Showing 78001 words to 81000 words out of 176330 words

Chapter 27 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

48



don ni na nemi a boye abun,mun fara son juna har ta kaimu ga buqatar muyi aure,na boye miki ne mami saboda ina sane da dimbin so da qauna da kike wa tilon danki,farinciki bazaya bari idan na sanar miki ba ki kasa sanarwa da wasu mutanen ba musamman wadanda

muke zqune gida daya da su wadanda bana buqatar kowa ya sani cewa maryam nake da muradin aura saboda tsaro,mami kinfi kowa sanin irin traps din da na shiga,an farauci dayuwata ba sau daua ba ba sau biyu ba kuma sau uku ba,wadansu trap din sun yi aiki wasu

kuma Allah ya kareni basuyi tasiri ba,na tabbata da ansan maryam ce wadda zan aura ba abun mamaki bane wani mummunan abu ya faru da ita''

''mami...ga maryam nan ta sake dawo miki a karo na biyu,saidai wannan karon uasha banban da sauran lokutta,wannan

karon ta dawo gareki da matsayi guda biyu,diyarki kuma aurukarki,nayi kwadayin ganin irin farincikin da zako shiga ta sanadiyyata ne mami shi yasa na sake dawowa da maryam cikin rayuwarmu,sanin maryam kikayi mami a fili amma a badini nafiki saninta kuma zu

wa gobe zan warware miki ita don wace a sarari ki gani,ina fatan samu sassauci cikin hikunci boye miki wadda zan aura da nayi mami na''

ga mamakinsu saiga mamin itama ta sauko gabansu,hawaye ne bisa fuskarta wani na nin wani,a rude abdallah yasa hannins

hi yana shate mata hawayen

''idan na bata miki mami kiyi haquri,hawayenki bala'i ne mami a gurina''

sai ta kasa cewa komai,jikinta ta janyosu gaba daya ta rungumesu

''barni abdallah na nayi kuka,kuka ne na tsantsar farin ciki ba baqinciki ba,tabbas addu

'a bata faduwa qasa banza,na jima ina addu'ar Allah ya baka mace ta gari,lokacin da maryam ta shigo rayuwarmu na fuskanci dukkan

halayenta na gari sai maji ina maka sha'awarta,domin hasken alkhairai da nake iya hangowa qunshe da ita,ganin hankulanku bai ga

mu guri guda ba yasa na fidda burin daga daina na dungumi yi muku addu'a gaba dayanku,kai har wayewar garin yau maryam ce a raina da ita na tashi har ka cimmani a kitchen tunanin maryam nake''

ta janye daga jikinsu bayan ta dauke qwallar idonta,kama han

nun abdallah tayi da na maryam ta hade guri guda bayan ta dora nata a saman nasu

''na godewa Allah da irin wannan zabi da ya mana baki daya,naji dadi matuqa da kasancewarki maryam cikin zuri'ata,maryam,ga abdallah nan amana ce na baki ita har bayan raina,

na baki amanar abdallah har abada,bani da kowa sai shi,ki zauna da abdallah cikin amana da aminci,abdallah kaima na baka amanar maryam,matuqar ka cuceta bayan zamowarka miji a gareta ban yafe maka ba,ku kula da junaku''abinda ta fada kenan tana jijjiga han

nunsu

Duk yadda yaso ya daure sai da ya kasa,qaunar shi da maryam qarara yake ganowa cikin idanun mamin,baiso maryam din taga kasawarshi saboda haka ya kifa kanahi saman hannun mamin ya sumbata cikin dabara ya goge qwallar idonshi

''nikam na dauka mami

,na dauka,Allah ya tayani riqo''

''kefa maryamu na



''ta fada tana kalllob maryam wanda kanta ke duqe take cure guri guda,abune goma da shirin suka cunkushe a qwaqwalwarta,zuciyarta na gaya mata wayo kawai abdallah yayi mata,mai yasa bata bar gidan salin a

lin ba tare da mami ma tasan wadda abdallah ya aura ba bare ta mata wanna kandagrakin mai daddaure jijiyoyin jiki



,zata iya watsawa mami mai dimbin alkhairai da karamck qasa a ido koko zata yarda ta zauna da abdallan ta sarayar da dukkan wani haqqi da 'yan

cinta da ya take,ya aureta ta sigar 'yar burum burum,zata barshi yaci nasara a kanta ya sameta a bulus ya sameta ta sigar qarfa qarfa da banga banga



,wani sashen na zuciyarta ke mata qarfafa ata gwiwar alqawari ya daukar mata,kuma ta riga da ta cika masa g

abar farko na yarjejeniyarsu,bata jin kuma zai karya alqawarin

daga qasa kuma hannunta yaketa yamutsa mata cikin wani irib salo da yake sa taigar jikinta tashi saboda nata hannun na kife ne cikin nashi tafin hannun,dob samun hanyqr tsira do son cire han

nunta daga nashi tayi saurin cewa

''na karba mami,insha Allahu''cikin zuciyarta tana sauya qudirin ma'anar na karba in don kada Allah ya tuhumeta

Mami dake sauri ta koma gun mutane sai gata ta rashe a cikinsu,hira sabuwa ta barke duk da maryam na rakub

e gefe guda,ga zaton mami surukuta ce da kunya irin wadda tasan maryam din ko da can baya da ita bare yanzun,saidai ga maryam kuwa takura ce data sanyawa zuciyarta na nemo amsoshin tambayoyin abdallah,sai ta hada amsar sai taji duka sun wargaje,idan ta kam

o nan ta qulla da can sai ya tsinke,ita kanta ta rasa dalilin da ya sanyata kasa barin gidan a lokacin da ta fahimci abunda ke faruwa,dik da tana ta bawa kanta amsar cewa girma da darajar mami ne saidai ita a karan kanta take jin amsar ba gamsashshiya bace

bare ta doshi abdallah da ita

''ina zuqa,bari naje kitchen indauko wayat na kira mr stephien,dinner nakeso a shirya mib sabuwa daga nan zuwa takwas na dare a compound din gidan nan''mamin ta fada ikin zumudi da farinciki tana fita daga dakin

bayan f

itarta shiru ne ya biyo baya,abdalla nata qate mata kallo ba tare data sani ba don kanta na duqe ne

''sai faman duqar da kai kike kamar wata mai gajeran wuya,amma dai ba haka mukayi da ke ba ko



,sauran qiris ki wargaza wannan matakin da kika kusa kammalas

hi,ki tashi ki dauko drink cikin fridge ki zuba kin,ki kuma zauna agaba na har sai maki tazo ta ganmu a haka dn mu sake wanke zuciyarta''

batasan lokacin da ta dago ba ta kalleshi da oily eyes dinta ba ta balla masa harara,idanu ya lumshe yana jin wani

abu na tsirga masa,ko banza buqatarsa ta biya,burinshin dama ya kalli oily and brown ayes nata wanda tun jiya rabonshi da su

''ka isa ma



''

''haka kika ce



''

''eh''ta bashi amsa kanta tsaye tana kawar da kanta daa kanshi,gyada kansa yayi cike da mamakin

tsiwarta

''za kuwa kiga kalar tawa isad,ki bar gani na kodaki gaban mami na baki muhimmanci,ina iya qin sakin naki naga wanda ya isa ya sani in sake ki''

bata san lokacin da kuka ya qwace mata ba

''tabbas abdallah ya gama raina mata hankali,a daki mu

tum a hanashi kuka haka ake,ita da ya kamata a lallaba ita ake raina ma wayo

dauke kanshi yayi gefe guda tamkar bsi damu bs,saidai shi kadai yasan zugin fitar hawayenta da yakeji,hakan ya sashi gaggawar fadin

''Allah ya baki sa'a kici gaba sa kukan har m

ami tazo ta ruskeki a haka,idan tabi ba'asi kuma na warware mata zare da abawa kinga daga haka ta daina ganin girma da mutuncin mu baki daya,ni kuma naqi sakinki tunda igiyar na hannu na,qarshe kiyi biyu babu''

Jin hakan ya sanyata miqewa da hanzari kum

a cikun nutsuwa ta durfafi fridge din,binta tayi da kallo a sace sakamakon yadda rigar tabi jikinta ta fidda surarta,ta ciro lemon ta dauki glass cup saman fridge,gabanshi tazo ta tsaya ta tsiyaya mishi ta miqa masa,qi karba yayi sai harara ma da ya gallam

ata

''kina tsammani idan mami ta shigo ta taddaki a haka kina bani abu ba zata zargi komai ba



kin min tsaye a ka kamar zamu shiga filin yaqi''

cikin qufula da hasala tace da shi wasu hawayen sabbi na bullowa

''ya isheni ya isheni fa,don me zaka dinga ju

ya ni kamar wata waina,wannan wanne irin abu ne



''

sake dauke kanshi yayi

''har yanzu ke din a matsayin matata kike,ko babu yarjejiya tsakaninmu dole kiyimin dukka abinda nace tunda ban sakekin ba,ruwanki ne ki rusuna ki bani ruwanki ne ki bar leminki

nima na riqe aure na''

ba maganar da taqi jinin ya fadeta kamar wannan,tilas ta rusuna ta miqa masa,sai da ya wani sha qamshi kafin ya karba,bayan zuciyarshi cike take fal da tausayi da qaunarta,daga shi sai Allah sukasan abinda yake ji cikin zuciyarsa

Ai kam a hakan mamin ta samesu

''a'ah me ya sameki maryam



''caraf ya karbe

''don nace ta miqon drink''girgiza kanta mami tayi tana miqar da ita tsaye

''a'sh banson sharri,bansan maryamu da qiwa ko ganda ba bare kan mijinta,halan bata da lafiya tafiyann

e batasonyi ko



''ta fada tana kallon maryam,sam ita bata fahimci ma'anarta ba rashin sanin me zata ce yasanyata saurin gyada kai don shine kadai mafita

''ayya sannu,hau gado ki kwanta bari in lalubo miki magani,kai kuma banason takura ka qyaleta ta huta

har ta warke,ko kuma na riqeta anan idan bakayi wasa tayi sati''

Wayyo Allah,ai duka sai a lokacin suka fahimci inda ta dosa,a tare suka hada ido ita da abdallah,wata iriyan kunyanshi da bata taba jin irinta ba ta saukar mata,da sauri taja idonta ta qul

ke gam,shi din na da sauri yaja qafafunshi ya fice a dakin don bazai iya hada ido da mamin ba tunda kallon da take masa kenan,ita kam ko a jikinta,cikin gurin da take ajiyar magungunanta ta duba ta fito da pain killer da paracetamol ta hado da ruwa ta kwow

a maryam din

''tashi kisha kinjk marya,kada ki biyewa abdallah ya cutar da ke ba tare da kin warke ba,idan kinga ma da takura kimin magana zan maganinsh don nasan halinshi da rawar kai sarai,idan kinki jikin bai miki daidai ba ki sanar min sai a haqura da

dinner din''ita dai kamar qasa ta tsage ta shige haka ta dinga ji,wannan abun kunya har ina,sai da taga ta sha ta kwanta taja mata bargo sannan ta fice a dakin

Tayi nisa sosai cikin saqe saqe da tunani taji dumin mutum a bayanta wanda sam bata san loka

cin da ya shigo din ba,a zabure ta miqe zata sauka ya damqeta da hannu daya

''kiyi a hankali kada ki fama ciwon naki''ya fada cikin salon rainin wayo,kasa motsi tayo abdallah zai kasheta kam wallahi,sai kuma ya hade rai

''kikaci gaba da kuka zuwa anjima

idanunku zasu kumbura,kinga idan anzo dinner sai ki tanadi amsar basu''ya miqe tsam daga gadon ya fice abinsa adakin bako waiwaye,ajiyar zuciya ta saki,sai da ya fita din sannan taji kamar ta bishi ta rufe da duka,gaba daya ma shi babu abunda ya shalleshi,

babban isue da ya kamata ace yana cikin rashin nutsuwa amma ko a jikinshi.

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Bayan ta kammala sallar magariba mami ta shigo

''yaya maryamu jikin,dinner din zai yiwu kuwa



''

kanta a duqe ta amsa mata da eh don kawar da zargin da mamin key

i na wani abu ya faru da ita,amma a zahiri ba don wannan zargin da mamin keyi ba da cewa zata yi bazata iya zuwan ba,saboda har yanzu zuciyarta cikin qunci take,nan mamin ta sakata ta shiga tayi wanka duk cikin dakin,mai makeup ta tadda na jiranta,hakanan

tanaji tana gani ta zauna aka zuba mata kwalliya ta gani ta fada aka sata ta shirya cikin wedding gown irin ta larabawa fara tas mai dige digen adon zaiba kadan kadan,rolling aka mata sak irin na larabawan wanda iyakarsa saman qirjinta,hill shoes shima da

earings sarqar hannu data qafa duka ruwan zaiba ne.

Kada kaso kaga kyawun da maryam din tayi,kusan duka cikin event din bikin da suka gabatar wannan itace shiga mafi kyau da tayi.

Tana zaune nan cikin bedroom din shiru kamar yadda mami ta umarceta,qo

far taji an turo wanda kafin ma ta daga kanta taga waye qamshin turaren data jiyo ya sanar mata,saboda haka taci gaba da dauke ganinta daga bakin qofar,tsayawa yayi kawai ya zuba mata ido cike da sha'awa da burgewa,tayi masa kyawu fiye da tunani,bai qara a

manna da kyawun da Allah ya bata ba irin yau,kasa controlling din kanshi yayi ya miqa hannunshi da nufin shafa lebenta da yaci jambaki maroon colour,har ya kusa da ita kome ya tuna kuma sai yayi saurin janye hannunsa ya daidaita nutsuwarsa hadi da cunkushe

fuska

''ki tashi muje mu ake jira''

sai a sannna ta daga kai ta kalleahi cikin sakannin da basu wuce uku ba ta qare mishi kallo

eh yes ta yadda abdallah mai kyau ne,sanye yake cikin jacket mai bala'in tsada da kyau fara tas da ita komai nashi farine id

an ka cire necktied dinshi takalmi da agogonshi duka ruwan zaiba kalar nata shigar sak,kau da kanta gefe tayi don bata son fiya hada inuwa da mutumin da ya yiwa rayuwarta karan tsaye

''kayi naka wuri nima nayi nawa''sunkuyowa yayi saitin fuskarta har numf

ashinsu na gware

''kin manta a idanun duniya mu masoya ne da mukayi auren qauna,qwarai ni airen qauna nayi amma ke da aka yiwa auren dole na fada miki dole ki ari acting na ma'abota so ki dorama kanki matuqar kina buqatar cikar burinki,wannan ne magana ta

da ke na qarahe,harshe na ya gaji da yi miki tuni''

Kanta ta sake kaudawa ta yadda babu yadda zai iya ganin hawayen dake qoqarin fita a idanunta,cike da zafin rai tace

''saidai kayi dukkan abinda kaga zakayi,kaga,nifa na gaji da wanna game din naka,ka

wai ka sallameni a yanzu na san inda dare yayi min''

''idan anqi fa



''

ya fada bayan ya miqe tsaue ya goye hannauenshi a qirjinsa yana leqa dan qaramin bakinta dake raahin kunya

''tilas ma ka sakeni tinda nace bana so bana yi akai gaba wataqila asamu ma

i tayawa''

Yaji zafin maganarta amma son biye mata balle a gamu da matsalar da tafi ta baya

''lallai kam yarinya wuyanki yayi kauri,naga alama kinga makwancina da yawa,don kin samu kamar ni abdallah na nuna sonki har na aureki kikeda bakin fadin haka,k

insan kalan 'yammatan dake rububi da fatan na zame musu miji ba tare da aisin kwabo na ba ma



''

A sukwane ta juyo tamkar mai jiran ya gama fada,ido cikin ido tace masa

''ni ba irinsu bace,na sha ban ban dasu nesa ba kusa ba,baka yimin ba sam ko kusa ko a

lama,kuma na fada na gaya maka bana sonka bana buqatar igiyar aurenka a kaina,ka ssakeni mana dole ne,kaje ka auri masu rububin naka,idan ka taya akace ba'ayi ai sai ka matsa ga masu yi inda kake da muhalli,bawai ka tsaya ka nace a inda babu muhallinka ba'

'

Mamaki kam kusan kasheshi yayi a tsaye,gadan gadan ya nufota yana fadin

''ba irin mu mace ke kalla kai tsaye tace bata son mu ba duk isarta da tsadarta,bamu cewa muna so ace ba'a son mu,ni abdallah na miki alqawari

sai na azabtar da zuciyarki da kala

r soyayyar da baki taba yiwa wani da namiji irinta ba''bai bata damar furta komai ba ua sirute gaba daya ita da wedding gown din nata harda 'yar purse dinta marching na kayan,dike doke da zille zille ta fara tana fadin ya saketa ita ba 'yar iska bace yana

sauka daga step din benen zuwa falon mami na qasa yana fain shi kuma tantirin dan iska ne sai yaya kenan



kafin su qaraso falon tuni ta soma jiqa fuskarta da hawaye,ajjiyeta yayi saman kujera ya dora qafansji daya saman kujerar kusa da cinyarta yana huc

i kadan kadan,sai da ya gama qare mata kallo kana ya bude 'yar jakarta dake hannunshi yaci sa'a kuwa ya samy tissue turare da powder,cirosu yayi ua cilla mata

''ki gyara fuskanki nan da minti biyu''

cikin muryar kuka tace

''idan naqi fa



''

wani dan gaj

eran qayataccen murmushi irin na gefan baki yayi idanunahi sun kada sunyi ja don ta soma bashi headach bai taba fuskantar irin wanna trouble ba daga gun mace,idan suka botsare basu da dadin sha'ani saidai ka bisu ta yadda suke so ka ka musu jan ido.

''m

eyi baya fada,kiqi yin kiga mai zai faru a aikace kinga ai yafi dadi akan na fada miki da baki''ya sauke qafanshi ya nufi fridhe ya ciro sassanyar ruwan swan na madaidaiciyar roba ya soma daddaka,sai da ya shanye tas ya juyo inda take,tuni har ta gyara ats

oronta na kada ya hanata takardarta,tamkar ya qyalqyale da dariya sai kuma ya maze yasha mur

tana shirin miqewa ya hangi igiyar takalminta ta kwance da sauri ya duqa don daure mata zata ja baya ya riqe qafan gam ya soma daure mata,lokacin mami ta ahigo ta

na fadin har yanzu basi fito ba me suka tsaya yi ne



,yanayin data gansu ya matuqar burgeta ta sake amanna da soyayyar dake tsakaninsu,tayi murmushi tana tunanin tana tsakiyarsu basu taba nuna mata soyayya suke ba saima fada kullum ashe ninketa suke baibai.

Compound di ya cika babu laifi da jama'a,wanda kusan rabinsu duka 'yan uwane irin mugun na jikin nan sai daidaikin maqota da abokai,tayi mamkin yadda adan taqaitaccen lokaci irin haka ma aka tara jama'a mai dan dama har haka,ko ina ka duba gurin walwal

i yake da decoratiom na farin yadi da wasu fararen fitilu,komai na gurin fari ne hatta da kayan mahalarta taron farine

tayi mamaki da ganin raliya da nasir lubabatu qanwarta batulu harda hindatu da jabir,to wama ya gaya musu wa ya gayyacesu



,daga sashi gu

da kuma nene ce da adnan sai zahariyya,idanun zahariyya da nene na kan abdallah duk wani motsi nashi suna ankare da shi,fatansu daya suga mummunan sauyi tattar da shi,yayin da adnan ya tattara nashi ma mujiyar kan maryam wanda babu abinda yake sai aukin ha

diyar yawu,cikin zuciyarsa yana yiwa nene Allah ya isa da ta hanashi mallakar maryam din har abdallah ya sameta,gefe guda kuma yana tainewa abdallahn yana fadin duk taurin ranshi ne ya jawo,amma yaci alwashin da zarar burinsu ya gama cika kota tsiya kota a

rziqi sai ya mallaki maryam din,ko nenen na so ko bata so,kai baiqi ya kawar ma da duk wanda zaice zai kawo masa cikas ba,zubaida na gida nene ta qulleta cikin dakinsu kana ta qullen bangaren ma baki daya,ta rantse ta maya babu inda zata fito har a watse.

cikin wani irin salo mai qayatarwa dinner din ta dinga gudana,kowa ranshi fari tas cikin burgewa,tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login