Showing 72001 words to 75000 words out of 176330 words
baki wallahi badai ni ba''ta buga qafa tayi ficewarta,tilas ta saki jamilan ta debo ruwan ta sheqa mata kana ta jata zuwa cikin daki tana fyace majina.
Gwanin sha'awa motocin ke tafi
ya cikin tsari da nutsuwa,sam babu irin mahaukscin gudun nan da 'yan kai amarya keyi,mitoci ne kimanin guda arb'in banda na security guda goma
wani matsananciyar faduwar gaba take fama da shi idan ta tuna izuwa gidan aurenta fa take tafiya,addu'o'i ne
fal cikin zuciyarta na samun sa'a da nasarar sabuwar rayuwar da zata fuskanta
πππππ
sau uku tana sako qafarta waje da niyyar fita saidsi ta kasa,sakamakon mutanen dake giftawa bata da buqatar kowa ya ganta,aiki ne na sirri wanda bata da buqat
ar haduwarta da wani,wayarta ta fara vibration jikinta na rawa ta daga,muryar nene ta cika dodon kunnenta
''kada fa kiyi kuskuren da zaki jawo mana bacin aiki,wannan ce damarmu ta qarshe''murya can qasa take fadin
''na gama aiwatar da komai nene,fitowata
ce ke neman gagara mutane na kai kawo a gun''
''kada ki kuskura ki wuce mintina talatin baki baro area din ba,wuce hakan na nufin bacin komai''din din din wayar ta katse,hankalinta ta msida sosai kan hanyar ficewarta,wuf ta faki idanu ta fice ta nufi ban
garen nasu cike da farincikin nasarar aikinsu
ππππππ
Qarfe goma da rabi ne na dare,gefan lallausan gadon dakin nata take a cure guri guda,tafiyar yan kawota da mintina ashirin yayyafi ya fara sauka wanda ya haddasa sanyi da garin yayi hade da q
amshin qasa,bai kankama ba ruwan hakanan yayyafin bai tsaya ba,kusan tunda suka tafi suka barta anan take zaune bata ko motsa ba
hayaniyan data soma ji cikin paflour na muryoyin maza daban daban suka qara mata fatgaba,ta runtse idonta tana jin yadda z
uciyarta ke dukan uku uku kamar zata yi tsalle ta fito
''ko baka fadi ba ba shiga muma za muyi ba don an dade da daina wannan''ta jiyo muyar wani daga cikinsu,tun tana jin hayaniyar tasu sama sama har taji dif alamun basu cikin sun fice kenan
da
gudu gudu sauri sauri ya qaraso cikin parlojt din saboda ruwan da ya sake danyin qarfi,duk da haka ya jiqa masa fararen kayanshi,ya tsaya ya kulle ko ina ya rage yawan qwayayen dake kunne kana ya doshi dakin kai tsaye
a hankali ya tura qofar dakin kan
a ajjiye tarin ledojin dake hannunshi,qamshin dake dakin kawai ya isa ya tabbatar maka rana ce ta musamman,tsaye gayi hannunshi harde a bayanshi,sai ya lumshe idonshi yana zuqar qamshin qasa hade da turaren jikinsa da na dakin baki daya yadda suka hadu suk
a fidda wani qamshi na musamman kuma na daban,gwagwarmayar da ya fada kacin samunta ta zama mallakinsa ya dinga dan tunawa,a hankali ya bude idanun nashi ya tsaya yana qarewa shigar tata kallo
gaba daya jikinsa ya saki lokacin da wani tunani ya darsu
a ransa wanda ya qada maaa qwarin gwiwa da azamar isa gareta,tamkar mai tausayin gadon haka ya hau ya dinga rarrafawa har ya isa gareta kana yayi zaman dirshan a gabanta
sannu a hankali ya dinga yaye mayafin dake kanta har ya cimma nasarar cireshi duk
a fuskarta ta bayyana,saidai ya cimma idanunta aruntse ne,ya karyar da kai yana ci gaba da kallon fukartata irin kallon da bai taba samun dama ya tsaya yayi mata shi ba,kyawunta yaci gaba da fito masa muraran,sosai ya shagala har baison abinda zai shiga ts
akaninsa da yanayin
Qememe zuciuarta taqi amincewa da daina mugun tseran gudun da take,gashi ya sata agaba,nauyi da kunyarshi sun hanata bude ido,jin shirun yayi yawa ya sanyata yanke shawarar bude idanun nata ko yama fita adakinne ma bata sani ba
da kadan da kadan ta dinga budesu har sai da suka kammala buduwa tar,da qafafunshi ta soma tozali a hankali ta dinga daga kan nata har ya sauka bisa fuskarshi da ruwan sama ya jiqa har ruwan da ya soma taba kanshi ke diga kadan kadan,batasan lokacin data
ta wuntsila gefe ba cike da *TSORO RAZANI DA FIRGITA BA* sakamakon wanda ta gani
*ABDALLAH* ne cikin daren nan cikin gidanta kan gadon aurenta
οΌ
,idanunta ke mata gizo koko meye
οΌ
,me yake faruwa ne
οΌ
,hauka ce ta samu qwaqwalwar abdallah ko bashi bane bam
a gaba daya aljanu kesan mata wasa da qwaqwalwarta da tunaninta,ina abdur rahim da ya bar abdallah ya keto dakinsu na sunnah
οΌ
dimbin tambayoyin da suka nemi jirkita mata qwaqwalwa kenan tashi guda ba tare da tasan duka amsoshinsu ba
*mrs muhamm
ad ce*
π
πππ
β
π½
β
π½
β
π½
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ
*ABADAN*
πΊ
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
ππΊππΊ
ππΊπ
πΊπ
π
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊπ
πΊππΊπ
πΊππΊ
ππΊ
π
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
π‘
*_home of expert and perfect writers_*
βΆ
3
β£
8
β£
*_JIRGINSO ZAYA TASHI KE DAI AKE JIRA ...'YAR GATA DUNIYAR SO.... KECE DA SARAUTA_*
πΆπΆ
*_na dawo gunki nazo baqo da sallama....ka
i kawo nayi qarshe...a qauna na tsunduma....kin jawo nayi roqo nazo ki ban zuma....na sawo dubi tufata mai kyau da karrama....ke naiwa kwalliyata shiga ta alfarma....._*
πΆπΆ
*_soyayya gaskiya ce ya zanyi in raina....wanda yake aac cikintaaa nima don na za
una.......nayi dare ban masauki gidanki in kwana....zo ka shige har abinci zan maka kwadon rama....._*
πΆπΆ
*_riqe sirri sai mai sirriiii....da fari a cikin taurariiiiii...._*
*wannan waqar na sadaukarwa da readers don jin dadinsu kana iya sauraronta
bayan kammala karanta wagga shafi*
ππππ
Matsowa kusa da ita ya sakeyi tattausan murmu kwance bisa kyakkyawan fuskarshi,duka hannayenshi ya ware da nufin ta iso gareshi,take jikinta ya soma bari,qwaqwalwarta so take ta tsaya cik da aiki sa
idai ta ware qwanjinta wajen hana hakan faruwa,bata da buqatar tsayawar tunaninta a yanzu,tama fi buqatarshi fiye da ko yaushe,ya sake matsowa gareta yana nufin janyo ta jikinshi
wata hadaddiyar tsawa ta sakar masa bayan ta dira daga kan gadon jikinta
na qyarma,tuni zuciyarta ta karye hawaye ya soma sintiri bisa fuskarta,dukkan tunaninta sun gama vata fyade abdallah yazo yi mata,tunda ba wannan ne karo na farko data taba ganinshi kebe da diya mace ba,amma wanne irin tsoro abdur rahim kewa abdallah da u
a bashi irin wannan damar
οΌ
,ko wani abu yayiwa abdur rahim din nsta har ya kai ga shigowa dakinta shi daya ba tare da wani qwaqqwaran motsi ko hayaniya ba.
Abdallan ya sake motsawa don biyota qasan,cikin daga sauti hargagi fushi bacin rai da tashin han
kali ta dakatar da shi
''dakata marar tsoron Allah,me kake nema da ni
οΌ
,me ya shigo da kai dakina
οΌ
,kana shirin tozarta sunnar ma'aiki
οΌ
,kana shirin cin mutuncin matar da bata yi maka komai ba
οΌ
,to Allah ya fika''
jikinta na rawa ra fara daddan na wayar dake
hannuna tun dazun da aka kawota lubabatu ta danqa mata a hannunta
Numbers din abdur rahim ne guda uku,saidai duka wadda ta kira sai taji ringin dinta cikin aljihun abdallah,cike da wani tsoron ta dago ta dubeshi,hawaye ne kawai ke kwaranya da sintiri
kan fuskarta
''abdallah
οΌ
,ina abdur rahim
οΌ
,me kayi mishi
οΌ
me ka yiwa mijina
οΌοΌ
''ta qarasa maganar cikin qaaraaji
baisan sanda yayi alkafura ya diro daga gadon ba,gadan gadan ya nufeta don ya riqeta ganin yadda take kuka tuquru tana dafe bango,saidai ka
fin ya kai ga riqeta ta goce
''kada ka tabani,kaji tsoron Alkah kasan cewa ni matar wani ce''cikin cool voice dinsa mai cike da jarumta da mazantaka wadda a yau rauni ya cikata ya saje maidata sassanya yace
''pls cool down mana,ki natsu in miki bayani ki
nji,ki saurareni''
''bazan nutsu ba,in nutsu ka cucu ne,me kake nufi abdallah,me nayi maka,ka shigo dakin aure na,banga mijina ba,na kira wayoyinshi suna jikinka,ka gaya min me ka masa
οΌοΌ
me kayi masa
οΌοΌοΌ
''
duk yadda yaso tayi shiru ta saurareshi abun y
a faskara,idanunta sun rufe bisa dukkan zatonta ko abdallah ya kashe abdur rahim ne
''ki zauna ki fahimceni...'''
''bazan fahimceka ba.....ina mijina.....ina ka kaimin mijina abdu........''
''maryam
οΌ
ni ne nan mijinki,ni ne mijinki ba abdur rahim ba,
ni abdallah da ni aka daura miki aure
οΌ
''ya fada yana nuna kanshi shima cikin daga murya har jijiyar wuyanshi na tashi
sai kukan nata ya tsaya cak,ta tsaya tana kallonshi tamkar doluwa ko sakarya,jin maganar tayi tamkar cikin mafarki,da saufi ta kama hanun
ta ta mintsina sai ta tabbatar cewa gaske ne,girgizq kantq ta shiga yi tana fadin
''ba kaine mijina ba,bakai ka aureni ba ni zaka yaudara
οΌ
''
''bari in baki shaida don ki tabbatar''ciro wayarsa yayi ya kira wasu nimbers,ga mamakinta sai ga muryar abdu
r rahim radau
''kai,bakasan ganganci bane kiran ango daidai wannan lokacin ba
οΌ
,ko baka shiga dakin marya bane
οΌ
''yake tambaya cikin sigar zolaya
''hmmm,abdul maryam zata amince nine mijinta kuwa
οΌ
''
dariya yayi
''a'ah,mai zai hana,idan ma taqi ta amince
ka dauketa kuje gidansu tunda su sun sani kaine ka aureta din,ko ni inzo gobe sai in dauko gimbiya muzo in mata bayani''
baiga qarasowarta ba sai waftar wayar da tayi,cikin rawar jiki ta kara wayar a kunnenta
''abdur rahim,ka cemin kaine mijina ba ab
dallah ba,ka gaya masa don Allah''
''kiyi haquri maryam bani na bada sadakinki ba bani ke neman aurenki ba,duniya bani ta shaida a matsayin mijinki ba duka wannan abdallah ne,nine *abdurrahim a fili a boye kuma abdallah,nike neman aurenki a gaban idonki a
bayan idonki abdallah ne*,banyi hakan ba don komai sai don *DACE DA JUNA* da kukayi ke da shi,babu wadda ta dace ta zauna da abdallah saike......''
bata bari kunnuwanta sun qarasa ji mata kalmomin da ta yiwa laqabi da munanan kalmomi ba ta saki wayar
ta tarwatse agun,taji daga baki mai tushe to shin kuma wa take jira
οΌ
me take jira da zai tabbatar mata fiye da abinda taji yanzun
οΌ
babu,babu shi,take taji garkuwar jikinta na raguwa,qarfinta yana yin qasa,sai ta soma sulalewa agun
da gudu abdallah ya i
sa gareta ya tallafota,tabbas da tana da isashen qarfi bazata yarda ta sauka ajikinshi ba,rungumeta yayi yana jijjigata,numfashinta na fita hakanan idanunta akansa suke hawaye na bin gefan kunnenta saidai numfashin na gware ne gurin fita,rungumeta yayi tsa
m cikin jikinsa cikin wani tashin hankalin,daukarta yayi tsam tamkqr wata 'yar tsana ya komar da ita kan gadon ya shimfideta.
mahaukacin bugu yaji ana yiwa qofar bangaren nasa ,sai ya sake diriricewa,cikin qanqanin lokaci kuma ya gayyatowa kansa dakiy
a da jarumta yana tafiya yana waiwayen maryam din tamkar wanda aka ce masa kafin yaje ya dawo zata bace ya sauko ziwa bakin qofar ya saka key din ya bude
jikinsa ta fado tamkar wadda aka hankado,cikin hanzari yasa hannunsa daya ya cireta daga jikinsa
yayi gefe da ita saidai ita qoqarin dawowa take zuwa jikin nasa tana gunjin kuka duk ta wani burkice kamar mahaukaciya
''wai meye haka zubaidq
οΌ
bana son hauka fa
οΌ
''ya fada cikin hargagi
''bazan iya ba abdallah,wallahi bazan iya jure rashinka ba,ka tausaya
min abdallah,ta yaya muna cikin gida daya zaka kwana da wata abdallah
οΌ
''
ya tabbata idan yace ma zaya tsaya bata baki ne wahal da kansq kawai zaiyi don ba zata taba fahimtarsa ba,kai infact ma a yanzu bai da time baijin yana da time din wani a yanzu a du
niya koma bayan maryam,ya tabbata idan yayi sake kwabarsa zatayi ruwa ne tsululu kuwa,a nashi zaton
da hasashen abun bazai kai bacn haka ba,yayi zaton cewa duk randa maryam din ta samu labarin shine miji a gareta zatayi farin ciki ne fiye da kowa kodon,dim
bin dukiya da Allah ya mallaka masa
ganin yadda take faman ahigewa jikinsa kamar hauka yasa yq cira hannu hankadata baya tayi taga taga kamar zata fadi
''ki shiga hqnkalinki zubaida,bana cike da iskanci da hauka kina jina ko,bace min da gani''
maima
kon tayi kamar yadda yace din sai ta qara tasowa kansa,cikin zafin nama yaja qofqr ya rufe ya maida muqullin,ta kuwa fada jikin qofar ta saki wani kukan tana bubbugawa iya qarfinta
''ka bude min don Allah abdallah,wallahi na kasa barci,na kasa cin abinci,
na gaza jurewa,ka bude min abdallah''haka ta dinga fada tqnq bubbuga qofar,yana jinta hqr ya haura sama ya barta anan
ruwan roba mai azabar sanyi yq ciro ya hado da cup ya koma dakin,yadda ya barya haka ua sameta sai qaruwa da ruwan hawayen fuskarta suka
yi
ajjiye cup din yayi a side drower ya haura gadon,ya zame mayafin dake jikinta ya wulla shi gefe,ya janyo cup din ya tsiyaya ruwan yana tsoma hannunshi cikin ruwan yana shafa mata a fuskarta zuwa wuyanta,duk da yanayin da yake ciki hakan bai hanashi
kin laushi da santsin fatarta ba,duk lokacin da hannunshi ya taba fuskarta ji take tamkar yana dora mata wuta ne a jikinta,zuciyarta,cike fal da tsanarshi,sannu a hankali numfashinta ya soma daidaita,qwarin jikinta ya soma dawowa,da sauri tasa hannunta ta
yi wurgi da hannunshi dake ci gaba da shafa mata ruwan,ta miqe dqga kan gadon tana shirin sauka,da sauri ya tareta
''ina zaki maryam
οΌ
''
''ina ruwanka da inda zani
οΌ
,ka rabu da ni
οΌ
''tayi maganar cikin tsawa,ganin da gasken fita zatayi yasa ya tareta ya ri
qe dukkan kafadunta,ta soma zile zille da qoqarin qwacewa tana fadin ya rabu da ita ya saketa,ci gaba yayi da qoqarin tsaidata
''ina buqatar hankalinki maryam,ina buqatar nutsuwarki,ki zauna ki bani dama muyi magana,ki nutsu ki fahimceni,me kike so ne
maryam,me kike buqata''
sak ta sakeyi tama kallonshi
''sai yanzu kake da buqatar hankali na
οΌ
,sai yanzu kake d buqatar nutsuwata
οΌ
me kake son gaya min,ka aureni ba da sani na ba kuma kace nutsuwata kake buqata
οΌ
wacce nutsuwa kake sa ran samu daga gareni
οΌ
,h
aka ake aure
οΌ
,ok saboda kana tsammani kana da dukiyar da zata iya kawo maka duk macen da kake so kamar yadda naji kana alfahari kana gayawa abokanka
οΌ
,koda dukiya zata iya kawo maka kowacce mace da kake miradi yes na yarda zata iya amma banda ni maryamu aci
ki,koda ina da muradin dukiyarka ina cewa saida izini na zaka aure ni
οΌ
,after all ma bana aonka abdallah bana qaunarka,bani da burin auren ire irenka ma,abu guda nake da buqata daga gareka shine ka rubuta min sakina guda uku a yanzu ka bani,ni kuma na maka
alqawarin bazan kwana maka cikin gida ba,ka sakeni abdallah ka sakeni
οΌ
''
ta qare maganar cikin hargowa
hannayensa ya harde aqirji yana kallonta,ba qaramin duka kalamanta sukayi masa ba,tunda ya tashi mace bata taba kallon qwayar idanunshi tace bata s
onshi ba,akoda yaushe kalmomin so yake samu da karba daga garesu,kalmomin da bai taba samin suna da dataja ba sai yanzun akan maryamun,ya fuskanci ba qaramin fita tayi daga controll dinta ba,kome zaya fada bai da tasiri yanzun cikin kunne da ziciyarta don
hakq ya dan jada baya,ya zame rigar jikinshi ya rage daga shi sai farar vest da dogon wandon shaddarsa,ya nufo inda take gadan gadan sai ta juya zata sa gudu caraf ya kamota,duk iya yada taso qwacewa abu ya faskara,qyaleta yayi taci gaba da qoqarin qwatar
kan nata har jikinta yayi tubus qarfinta ya qare
''haka kurum zaki bata mana farin darenmu kan dalilin ki wanda kika qi tsayawa kiji nawa dalilin,dare ya tsala lokqcin da ya kamata mu samu hutu amma kin hana mana''ya fada yana mirginata tare da zuge m
ata zif din rigarta,ganin yana qoqarin cire mata rigar jikinta ya sanya ta sake sakin wani kukan cikin dausashshiyar muryarta da kuka ya dasheta tana ci gaba da qoqarin ture hannauenshi wanda saboda tsabar rashin qwarin jikinta ko motsi hannun nashi baiyi
ba
''ka qyaleni abdallah,wallahi idan ka taba mutuncina zan maka Allah ya isa kuma bazan taba yafe maka ba''
duk da yana cikin rashin nutsuwa sai da ta bashi dariya
''kome zan miki ma ai nawa ne,dukkaninki halas dina ce,so ko kin min Allah ya isan ma ba
bina zata yi ba''ya qarasa sabule rigar tata,hannayenta tasa ta fara kare qirjinta tana cewa
''ka zalunci rayuwata abdallah,zamu tsaya fa hisabi gaban Allah''
hannu daya yasa ya kawar da hannayen nata wanda ita iya ganinta duka qarfinta tasa gun kare su
,ya balle bra din ya zameta daga jikinta,take numfashinsa ya dauke da sauri ya lumshe idanunsa kana ya squka agadon ya isa bakin wardove dinsu ya zabo rigar bacci mai adon fari da pink mai sulbi da taushi ,saidai kafin ya qaraso har ta isa bakin qofa cak y
a sake daukota kamar wani kara ya maidota kan gadon ya danneta da rabin jikinsa ya sanya mata kayan baccin
fillow guda ya ajjiye musu bayan ya duba lokaci qarfe biyu da rabi na dare,cikin jikinsa ya jata ya matseta gam suka kwanta ba tare da ya damu d
a sauya nasa kayan ba,yana jinta tana wutsil wutsil dinta da dan ragowar qarfinta hade da hawaye don tuni muryarta ta gama dakushewa koda tayi maganar ma ba fita take ba,gashinta mai sulbi da taushi kawai yake shafawa yana jin digar hawayen nata tamkar na
dalma kan tsokar zuciyarsa.
a hankali ya zagaya da kansa kan kunnenta ya rada mata
''kiyi haquri,na yarda na cutar da ke amma relax pls mu barwa gobe,kome kikeso zan maki,kiyi bacci zuciyarki tayi sanyi''
''ka sakeni bazqn kwana daki daya da kai ba
bare jikinka,ka sakeni abdallah''abinda take ta fadi kenan saidai ina muryarta bata fita bare yaji abinda take fada,gaba daya ma taga ya maia abun kamar wani wasa saboda tsabar qarfin hali irin na abdallahn.......