Showing 27001 words to 30000 words out of 129261 words
sanar da duniya wacece matar ubansa da ta......
Bugun k'ofa ne yasa Didi shiru, shima kuma tunaninsa ya
yanke a wajen, Nanna ce ta shigo da
Sauri ba tare da la'akari da Didi da take zaune ba ta rungumeshi a jikinta tana sakin kuka. "Tafiya zamu yi England Dear ba zan yarda su salwantar min da rayuwarka ba, dama ni na tilastaka sai kazo, ban san lamarin k'as
ar nan ya tab'arb'are haka ba."
Ta fad'a tana shafa gefen fuskarsa da sakar masa peck a kumatu, sai ji tayi Didi ta ce "Auzubillahi, Kice Nanna duk harkar nasara kin d'abeta tsaf a kanki, yanzu baki ji kunya ba da ranar Allah kike dak'umarsa da manna mas
a sumba a kumatu, sabida ki nuna
Mana ke jarababbiyace." Tsit Nanna tayi tana wasa da zoben hannunta, hankalinta ne a tashe sam bata lura da Didi da take d'akin ba balle su Hamda, duk da ita a wajenta hakan ba wani abu bane, musamman dubi da can yarda suke
rayuwa.
Nanna tsit tayi tana jin Didin na sababi kamar ta ari baki, kafin ta mik'e tsama tana kallon Hamda Ta ce "Ai sai mu tattara mu tafi tunda jarababbiyar matarsa tazo, kada kuma tayi abinda idanunmu zasu makance, ah to don kinibibi kina son mijin ki
ka tsallake kika tafi kika barshi, kin tafi agolanci gidan uwarki."
Nanna dai ko tanka mata bata yi ba, don da zarar zata tanka mata sai Hammad ya k'ifta mata ido alamar tayi shiru. Tana kallo Didi ta tasa y'ay'anta a gaba tafi da su duk da Abulkhairi yas
o zama amma ta ce "Sam, ba zan barka ba, haka kawai suje su bud'e maka ido a banza a wofi, don ina kallon almurin ubanka yarda yake narke idon nan shima jaraba ce take ci sa, sai azo ana abinda ba shikkenan ba, sahunka a likkafa ka wuce mu tafi, har kwad'o
n zogale zan maka." Abul Khair tilas ya bita, suna fita Hammad ya saki murmushi kawai yana mamakin yarda tsohuwar bata jin kunyar furta duk abinda yazo bakinta.
Ita kuwa Nanna b'ata fuska tayi sosai don abin na Didi ya bata haushi, haka kawai ta hau mata s
ababi akan abinda ba shikkenan ba har da wani cewa Agolanci taje gidan mijin Uwarta, kullum sai tayi mata wannan gorin. Hammad ya ja hannunta yana murzawa a hankali da sauri ta janye
hannunta, "Rufa min asiri, kada tayi mantuwa ta dawo kaga da gaske sai ta
sake manna mana sunan Jarababbu.
Hancinta ya ja cikin wata irin murya ya ce "Kamar fa Didi ta shiga zuciyata, jarabarce take ci na, kin san ta riga ta gama sanina tun ina yaro." Ya fad'a yana kashe mata ido da ya sata sakin murmushi tana sunne kai a jikin
sa, da gaske ita ma tayi kewarsa. A cikin kunne ya rad'a mata "Close the door." Sosai jikinta ya amsa yanayin yarda yayi mata magana har bata san sanda ta sake shigewa jikinsa ba.
_____________________________
Kwanansa biyu aka sallameshi, ya samu sa
uk'i sosai duk wasu rauni na jikinsa sun warke illa kafad'unsa da suke d'an masa ciwo kad'an.
Sai sannan Mahmah Ta ganshi duk da gorin da Didin tayi mata bai sata taje ba, don ta san da zarar taje d'in itace dai mutum ta farko da zata fara yi mata gori. Y
a fara yamad'id'i da ita taje duba d'an fari duk da sunyi mata kara, shi yasa tayi burus da zancen Didin bata je ba.
Hamda ce ta gyare musu b'angarensu tas, sai zabga k'amshi yake, sannan su kayi musu sakwara da miyar egusi, aka had'awa Hammad zob'o mai
abarba.
_____________________________
Da Yamma Ammi ta shiga dubashi, fuskarta d'auke da murmushi, ta sauke idanu a kansa, shi kuwa yana ganinta yayi kicin-kicin da fuska, baya buk'atar ganinta sam. Ta kuwa ci sa'a Nanna ta shige d'aki can ciki ta ba
r Ammin daga shi sai ita. Cikin wani salon murya ta ce "To ya jikin naka? Dafatan yanzu ka san ba wasa nake ba da nace maka zan iya aikata kisan kai, ko don waccan maganar ta mutu, ina so na sake jaddada maka matuk'ar ka cigaba da k'ok'arin fallasa sirrin
a tabbas rayuwarku kai da y'ar uwarka ko nace y'ar.........hmmn tana cikin had'ari don wallahi daga kai har ita zan iya b'atar da ku daga Doran k'asa, don haka ina k'ara jan kunnenka be careful." Ta fad'a tana shafa gefen wuyansa inda raunin yake had'e da
sakar masa wani kafirin murmushi ta ce "Mu huta lafiya, Kayi kuma gaggawar had'a ya naka ya naka ka bar k'asar nan shine kwanciyar hankalinka kai da waccan yarinyar....." ta sa kai ta fice tana sake sakin murmushi, Turus tayi a bakin k'ofa, cikin fad'uwar
gaba bayan sun yi ido biyu da..........ALKALAMIN NAZEEFAH SABO NASHE.
08033748387.
YA ABIN YAKE?
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
On Wattpad
@Nazeefah381
14
_____________________________
_______
β
π½
β
π½
β
π½πππ
β
π½
β
π½
β
π½
Ido biyu suka yi da Mahmah da take shirin shiga duba Hammad d'in, suka shiga kallon-kallo kowa da abinda yake rayawa a ransa, musamman Mahmah da haka kawai gabanta ya yanke ya fad'i.
Ammi ta d'an saki yak'en murmushi don
bata son Mahmahn ta zargi komai a ranta, duk da hakan ma bata tsira ba, don Sadiya Ta san tabbas ba wani dalili Sakina ba zata sakar mata murmushi ba, yarda ta tsaneta har kowa ya fuskanci hakan. Ga mamakinta sai ji tayi Sakinan ta ce "Ya kuma mai jiki? To
Allah ya tsare ya sake kiyaye gaba, ai ma an auna arziki." Mahmah ta d'an yi murmushi kawai had'e da furta Ameen tana shigewa cikin sashennasa, haka kawai zuciyarta ta k'i yarda da lamarin Sakinan. Tana shigewa Sakina ta saki tsaki murya can k'asa ta ce "
Algunguma, da ni kike zancen, shegiya bak'a kawai kin zo kin mamaye gida."
Wayarta da ta shigo ne yasa ta saurin shigewa b'angarenta, ganin Kady ke kiranta. "Sakna mu godewa Allah yara dai sun yi kasuwa, Senator Aruwa na sonΒ Β Β Β Shi kuma D'an majalissar
birni da kewaye yana son.Β Β Β Β Β Β Β Β Wata irin shewa Sakna ta saka, don tsananin farin ciki bata san sanda ta dinga k'wala musu kira ba.
Su d'inma a sukwane suka fito samun labarin ya saka su rungumar juna suna shewa da gaske abin ya zo musu tamkar alm
ara a lokacin da suka cire rai.
Ammi ta gargad'esu da jan bakinsu su tsuke gudun y'an hana ruwa gudu, ko zancen za suyi, sai dai suje gidan Kady, ta kalli Muneerah kafin ta ce "Saura kuma don ubanki na ji labarin ya fita, yanzu ke kika rage min na samo mik
i wani gwaskan d'an kasuwan ko b'arawon gwamnati, don ta waccan banzar bana tata kowa ma ya aureta ba matsala ta bace."
Turus y'an uwan suka yi, zuk'atansu cike da tambayoyi game da dalilin da yasa Ammin ta tsani
y'ar uwarsu, kullum abin yana damunsu ganin
dai Ammin bata son yawan zancen yasa suka tattara suka watsar da lamarin.
Wannan karan dai kam sai da Munira tayi k'uru ta ce "Wai Ammi me Hamda tayi miki kika tsaneta har haka? Alhali Ko mu da kike nunawa k'auna ba ma yi miki biyayyar da Hamda take yi m
iki."
Wani kallo Ammin ta jefeta da shi kafin ta ce "To uwata naji duka tukunna kafin na sanar miki, wallahi duk ranar da kika kuskura kika sake yi min makamanciyar wannan tambayar ranar na lahira ma sai ya fiki jin dad'i kinibabba kawai." Sunkuyar da kai
Kawai Muneerat tayi kafin ta mik'e ta shige bedroom d'insu da sauri. Tayi alk'awarin sai ta binciko dalilin da yasa ake yiwa y'ar uwarta wannan tsana ta ba gaira ba sabar, sam bata yarda da dalilin wai don an haifeta a mace bane, akwai dai wani b'oyayyen l
amarin da dole zata bincikoshi. Ammi ta bita da banzan kallo sai taji ma duk farin cikin da take ciki ya b'ace b'at, saboda wannan zancen da Munira ta tsillo mata na waccan bak'ar yarinyar mai kalar mutanen Habasha. Ta ja tsaki kawai had'e da mik'ewa.
____________________________________
Zunnuraini, bayan kwana hud'u da had'uwarsu ya zo, cikin shigarsa ta alfarma sai zabga k'amshin turaren Miyaki yake yana asalin.
Suna zaune gaba d'aya a parlourn Didi har da Nanna da Hammad da yaransu sai Hamda da ta
ke gefe take tsakurar tuwon kamar bata so, haka kawai yau ta tashi da yanayi na fad'uwar gaba da b'acin rai shi yasa take zaune a gefe, duk da surutun da Kamla take damunta da shi bai sa ta cire damuwar da take ranta ba.
Sallamar yaron da yake musu sharar
harabar waje ne ya dawo da ita cikin duniyar tunanin da ya zurfafa jin yace "Wai ana sallama da Hamda."
Da sauri ta kai idonta wajen da Hammad yake, sai dai ko alamar yaji zancen bai yi ba, gaba d'aya hankalinsa yana kan Abulkhairi da suke buga TV game,
a gark'amemiyar t.v d'in da take parlourn.
Didi tsaki ta ja tana zabga mata harara ta ce "Ji min y'ar banza, shin baki ji ana sallama da ke bane?" Jikinta a salub'e ta mik'e ra shige d'aki, Kamla na binta a baya, sai yanzu ta gane dalilin b'acin ranta, da
fad'uwar gaba, duk sabida a karo na farko saurayi yazo zance wajenta. Ba abinda ta saka a fuskarta sai ma zumbulelen Hijabin da ta saka da ya kai mata har idon sawu, sannan ta rik'e hannun Kamla suka fice, ta k'asan Ido Hammad yake kallonta, ya saki ajiya
r zuciya, a ransa yana mata fatan dacewa da abokin zama Na gari don shine kad'ai abinda Zai saka ta samu peace of mind Ta huta da gallababbiyar Uwarta.
A can bakin gate ta tarar da shi saman bonnet d'in motarsa yana danna waya hasken farin wata ya haske
kyakkyawar madaidaiciyar fuskarsa, har a zuciyarta take jin Zunnuraini ya kwanta mata kuma zata iya zaman aure da shi. Don ita dai bata hango makusa tattare da zubin halittarsa ba.
Cikin nutsuwa take takun, hannunta rik'e dana Kamla har suka isa inda yak
e. Ya d'ago fuskarsa cikin murmushi yana tsareta da idanunsa gaba d'aya yarinyat ta gama tafiya da imaninsa tun ranar da yayi tozali da ita duk da bai ga zubin halittarta ba ta fuska kam tayi masa hundred percent irin matar da yake so, mai matsakaicin kyau
ba mai manyan kyau ba.
Tsawon lokaci suka d'auka suna hira kafin ya sake sanar da ita ainahin wanene shi da sunan mahaifinsa da komai, sai dai gabanta ya fad'i jin cewa yana da mata har da yara biyu. Ganin ta firgita ya saki murmushi kafin ya ce "Kada f
a ki damu, matata bata da matsala kuma ba gida d'aya zan had'aku ba." Murmushi ta d'anyi lokaci guda kuma yana sake burgeta ganin ba halinsu d'aya da sauran maza ba masu kushe matansu na gida a yayin da suke neman aure madadin haka ma shi yabon tashi matar
yake, nan take zuciyarta ta sake amincewa da shi hundred percent.
Da zai tafi ya mik'a mata sabuwar waya dal a hannunta, ganin ta k'i karb'a sai ya mik'awa Kamla had'e da fad'in ya sunan k'anwar tamu don da gani babu tambaya k'anwarmu ce ga kama nan b'a
ro-b'aro. Hamda murmushi ta saki kafin tace Baka canka daidai ba, Niece d'ina ce ba k'anwa ba." cikin mamaki ya ce "Ai kuwa wannan ko y'ar waye tabbas mu ya haifawa y'a don kamar babu banbanci. Masha Allah, Idan kin gama shawarar please ki fad'a a gida Zan
turo magabatana so samu ne ma ki azimi a gida na, amma na san yayi wuri don haka zan barshi Immediately after Sallah Insha Allah." Da sauri ta shige Gida cikin matsananciyar kunya.
Da murna Didi ta karb'i kwalin wayar tana cewa "Masha Allah, haka muke s
o kab'akin arziki, kice saurayin naki mai d'an maik'o ne? Har da dalleliyar waya haka, gaya min waye ubansa anan garin? Burina ki auri wanda uwarki zuciyarta zata kusa bugawa ta mutu kowa ma ya huta, Allah yasa dai Ubansa yafi d'angote kud'i."
Wani tsaki
Hammad ya ja kafin ya ce "Ai duk halinku d'aya da Ammin shegen son abin duniya, madadin kiyi mata fatan samun mutumin k'warai sai ki wani ce Allah yasa Ubansa yafi d'angote kud'i, mhmn don dai baki san arzikin d'angoten bane, ke kuma shashasha ki tsaya da
ka tatata kada ki samo mutumin arziki ki tsaya neman mai dukiya
Ba mai zuciya ba."
Sak'ek'e Didi tayi tana kallonsa baki a mele kafin tace "Kaji min mutum banda kai d'in wanta ne da sai nace bak'in ciki da hassada kake mata, waye yak'i dad'i a duniya ina
ce ko kai yanzu d'iyar d'angote Ta ce zata aureka murna zaka yi."
Bai bi ta kanta ba ya fice don ma ya cusa mata takaici har da jan hannun Nanna kamar zai mayar da ita ciki, duk da Nannan na turjewa Didi ta ce "Jarababbe, jarabar ta motsa ai ni yanzu lama
rinku tsoro yake bani, mata ki bi ki nanik'ewa miji, Allah dai ya kyauta." Dariya kawai suka fita suna yi. Hamda ma dariyar take kafin ta shige d'aki tana dafe da k'irjinta saboda tsananin bugun da yake mata.
__________________________
Ciwon cikin da
ya murd'awa Muneerah cikin dare da misalin Sha biyun dare ne ya sata fitowa daga bedroom d'insu don ta samo magani a first aid box da yake d'akin Amminsu.
Kasancewar dare ne kafin ta murd'a k'ofar d'akin ta ji sautin muryar Ammin da alama waya take jin ta
na kiran sunan Hamda yasa ta dakata da bud'e k'ofar ta kara kanta sosai a jikin k'ofar sai taji Ammin ta cigaba da cewa "Kin san sarai ta yarda aka samar da yarinyar nan? Ta yaya kike tunanin hankalina zai kwanta idan ban kawar da ita ba, duk ranar da Umar
ya san maganar nan na ha'intarsa da nayi ha'inci mai muni ina tabbatar miki Mami ba zan kwana da igiyar aurensa ba, don Allah Mami ki nemar min mafita wallahi kaina ya k'ulle, na rasa yarda zan yi, don na lura yaron nan bai k'i ya fallasa sirrin nan ba ko
da shi zai kwana a ciki, na tabbata akwai abinda Hammad ya taka shirunsa ba yana nufin ya hak'ura bane musamman da na san ya kwana da sanin cewa ni na turo mutanennan suka yi masa duka cikin dare.......
Wata irin hajijiyace ta fara d'iban Munirat ji da g
aninta duk suka d'auke na wuncin gadi, a take ta kurma wani uban ihu........
β
π½
β
π½
β
π½
β
π½
Jikar Nashe//DON SAMUN WANNAN LITTAFIN KYAUTA NA YA ABIN YAKE SHIGA WANNAN LINK D
β
IN ZA
β
A DINGA TURASHI SAU UKU A RANA.
DAGA ALKALAMIN NAZEEFAH SABO NASHE
β
Open
this link to join my WhatsApp Group: https://
chat.whatsapp.com/5Y2EmZDu7OvHg6iDTCY81D
ALK'ALAMIN JIKAR NASHE
(Mai tak'ama da ikon Subhana)
YA ABIN YAKE?
08033748387
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b
283a378e
On Wattpad @Nazeefah381
(Daga yanzu ba zaku sake samun wannan book d
β
in ba idan kuna son cigaban labarin a kyauta kai tsaye ku shiga group d
β
in ZAUREN JIKAR NASHE. Zaku dinga samunsa update uku a rana kullum. Duk domin jin da
β
dinku. Nagode.)
15
β
π½
β
π½
β
π½ππππ
β
π½
β
π½
β
π½
__________________________________
Da sauri Sakina ta fito daga bedroom d'inta, hankalinta a tashe dafatan Munira bata ji abinda take cewa mahaifiyarta a waya ba.
Turus tayi ganin Muniran a k'asa tana dafe da gwiyoyinta hawa
ye shab'e-shab'e a fuskarta, alamarta ya nuna kamar fad'uwa tayi. Sakina ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce "Ke kuma lafiya cikin darennan kike kurma uban ihu?" Munirat ta tattaro duk wata nutsuwa Ta saka a fuskarta, bata son Ammin ta fahimci ta ji zancen d
a take, ta san idan har ta gane zata iya d'aukan ko wane mataki a kanta, don haka murya na rawa ta ce "Ciki na ke azabar ciwo, kuma na zo amsar magani sai na zame anan." Ammi ta saka hannu ta mik'ar da ita had'e da fad'in Ayya muje ki sha maganin to, ko da
i period pain ne?" Ta girgiza kai jikinta a salub'e, kafin ta bi bayan Ammin zuciyarta na sake mamakin halayyar Ammin.
Tana shan maganin tayi saurin ficewa daga d'akin, nutsuwa take buk'ata gami da dogon nazari akan maganar nan da ta jiyo, tabbas biri yay
i kama da mutum, amma waye uban Hamdan shine abinda ta kasa ganewa.
Ta dad'e tana juyi a saman gadonta dafatan barci ya kwasheta amma ina wannan dare kam tuni suka yi hannun riga da barci, ciwon cikin ma tuni ta neme shi ta rasa, k'wak'walwarta ta tafi
dogon nazari, tunaninta ya tsaya cak zuciyarta na wani irin bugu bata son abinda take tunanin ya tabbata, bata fata ko kad'an idan hakan ta kasance ba Ammi kad'ai ba su kansu abin kunya ne a wajensu.
HAMMAD zuciyarta take ta bata a matsayin uban da yayi
cikin Hamda, idan ba haka ba me zai saka y'arsa tayi kama kwabo da kwabo da Hamda, kamar da kana gani ko ba'a fad'a maka ba zaka san sun had'a jini d'aya. Ta runtse idonta wasu hawaye na zubo mata, ya zama dole ta fallasa sirrin nan, ko Ammi Ta hankalta ta
nemi tuba ga Allah, Sannan zuciyarta itama ta huta da dogon tunani, idan ba haka ba kuwa tabbas zuciyatta zata buga. Ranar dai kam akan idonta aka yi kiran Assalatu abinda bata tab'a yi ba kenan a rayuwarta.
_________________
Sukuku ta tashi da safen,
duk da barcin da yake rinjayar idonta, amma ba zata iya yi ba, Neman wanda zata tunkura da zancen take direct zuciyarta ta amince ta jewa da Anty Lauratu da zancen idan yaso ta gaya mata kada ta sake ta ce