Showing 27001 words to 30000 words out of 176330 words
har gida ina kwance kudi
zasu dinga shigowa
ta waiwayo hannunta dauke da plate cike da tsiren tukunya wanda ya ji kayan hadi ta miqawa abdallah wanda ke tsaye qiqam a bayanta hannayensa harde bisa qirjinsa yana ta zuba mata surutu
''ungo,ai yanzu kam ka qyaleni na fita ko''
yas
a fork guda biyj cikin plate din sannan yace
''kin gama wannan mami na,sauranki ci,don kin sani tare zamu ci''
girgiza kai tayi tana goge hannunta da doster din kitchen
''haba abdallah,me yasa wani lokaci kake da rigima kamar yaron goye
?,
kace tsiren tuk
unya kake so nace maryama tayi ma kace baka so nawa kake so,yanzun kuma kace sai na zauna munci tare,kaci naka ka ajjyemin nawa,idan na dawo sai naci,ina da patient da nace yau suzo su same ni''
''yau througout ba inda nake so ki fita,duk sun maida min ke
kamar wata engine,weekend din ma ba za su barmin ke ki huta ba,kuma ma ni mami bazan iya ci ba idan babu ke''
''alright,ga maryama nan ta wakilceni sai kuci tare''ta fada tana daukan mauafinta dake saqale kan qofan kitchen din
ya kalli maryama ta wutsiy
ar ido wadda ke fasa qwai cikin bowl zata hada potatoes bolls sannan ya harareta kadan ya dauke idonshi ya maida kan mamin
''mami kina ragemin matsayi gunki,babu wanda zai iya replacing dinki a guna''
''to tunda ba zaka kaci da maryama ba sai na turo mak
a zubaida,ita ai na zaka qi ba tunda masoyiyarka ce ko''ta fada tana ficewa a kitchen din
maryam wadda kanta yake sunkuye tana kada qwan bata san lokacin da dariya ta ciyota ba don tuna dramer din da suka gama shi da zubaidan dazun da safe,bata snkara ba
dariyar ta subuce ta fito
hannayeshi harde bisa qirjinshi as usual,a hankali ya dora kyawawan qwayar idanunsa gefen fuskarta wanda dimple dinta ya fito radau saboda motsawar fuskarta,sai taji duka ta sha jinin jikinta duk da ba kallonshi take ba,cikin sec
ond daya tayi qoqarin mai da fuskarta yadda take
hijabinta taji an damqa hade da jawota wanda har hakan ya haddasa fadowarta jikinshi,cikin zafin nama taji ya ja hijabin ya cireshi sannan yayi wurgi da shi,cike da azama tayi gaggawar barin jikinshi,a tsor
ace take kallonshi tare da takure jikinta guri daya,sanye take da fitted gown na atamfa wanda yabi lafiyar jikinta,a qa'ida dinkin ya mata kadan amma son da takewa atamfar yasa ta kasa bayar da ita,dalilin da yssa kenan duk lokacin da ta sakata hijabi take
sawa
tuni oily eyes dinta suka qara sheqi kan wanda suke da shi a da sakamakon taruwar qwalla cikin idanunta,zuciyarta bugu take wanda a take jin ya wuce qa'ida,tama kasa hada ido da shi kamar yadda ta kasa motsawa,saboda idan tace zata motsa din tofa ko
ina na jikinta zai motsa din ne
hucinsa taji a gabanta,a hankali ta dago da kanta don kallin abinda ke gabanta,tafin hannunshi ne mai dauke da zara zaran yatsu bude,tsakiyarshi kuma kunama ce qatuwa,saura kadan nunfashinta ya dauke,da sauri ta ja baya sa
nnan ta daga kai ta kalli fuskarshi
gumi ne sosai yake hadawa yayin da idanunshi suka soma sauya kala bisa dukkan alamu ta hahharbeshi bama sau daya ba,a gigice ta koma gabanshin taci burki ganin yana tsaye qiqam yana kallon abunda ke hannun nashi
tamkar
ba wani abu bane mai cutarwa,hannunta ta saka ta tankwabe hannun nashi kunamar tayi tsalle ta sauka gefanshi,takalminshi ya sanya ya taketa
batasan ta kama hannunshi ba tana lalubar inda dafin yake ba sai da taji ya fisge hannun yana fadin
''mtswee,sakem
in hannu dafi na shigar mutum sai ua masa illa kin tsaya shashanci''
hannunshi ya saka ya riqe inda yake tsammani iya nan dafin ya tsaya
zaune yake a falon tunda ya fito a kitchen din,da alsmu xafin harbin na damunshi sosai,duk da 'yan dabarun da yayi,du
k sai ta shiga damuwa tana jin itace sila,ta rasa da me zata taimaka masa,duk sanda ta matso gun da yake sai ta kasa tabuka komai saboda kwarjinin da yake mata,qarshe sai tq koma kitchen din ta dauki wayarta ta kira mami ta sanar mata
sosai mamin ta rude
tace ta gaya mishi ya taho asibiti yanzun lallai
kwance ta sameshi saman doguwar kujera
a darare ta matsa kusa da shi kadan cikin sassanyar muryarta
''mami tace ka sameta a asibitinta''
sam bai ji isowarta gun ba sai saukar siririyar muryarta
jin shir
u ya sata sake maimaitawa
kusan minti uku kafin yace
''leave me alone pls,bani son naci tunda ni ba kurma bane,sannan bani son gulma,har kin kirata saboda tsaban gulma,bace min a gun''
bata damu ba tunda ta isar da saqon mamin dai,kitchen din ta koma ta
fara soya patatoes bolls din duk da rabin hankalinta na ga abdallah wanda bata ji motsin tafiyarshi ba,dalili kenan da yasa taa kammala suyar ta sauke man ta leqo falon,yana kwance abinshi yadda ta barshi,sai 'yar nutsuwar da ta samu tayi qaura,waishi wan
e irin mutum ne da ciwo ke cin jikinshi amma bai damu ba
cikin dan qwarin gwiwar da ta tattara ta sake nufarshi da nufin tunassr da shi koda qila ya manta,saidai kafin ta qarasa wayarshi dake ruwan cikinshi ta dauki sassanyar ringing alamun shigowar kira
da alamun kasala ya dauki wayar ya duba mai kiran nasa ya amsa bayan ya maidata handsfree ya dorata saman cikin nasa
''abdallah yaya me na jika shiru
?,
ko maryama bata sanar maka saqona ba
?
''
cikin murya mai kama da ta mai bacci yace
''ta gayamin mami,k
awai....''
''ya isa bana buqatar uziri,na baka minti talatin in ganka a office dina ok
?
''
''yes mami''ya fada daga bisani wayar ta katse
cikin sanda ta juya don komawa da baya tunda bai ganta ba
''dakata a nan''ya fada cikin kaurara murya,cak ta tsaya
din yayin da shi kuma ya miqe a hankali
''sai ki fito amma zan sake maimata miki ni bani son shishshigi''daga haya ya juya yayi waje
motoci hudu ne baqaqe masu azabar kyau a jere,tun kafin ta qaraso taga abdallah tsaye jikin daya,xubaida ce ke fuskantart
a bisa alamu magana suke,isowarta ne ya sanyata jin maganar qarshe da abdallah ke fadi
''nacinki kullum sawa yake ina dada tsanarki,bana son shishshigi bana son naci kuma bana son takura,ki tambayi nene tun asali ke ba type dina bace,bazan taba auran mace
n da bata yimin ba,ba ko wacce irin mace nake so ba,for now ya kamata ki gane hakan''
ya sanya hannunsa ya janue hannunta data tokareshi da shi ya bude bayan motar da kanshi
''naji abdallah,amma atleast dai a yanzun ka barni na raka ka asibitin bai canca
nci ka tafi kai daya ba''
ko kallo bata isheshi ba don tuni ya gama maganarshi da ita
ya juya bayanshi yace da daya daga cikin security dinshi su rage biyu daga cikin motocin da biyu za'a tafi,ya rufe maganar da fadin
''ko kun manta muna bincike kan alh
j haladu uba mai qusa,kuma banson yasan ina cikin garin nan,ku kiyaye''
''yes,sir''ya fada cikin girmamawa
kusan tare shi da zubaida idonsu yake kan maryama dake tsaye daura da su
''me kika tsaya kina wa mutane a gurin
?
''
cikin tattausan muryarta tace
''bansan wacce mota zan shiga ba ai''
''saikiyita sanqamewa anan har a tashi qiyama''ya fada yana shirin shigewa motar
''amma abdallah wannan ita kuma fa
?
''
wani kallon biyu babu ya mata cike da quluwa da tarin tambayoyin da nabu macen da isa ta masa s
u idan ba maminshi ba,tsaki ya ja mata sannan ya ja motarshi ya bame
sun gama reverse suna shirin ficewa maryama dake motar baya cikin gidan baya a takure saboda su uku ne maza biyu ita ta ukun taji an dakatar da su,abdallah ne ya fito ya qaraso har gaban
motar,glass din duka motar yasa suka sauke ya qare musu kallo sannan yace da na gaban motar
''you are verry stupid lawal,oya getout ka koma baya,ke kuma ki fito ki dawo gaba saunar yarinya kin shige cikin maza kin wane qwame''
yana tsaye akayi hakan san
nan ya bisu da tsaki ya kona tashi motar duka direbobin suka ja suka fice a gidan
*ABDULLAHI SPECIALIST HOSPITAL* shine abinda ke rubuce jikin wani makeken allo dake maqale a goshin ginin benan asibitin,wanda ko daga ina ka taho zaka gani saboda girman al
lon da rubutun da kuma tsahon benan,gini ne na alfarma tamkar ba asibiti ba,komai neat bisa tsafta tsari da kuma qwarewa,tun daga parking space ma'aikatan dake cikin harabar asibiti leburori da masu gadi suka soma tururuwar zuwa gaida abdallah,ga mamakin m
aryam hannu yake basu suna mudabaha cikin fara'a da sakin fuska
a haka suka ratsa cikin asibitin har zuwa sashen da office din mami na musamman yake
''wonderful,abdul dama kana nigeria
?
''suka ji an fada,wani matashi ne wanda ke nufosu yake fadar haka,san
ye yake cikin qananun kaya wanda kallo daya zaka mishi kasan dan birni ne yasan gayu gayu ya sanshi,ba wani mugun kyau ne da shi ba amma iya adonshi ya bashi sunan kyakkyawa
da fara'a sukayi musabaha da abdallah
''idan ban manta ba shekaru biyar rabona d
a kai abdallah,yanzu laifin kudrat sai ya shafi mansur
?
''
dan qaramin murmushi ya saki kana yace cikin basarwa
''manta kawai friend ya bayan rabuwa
?
''sai alkhairi abdul,hala wannan ce madam din tamu
?
''
wani haushi ya kama abdallah don yasan ba kowa yake
nufi ba sai maryam,sai ya zuba mata ido yaga yadda zata karbi maganar,babu abinda ya fuskanta tattare da ita don kanta a sunkuye yake jinta take kamar ta,zura a guje,ta takura matuqa cikin tafiyar nan
maida kallonshi yayi gun mansur
''kada ka sake fadi,
cook dina ce,nazo ganin mami na ne ta shigo cikin sahun bodyguard''
murmushi mansur din yayi
''tofa wannan karon babu rabuwa abdul,bani adress dinka,zan sameka har gida,ina da magana da kai''
saboda yanayin aikinshi yasa bai bashi adress din gidan ba ka
i tsaye sai ya amshi phone num din mansur din yace zai nemeshi duk lokacin da zasu hadun,sukayi sallama kana suka nufi office din mami
duka a waje suka tsaya abdalla ne ya shiga ciki,fitowar mamin kenan daga toilet ta daura alwala
''ina maryam din''ta ta
mbayeshi tana shimfida abun sallah
''suna waje''
''kana nufin har ita din''
''eh mana mami,har da ita''
''koma ka shigo min da ita''
cikin shagwaba yace
''yanzu mami a gabanta za'a min treatment din bayan da zafi kuma salon ta raina ni''
ita dai mam
i bata kulashi ba ta tayar da sallarta,tilas ya koma yace da lawal ya shigo da ita
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:52 PM] 80k:
💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺
*ABADAN*
🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
🌺💖
💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺
▶
1
⃣
9
⃣
teburin mamin yayi zamanshi yaja laptop dinta yana danne danne
ya barta nan a tsaye,a haka mamin ta kammala sallarta ta shafa addu'o'inta
''sannu maryama ya akayi kunama ta sami abdallah
?
''mamin ta fada cikin kulawa tana linke sallayarta
''tsautsayi ne mami''taji abdallah ya amshe zancan yayin da tayi duru duru tana
tsaka da neman amsar da zata bawa mamin
''Allah ya tsare gaba to,amma ya kamata ka daina zuwa gun da ta samekan,don nasan bazai wuce cikin garden ba''ta fada tana hada allurai cikin syringe
maryama tsayawa kawai tayi tana kallon yadda abdallan keta
marairaita kamar qanqanin yaro,ita abun ma kunya ya dinga bata,amma shikam ta fuskanci ko ajikinshi wai an tsikari kakkausa
''wannan matarshi zata sha fama da shagwaba,mami duka ta sangartashi''tayi gulmarshi cikin zuciyarta,da sun hada ido sai ya maka ma
ta harara hakan ya sanya ta dauke kanta ta maida kan dan wani qaramin frame me masifar kyau dake kafe kan table din mamin,hoton wani yaro ne wanda bazai haura shekaru takwas ba cikin shigar tazarce da hula da takalmi sawu ciki,ko shakka babu wanna hoton ab
dallah ne lokacin quruciyarshi,kyawunshi ba loka in girmanshi ne kawai ba kyawu ne na tun usuli
ya lura hoton take kallo don haka ya miqa hannu ya tuntsurar da shi,ya dan bada qara sakamakon haduwarshi da table din har sai da mami ta dago ta dubeshi s
annan ta dubi frame din,ta fuskanci abunda yake nufi don haka murmushi kawai tayi can qasan ranta taci gaba da abunda take
bayan mamin ta kammala bashi duka wani taimako na kashe radadi da kuma tsaida dafin sai ta hada mishi da magani,minti goma tsaka
ni mami tace ya taahi su wuce amma sai ya marairaice kan cewa bari ya huta,wayarshi dake gefan system din mami ta dauki kida,kamar bazai daga ba amma yana dubawa yayi hanzarin dagwa
''sir,munga alhj haladu uba mai qusa yanzu cikin asibitin nan''abinda aka
fada kenan da ya sanyashi hanzarin miqewa,mami ta dubeshi
''lafiya abdallah
?
''
''mami ina zuwa,just twenty minute''bai tsaya sauraron komai ba ya fice daga office din,yayin da mamin ta bishi da kallo cikin ranta tana masa addu'a,ita kanta mqryam din bin
shi tayi da ido cikin mamakin me ya sanya masa kuzari haka lokaci guda,mutumin da anyi anyi ya tashi a tafi gida ya qiya
?
ya tsaya shagwaba
shudewar kusan sa'a biyu har mami ta soma nuna damuwa sai gashi ya dawo,zufa duka ta wankeshi,cikin kulawa mamin
ta dubeshi
''lafiya dai abdallah
?
''ta sake tambayarshi karo na biyu
''mami na samu nasarar kama alhj haladu,saura alhj hamza naira''ya bata amsa yana tsiyaya ruwa mai sanyi cikin tambulan na glass
ba mami ba,hatta da maryama dake zaune can gefe b
a qaramin burgeta yayi ba,tana tsammanin dazun nan taji uana zancan neman mutumin amma har ya sami nasarar cafkeshi cikin abunda bai gaza awa daya da rabi ba,fuskarta qunshe da madaukakin murmushi take fadin
''masha Allah masha Allah,lallai dana daya da d
aya ne,baka tsinta aqasa ba abdallah,fata na Allah ya tsaremin kai yaci gaba da yi maka jagora,ya baka ikon ci gaba da tsayawa akan gaskiua,ya rabaka da aikinka lafiya''
yana kurbar ruwan sanyin yana ratsa qwaqwalwarsa sannan sanyin dadin addu'ar maha
ifiya na sake shigarshi
''ameen ummi na,kullum addu'arki ita ce sirrin nasarata a rayuwa''
cikin mintina gona suka bar asibitin harda ummin don lokacin tashinta yayi
Sashensa ya wuce mami ta haura sama itama don kintsawa yayin da maryam kuma ta koma
kitchen don kammala masu abincin dare tunda tuni an fara ahirye shiryen kiran salla,fashin sallar da take ne ya bata damar ci gaba da ayyukanta
shigarta kenan ta kunna gas tana shirin aza tukunya samanshi taga kamar anyi wuf an fice daga kitchen din,da s
auri tabi hanyar fitan itama tana dube dube,bata ci nasarar ganin kowa ba sai adnan yayan zubaida dake shigowa cikin waiting room,wanda sairan qiris suyi karo da shi tayi saurin ja baya atsorace
kallo yake qare mata hade da wani shu'umin murmushi wand
a hakan ya sanyata ta tsargu,ta tsani namini mai kallo don a aqidarta takan fassara mutum ne kawai da dan iska
''yi a hankali mana baby kada ki jiwa wannan kyakkyawan jikin ciwo ko''babu abunda tace da shi sai juyawa da tayi cikin sassarfa ta koma kitchen
shi kuma ya mata rakiyar idanu,sai da ta bace ya wani lashe labba kana ya shige bangaransu
nene tayi saurin damqo wuyan rigarshi don ta fuskanci baima gansu ba a inda suke labe ita da zahariyya suna gano farfajiyar waiting parlour wucesu zaiyi,a raza
ne ya juyo
''banza solobiyo kawai,harka wani tsorata,amma ka iya tsayawa kana qarewa jikin yarinya kallo''
kansa ya shafa yana fadin''to ai nene ba laifi bane''
''kaga ni ba wannan ba,kaga alamun yarinyar nan ta fuskanci an shiga kitchen dinsu ne
?
''
''
eh to,ni dai na ganta a gurguje da alamu wani ta biyo''
''hanyar ina kaga tayi
?
''
''hanyar valcony''
ajiyar zuciya nene ta saki
''Allah na gode maka bata ga ko waye ba,kuma da alamu bata fuskanci komai ba''
''ya
?
nene
?
''adnan ya tambaya yana dagawa
uwar gira
''mun aiwatar da aikin mu,saidai mu jira sakamako kuma,indai kuwa sakamako yazo da kyau,to mafarkin kowannen mu ya gama cika,don wannan karon indai aikin mu yaje inda ake buqata to babu makawa burinnu sai ya cika''
tsallen murna yayi
''that's
why nake sonki nene,amma....''
ya katse maganar jin takun saukowa daga saman bene,zubaida ce,itama dubansu tayi kamar yadda suka dubeta,ganin yanayin fuskartq bai sauya ba ya tabbatar musu bata ji komai ba,gurin t.v ta nufa ta kunna sanna ta kamo tashar
da take da buqatar kalla ba tare da tace da su komai ba,haushinsu duka take ji don dazun sun dqn haura sama kan yadda take son abdallah yana yarfata
_kuyi haquri da wannan sakamakon na wuni gurin mama na da bata jin dadi sosai,muna buqatar addu'o'in
ku,na gode_
*mrs muhammad ce*
👑
📚
📚📚
✍
🏻
✍
🏻
✍
🏻
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*20
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
Gab da isha'i ta kammala tuwon semovita miyar busashshiyar kubewa,kan dining ta jera konai yayi net sa
nnan ta barwa baba uwani gyaran kitchen kamar ko yaushe ta shige bedroom dinta,wanka tayi ta shirya cikin atamfa doguwar riga ta haye gadonta don ba salla zata yi ba
research ta shiga yi kamar yadda al'adarta take lokaci bayan lokaci idan ta samu kanta fr
ee kamar yanzun
takwas da rabi da mintina hudu kiran mami ya shigo wayarta,a ladabce ta daga
''maryamu an kammala abinci ne
?
''
''eh mami na kammala''
''ok,taimaka don Allah ki shirya abincin cikin folding basket ki kawo nan sashen abdallah anan zamuci,
nazo bashi magani kuma ya ruqeni''