Showing 159001 words to 162000 words out of 176330 words
duniya da lahira,Allah qara maka lafiya da tsawon kwana mai amfani,ya cika rayuwarka da farinciki nutsuwa da kwanciyar hankali,yasa kayi kyakkyawan qarshe,babu shakka ka gama mana komai a rayuwa,addu'arka garemu na bin mu har kullum muna ganinta,All
ah ya jiqan magabatanka ya maka jagoranci tare da dukkan nagartattun iyaye kamar KAI_*
🙏🏽🙏🏽💖💘😍😘💝
❣
Komawa tayi taci gaba da rubuce rubucenta kafin allurar tabi jikinta tabar abdallah nan a tsaye maryam a kwance ta nutse cikin ko
gin kunya,cikin mintina da basu wuce takwas zuwa goma ba baccin ya fara dibar maryam,babu bata lokaci lokaci kuwa yayi awan gaba da ita ta fara anccinta sadidan dama kuma ga baccin jiya data ci bashinsa bata yishi cikakke ba
Mami ta waiga taga ta fara
nisa a baccin,sai ta ajjiye biron hannunta,ta jawo wayar girke ta tafi da gidanka ta danna wasu lambobi,bayan an daga ta lissafa kayan aikin da take da buqata,ba acika minti goma ba kuwa sai ga nurse ikilima wadda ya baiwa short note ta kaiwa doctor farid
a,ya faki idon mami ya watsa mata harara sai ta sadda kanta don batasan laifin me tayi ba,amsar kayan mamin tayi ta nufi drower din kusa da gadon ta ajjiye saita waiwayo ta dubi nurse iklima data ci gaba da tsaiwa
''da wani abun ne
?
''mamin ta tambayeta ta
na saka hands glove,da sauri ta girgiza kai
''a'ah,ban sani bane madam mo kina buqata ta akusa''kai ta girgizw mata tana fadin
''a'ah jeki abinki,personal issue ne''
''ok,to''ta amsa mata ta fice kamar zatayi tuntube saboda yadda abdallah ke zabga mata
harara,bayanta mami tabi ta sakawa office din key kana ta dawo ta soma bincikar maryam data dade duniyar bacci
Sosai mamin ta tausaya mata don ta lura ba qaramar barna yaron nata yayi ba,har sai da ta daga kai ta dubeshi don ta sake tabbatarwa abdalla
hn ta ne
?
,suna hada ido ya sunkuyar da kanshi wata kunya na jibgarsa ta ko ina,sai ua sake miqewa zai fice don ya rasa inda zai tsoma ransa
''kada ka budewa mutane qofa malam''haka kawai tace masa cikim dakiya,dole ya dawo sum sum ya zauna,ta fidda kayan
yin dinki don dama ta tsammaci haka shi yasa ta bada order din a hado mata da su,shi kansa sau dqya ya kalli yadda ake dinkin ya dauke kan ya dauke kansa taigar jikinsa na tashi cike da tausayi,sannu a hankali cike da qwarewa ta gama dinkin tsaf,ta jawo pa
per ta rubuta sunan magunguna kana ta zare safar hannunta ta koma kan kujerarta ta zauna tana kallon abdallahn
''duk yadda zakaji kunyar maminka dai baka da kamarta,yanzu ba don Allah ysa mun hadu da nurse halima ba na amshi takardar nayi musanyan off
ice gun farida zaka kai case din
?
,kana da tabbas bakinta zaya yi ahiru kan abinda taga kayi,this is d lasr warning kada ka sake irin wanann ganganci,ni mamarku ce abokiyar sirrinku ka fahimta
?
''kansa a qasa ya
amsa mata yana sake qaunar mamin nasa,batason
kowa ya zama mai jibantar lamuransu idan ba ita ba,shikam Allah ya bashi uwa ta kere sa'a
Gyaran murya ta sake yi sai da gabansa ya fadi
''and then.....''sai kuna ta danyi jim shima yayi shiru yana jiran cewarta
''is ok''kawai tace tana maida glass
din idonta,takardar hannunshi ta miqa masa
''ka fita wani clinic ka siyo wadan nan magungunan,kana ka biya reception ka biya kudin ganin likita''sai da ya dago ya dubeta,kudin ganin likita kuma,shi tunda yake bai taba jin koda wasa ance ya biya din ba,dub
anshi tayi ganin yayi shiru
''yadai
?
,ko ka taba ganin ana aiki kyauta a sibitin private,likita doctor farida kazo gani kuma na maka aikinka kaga you must to pay''sai ya sosa kai ya matsa daga inda yake din yana cewa
''ni ban taho da kudi ba doctor,atm ne
ajiki na''
gira ta daga sanann tace
''ok,ai suna da p.o.s ka basu su cira,ko da yake akwai kudi hannuna bari na ranta maka ka biyani''ta fada tana jawo hadaddiyar hand bag dinta dake saman table din too match da kayan jikinta ta zaro sabbin yan dubu dub
u ta miqa masa,hannu biyu yasa ya amsa kana yace
''na gode Allah ya bani ikon biya''saura kadan ta fashe da dariya ganin yadda ya wani koma duka kalar tausayi amma sai ta dake,tana son koya masa lesson ne,haka ya juya ya fita ita kuma ta saka dan labulen
nan na da ake rufe mara lafiya mai tayoyi ta kare inda maryam ke kwance taci gaba da duba patient
Har qarfe biyu maryam na baccinta shi kuma mami ta shanyashi a reception yana jira,sai da ta gama da dukkan patient din nata kana ta tura wata nurse ta k
irashi,kan abun sallah ya tadda mamin zaune da alama sallar azahar ta idar
''kayi salla ne
?
''ta tambayeshi
''ah....ina shirin...ina shirin zuwa nayi kika kirani amma bari naje nayi sai ma dawo ko
?
''ya fada a daburce,tsakanin uwa da da sai Allah,ganin yad
da yau ya maidata kamar ba maminsa ba yasa ta dan sassauta masa
''da toilet anan shiga kayi alwalar ga abun sallah kazo kayi''
''to''yace kana ya nufi toilet din yana satar kallon maryam dake bacci har yanzu
Satar dubanshi take yana sallar,gaskiya n
e maganar hausawa dake cewa da sannu wataran yaro zai zama ango,yau abdallahn ta ne ya zama ango,turo qofar dakin akayi wani matashine baqi sanye da unifaorm mai dauke da tambarin sunan asibitin ajiki,hannunshi biyu riqe da kwanduna yayi sallama mamin ta a
msa tana fadin
''bashir,har an kawo''
''eh hajiya''ya fada yana dire su a gabanta,ta jawo,kwandon tana fadin
''sannun baaba uwani kaima sannunka''ya rusuna cikin girmamawa ya amsa kana ya juya zai fice wata matashiya ta shigo itama dauke da leda baqa,it
a dinma fuskarra dauke da murmushi da girmamawa ta ajjiye ledan tana fadin
''mami gashi''ta ciro canjin tana miqa mata
''a'ah zainaba riqe kyasha ruwa''murmushi tayi tace ''na gode''
''a'ah nice da godiya''ta ja musu qofar ta fice mami ta janyo ledar ta
na dubawa,abdallah ya dan saci kallon mamin
''wo...mami...mami,wato kudin da tasa ya kai reception na ganin likita ashe sawa tayi akaje aka siyo kayan amfani da su,irinsu tea flask,rigar sawa daya cup plate sabulun wanka turare da silifas sai abin sallah
duka daidai,saidai baisan me zatayi da su ba,tunanin da ya fado masa ya sanyashi yin addu'ar Allah yasa ba kwantar da su zara ce zata yi ba
motsin maryam ya ja hankalinsu,sai tayi saurin maida idonta ra rufe tana fadin dama bata farka ba cikin zuciyar
ta,mamin ta qaraso tana mata sannu tare da tambayarta akwai wani pain da take ji,idanunta a rufe take fadin a'ah
''to sauko a hankali ki je toilet ki wanke bakinki kiyi alwala kizo kiyi sallah azahar tayi har taso to gota,kiyi a hankali fa banda gaggawa d
a dinki jikinki kada ki ja masa matsala''
''wayyo Allah na,abdallah ka gama da ni,yanzu mami ce tamin dinki ma''take fada azuciyarta,mamin ta gama karantarta don haka tace
''ki saki jikinki maryamu,ko baki yarda ni maminki bace
?
,tamkar nina haifeki kinji
''kai ta gyada sannan mamin ta kamata ta taimaka mata ta sauka
a zaune tayi sallar gogan sai kallonta yake,mamin ta ganshi amma sai ta dauke kai ta jawo plate guda daya babba ta zuba musu abincin,shinka fa ne da miyar kifi da salad da tumatir da cocum
ber,saukowa tayi qasan gun bayan ta shimfida sabuwar abun sallar ta saka hannu ta fara ci bayan tace musu''bismillah''
tsuru maryam tayi abu goma da ashirin itamakam bata iya cin abinci tare da mamin abdallag kuwa tuni ya tsoma hannunshi dama shi sabonshi
ne tare suke ci,ga kuma uwar yunwa dake addabarsa dama tunda baici abincin safe ba,rabonsa da abinci tun jiya da daddare,ganin har sun fara ci bata sanya hannu ba yasa mamin yi mata magana
''saka hannu mana 'yata,baki ga abdallah bane''kanta aduqe ta sak
a hannun suka fara cin abincin gwanin sha'awa,da wanann damar tayi amfani cikin hikima da hila take dada jan hankalinsu kan zaman aure
Sai da suka qare tas tasa abdallah ya gyara gun,nurse ta kira tace ta saka cleaners su gyara aminiyy one zata ajjiye
oatient,ta juya ta fice bayan ta amsa mata,sai abdallah ya zura mata ido yana neman ba'asi
''daina kallo na haka nan,anan zan ajjiyeta sai gobe zaku koma gida''
''ni wallahi dama sati biyu kika ce mami''maryam ta fada azuciyarta,fuskarsa ta dan sauya ta
na kure da shi
''yes,ko kuma in dauketa mu tafi gida bayan one week ta kom''da sauri ya saki fuskarsa tare da fadin ''a'ah'' cikin zuciyarsa yace''da asara ai gwara gidadanci''tilas ya sawa zuciyarsa haquri yana ji yana gani
Sai bayan isha'i mamin ta
barosu ta koma gida tace zata turo baaba uwani,bai ce wa mamin komai ba don yasan yanzun da yayi magana cibi zai zama qari,qari ya zama qaabaaba amma ya riga ya qudurce babu wani baaba uwani da zata kwana masa da mata
kiransa tayi a waya bayan ta fita di
n,a bakin mota ya taddata tana tsaye bayan ta bude side din da zata shiga,fuska a hade tace da shi
''abdallah....ka shiga taitayinka kana jina ko
?
,banason ci da zuci da rashin hankali,ba qaramin cutar musu da yarinya kayi ba,bana sin rashin haquri makaman
cin haka ya sake faruwa kaji na gaya maka,idan na haka ba matakin da zan dauka maka bazai ma dadi ba''shidai kansa na qasa har takammala ya shiga bata haquri,bata ce komai ba ta shige motarta ya fufe mata yana fadin''a sauka lafiya''bata tnaka masa ba ta k
unna motarta tayi gaba,da sassarfa ya juya ya koma cikin dakin don ya qagu yaji dumin maryamansa,wuni guda yana ganin yayi qoqari
ya iso gareta inda take kwance kan gadon dakin,qafafunsa na qasa daga cikinsa zuwa kansa yana saman ta ya daudaitafusk
arsa da tata
''kin ga abinda kika jawo mana ko
?
,haka kawai daga fara amarci zamu bige da jinya a asibiti
?
''
fuska ta bata tana zumburo baki
''na jawo mana
?
,bama kai ka jawo min ba,duka ka gama bami kunya gun mamin haka kurum''
Dariya ya qyalqyale mata
da ita kana ya kama lebanta da ya burgeshi ya dan ciza a tausashe
''bake kika ce kamar mace yar uwarki kike kallo na ba,i hope kin banbance tsakanin aya da tsakuwa ko
?
,kin yarda abdallah ba rago bane,a karo na farko yasa an baki gado
?
''
kunya ta ka
mata ta tura kanta qasan kanshi,har yau tana iya tuna lokacin data fadi maganar,a lokacin faduwar gaba take ji da bugun zuciya sosai tattare da ita,amma sam taqi kawowa zuciyarta abdallah take so,yasan ya sata jin kunya don haka ya dora da fadin yana ya ju
jjuya kansa
''nima nasha kunya maryam na fiki shan kunya ma,gwara ke bacci kike abinki,ni fa har fada aka yimin''dariya ta kamata ya ja hancinta yana fadin
''ni kike ma dariya ko,zamu hadu ne,an shiga haqqina ma baki damu ba ko,yau fa ko dumin jikinki ba
nji ba gaba daya dear na''ya fada ya na lalubarta
ganin abinda yake yi ne ya sanya ta cikin shagwaba tace
''dinkina fa zai farke''zaro ido yayi kana yq daga ta don yasan matuqar ya farke din shi da mami Allah ne zai rabasu,kujera ya janyo ya dawo g
aban gadon kamar zai shige cikinta hannunta cikin nasa ya dora kansa saman gadon suna fuskantar juna
Sauya salon muryarshi yayi cikin rada rada yace''yanzu ya za'ayi baby,nifa gaskiya mayen abun nan ne,yanzu ma a kame nake''ya qarashe maganar yana wan
i kashe mata ido,sai ta bata rai cike da tsoro
''dole ki zama jaruma baby,idan kuma kinsan ba zaki iya ba ki gayan tun wuri na fara neman aure''ya fada cikin salon jan fada,ai kam sai ta fasge
masa da kukan shawagwaba,shi kuma ya lalace gurin rarrashi dag
anan ya samu ya rage zafi abinsa,bata hanashi wannan ba kam,saboda ta fuskanci cikin sahun da yake a amzaje,idan ta hanashin ba shakka ta shiga haqqinsa sosai tunda jinya takeyi ba zata iya masa abinda ya wuce hakan ba
Allah ya rufa asiri yana shiga b
ayi baaba uwani ta shigo,nan ta zauna tana yiwa maryam sannu da jiki,cike da kunya take amsa mata,lokacin da ya fito sannu da zuwa kawai ya yiwa baaba uwanin ya fice bayan ya jefi sahibar tasa da wani kallo mai cike da qauna da bege,baifi minti goma da fit
ar tasa ba siga wata nurse ta shigo,tace baaba uwani ta taso a nuna mata dakinta inda zata kwana,nan din akwai mai kwana da madam maryam din,bata musa ba ta bita don ba sanin tsarin asibitin tayi ba batasan duk plan din abdallah bane,sai data fice kana ya
dawo dakin harda maida key kana ya shigo ya fidda kayan jikinsa ya bar singlet da three quater ya qarasa gaban plasma din dake jkkin bangovya dauki remote na reciever din,kansa tsaye ya dale gadon da maryam din ke kai a kwance bayan ya bata magungunanta ta
sha,jikinsa ya janyota ya rungumeta tsam bayan ya sauya musu tasha zuwa mbc bollywood cikin sa'a suna film din geet,lumshe idonta tayi ta sake narkewa cikin jikinsa,don tana bala'in son film din,hakan ya qara mata shauqi ya kuma hanata cewa abdallah komai
tana jinsa yana ta rage zafinsa a zafafe kamar zai hadiyeta,saidai data fuskanci zai sauya akala zata dakatar da shi,shikam ko hakan ma ya masa,ya fi masa ace baya kusa da ita
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
qarfe goma mami ta iso ta sallamesu bayan ta sake dubawa ta
tabbatar da komai normal,gargadi kam abdallah yasha shi,har ya kasa daurewa ya dafe kansa qasa qasa ''abdallah ka shiga uku,Allah ne kadai gatanka''
''baka shiga uku ba sai ka sake ganganci na dauketa gaba daya lokacin zaka tabbatar ka shiga tara ma ba uk
u ba''bai zaton zata ji ba din haka ya fece ya bar musu dakin
Da wannan dama abdallah yayi amfani ya shirya tafiye tafiyensa don gyara duk wata harka ta kasuwancinsa da ta samu baraka kamar kamfanoninsa da sauransu,wadda su nene da ahalinta suka so yi
n tsallen badake a kanta,kwana goma ya tsara zaiyi,din baijin zai iya zama guri guda da maryam bai tsallake sharadin mami ba,ya tabbata kafin dawowarsa aidai ra warke,idaan yaso yaci duniyarsa da tsinke son ranshi,don da baaba uwani ra hadosu saboda ta kul
a da maryam din ta warke sarai kamar wata me jego inji abdallah
Ana jibi zai tafi yayi niyyar gaya mata,ita ke kawo masa abinci har sashensa,kamar ko wanne lokaci taci kwalliyarta tsaf cikin atamfa fitted gown,babu wata sura tata da bata bayyana ba,qa
mshin ta kawai ya isa ya daga maka hankali,yana cin abincin ne kawai amma duka hankalinsa na gareta,daga qarshe ma fita yayi daga kansa abinci ya tureshi ya miqa mata hannu,take ta taso cikin taku na daukar hankali ta qaraso gareshi,kan cinyarsa yayi mata
masauki kana ya mannata da jikinsa ya saba aikin nasa na rage zafi,luf tayi tana karbar saqonnin da duk yake aika mata,cikin salo na jan magana yace
''ke kanki kina karbar saqonni na,amma yanzu da zance zamu fara lacture saikiyi tawaye''
aikam tuni ta za
ro ido don har yanzu bata manta wuyar baya ba,narkewa tayi ta marairaice masa,cikin wata shishshiqa ta kissa tace masa
''amma ka sani fa my ban warke ba''
''i know,shi yasa nace gwara na danyi nesa duk da zuciya bafa so''sai tayi hanzarin juyowa ta dubes
hi
''kayi nesa kuma,kamar yaya
?
''
girarsa ya dage mata ya kashe mata ido daya
''zanyi tafiya inje in gyara kamfanoni na da aka so durqusarwa,kwana goma in sha Allahu na kammala,kafin na dawo nasan kin warke kinga sai shiga aji da daukar lacture ko
?
''
Duk da ya bata kunya amma sai da ta sa masa kukan shagwaba''amma daga yin sati daya sai kace zakayi tafiya
?
kasan bazan juri rashin ganinka ba har kwana gona
?
.....nidai gaskiya.....gaskiya.....''ido ya lumshe shagwabarta na sake rudashi ne sosai
''nima
haka my dear na,nasan halina,indai naci gaba da zama din bazan iya jurewa ba,idan kuma kin amince muci gaba da darasi to''sai kuma tayi luf bayan ta noqe kafada,dariya yasa mata yana fadin
''you see''
hannunta ya kama ya dora a qirjinsa daidai zuciyarsa
yace
''kada diya na ta ta damu,kin manta zuciyarmu guda daya ce,nisan dake tsakaninmu ne kadai zai raba mu amma muna tare ne,koda mutuwa dayan yayi to muna tare,after all ma gwara nayi tafiyan tun yanzu,saboda idan aka wuce yanzu gaskiya bazan iya yinta b
a,kinsan ni ba ragon malami bane,dali barce dai na samu raguwa''kai abdallah na kasheta da salonsa,sai ta kasa ce masa komai,ranar bara baro bangaren ba sai kusan sha daya
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Washegari sai ganin lubabatu tayi yasa andauko mata ita,tayi mur
na kam qwarai duk da cike take da kewar tafiyar tasa,mami ma da ya gaya mata cewa tayi idan maryam ta yarje masa yaje shikenan,don ta riga da ta sani tafiyar tasa ce kawai zata sa yabar mata maryam din ta warke yadda ya kamata
Kuka take sosai sai ta
ji zuciyarta tayi matuqar quntata batason tafiyar tashi,bata taba sanin rabuwa da masoyi haka yake da daci ba sai yai,ashe haka matan da mazansu ke tafiye tafiye suje ji,tun hisham na matsa masa horn har ya gaji ya daina don ya bararraje a gabanta yanata f
aman aikin lallashi,so yaje yaga ba hawaye ko daya cikin idanunta amma hakan ya gagara,daga qarshe ya dubeta cikin karaya
''anya dear na ba haqura zanyi da tafiyar nan ba''da sauri ta girgiza kai
''nikam gwara kaje,sai gaba kuma mun sake watanni kace zak
a je
?
,tab,aikam,nazan yarda ba''dariya taso bashi,sai ya hade hannayensu
''is ok,indai kina son na tafi to ki share hawayen kinji''da kai ta amsa masa ta fara sharewar yana tayata,sai da yaga fuskar tata tayi fes sanann ya ciro mata hijabi ya saka mata,ya
kama hannunta suka sauko,ya dubi fuskarta yadda tasha kuka sai yayi sha'awar tsokanarata
''ashe maryama ta abdallah ce,ashe maryama na mutuwar son abdallah,ashe rabuwa da