Showing 60001 words to 63000 words out of 176330 words

Chapter 21 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

60

ba zata fasa ba''

murmushi mami tayi tana janyosu gabanta tare da fadin

''kai kice mata kam mun gode qwarai,kamar kuwa tasan yau bamuyi girki ba nace maryan ta bari sai sahur aikin yayi yawa''inji mami sanda ta

ke hude flask din,rake kuwa qamshi ya cika gurin

''ki mata godiya''inji mami sanda zahariyyan ke nufin fita

''zata ji kam''ta amsa mata lokacin da take qoqarin sanya qwayar idanunta cikin ta maryam a fakaice,cikin sa'a kuwa suka hada idon,wanu mummuna ka

llo mai cike da gargadi da jan kunne tayi mata kana ta fice

Gaba daya ta saki cin abincin ta zurfafa cikin tunanin yadda zata salwantar da abincin ba tare da tabar kowa ya dandana ba,tayi imani komai zasu mata ba zata iya bari tana gani gaban idonta wan

nan ahli su salwanta ba,qarshen butulcin da zata musu kenan wanda ba zata iya yafewa kanta ba har abada,cikin haka taga mami na kiciniyar bude food flask din zata zuba,da sauri ta miqe tana fadin

''mami barshi in zuba miki mana ''tuni har ta isa gabanta t

a karba don kada ta yanke mata hanzari tace ta barshi,ta jawo flask din miyar gaban table din sosai ya zama rabi kan tebur din yake zaune rabi kuma free ba matokari,sai ta jawo na abinci ta bude,da plate a gabanta amma sau tayi dabarar miqa hannunta tavdau

ko na can sashen da abida ke zaune

Tana daukar plate din ta sakeshi kan flask din miyar take nautin tangaran din ya rinjayeshi sukayi qasan table din suka tarwatse kan tiles,tangaran din ya koma piece,taja baya da sauri tana salati tate da kallon gun da

abincin suka kife

''subhanallahi ya haka maryam



''

''for god sake mami yanzu wannan wane irin kidahumanci,ita din qaraman yarinyace da zata kifar da abinci flask biyu,kayi magana kuma yanzun mami ta ji haushinka ta saka a black list''ya qarashe maganar

cikin bacin rai yana yayyarfa hannu da jujjuyawa hagu da dama kan kujerar da yake zaune

harara ta balla masa sannan ta kalli maryam

''ina fata baki ji ciwo ba maryamu''

kai ta gyada zuciyanta na wani irin gudu gefe daya kuma tana hamdala ga madaukaki

n sarki da ya bata nasara a sauqaqe ta rabasu da abinda zaya hallakasu,ita ta tsaya ta gyara gurin duk da momi tace ta bari sai ta huta tukyn amma sam ta qiya,bazata iya ba don ko quda bata fata ya dandana abincin,balle ma ta tabbata ban da awa biyu ko uku

indai da gubar abincin zai fara ratattakewa

ta gyara gurin tsaf ta kwashe bayan ta rage kadan ta samu yar roba ta zuba hade da miyarshi ta shige da shi dakin gadonta ta tura ahi qasan gado,sai da ta gama komai kafin ta kwanta ta jawo robar don dubawa,c

ikin awa uku abincin ya fita kamanninsa kamar wancan,batasan lokacin da hawaye suka soma zuba daga idonta ba

mutum abun tsoro Allah abun tsoro

yanzu dan uwanka bil'adama kake da buri yaci wannan abun



waishin wanne rin laifi ne abdallqh ya yiwa mutane

n nan ne haka da zafi da suke da burin rabashi da soron duniya



sai kace mudin an mana wahayin tabbata acikinta



kwana nawa ne kaima ka hada ya naka ya naka ka qara gaba



koda shekara miliyan zakayi wataran dai sai sun qare din ka tafi.

itakam ko kadan

batq ga abun morewa ba wajen cutar da wani bayan ka san cewa Allah bazai taba qyaleka ba sai yabi kadi,duk wanda yaci nanin nanin dole ta cishi

cike da kasala da mutuwar jiki ta shige toilet dinta tayi plushing din duka abincin ta wanke robar ta wullar

a dust bin

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Sallah bikin daya rana,cike da walwala farinciki bikin sallah ya soma gudana cikin duniyar musulmi baki dayanta,sai a lomacin mayama ta dinga ganin dangin su mami da na mahaifin Abdallah,don kusan kullum ne sai sunyi baqi,sab

oda haka bata samun zama aosai,damuwarta daya ma kada abdur rahim yace zaya zo ya samu bata da lokaci sai gashi bai ma nemi zuwanba iyakaci waya sai saqon,barka da sallah daya turo mata na credit din dubu goma yace kuma ta jirayi kayan salarta duk ranar da

zaya zo

Ta fuskanci ba kadan bane maso sun abdallah cikin danginsa daga na mamin har na abbaanshi,kishi ke hana abida zama ciin gidan tayi ficewarta yawo sai dare

''rashin sani yafi dare duhu''maryam kan fadi hakan cikin zuciyarta ko kuma tace

''bono

no rufin qofa da barawo''a duk sanda taga abida na wannna haukar kishin nata don bata da masaniyar kai kudi abdallah daga ita har zubaidan bare salma da saddiqa da bama ganinsu ake ba,har ga Allah tausayinta takeji kan fadawa son botsatstsen mutum irin abd

allah,wanda koda yana sonki zaki sha wuya da shi bare kuma baiyi da ke a ganinta

hudu ga salla suka fara samun sararawar baqin duk da ana cikin dai hidimar sallah da shagulgulanta

da la'asar ne babu dadewa da gama salla wayarta ta fara ringing,tana kan

cinyarta din haka ba jinkiri ta daga,muryar jabir ta tsinta yana mata sallama,ta amsa masa kana suka gaisa amutunce

''mai yayi zafi haka ido zaici wuta maryam,a qalla dai ai ko barka da salla a kirani ayimin''

ta dan saki murmushi

''kayi haquri,na ahig

a sabgogi ne da yawa,ayyuka sun kacame min kusan yaune ma kadai na dan samu kaina''

''gaskiya ne,ai manya dama sai da uziri''dariyar zolayan da yayi mata tayi,kafin tace komai ya dora da fadin

''ko zan iya ganinki,maryam



''tavdan fiddo ido waje kamar yan

a ganinta

''yanzu



''

''eh idan da zan samu yau din da nace miki na gode,amma da zakimin alfarma da sai mace miki mu hadu gobe''

tunaninta daya ina zata ce mishi su hadun



,sam bata da sha'awar kawoshi nan gidan kamar yadda ko kusa ba zata yarda su hadu

gidansu ba

ajiyar zuciya ta saki

''babu damuwa,muna iya haduwa gobe kamar hudu na yamma a gidan zoo ko



''

''kin ko san a itin kwanakin nan cika yake,anya zamuyi magana anutse kuwa



''

''eh nafison gurin jama'a din ai,kuma akwai bangaren da zamu iya zam

a da babu cikowar''

''shikenan babu damuwa na gode,amma baki tambayeni,mai yasa nake da buqatar mu hadun ba''

murmushin ta kuma yi

''a tun sani na da kai da alkhairi,na sanka,don haka yanzu bazan canza in maka zaton sharri ba,kaga kenan ina tsammatar

jin alkhairi ne daga bakinka''sosai yaji dadin irin shaidar da tayi masa,har yau bai fasa yaba kyawawan halayen maryamu ba,kowa tana masa kallon mutumin krki ne kamarta,hakanan tana kowa kallin mai kyakkyawar zuciya kamar yadda ita din take

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

Qarfe hudu suka fita daga gidan zuwa gidan zoo din ita da hindatu,dukkaninsu cikin kwalliyar atamfa suke riga da skert,sunyi kyau kam masha Allah

a can suka taddashi har yana zolayarsu sai yaci tararsu sun mishi african time,yayi kyau abinshi cikin

dinkin kufta ya dswo jabir dinshi na ainihi,kyakkyawan matashin saurayin nan mai yawan ado da fara'a jabiru

gurine kebantacce dake can cikin ainihin gidan ajiyar namun dajin na garin kano,tamkar lambune ska yishi na musamman kudin shigarshi ma daban ysk

e kusan ba kowa ne ma yasan da gurin ba,kujera ce irin ta siminti suka zauna a dayan shima ya zauna a dayan,sabuwar gaisuwa suka sake,maryam ta dubi jindatu tace dan bamu guri kadan to tace kana ta miqe,jabir din yace

''ai da kin qyaleta ma don maganan ya

shafeta''ta yi gaba amma ta jiyo abinda yace din sai gabanta ya fadi hakanan

''maryam,haqiqanin gaskiya na yaba da kyakkyawar tarbiyyar da kuka samu,sannan nayi baqinciki qwarai da gaske da rasa ki da nayi duk da nasan cewa komai qaddara ce daga ubangi

ji,saidai ina kwadayin hada iri da ku maryam,ina neman wata alfarma guda daya,Allah yasa wannan karon bazanyi failing ba''

cikin tattara dukkan hankalinta a kanshi tace

''babu wata alfarma da bazan iya maka ba indai ina da iko kima bata keta haddin shari

'a''

''be keta ba maryam''ya fada yana murmushi wanda ya qara masa kyau da kamala

''so nake ku bani hindatu''

idanu ta zazzaro tamkar taga wani abun tsoro idanunta kan jabir din

''jabir........shin ka manta alaqar dake tsakanin hindtu da jamila ne



,y

a da qanwa ne fa



''

''koda na taba sanin jamila a matsayin diya mace hindatu bata haramta gareni ba tunda igiyar saki ta raba tsakaninmu balle babu abinda ya taba shiga tsakanina da ita na auratayya,yadda aka kaimin ita haka na dawo musu da ita,so kika ba

bu maganar janamin auren hindatu kenan''

kai ta girgiza''haba jabir,yau ko maqota muke mu da su jamila ai duniya ta zagemu balle iba daya''

''ya kamata kiyi amfani da ilimin da Allah ya huwace miki,ki dinga saka addininki gaba da al'adarki,babu wani ab

u da ya jaramta min auren hindatu koda kuwa ke na aura matuqar mun riga da mun rabu''

cikin girgiza kai tace

''haba jabir,amma dai ai ana barin halas don kunya''

take yanayin fuskarsa ta sauya

''gwara maryamu ki fito kanki tsaye kice min ba kyason ta

rayyata da hindatu,gwara ki cemin jabir ba zamu baka hindatu na tafi qarfinka

wace iriyar kunya kike magan akanta ne maryam



su waye kima wadan da za'aji kunyar



ko kin manta jin kunyar mara kunya asara ce



har kin manta da abunda suka miki ne,shin a l

okacin da suka aikata din ba'a halicci kunya ba ne ko kiwa akwaita sune basu da ita



''ya qarashe maganar cikin bacin rai,ta bude bakinta zata yi magana ya dakatar da ita da hannunshi kana yace

''dakata maryam,bana buqatar kice komai,tun yanzun na cireki d

aga batun nan,ban neman kimin komai,zan yiwa kaina yaqin samun hindatu,naki kawai ido addu'a da fatan alkhairi''bai bata damar cewa komai ba ya tashi ya nar gin yabi hanyar da hindati tayi

kimanin minti talatin ta gaza tashi a gun,wani bangaren na zuciy

arka na gaya mata bata kgautawa jabir ba,mai son naka ai ya gama maka komai,yayin da wani,bangaren kuma ke ganin dai dai tayi,don rigima ce zata riri ba qarama ba cikin gidan,daya barin uace mata,to sai me



,da ba naki bane jabir din suka aikata abinda suka

aikata suka maidashi nasu



to ai dama idan mai guri yazo mai tabarma nade kayarshi yake

shiru shiru hindatun ma bata dawo ba,ta ciro wayarta tayi kiranta,abun mamaki sai taji jabir ne ya daga,kafin tace wani abu ya rigata

''kada ki cikata da fada gamu

nan zuwa''hangame baki tayi tana kallon wayar,bata qarasa daskarewa ba sai da ta jangosu sun jero suna tafe suna qyalqyala dariya hannun jabir din riqe da fararen ledoji masu dauke da tambarin sahad store

duban hindatun tayi saivtaga yarinyar ta waske mat

a tamkar babu wani abu da tayi,kabir me ya katse kallon da take mata ta hanyar ajjiye mata leda daya kusa da ita

''kada ki cinye min gimbiyata ki barta hala,s

duka sauran tuhumarki ki hadiyeta na karbi tutar hindatu''

bata data cewa kallinsu kawai take,

haqiqa ta san cewa indai hindatu tayo,nasarar auren jabir bata da sauran matsalar rayuwa,miji na gari kam ta gama samunshi,suka qaraci mata shaqiyancinsu suka miqe don tafiya,nan ma ya kasa ya tsare kan shi zai kaisu,hindatu ta takura tolas suka bishin ya

ajjiyau har qofar gida

suna shiga soron gidan maryam tayi saurin janyo hindatu da har tayi gaba

''hindatu ashe baki da tunani



''

ta zumburo baki

''me kuma nayi adda



''

''kin manta waye jabir tsohon mijin yayarki jamila



''

sai ta kwashe da dariya ha

r maryam na toshe mata baki kada ta dauko hankalin mutanen gidan

''nice ta biyu wajen sanin waye jabir bayan ke ta farko,to wai ma anty don autukina yaje aikin hajji sai in kasa zuwa in sauke farali nima saboda kunya



,jabir yayi min adda don na tabbatar y

ana da nagarta tunda har kika amince da shi a baya''

sai ta kuma yin qasa da murya

''baya ga haka adda wannan wata qatotuwar dama ce garemu ta rama duka cin kashin da aka mana,wallahi sai na dauki fansar duk baqincikin da suka cusa mana''

ta fuskanci

da gaske hindatun take

''Allah ya taimaka''ta fada kana ta shigeta cikin zuciyarta tana musu addu'ar tabbatar lamarin cikin nasara da farinciki

🎄🌲🎄🌲🎄

Batasan ya akayi ba itadai taji an kawo kudin hindatun har da kudin sa rana jimillar naira dub

u dubu dari uku dubu dari kudin aure dubu dari biyu kuma kudin sa rana,hakan ya sanya baba yace ta shaidawa abdur rahim ya turo a saka rana,su din ma kudin sa ranar suka bada naira dubu dari biyar,kudin sun bawa maryam din mamaki,murmushi abdur rahim din y

ayo yace

''ko nawa na bada kudin aurenki yayi kadan maryam,kinfi qarfin haka,me din mai tsada ce''murmishi kawai tayi tana sake ganin qima da darajar son da yake mata

duk abin nan da ake jama'ar gidan basu da masaniya,kusan duk ranar da za'azo din bas

u gidan suna yawon asara yawon bidar asiri,asara goma da ashirin babu kudinsu ba imani

*mrs muhammad ce*

👑

📚📚📚



🏽



🏽



🏽

[9/17, 12:54 PM] 80k:

💖💖💖💖💖💖

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺

💖💖💖💖💖💖

🌺🌺🌺🌺🌺🌺



💖🌺💖🌺



💖🌺💖



🌺

💖



💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

🌺💖🌺💖🌺💖



🌺💖🌺💖



🌺💖🌺



💖🌺



💖

© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

*_home of expert and perfect writers_*





3



5



👇🏾

*wannan

page naku ne*

👉🏾

*_haske writers asso_*

👉🏾

*huguma conversation and novels rooms_*

👇🏾

*da kuma*

👉🏾

*Zauren biebie isah*

*Allah ya bar qauna*

👍🏽



🤘🏽

*_Ankarbo daga imam bukhari r.a,manzan Allah s.a.w yace_*

*_(qarami ya yiwa babba

sallama,matafiyi ya yiwa wanda ya taras,jama'a 'yan kadan su za suyi yawa masu yawa)_*

*_a wani hadisin da imamu muslim ya rawaito daga annabin rahama s a w yace(wanda a zuciyarshi akwai girman kai daidai da qwayar zarra bazai shiga aljanna ba)_*

*Al

lah kayi mana tsari kada ka haramta mana aljannarka,ka hanamu dukkan wata baiwa ko ni'ima taka da zata yi sanadin zamowa masu girman kai*

Fadar irin farincikin da mama da iyalinta ke ciki ma bata baki ne,sunyi amanna cewa wannan ce shekarar

farincikinsu,addu'o'in da suka dade suna qwanqwasawa qofa yau kam an bude musu dukkan qofofin,duk wani tsohuwar ajiya ta mama data jibanci kadara ta daga ta saida,ta yiwa bikin shiri matuqa da gaske,ga dangi masu zuciyar yi mata da Allah ya hadata da su

takanas suka ziyarci gaya ta saida manyan gonakinta na gado guda biyu,ba qaramin kudi ta samu da su ba kasancewar yadda a yanzu kowa ya koma noma gonakin daraja suke,tuni ta fidda kudin kayan gado kayan kitchen da sauran tarkace na hindatu,maryam kam da

ma da yan kudadenta da take sa ka ran zasu isheta sayan kayan gado,ga mamakinsu saiga kudade baban su ya damqa masu a boye yace sukaje su zabi kayan gadon da suke so,shi din ma gonakinsa biyu ya siyar dake gayan,dama bashi yake amfana da su ba yan uwansa n

e,cikin rufin aairi, Allah sai gasu sun tashi da kayan gado na kere sa'a masu kyau tsada da aminci

bata sake shiga farinciki matsananci ba sai da mami ta damqa mata passport dauke da visa ta qasashe biyu saudiyya da china

''maryam,inason inje siyayya

r lefen abdallah ne,sannan ke kanki ina son in miki siyayya irin wadda uwa take wa diyarta,naso 'ya mace amma Allah bai bani ba,to a yanzun kuma sai Allah ya bani ke,naso ace lokacin bikinki da abdallah bai hade ba da ina mai tabbatar miki anan gidan zaki

zauna har akammala taro a miqa ki gidanki,saidai duk da haka bikin magaji ai bazai hana na magajiya ba,zamu fara zuwa china muyi siyayya sanan mu dawo saudiyya muyi umara,kuyi addu'a kowannanku ya roqawa kanshi alkhairi kan sabuwar rayuwar da zaya shiga,ni

da ke ne da abdallah''

rasa bakin da zata gode mata tayi saidai ta tsinci kanta cikin zubda qwallar farinciki,tabbas uwa ce,mami uwa ce wadda tasan ciwo da darajar 'ya'ya,babu shakka ko ita ta tsugunna ta haifeta iyakacina binda zata mata kenan,haduw

ars ta tabbatar daga Allah yake,bata manta yadda taqi taji batason aikin gidan mamin ashe alkhairi ne Allah yake nufinta da shi,gaskiya ne maganar Allah haka take da yake cewa cikin alqur'a ninshi mai girma

(zaku iya qin abu kuma alkhairi ne agareku,sanna

n zaku iya son abu kuma sharri ne a gareku,Allah shine ya sani ku baku sani ba)

mama kam rasa mai zata fada tayi,babu shakka duk yadda kaga Allah yayi da rayuwarka baiyi don zalunci a gareka ba,yayi ne saboda shi ne mafi sani ga abinda ya dace ga bawa

nsa

raliya har da hawayen farinciki

''damuwarki tazo qarshe diyana,Allah ya yanke miki,maqiya kuma sai su kashe kansu don baqinciki''abinda ta dinga fadi kenan fuskarta qunshe da murmushi

hindatu kam buri ya cika,don tace ko iya haka Allah ya barsu sun

gode masa,Allah ya nuna isa da buwayarshi,itama tata visa din umarar na nan jabir ya tanadar mata bayan sun angwance da wata daya

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

qarfe biyu na azahar jirgin ethopian airline zai debe su zuwa ethopia inda anan zasu fara yada zango kafin

su isa qasar sin,cikin masu rakiyar tasu harda jabir da hindatunshi,abdulrahim sai zubaida,raliya da yaronta fadil,

ranan ne abdulrahim suka fara haduwa da jabir,tuni ya dade da sanin waye jabir din da kuma matsayin da yake kai a yanzu a gun maryam di

n,don haka gaisuwar mutunci sukayi tamkar sun jima da sanin juna,kusan dukkansu sama sama suka gaisa da abdallah yaja gefe yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login