Showing 54001 words to 57000 words out of 129261 words

Chapter 19 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

71

a bakinta tana taunawa tana jifansu da wani murd'ad'd'en kallo da kowa ya kasa gane ma'anar sa. "Bayan Tawon lokacin da bakina ya tamu a date Yau All

ah ya bute min ti Alhamdulillah" kaf ahalin wajen da suka ji muryar Didin ba wanda bai d'ago kai ya zuba mata ido ba. Cikin tsananin farin ciki idan ka d'auke Ammi da take dariyar yak'e gabanta yana dukan tara-tara, duk da k'ok'arin tattaro nutsuwa ta sawa

kanta al'amarin ya gagara sai share gumin da yake tsatstsafo mata take "Ta kanka zan fara Umaru, tabbat da utmanu yana raye tai ya yi Allah wadaran halinka. Ina aka tab'a tali'a haka fitabilillahi ba a

Ji ta bakin Hammad ba ka zartar da hukunci. Ko da yak

e ni ba dan te komai ba amma Hammad dai do ya warware k'ullin kowa ya fahimci yarda abin yake. Ku tati ku bani wuri dama abinda dan fad'a kenan kuma don uwal mutum ya take danne min baki."  Ta fad'a wurgawa Sakina harara. Lauratu kam sai da ta dara son ran

ta kafin ta kalli Didin ta ce "Ikon Allah Didi maganarki ta koma ta yara." "Ta uwal yala ta koma ba ta yala ba kin ga laulatu ki kiyayeni. Ja'ila kawai ki tattara tilginki ki tafi an gode da diyala." Lauratu ta k'unshe bakinta sannan ta shige d'aki.

___

____

Tunda ta koma sashenta ta ja hannun Kady suka danna uwar d'aki sannan ta rufe k'ofa har da murza key. Ba kad'an ba lamarin ya gigita ta. Ta dubi Kady ta ce "Aminiya na shiga uku wannan almurar matar so take ta jefani a masifa, yanzu maganr dawowar Ham

mad take wai ya zo ya warware musu yarda abin yake." Ita kanta Kady zufa ce take keto mata gaba d'aya kanta ya k'ulle ta rasa mafita in dai haka ne kuwa tabbas suna cikin gararin masifa ta dad'e cikin nazari kafin ta

d'ago ta ce "Kurciya za'a yi masa ya ji

sam ba ya son dawowa Nigeriar ma har almurar tsohuwar nan ta mula tukunna." Sakina ta saki ajiyar zuciya tabbas wannan shawarar ita ce hanya mai b'ullewa madalla da samun k'awar arziki kamar ki Kady."

______________

Wata iriyar duniya suka wulla dag

a ita har shi har bata san sanda alamuran suka jirkita zuwa yarda ba tayi tsammani ba, har sai da ta ji ya amshi mutuntakarta ta d'iya mace sannan ta ankare bayan ta ji wani zafi da rad'ad'i da ya ratsa mata har k'ololuwar kanta. Didi kawai take kira tana

sake kai masa bahagon cizo.

Murmushi kawai take sake bayan ta gama tuna duk abinda ya wakana tana kalli bayansa yana shigewa toilet don yin nasa wankan da kansa ya taimaka mata ta yi wankan saboda d'an banzan raki da take masa sai yau ya tabbatar shagwab'a

b'b'iya ya aura kalar matar da yake so. Ta mik'e zaune da kyar tana bin d'an b'ingilin towel d'in da yake jikinta da kallo kunya ta kamata ta yi saurin suturce jikinta da undies sannan ta saka doguwar riga har k'asa. Duk abinda take tana yinsa da sauri ne

bata san ya fito ya sameta ga zafi da rad'd'in da take ji yana sake hauhawa yana neman haifar mata zazzab'i kan kace meye wannan kuwa hak'oranta sun fara barazanar datsewa cikin sauri ta shige cikin bargon tana kakkarwa still ba ta daina jin sanyin ba.

Y

a dad'e a toilet d'in cikin nishad'i yake lumshe idonsa tabbas da kansa yau ya yarda da wani mawak'i yake cewa mata suna suka tara. Ashe ba k'aramin gata ya yiwa kansa ba da ya auri Hamda ni'ima daga indallahi.

Bai k'i a lokacin ma ya sake kusantarta ba sa

i dai ya lura Hamdan akwai d'an banzan raki bata daga cikin layin mata masu juriya a wannan fagen. Da kyar ya fito daga kwamin wankan sanye da rigar wanka yana goge sumar kansa da towel fuskarsa fal murmushin da ya kasa barin fuskarsa.

Da wak'arsa ya fit

o idanunsa suka sauka a kan ta da ta k'udundune kanta tana rawar d'ari da sauri ya k'arasa bakin gadon ya d'an bud'e dubet d'in. Ta yi saurin janye wa "Please Yaya Hammad sanyi" cikin mamaki ya saka hannunsa a jikinta ya ji zafi rad'au da sauri ya ce "Kai

me ya sameki yanzu-yanzu?" Ba bakin magana sai kakkarwa take tana k'ok'arin sake k'udundune jikinta. Shiga cikin bargon ya yi ya jata jikinsa sosai ya rungumeta yana lalubar kiran Doctorn da zai zo ya duba ta. Shafa gashinta kawai yake yana sake gaya mata

wasu dad'ad'an kalamai " sannu kin ji zuciyata mhmn ni ne ko? Ki yi hak'uri sweetie ba zan sake ba." Shi kansa wasu abubuwan bai san yana fad'a mata su ba. Jin sa a jikinta ya d'an lafar mata da zazzab'i sai dai bata daina jin zafin da take ji a k'asanta b

a.

Da kansa ya shigo da Doctor d'in ya bata magani har da allura da sai da ya matseta sosai a jikinsa yana hura mata kunne sannan ta yarda aka yi mata allurar.

A jikinsa barcin wahala ya d'auketa yana ta aukin shafa bayanta kamar k'aramar yarinya. Shi ka

nsa

barcin ne ya d'aukeshi cikin annashuwa da tarin farin cikin da bai tab'a risksr kansa a ciki ba.

Kiran sallar azahar ne ya farkar da su. Ita ta fara tashi ta bud'e idanunta da suka yi mata nauyi kad'an ta zubesu akan fuskarsa mai tarin haiba da nutsu

wa. Ta saki murmushi tana ji tamkar ta sa hannu ta ja pointed nose d'insa. Sai ta ga ya bud'e idon ya zuba mata idanunsa cikin nata yana sakin murmushin ya jata jikinsa "Kwanta ki huta Nuri ta" ta k'udundune kanta a k'irjinsa a hankali cikin matsananciyar

kunya ta ce "Sallah" Da sauri ya mik'e yana duban agogo sam ya manta da d'auko su Kamla a makaranta. Shi ya ja su Jam'i suka yi Sallah sannan ya kalleta ya ce "Bari in d'auko yara a makaranta mai zaki ci in siyo miki." Girgiza kai ta yi kawai ta ce "Bakoma

i zan sha tea"

Da kansa ya je kitchen d'in ya had'o mata tea mai kauri ya kawo mata. Da kyar ta runtse idonta kafin ta shanye. Ganin yanayin jikin nata yasa ya yiwa Musty waya akan ya taimakeshi ya d'auko su Kamla cikin dariyar shak'iyanci ya ce "Ka tafka

tsiyar kenan an samu y'ar shila." Tsaki Hammad ya ja kafin ya ce "Allah ya shiyeka saura idan ka je d'an banzan surutunka ya sa ka gaya mata na yi aure ba yanzu nake son ta sani ba." Musty ya ja tsaki "Ni fa ban ga dalilin b'oye mata ba, ka sanar da ita k

awai Malam ai ba ita take aurenk ba." Bai jira abinda zai ce ba ya katse wayar Hammad ya dafe kansa tunani fal ransa kada Musty ya jik'a masa aiki shi ba yanzu yake son sanr da ita ba.

Musty na parking Nanna ta fito daga gidan mamaki da fargaba fal rant

a saboda hakan bata tab'a faruwa ba wani uzuri bai tab'a saka shi k'in d'auko mata yara a makaranta ba. Ta daure ta k'arasa cikin fargaba ta ce "Lafiya Musty ina Dear na na ga kai ka d



aukosu?" "Yana wajen amarya mana"

Kash!

Jikar Nashe ce.ALKALAMIN

JIKAR NASHE.

YA ABIN YAKE?

08033748387.

24

Haka Mustyn ya so ya ce a zahirance sai dai ya tuna warning d'in abokinsa akan fad'ar hakan don haka ya guntse furucinsa had'e da sakin murmushi kad'an ya ce "Afuwa uwargida ya d'an shiga busy ne a office s

hi yasa ba ki gan shi ba." Nanna ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa kafin ta ce "Ko da na ji, ai shikkenan ku wuce mu je gida kuma tun d'azu fa nake kiran wayarsa ta k'i shiga."

Musty ya d'an saki murmushin sa kafin ya ce "aikin da yake yi ne mai mahimma

ncin gaske ne shi yasa ba ki gan shi ba." Ta d'an tab'e baki ta ce "Allah ya taimaka ka gaisa min da madam." Ya d'aga kai yana fisgar motar sa da sauri zuciyarsa fal da tunanin yarda za'a kark'e da wannan aure na abokinsa da kai tsaye zai iya kiransa auren

Drama. Ya saki murmushi yana jijjiga kai tabbas Hammad akwai k'wallan shege. Ko da ya kira wayarsa still a kashe take.

__________________

Sai magriba sannan ya fara shirin tafiya gida. Bayan wuni da yayi yana jigilar ta da jinyarta da gaske ya lura Ha

mda raki ne da ita na gasken gaske. Gaba d'aya ta bi ta narke masa. Yanzun ma tana zaune tana ganin yarda yake shiryawa ya d'au kayan da ya zo da su ya mayar jikinsa sannan ya zauna a gefenta yana mata kallon k'asan ido murmurshi fal fuskarsa. Gefen kumatu

n ta ya shafa kafin ya ce "Nuri ta zan tafi. Gobe ki shirya da wuri za muje shopping kin ga saura 4 days azimi. Duk dama ina tunanin kafin sallah zamu wuce gida don Gwaggo Asma ta matsa sai na koma." Shiru ta yi masa tana cono bakinta alamar zuciyar a kusa

take. Ya matso da ita jikinsa sosai yana k'ok'arin lalubo k'wayar idanunta da ta runtse cikin muryar shagwab'a  ta ce "Ni tsoro nake ji." Ya bud'e ido yana kallonta sosai cikin mamaki da ganin hawaye na malala a fuskarta. Ya sa hannu ya share mata hawayen

saman fuskarta yana mamakin rigimarta "Yanzu me kike son ayi? su nan garin fa ba su da aljannu balle ki ce tsoro kike ji ba abinda zai sameki fa." Turo baki tayi kawai ta mik'e ta shige d'aki zuciyarta a tunzire gani take bai damu da ita ba, idan banda ha

ka ta ya zai tsallake ya bar ta a condition d'in da take, don kawai ba ya son b'acin ran matarsa.

Ya dad'e rik'e da kansa kafin ya mik'e yabi bayanta waya a kunne yana neman layin Nanna. A karo na farko Hamda zata saka shi yiwa matarsa k'arya. Kafin ya s

higa bedroom d'in Nanna ta d'au wayar ranta a b'ace ta ce "Yanzu Dear ina ka shige tun fitar safe?" Ya saki ajiyar numfashi kafin ya ce "Nanna am sorry aiyuka ne suka rincab'emin sai da asuba Zan dawo please take care ki rufe gidan." Kafin ta ce komai ya k

atse wayar ya kasheta gaba d'aya sannan ya shiga d'akin a zuciyarsa ya ce "Bari naje na ga Danger sam bai San yarinyar nan itama y'ar rigima bace sai yanzu.

A zaune a gefen gadon ya sameta fuskarta a had'e sosai da alama ma hawaye ta gama sharewa.

Yana mu

rmushi ya k'arasa kusa da ita kafin ya zauna a gefenta yana zuba hannayensa cikin tattausan hannunta "Shikkenan hankalinki ya kwanta ba zan tafi ba sai da sassafe."

Ji tayi abinda ya tsaya mata a k'irji ya fad'a mata ta d'ago tana haske fuskarsa da murmush

i ya lakace mata hanci had'e da jan hancin "Rigima idan ban da son kai haka kawai ki yiwa mata fashin mijinta, yanzu yau ya kike so ta yi bayan mun saba kwana gado d'aya." Wani kallo da ta watso masa ne ya saka shi sakin dariyar da bai shirya ba Ya dafe k'

irjinta yana fad'in "Zuciyar ta kwanta kishi ko? Ashe ana so na?" Ta lumshe idanunta kawai tana ture hannayensa "Ana so ana kaiwa kasuwa ai tunda kika ce sai na kwana yau kuwa zaki fanshi Nanna duk wani abinda take min kema

sai kin yi min shi. Wanka kafin

na kwanta ta kuma shayar da ni tea da bakinta." Da sauri ta waro ido wata matsananciyar kunya na kamata ta ce "Ni fa ba don haka na ce ka kwana ba tsoro nake ji." Murmushi kawai ya saki yana janta tsaye tana tattale k'afa da kyar taje tafiya tsaf ya sunkuc

eta "Yarinya idan ma za ki mik'e ki mik'e yau mai till down ce." Ta runtse idonta jin lab'b'ansa a saman nata.

______________________

Ammi hankali tashe take kallon malamin da suke zube a gabansa kafin ta ce "Malam ban gane ka yi iya yinka asiri ya k'i

shiga jikinsa ba?" Fuskarsa a d'aure ya ce "Hakan da na gaya miki shine gaskiya kuma duk wanda ya ce zai sake miki asiri akan yaronnan ya ci shi k'arya yake yanzu jikinsa a tsare yake kuma kullum sai ya yi azkar bana haufi akan haka.don duk aljannin da na

tura jikinsa a k'one yake dawo min." Sakina da Kady suka runtse idanunsu cikin tashin hankali suka mik'e. ko sallama ba su yi masa ba suka fice.

Ko a mota maganar da suka dinga yi kenan,  Sakina ta ciji yatsa ta ce "Ga shi gari ba kusa ba balle mu k'adda

mar masa ina ga Didin kawai za mu aika da ita lahira don ni dai itace matsalata."  Kady girgiza kai kawai ta tabbatar mata hakan shine maslaha. "Ki nemi guba mai k'arfi ko ta shak'awa ce a saka mata a turaren wuta ta shak'a ta margaya." Suka tuntsire da da

riya had'e da tafawa don suna hango alamun nasara a tare da hakan. Kady ta saki dafa ta kafin ta ce "K'awata kafin hakan ya faru sai kin san yarda kika yi kika had'a gagarimin tashin hankali tsakanin Asma'u da Umar don na lura itace matsalarmu." Sakina ta

girgiza kai tabbas ta yarda da Zancen k'awarta tabbas Asma'u ita ce matsalarta a wannan tafiyar. Ta shiga tunanin irin makircin da zata k'ulla mata. Murmushin mugunta ta saki tana dafa kafad'ar Kady "In dai wannan ce ki bar ni da ita a darennan Ba sai gobe

ba zan yi maganinta. Ba dai yau girki na ba sai na zautashi na rikita masa kwanya na gigitasshi kafin na wuntsilo masa da maganar Shegiyar." Dariya sosai suka saka har suna sake tafawa Kady ta ce "K'awata ai na san ki ta wannan fannin ba sauk'i kina ragar

gazar y'an mazan. Na rasa wace irin baiwa Allah ya baki da har yau ba ki fara salamcewa ba." Sakina ta yi murmushi kawai kafin ta yi reverse da mota tana fad'in "Shima gogan kullum zancensa Kenan kullum kamar sabuwa nake dal a leda."

Haka dai suka yi ta hi

rarsu da makircinsu kafin su isa gida.

Asma'u ta samu Sadiya a d'akinta. Ta mik'a mata wayar hannunta bayan ta danna recording d'in da ta d'auki su Sakina kaf hirarsu ta d'azu ta fito a cikin wayar. Tsananin mamaki da frigici ya kama Mahmah ta kalli Asm

a'u kafin ta ce "Yanzu Umman yara shaid'anancin Sakina har ya kai haka? Ita ta rufewa Didi baki fa na ji tace." Asma'u ta girgiza kai "Sharrin Sakina ya zarce hakan, kada ki gayawa kowa lokaci kawai nake jira da zan bayyanawa duniya wacece Sakina? Ki kuma

tursasa Hammad ya dawo a yi mai gaba d'aya. Yanzu dai kin tabbatar da cewa k'arya take Hamda ba jinin Hammad bace?" Sadiya ta girgiza kai cikin jinjina girman lamarin ta ce "Tabbas! Idan kuwa haka ne ya zama dole d'anki ya dawo nan kwana kusa ya dawo mata

da shegiyar y'arta da ta nanik'a

masa ta je can ta nemi Ubanta. Ranar zan ga Abbu da wani ido zai kalleni bayan ya gama tozarta ni a idon matar nan duk abinda na yi ban iya ba Sakina ce ta iya. Sau tari ya sha kira na da Sakina madadin Sadiya. Shimfid'ar a

ure kuwa tuni na sallama mata don ko na kai kaina raina ne yake b'aci. Abincina sai ya ga dama yake ci. Akwai ranar da fa cikin dare ya buk'aci na siyar masa da kwana na ya je ya tara da Sakina wallahi Asma'u ranar kukan jini ne kawai ban yi ba sabida bak'

in ciki. Shekara da shekaru fa bak'in ciki da nake fuskanta kenan." Hawaye ne kawai yake malala a idanunta alamar abin yana mata ciwo sosai. Asma'u jikinta ya yi sanyi da jin wannan babbar lamarin tabbas sun san d'an Uwansu baya adalci a tsakanin matansa a

mma sam bata san lamarin ya ta'azzara har haka ba. Ta jinjinawa hak'uri irin na Sadiya da tarin kawaicinta tsawon shekaru tana k'unshe da wannan bak'in cikin tana danneshi a ranta. Tabbas ta cancanci lambar yabo. Kasa ce mata komai ta yi illa kama hannunta

da ta yi ta manna mata wayar da Kiran Hammad ya shigo alamar ya ji Kiran da suka yi masa bai d'aga ba ya biyota. Muryar Sadiyar a dashe ta ce "Hello Hammad kana ji na?" Da sauri Hammad ya amsa da "Eh Mahmah ina jin ki, ya na ji kamar kuka ki ke lafiya dai

ko?" Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce "Ya Zama dole gareka ka bi umarnina in dai ni na durk'usa na haifeka ka tattaro ka taho Nigeria a satin nan. Kuma taho musu da shegiyar y'ar su idan kuma ka k'i ina tabbatar maka ba ni ba kai."  Ta kashe wayar bayan ta

kalli Asma'u Tana murmushi ta ce "Ummansu idan ba haka na yi masa ba ba zai zo ba, yanzu kuwa na tabbata hakan da na yi masa zai saka shi ba shiri ya taho." Asma'u ta girgiza kai ta ce hakan ya yi.

Shi kuwa Hammad kasak'e ya yi da wayar a hannunsa yana

shafa kan Hamda da ta dage sai ya sata ta yi barci kafin ya fice bayan sun yi sallahr asuba. Tana jinsa tayi lamo a jikinsa sam rabuwa ce bata son yi da shi. Tana son jinta a jikinsa manne da juna musamman Idan yana shafata sai ta ji ta a wata duniyar da b

ata fatan abinda zai raba su. Ta sake juyi a jikinsa ta na d'an bud'e idonta a kansa ya sakar mata murmushi "Bari muje na yi mana booking flight zuwa nan da nextweek za mu tafi Nigeria Mahmah ta matsa." Sosai ta ware idonta a kansa har hakan ya saka shi ka

iwa idon sumbata murya a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login