Showing 12001 words to 15000 words out of 176330 words
cewa kenan
''kamar yadda jiya na shaida miki a waya aiki ne ya samu,yayi shige da na gurina amma yana da bambanci domin wannan a gida zaki dinga yinshi,zaki s
amu albashi mai tsoka fiye da na gurina''
ta,dubeta da aily eyes dinta''mama wanne irin aiki ne a gida
?
''
''kinsan marigayi *alhaji abdulkareem mai nasara*
?
''
sai da tadan shiga tunani sannan tace
''eh ina jin sunanshi mama''
''yauwa,kinga sanannen mu
tum ne kuma fitace tun kafin rasuwarshi,yaro daya Allah ya basu wato *Abdallah*duk da cewa yana da wata matar amma Allah abi bata haihuwa da shi ba,saidai ya riqe mata nata uaran da ta taba haifa awani gidan mata ne su biyu da nimiji daya yanzu haka duka s
una tare a gidan duk da rasuwan shi alhj abdulkareem din hakan baisa sun raba mazauni ba,mamanshi na matuqar sonshi da kaffa kaffa da lamuranshi,duk da haka ana farautar rayuwarsa don kusan sau biyu kenan ana zuba poising abincinshi,ta rasa daga ina matsal
ar take,kuma duk lokacin da hakan ya faru idan aka tashi binncike sai a samu da hannun kukunshi,hakan yasa take canza masa kuku kala kala,amma har yau babu wanda hankalinta ya kwanta da shi
abdallah shine shugaban jami'an tsaro na farin kaya wato *S S
*na nijeria gaba daya,wanda aikinsa kansa na buqatar ya zamo cikin kulawa da tsaro na musamman
bata da lokacin zama agida kasancewarta cikakkiyar likita kan fannin matsalolin da suka shafi mata,wannan ne yasa ta bayar da cigiyar amintacce ko amintacci
ya wanda ya qware kota qware afannin girki,to qawarta aminiya ta ce hakan ne yasa ta bani cigiya ni kuma naga ke kika fi cancanta da wanna aikin maryam,ina fatan kin fahimceni abunda kuma ya shige miki duhu kina iya tambaya ta''
shiru tayi domin tana
jin abun da kamar wuya,sam bata ji ya kwanta mata ba aikin,tamkar aikatau zata tayi,kenan tunda aikin dafa abinci zata gidan wasu
?
,anya kuwa zata iya amsar tayin maman,amma tana jin nauyinta ,ba zatq kallon tsabar qwayar idonta tace mata a'a kai tsaye ba,k
usan minti biyi sannan ta ajjiye numfashi
''ina ganin mama zanje na sanar da maga batana tukun,idan yaso duk abinda suka yanke akai zan sanar miki''
''yayi kyau,hakan dai dai ne maryam,wannan shike dada nunamin hankalinki da kaifin tunaninki,amma ina fat
an bazaki watsa min qasa a ido ba''
''insha Allahu''
ta fada ka a qasa''
a haka sula rqbu bayan ta baiwa hindatu dubu daya tace ta siyi kayan kwalliya
cikin mota hindatu ta isheta da karadin wallahi yaya maryam ki amshi aikin nan
murmushi kawai ta
yi
''yarin ya ce ke hindatu har yau baki da hangen nesa''
''to,ya maryam meye aibu a ciki
?
''
bata amsa mata ba sakamakon jin ringing din wayarta da tayi ta soma kiciniyar cirota dqga aljihun jakar,raliya ce mai kiran
''hello ummin fadil''
''na'am mom
myn fadil kina ina ne
?
''
''kin ganni a hanya na dawo ne a wata unguwa''
''yauwa don Allah ina son ganin ki ne ya za'ayi
?
''
''babu damuwa bari kawai na qaraso''
''yauwa ta gurina''
dariya ta bata tace ''sai na qaraso''ta maida wayar jaka sannan ta yiwa
mai adaidaita bayanin inda zai juya da su''
🎄🌲🎄🌲🎄🌲
''daga ina kuke da yammacin nan ne
?
''raliya ta tambayi maryam sanda take dire musu drinks
''hmmm,wallahi kinga haj atika ce tayi kira na,wai ta samamin aiki gidan marigayi abdul kareem mai na
sara''
sai taga fuskar raliyan ta sauya ta dan tsuketa
''ba zaki koma wani aiki ba,aure zakiyi maryam''ta gada kai tsaye tana kallon maryam din
ba tare,da kawo komai cikin zuciyarta ba tayi murmushi
''banda abinki qawata ba sai Allah ya kawo mijin ba
?
'
'ta fada cikin rashin kulawa
''Allah ya kawomiki miji maryam''sai da taji qirjinta ya wani irin buga
''miji
?
,wa ya gaya miki,qarya ne ni babu mijin da na samu''
matsowa tayi sosai ta kama hannayen ta
''maryam kin amince da ni kin kuma yarda da amincin
dake tsakaninmu
?
''
''me ya kawo wannan tambayar kuma raliya
?
''ta tambayeta cikin yanayi na shiga duhu
''maryam so nake ki auri nasir mijina''
a hagunce take kallon raliyan,jo tayi lamar ta doka mata guduma atsakiyar ka,gani take kamar ba'a hayyacint
a take ba''raliya,me kika sha yau,ko baki da lafiya
?
''
murmushi tayi
''nasan zaki fadi haka maryam,amma ras nake,kuma nasan me nake,cewa nayi mijina nake so ki aura nasir''
''shi ya aiko ki lo ke kika aiko kanki
?
''ta tambaueta tana mata kallon ba a hayy
acinta take ba
''ni na aiko kaina tare da amincewarsa''
zame hannayenta tayi ta miqe
''idan kin warke kya kirani muyi maganar da kika rani domin ita,don dai wannan ban daukeshi da muhimmanci ba''
kamo hannunta tayi
''zauna maryam,wallahi a hayyacina n
ake,kuma lafiyata lau''
wani kallo ta watsa mata''sake ni raliya,ni 'yar halak ce kuma nasan halacci na kuma yi imani da akwaishi,idan haka kike to ni ba haka nake ba,idan kuma nasir din ne ya saka ki to ki gaya masa ni maryam 'yar halak ce''ta zame h
annuwanta ta fice yayin da raliya ta bita tana qwala mata kira amma ko waiwayota bata yi ba,hindatu dake farfajiyar gidan tana waya itama wucewar maryam din ta gani sai binta tayi a baya
kuka zata yi ne ko ihu
?
me kuma yake shirin faruwa da ita
?
me yasa
guguwar rayuwa ke walagigi da ita
?
,yau wai amiyarta ke gaya mata ta auri mijinta,ta ina ta yaya ma zata iya auren mijin raliya ko su biyu ne suka rage a duniya,ko da suka ke gida mama kasa gane kanta tayi,don tunda ta shigo gidan dakinta ta wuce kai tsaye
,cikin damuwa maman ke tambauar hindatu me ya faru da maryam din
''ni dai mama da mukaje gidan hajiya lafiya lau muka fito,kuma iki ta samar mata gida alhj abdulkareem mai nasara,amma dai mun biya gidan anty raliya,to nidaiina waje bansan me suka tattauna
ba naga dai ta fito da sauri ma biyo bayanta''
''alhj abdulkareem mai nasara
?
''mama ta maimata sunan don ba boyayyen mutum bane,mai arziqi ne na gani a fada wanda akayi qiyason duka nigeria babu wanda ya kama qafarshi
''to Allah ya kayuta,indai rali
yance ai ba'a ashiga tsakaninsu,idan kuma aikin ne ma zamuji,qyaleta hindatu,nasqn zata min maganar da kanta''don shaquwar dake tsakaninsu yasa maryam bata boyema maman tata duka damuwarta
*mrs muhammad ce*
👑
📚📚📚
✍
🏻
✍
🏻
✍
🏻
✍
🏻
[9/17, 12:5
0 PM] 80k:
💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺
*ABADAN*
🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
🌺💖
💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖
🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺
▶
9
⃣
kwana guda da yini daya bata ce da maman tata komai ba,itama zuba mata idon tayi bata tambayeta ba
kwana na biyun ne qarfe uku taji sallamar raliya,tana kwanv
e can cikin dakinsu saman katifarta,don yanzu zaman daki da kwanciya kuma ta aira wanda hakan baya rasa nasaba da yawan tunanin da take fama da shi,sai da gabanta ya fadi lokacin da tqji suna gaisawa da mama ta fadi mata tana cikin dakin
jawo dankwali
nta tayi tana dauraqa tare da qoqarin yashi duka a lokaci daya,raliya ta iso bakin katifar ta zauna bayan ta shimfide fadil dake sharar bacci a gefanta
''na gode diyana,na gode''
''ai ni ke da godiya''ta fadi tana sake matse fuska
''wai ni zan ta kirank
i maruam amma kiqi dagawa
?
''
''kadan ma kika gani matuqar kina kan qudirinki,nan da dan qanqanin lokaci zansa almakashi na datse igiyar mu'amala ta dake,tunda ba son Allah da annabi kuke min ba,so kuke ku cutar da ni''
dafe bakinta raliya tayi tana kallo
n maryam din kamar yau ta fara ganinta,ta sani babu shakka ba qaramin baci ran maryam din yayi ba tunda har ta iya furta mata haka,tafi kowa sanin halinta na rashin son fada da tashin hankali
''sonki muke kuwa maryam,saidai ke dake ahirin juya manufar
mu ta alkhairi ki maisheta ta sharri,meyw aobu cikin aurenki da nasir maryam
?
''kafeta tayi da ido cikin bacin rai tace
''baki bar maganar,nan ba kenan ko raliya
?
''
''ta yaya kikeso nabar alkhairin da na hango miki ha wofanta kenan a banza
?
''
''lallai ba
bu shakka kin gaji da hulda da ni.....ina zuwa''sai ta yunqura ta miqe kana ta fice
mintina kadan sai gata sun shigo tare da mama
''wai me ya hadaku ne da raliyan
?
''maman ta tambaya tana daga tsaye ba tare da ta zauna ba
''mama kinji abunda raliya k
e fada kuwa,ba shakka ina tsammanin ta haukace ne,wai mama na auri nasir mijinta fa take cewa''
ba shiri mama ta nemi giri ta zauna,ta dubi raliya sosai
''da gaskene abunda maryama ke fadi
?
''
cike da tabbatarwa ta girgiza kai
''eh mama haka ne,ni a gan
ina ni da maryam mun zama daya,na yadda da ita na kuma aminta da kyawawan halaye da dabi'unta,na tabbata ba zata cuce ni ba,to mama laofi ne don na gayyatota tazo mu zauna qarqashin inuwa guda
?
''
azafafe maryam tace
''kinjifa mama irin abunda take ce
wa,ro billahil azim indai raliya bata sauka daga kan bakanta ba na miki rantsuwa mama har da Allah daga yau babu ni babu ita har abada''
tsot dakin yayi son su kansu aun sani matuqar maryam ta rantse akan abu to sai ta aiwatar,kuma alamu duka sun nuna iri
n yadda batun ke taba mata zuciya ba qarami bane,maman ce ta soma magana
''koda maryamu ta amince da maganar ma ni bazan amince ba,haba raliya aisai duniya ta zagemu,jama'a su saka mu a tadinsu,idan banda abunki ma raliya kwata kwata shekarunku nawa da yi
n auren,banda quruciya haka kawai kuna zamanku gwanin sha'awa ki dinga kira ma kanki kishiya uhm raliya
?
,na roqeki nima ki bar maganar haka nan kinji
?
''
qwalla ta cika mata ido ta tausayin maryam don qaunar da take mata ta fisabilillah
''shikenan mama,ko
da baki roqeni ba zan bar zancen ko don kada na rasa aminiya irin maryam,saidai....maryam na gode,na gode da kika nuna min iyaka ta''
duk da taji rashin dadin batawa raliyan da tayi amma sai taji kamar an tafiyar mata da wani qullutu da ya tokare mata wuy
a,sai taji damuwarta ta rage farashi zuwa kaso tamanin
durqusawa tayi bayan ta miqe tana qoqarin daukar fadil tace da mama
''mama ni zan wuce''
''kinga malama ajjiye fadil din ni zan daukeshi,tunda ba ke kadai bace ai uwarshi ba''cewar maruam tana y
afagyalenta don yi mata rakiya,don ta fuskanci tafiya,zata yi,ta san halin raliya ciki da bai tasan fushinta koda ta tsaidata ma ba hirar atziqi zasu yi ba
''ni kadai ce mana uwarsa tunda kinqi ubansa''ta maida mat martani tana qoqarin ficewa,murmushi kaw
ai maryam din tayi ta saba fadil din ta biyo bayanta
''halan driver ne ya kawoki
?
''
''ban sani ba,idonki ya baki amsa''tave da maryam din lokacin da auka fito tana gaba ita na binta abaya,mirmuahin dai ta kuma yi har beuty points dinta suka loba
''A
llah ya baki haquri,yau kam ai akan gwiwa kike sai lallabe''
''a'ah,akan haba nake''
amsar da ta bata ta sanya maryam tuntsirewa da dariya har itama raliyan ta dan murmusa don fushinta da maryam ba ya wani tasiri
suna isa gaban motar ta ganshi zaune,shi
ya kawota kenan,raliya ta bude ta shiga yayin da maryam ta galla masa harar lokacin da suka hada ido,dariya ya tuntsure da ita yana kallon raliya da tayi kicin kicin
''kada kice komai,don babu ruwan nasiru,kinga kanwar nan''
''babu wani nan,waye baisan
halinku maza ba,to wllahi bari kaji,idan ka sake ka yiwa aminiya ta kishiya ban yafe ba koda wace ce kuwa,ke kuma kici gaba da nema masa aire kinji ko solobiyo''ta fada harda dan kama kunnen raliyan
dariya abun nata ya basu
''ni don Allah sake min kunne,
tunda kin gujemu dai ba shikenan ba''
''indai irin wannan gudun ne raliya am sorry to say....zanta gudunku har abada''ta dan ja da baya ta rue musu qofar tana murmushi sanna ta dan sara mata shigen yadda sojoji suke
''Allah ya huci zuciyar ranki shi dad
e,oya kai kuma kaja mini aminiya ta ahankali''
''oho dai abanza tinda yau gaku a rana''ya fadi yana yiwa motar key tare da cillawa raliya gwalo
''wlh a inuwa ka ganmu,kuma duk qwaqwqwafinka ba zaka taba ganinmu a rana ba,ku sauka lafiya,sister am sorry,s
ai munyi waya''
koda ta koma gidan cikin al'ajabi suke tattauna zqncan da mama,maman ta kuma yabwa qwarai da irin qaunar dake tsakanin maryam din da raliya,ta musu addu'ar Allah ya dorar har tsufansu
sai a san nan ne maryam ta samu sukunin yiwa maman
zancan aikin da hajiya atika ta samar mata,shiru maman tayi kamar yadda maryamun tayi tana jirqn cewa maman,shudewar mintina kusan biyu kafin tace
''ke me kike gani game da aikin,tunda kinga azahjrin gaskiya zamanki babu aikin babu dadi,tunda kin riga ki
n saba,hakanan zai debe miki kewa,baya ga haka harkar makarantar hindatu wa zqi ci gaba da daukar nauyinta idan har kika daina
?
,amma ke me kike gani mene ra'ayinki
?
''
''aini mama banida wami zabi sai abunda kika ce''
''kina da zabi mana maryamu zan
tauye miki haqqinki ne
?
,amma dai abinda yafi kawai shine kici gaba da addu'a,Allah yayi miki zabi mafi alkhairi''
''ameen mama''
da haka suka saki maganar suka shiga kuma wani batun daban kuma,haka rayuwarsu take su uku suke yinta,su kashe su binne abin
su babu maiji,hakan ne ke qara haushinsu,cikin zukatan al'ummar gidan
sati guda da maganarsu da haj atika amma har yau ta kasa yanke komai a kai,kwana bakwai daidai da azahar tana sharar tsakar gida ta jiyo sallamarta,cike da mamaki ta yi mata sannu d
a zuwa sannan tayi mata jagora zuwa dakinsu
ruwan sanyi na pure water da alalen da sukayi ta ajjiye mata sannan ta zauna suka gaisa
''baki da kirki maryamu''haj atika ta fada tana dubanta
murmushi tayi ta dan sunkuyar da kai
''kiyi haquri mama''
'
'tashi kike abunki da mamanki ma zanyi magana,ko abbanki yana nan
?
''
''eh,bari na dubo miki''ta fadi tana miqewa,
taci sa'a kuwa yana niyyan fita ta tadda shi,ta sanar da shi sannan ta zura mayafinta ta fita gidan maman fatima maqociyarsu
mintina ta
latin suna cikin hira isyaku ya shigo yana zumbure zumbure
''ke kije bana yana kiranki''ya juya ya fice abinsa,maman fatima tace
''oh ni Allah,Allah ya kyauta''
''hmmmm,ameen bari naje maman fati sai anjima''maryamu tayi mata sallama ta fice
bata t
arad da haj atika ba,sai babanta da mama dake zaune
''baba gani''ya fada bayan ta samu guri gefe da su ta zauna
''maryam''
''na'am baba''
''ki shirya gobe idan Allah ya kaimu ki hada duka abunda kike da buqata hajiya zata zo zaki tafi gidan nan da kuka
yi magana da ita ta samar miki aiki''
cikin rashin fahimta ta dubeshi
''amma baba ni ina ganin koda zanyi aikin ma ai bani da buqatar tafiya da kaya na,tunda ba wani garin bane ko
?
''
''ke,bani son sakarcin banza,na riga da na gaya miki,ki hada kayanki,s
una da buqatar zamanki ne a can gidan,yo idan kin zauna anan din me zaki tsinana min,illa inyita ganinki baqinciki na ci gaba da damu na
?
,kije kawai banason kuna sauran qorafi kinji ko
?
''
kai ta gyada hawaye na layi bisa kuncinta,wannan sam bai dadash
i da qasa ba ya miqe ya fice abinsa,kai ta hada da gwiwa ta rushe da kuka,duk yadda taso daurewa zuciyarta ta kasa
''wai me yasa baba baya sona ne mama,me nayi masa
?
''ta tambaya cikin kuka
''kul maryam,kada na sake jin wannan mummunar maganar a bakinki,m
ahaifinki ya isa da ke,saboda haka nima bana buqatar wani qorafi kibi umarninshi kawai''
bata iya cewa konai ba face miqewa da tayi ta shige dakinsu zuciyarta na zafi tare da jin tsanar wannan sabon aikin,aikin da zai nisanta ta da mahaifiyarta,zai nisan
tata da 'yar uwarta,mama binta tayi da kallo tana jin tausayin diyar tata sosai na sauka cikin zuciyarta,addu'a kawai take mata cikib ranta Allah ya yanke mata wahala,ya kawo lokacin da zata zauna ta huta cikin dakin mijinta
🎄🌲🎄🌲🎄
jikinta duka a
sanyaye take shirya kayanta cikin sabon dan trolly dinta mai kyau pink wato ruwan hoda,hindatu ce ta rufe mata sannan ta jawo mata shi cikin parlour don bata da kuzarin da zata iya janshi
tsaye tayi cikin falon ta kasa cewa maman nata komai,don haway
e ne fal cikin idanunta da suya da zuciyarta ke mata,ji take kamar ta bar gida kenan,tana jin tamkar ta bar mamanta kenan,sai maman ce tace
''kuje hindatu jiranta suke,Allah ya bada sa'a,abu guda zan fada miki,ki riqe mutuncinki a duk inda kike,ki tsarw k
snki maryam ki kuma ji tsoron Allah,don babu wani abu da zan iya yi miki a lahira,iya kacin amfani na a duniya ne wajen tunatar da ke bin hanyar Allah,ki riqe amsna ki zauna da kowa lafiya''
kuka ta saki ta fada jikin mama,sai da taci kukanta sannan a sab
ule ta fice hindatu tabi bayanta da akwatin
sam basu lura da su ba sai shewa suka ji,inna hadiza nw da binta har da tafawa kamar sa'annin juna
''haka dai za'a qare a boyi boyi''inji inna hadizar,hindatu na shirin maida mata martani maryam ta damqe ha
nnunta ta jata suka fice ba tare da ta bata damar tsayawa sun taya yinsu ba
*mrs muhammad ce*
👑
📚📚📚
✍
🏻
✍
🏻
✍
🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k:
💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺
*ABADAN*
🌺🌺