amsa mata yana ci gaba datuqinshi

a gurin ajjiye ababen hawa suka yi oarking duka motocin nasu,mami ta riga fita saboda isowar sh

ugaban asibitin din ya tarbeta,abdallah na qoqarin fita maryam tayi saurin riqoshi da qarfi har sai da ya dawo ya zauna don bai zata ba,ido ya kashe mata guda daya yana fadin

''ya akayi baby da magana ne

?

''kicin kicin tayi

''yanzu shariky don kawai ina c

in garin kwaki sai ka gayama mami don Allah

?

''ido ya dan zaro

''to menene don mace kina shan gari dear na

?

,na tsammaci ciwo ne shi yasa na gaya mata ko zata rubuta miki magani''

''kada ka sake don wallahi ka bani kunya''kiss ya bata a goshi kana yace

''

is ok,afuwan my sister''dariya ma ya bata tana zaune ya zagayo ya bude mata side dinta ta fito bayan ya sake gyara mata zaman hijabinta,duk yama tasa gun tsayawa don gaba daya atsarge yake,gani yake wai kallonta ake,security din ma da suka saba binsa a bay

a yace suyi gaba su zasu biyo bayan nasu,don kada wai su dinga kallonsu ta baya

kimanin su goma sha biyar suka kutsa kai cikin asibitin,daki daki suka dinga bi suna raba taimako,kudade ne masu tsoka suka dinga bayarwa tare da biyan kudin magunguna ga

duk wanda ya kasa biya,wayyo Allah,kada kaso kaga abun tausayi kala kala,talakan qasata yana cikin wani hali,talauci yunwa fatara jahilci duka ya tattaru ya narke a kansa,wasu har kukan dadi suka dinga yi,maryam kuwa tuni zuciyarta ta karye,tunvtana share

hawayenta a boye har ta saka kuka saboda azabar tausayinsu,abdallah ne ya fara jin sheshsheqarta,gefe ya janyeta hankalinsa a tashe

''sai da nace kiyi zamanki a gida dear kkka ce sai kinzo bayan ba lafiya ce da ke ba,sai na maida ke gida idan ba zaki iya

jurewa ba''da sauri ta goge hawayen tana danne kukan din batason ya maida ta din,ganinsu na qara mata imani tare da godewa Allah kan matsayin da take kai,ya zabeta ya dorata ba don tafisu ba,ta yiwuwu a cikinsu ma akwai wadanda suka fita kusanci da Allah a

mma ya jarrabesu don ya sake tabbatar da imaninsu da shi,duk da haka fakar idinsa ta dinga yi tana goge hawayen ta handkherchief sabida abun tausayin ya isa

A haka suka gangara dakin 'yan haihuwa,tsoro ya kama maryam sosai ganin masu larura kala kala,

akai kai ta dinga gigr hawayen nata wanann karon,ta tsorata sosai da haihuwar,daga bakin wani daki suka ga jama'a tsaitsaye agun anata hayaniya,mami ta tambayi jama'ar dake tare da ita,daya cikinsu ya mata bayani

''yarinya ce aka kawota daga gidan mahauka

ta zata haihu,ta jima agunsu ana bata magunguna ashe ba mahaukaciyar ba ce,to da suka kawota sai kuma suka yi tafiyarsu suka barta,kuma bazata iya haihuwa da kanta,ba don bata da isashiyar lafiya da zata iya jurar naquda,shine ake ta neman wanda zai sanya

hannu kan fike din da za'a mata aikin an rasa mai yin signing tunda ba'asan kowa nata ba,shine aka fito da ita daga gadonta aka sanya wata akai kafin asan yadda za'ayi da ita''haushi takaici da tausayin yarinyar ya kama mami duk da batasan ko wacece ba,fad

a ta dinga yi sosai

''saboda tsabar rashin imani,ko cikinku ai a samu mai saka hannu dai,sanadiyyar haka fa tana iya rasa ranta,kuma idan ta mutu shikenan ta mutu a banza sabida bata da gata bata da galihu ko''da wannan fadan da takeyi suka qarasa gun da

take kwance tana matagugu

Ba qaramin tsorata mami tayi ba da ganin zahariyya kwance male male cikin wani mawuyacin hali,batasan lokacin data isa gareta ba tana kiran sunanta saboda tsabar tqusayinta daya kamata,lokaci guda ta manta duk wani abu da suk

ayi mata ita da uwarta,kafin ta qarasa gabanta abdallah ya shiga tsakaninsu cikin tsananin nacin rai yana girgiza kai,tuni,idonsa ya sauya kala

''kada ki isa gareta mami ki barta don Allag,wannan shine sakamakon abinda ta aikata a rayuwarta,kallo daya zak

i mata ki tabbatar cewa sakamako take karba''

tsawa mamin ta daka masa''matsa daga gabana kafin na tsinka maka mari abdallah,baka da hankali ne

?

,kasan naquda kuwa

?

,kasan irin azabar da take ji yanzu haka

?

,ciwon 'ya mace na 'ya mace ne''cewar mamin cikin f

ushi,ba musu ya kauce ya bata gu don baison bacin ran mahaifiyarsa

Ba qyamata ko tsangwama mami ta tattarota jikinta cike da tausayi,suna hada ido da mamin itama ta fara kiran sunanta,fadi take mami ku yafemin keda abdallah,kuyafemin mami mutuwa zan

yi,tuni mamin ta bada umarni aka dauko gado don dorata a ahigar da ita tiyatar gaggawa,ana shirin daujarta tace ta saki murmushi tana kallon mamin

''mami,dama qyaleni kukayi kada ku bata lokacinku,don nasan cewa mutuwa zanyi,kuma ina farinciki da hakan,ta

yiwuwu Allah ke sona yayi nufin wankeni daga zunubaina da zai dauki raina ta hanyar naquda,mutuwata a yanzu ta fiyemin rayuwata mami''

tuni hawaye ya cika idon mamin,duk da haihuwa daya tayi amma har yau bata mance zafin naquda

''ki daina fadar haka zah

ariyya,mata nawa ne suka haihu gasunan lafiya da su,ciwo ai baisan inda rai yake ba saidai idan kwana ne ya qare''sai taga idonta na kallon wani guri ne daban,a hankali taji ta ambaci''habiba''

duka sai suka juya,wadda aka ambata da habiban ce ke qarasowa

inda take,zubewa tayi a gun tana kiran sunan zahariyya,ba wanda yasan alaqar dake tsakaninsu don haka mami ta sake bada umarni a dauki zahariyya a wuce da ita dakin tiyata,da sauri zahariyya ta tsaidasu

''mami,na fada muku wallahi a yau zan mutu bazan sa

ke kwana ba aduniya,da tiyatar da zq'ayimin gwara ki barni nayi magana da wanann baiwar Allahn''jikinsu gaba daya yayi sanyi don haka mami ta matsawa habiba ta iso tana zubar da qwalla

''zahariyya,naga sakayya ta daidai abinda na aikata a rayuwata,aahe da

gaskene son zuciya bacinta

?

,ashe da gaske idan baka godewa Allah ba zaka godewa azabarsa

?

,ashe daidai ne da ake cewa idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wataqila kai zaka iya fadawa

?

,tabbas Allah ba azzalumin sarki bane kuma baya zalunci saidai

bawa ya zalunci kansa......''

*mrs muhammad ce*

πŸ“šπŸ“šπŸ“š

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺



πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–



πŸ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

πŸŒΊπŸ’–

🌺

πŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–

Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

πŸ’‘

*_home of expert and perfect writers_*



β–Ά

6

⃣

8

⃣

*Fiyayyen halitta dan gatan Allah Annabi muhammad S A W yace:((idan wanda kuka yarda d

a addininsa da halayensa/dabi'unsa yazo muku(neman auren 'ya'yanku)ku aura masa,idan ba haka ba

☝

🏽

(kuka hanashi),FITINA DA FASADI MAI GIRMA ZAI YADU/WANZU A BAYAN QASA))*

Juya kai kawai zahariyya take don ta qagu taji me ya faru da hqbiban d

uk da azabar da take ji,cikin kuka habiban ta dora

''na koma gaban mama na da baaba na,ba qaramin farinciki mahaifina yayi ba don ga zatonshi sace ni akayi tunda mamana tace masa bata nayi,haka nan itama mama tayi farinciki,tace nayi shiru da bakina kada

na sanar da kowa halin da na fada da sanadin shigata wanann rayuwar da nayi,da na murmure zan koma gidan mijina,haka kuwa akayi bayan na soma murmurewa da wata biyu aka mayar da mi gidan enginer abubakar,a lokacin da aka maidani baya nan ya tafi umara,kada

kiso kiga farincikin da fatima tayi,sai tausayin kaina ya kamani,naso ma cuceta amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai ya kareta daga sharrina ba tare da ita din ma ta sani ba,yarona wallahi fes da shi kamar sauran 'ya'yanta bashi da wata damuwa

,sati na daya da komawa kafin enginer ya dawo na fara wani zazzabi mai zafi,wasa wasa sai tari,ba'a jima ba quraje suka feso min,idanuna suka canza kala,fatima ita ta tambayi engineer ya bata dama ta rakani asibiti''

sai habiba ta tsaya ta fashe da ku

ka tana tuna irin bala'i da tashin hankalin da ranar tazo mata da shi,da qyar ta saisaita nutsuwarta sannan tace

''abin takaici da baqinciki zahariyya gwajin farko aka gane ina dauke da cuta mai karya garkuwan jiki cutar sida wato HIV''kusan tare suka fas

he da kukan wannan karon dom tuni zahariyya tqyi amanna itama da cutar ajikinta,tunda babu shakka habiba ta samo,cutar ta ne daga jikin malam na hayi,to kuwa dole itama ta kamu da ita babu shakka,kuka sukayi sosai kana habiban tace

''hakanan fatima babu y

adda zata yi badon taso ba sai don kare lafiyarsu ta sanar da engineer ,bai bari ya dawo ba ma ya aikomin da saki uku qwarara,ban boyewa fatima komai ba kan dalilin fadawata wanan haki,wallahi baiwar Allah kuka ta dinga yi cike da tausayina ,hakanan tamin

alqawarin riqe min yarona riqo irin na amana,da kanta ta daukeni ta kaini har gida,bqn boyewa mama komai ba din tana daga cikin wadanda sukaui silar fadawatq wanan mummunar rayuwar,abun mamaki qarara mama ta nuna qyamata atake agun,harda saiya mazauni saba

nin wanda take a dazun da nazo gidan

Tun daga ranar na fara ganin tsantsar tsana da qyama daga gurin mama na hatta da qannena ba'a barsu a baya ba,duka babana baisan me ake ciki ba shidai ya san cewa an sakeni kuma ya nemi engineer amma yaqi sam ya

sanar masa dalilin da yasa ya sakenin,yanzu nan da kika ganni na taho ne domi amsar magani da yin jinya,saboda kaucewa idon jama'a da maganganunsu yasa na baro yaho garin da babu wanda ya sanni,don nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login