Showing 60001 words to 63000 words out of 129261 words

Chapter 21 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

81

kika kwace mata ni ya zama dole ki rage kishin nan don har yanzu Nanna bata san na aureki ba

ne da kin gane kalar kishinki bakomai bane akan nata. Shekarar mu kusan nawa ko gado ba ma rabawa sai ta kama dole ko haihuwa ta yi bana yarda mu raba d'aki. Kullu yaumin manne take a jikina." Wannan karan Hamda ji ta yi kamar kanta yana son darewa biyu da

sauri ta runtse idonta cikin b'acin rai ta ce "Ka san da haka wa ya ce ka aureni me yasa baka bari zunnuraini ya aureni ba? Ko kuma ka kyaleni na samo mijina ba mijin wata ba." Da sauri ya d'alle bakinta cikin jin zafin furucinta ya kuma manne ta da jikin

sa yana ganin kamar wani zai kwace masa ita. Haushin lafazinta ne ya sa ya dinga datse leb'ensa ya kuma kakkafe ta da idanunsa "Kada ki sake min kwatankwacin wannan furucin. Shi kansa Zunnurainin ji na yi kamar na harbeshi san da na ganku kuna zance. A zuw

ansa na biyu kuwa da kaina na sameshi na ja kunnensa akan cewa an miki miji ya ja mutuncinsa. Ta yi lamo a jikinsa tana jin yarda yanayin bugawar zuciyarsa ya sauya ashe shima dai yana kishinta ba ita kad'ai take kishinsa ba. Shafa kanta ya yi ya jishi cun

kus alamar yau bata taje ba.

Ya ja gashin sosai kafin ya ce "Dole gobe da kaina na kai ki saloon a gyara gashin nan ya yi tauri da yawa ba irin na Nanna bane mai taushin gaske." Da sauri ya rik'e bakinsa dariya na shirin kama shi ganin yarda ta yi da fuska

ya ja karan hancinta "Seriously gashin Nanna ya fi na ki kyau ko don ita tana gyarawa ne. Ke ma ki dage da gyara don ina son inji gashin mace yana sulb'i. Bata san sanda ta kai wa hannunsa cizo ba cikin takaicin maganganunsa sannan ta fad'a jikinsa tana s

hirin saka kuka ya yi mata abinda tilas ya sata had'iye guntun hawayen shagwab'arta.

______________

Haka dai suka dinga zuba soyayyarsu har ana i gobe azimi don haka da daddare ya zaunar da ita kusa da shi murya k'asa-k'asa ya ce "Please mu yi magana t

a fahimta, gobe azimi gaskiya ba zan iya jurar ganinki da rana na kyaleki ba. Ba tare da na ji wani feeling a raina ba. Ina gudun karyewar azimina don haka zan dinga zuwa bayan magriba na tafi da asussuba na sanar da Nanna aiki na ya koma na dare so ba ni

da fargaba ta wannan fannin." Runtse idanunta ta yi tana jin kunyar kalamansa don duk da a lokacin ta d'an fara sakewa da shi. "Nan da 3 days za mu tafi Nigeria insha Allah, dad'in da na ji ma ba ku fara lectures ba har ma je mu dawo ma da izinin Allah." T

a d'an d'aga kai tana jin yarda k'irjinta yake bugu a duk sa'ilin da aka ambaci Nigeria.

Haka dai suka dinga morewa amarcinsu kafin ranar tafiyarsu ta zo. Da kansa ya kai su Khairi gidan Abba Musty kuma sam ba su damu ba murna ma suke don da sa'anninsu a

gidan kuma school d'in su d'aya. Ga Abba Musty da son yara.

A daren ranar a gidan Nanna ya kwana. Don haka Hamda kwan ta yi tana sallah da addu'ar kada Allah ya kawo abinda zai rabata da Hammad. Ubangiji yasa zamansu ya d'ore har aljanna. Tuni ta shirya

akwatinta tsaf.

Da safe kuwa da kyar ta mik'e don tafiyar rana za suyi. Wanka ta yi sosai ta sanya wata doguwar riga mai masifar kyau light purple ta yane kanta da mayafin rigar. Kyau kam ta zuba shi a ranar da duk wanda ya kalleta na tabbata sai ya sak

e jiyowa ya kalleta.

Tun a mota Nanna da taga yayi parking a k'ofar gidan ta kalleshi "Me za muyi anan ko mota zaka ajiye? Wai gidan ma waye tukunna?" Fuskarsa a d'aure ya ce "Wace tambaya kike so na amsa miki? Ko gidan ma waye ai yanzu zaki gani."

Ya f

ad'a yana ficewa daga motar. Wannan karan madadin ya bud'e da key kamar yarda ya saba sai ya danna door bell

Hamda da take zaune mamakin waye ya kamata ta mik'e a hankali ta bud'e k'ofar. Kallo d'aya ya yi mata ya d'auke kai "Oya ki yi sauri ki fito muna

mota." Daga haka ya juya. Hamda da take tsaye turus ta yi tana kallonsa tana mamakin dalilin canjin fuskarsa ko don ya d'auko Hakimar tasa ne?

Cikin takaicin lamarin ta juya da sauri ta rurrufe ko ina na gidan sannan ta kashe kayan wuta. Tana tsaki ta j

a trolley d'inta ta fice daga gidan.

Tun daga nesa Nanna take jifanta da wani irin kallo gabanta yana dukan tara-tara ganin yarda

Hamdan ta fito ta yi wani azababben kyau fatar jikinta ta murje sosai asalin natural skin d'inta ta sake bayyana zallan kyant

a game da laushi da santsin fata. Ta amince Hamdan number one ce a wajen kyan fata, don ko farin mutum ba zai gaya mata d'aukar ido ba. Sanin cewa tare yake da matarsa ya sa ta had'e fuskarta tamau tamkar bata tab'a dariya ba. Da kansa ya fita ya bud'e mat

a boot d'in motar ta cilla trolley d'inta a ciki. Idanu take so su had'a kawai amma ya fuske ya d'auke kansa don ya san muddin zai had'a ido da ita to komaima zai iya canjawa. Takaici ya sake kumeta wato sabida yana tare da matarsa yana tsoron b'acin ranta

shi yasa ko kallon arziki ba zata samu daga gareshi ba? Ta ji kamar ta zunduma ihu ganin har ya shiga motar ya tayar bai damu da ya ce mata ta shiga ba. A zuciyarta ta ayyana tabbas auren mijin wata masifa ne. Ji yarda ya banzagatar da lamarinta da su kad

'ai ne ta tabbata yarda yau ba sa azimin nan saboda tafiya sai ya kusanceta kafin su taho amma saboda munafunci jibi yarda ya yi shakulatun b'angaro da ita. Jikinta a sanyaye duk da fuskarta bata nuna karaya ba ta bud'e bayan motar ta shiga. Tana gyara Gla

ss d'in da yake fuskarta. Idanunta cikin na Nanna da ta lura tana yi mata kallon mamaki. Ba k'aramin dauriya ta yi ba ta angije abinda yake ranta murya a cunkushe ta ce "Ina kwana Maman Kamla?" Nanna ta saki hucin b'acin rai kamar ba zata amsa ba sai kuma

itama ta mayar mata a cunkushen "k'alau." Daga haka ta ja baki ta tsuke itama Hamdan gefen window ta mayar da kanta tana kallon kyau da tsarin garin Birmingham d'in. Shi kuwa ta cikin black glasses d'in da yake idanunsa yake k'arewa Hamda kallo shi kansa y

ana mamakin yarda jikinta ya sake murjewa ya yi kyau. Shi kad'ai yake murmushin ganin yarda take cika tana batsewa shi kansa ya yi mamakin yarda har ya iya basar da ita haka? Tabbas nan gaba akwai darun rigimar da zata sassauke masa idan suka kad'aita. K'

okari yake kawai su had'a ido sai dai ta basar da lamarinsa, ko kallon inda yake bata sake yi ba ta ba banza ajiyarsa.

Har suka isa Airport d'in ba mai magana a cikjnsu kowa da tunanin da yake a zuciyarsa. Nanna kam kasa daurewa ta yi kafin su fita daga m

otar su je airport d'in ta ce "Ke kuma ina mijinki ya barki kika taho ko rakiya babu?" Da kyar Hamda ta had'iye abinda ya tsaya mata a wuya ta fice daga motar kawai ba tare da ta bawa Nanna amsa ba. Gaba d'aya ma haushin Hammad take ji idan banda munafunci

me yasa har a lokacin ya kasa sanar da matar tasa ya aureta? Kada fa ya cuceta ya kaita y baro. Tunanin da ya sark'eta kenan ta shiga taune lips d'inta ba tare da ta shirya ba.

Ganin bata san yarda zata nufa ba, yasa dole ta ja tunga ta tsaya tana kallo

sanda suka taho sai ta ga tamkar da gayya ma Nanna take sake shigewa jikinsa tana nannarkewa tsaki ta ja a fili har tana zabga musu harara ta cikin glass d'in da yake idonta. Har suka zo ta gefenta suka wuce Hammad ya sauke idanunta a kansa yana sakar mata

murmushi kad'an. Ta kau da kanta ita kuma tana jifansa da harara.

_______________

Gaba d'aya Mahmah (Sadiya) cikin farin ciki take na dawowar Hammad ya warware bak'in k'ullin da waccan makirar matar ta k'ulla.

Lokacin ma tana aikin shirya musu a

binci a kitchen.Umma Asma'u ta shigo fuskarta fal fara'a don yanzu sam bata da buri irin na tozartar Sakina. Musamman ganin yarda take k'ok'arin lalle sai ta had'a ta fad'a da d'an uwanta. Abinda ta yi mata ranar ba k'aramin tsaya mata ya yi a rai ba daga

ita har Didi da kyar suka runtsa a daren ranar Didi juyi kad'an sai ta ce "Iyye Ba takka lamalin Umaru ya girgimama. To ba dani da a yi wannan itkantin ba babu matal da zata zo ta laba min kanku. A to Takina dai te dai ta ci kanta."

Asma'u ta dafa kafad'a

r Sadiyan ta ce "Hope dai ko Abbu baki sanar da shi dawowar ta su ba, don haka waccan makirar matar zata iya wargaza shirinmu. Ko ba haka bama na fi son yarda ta sakankance d'in nan ta gansu bagatatan lamarin zai fi jirkita tunaninta." Sadiya ta saki murmu

shi kawai had'e da gigiza kai a fili ta ce "Allah yasa shi uban gayyar Abbun ya yarda, don jiya ban da na kai zuciya nesa tabbas da na bar gidannan. Daga fa ba masa nasiha akan duk abinda ta kawo masa dangane da maganar mutane ya fara tsananta bincike tuku

n kafin zartar da hukunci." Shikkenan ya dinga sakar min bak'ak'en maganganu har da min gorin da ma ai tunda ni zab'in Didi ce dole ta fi so na, shi yasa kuma kuka fi so na aka saka masa mata a gaba to shi haka yake son matarsa duk da munin halinta da muke

gani shi baya gani ciki da banta kawai kyanta yake gani. Bai tab'a sakar min bak'aken maganganu ba kamar jiyan nan." Ta fad'a tana runtse idanunta har tana shirin yankar kanta da wuk'ar da take hannunta da sauri Asma'u ta rik'e hannunta "Me ye haka kike y

i Sadiya, sai kin jiwa kan ki ciwo a banza a wofi? Ina hak'urin da kika had'iya na shekara da shekaru sai yanzu da komai yazo gangara zaki zubar da ladanki. Ki jure kwana kad'an ya rage ko nace awoyi kad'an." Sadiya ta share k'wallar da ta sake kwaranyo ma

ta tana sakin murmushin dole. Ita kanta ta san hak'kkinta kad'ai ba zai bar Sakina ta zauna lafiya ba don ta d'au tsawon shekaru tana cuta ta zahiri da ta bad'ini. Asma'u ta cigaba da kwantar mata da hankali har sai da ta tabbatar ta samu nutsuwa tukun na

ta fita daga sasan nata.

______________

Zama kawai ta yi a gefe a airport d'in tana bin jama'ar da suke wucewa da idanuwa. A zahiri idan ka ganta sai ka zata da ma ta saba da zuwa airport sam ba alamar rashin wayewa a tare da ita.

Fuskarta sam ba a

nnuri kuma inda ta nema ta zauna suna da tazara sosai a tsakaninsu. Amma duk da haka tana hango yarda suke hira cike da murmushi a fuskokinsu alamar suna cikin nishad'i. Ta ciji leb'anta ya fi sau nawa da zai cire tabbas da ya gaji leb'en ya cire. Ta ayyan

a ya zama dole ta nad'awa Ya Hammad sarautar mayaudaran duk duniya. Sab'anin hasashenta da tunaninta gangar jikinsa ce kawai a tare da Nanna zuciyarsa gaba d'aya tana d'amfare da ita. Duk abinda take yana kallonta ta cikin glasses d'insa. Yana kuma son ya

jita a jikinsa ba Nanna da ta shige rabin jikinsa ba.

Hamda ta sake sakin tsaki ganin yarda Nanna ta kwanta ta sanya kanta a cinyarsa wai sanyi take ji

jijjiga kai kawai ta yi kafin ta juya musu baya ta daina ganinsu gaba d'aya sai dai jikinta da zuciyar

ta wani irin b'arin b'acin rai suke yi. A wannan halin ta ke har ta ji an fara kiran su alamar tafiyarsu ta zo. Tana ji ta yi burus da shi. Ta ayyana ko Nigeriar suka je ba zata kulashi ba kai sai ya ma sakeni ni ba Zan iya zama da mijin wata ba." Ta fad'a

a fili ba tare da ta san yana tsaye a kanta ba hannayensa zube a cikin aljihun jibgegiyar rigar sanyin da take jikinsa. Murmushi kawai ya ke jifansa da shi. Jikinta ne ya bata yana gurin don ta ji kaifin idanunsa da suke yawo a jikinta hakan yasa ta k'i t

a d'ago ta kalleshi. Ta dai tabbatar Nanna ba ta wajen shi yasa ya zo ya tsaya yana jifanta da kallo da wannan muggan idanun nasa. "Yarinya zaki ta shi ko sai na sunkuceki?" Ya fad'a cikin wata irin husky voice da ya yi whispering a kunnenta. Ta d'auke ida

nunta tana k'ok'arin kawar da b'acin ran fuskarsa "Ina matar son?" Ta fad'a ba tare da ta kalleshi ba. Murmushi ya saki kafin ya murza hannunsa cikin dokin wuyanta "Ta je toilet." "Mhnm kawai ta ce tana k'ok'arin janye jikinta "Ai gwara ka koma kafin tazo

ta kama ka." Dariya ce taso sub'uce masa sai dai ya maze ta gefen ido ta ga ya ciro wata k'waya ya cilla a cikin lemon da yake hannunsa da mamaki take kallonsa har shima ya d'ago ya sakar mata murmushi "Ina son kasancewa da ke Nuri ta, don haka zan saka ta

barci maganin barci Zan bata da zai d'auketa some hours da zarar mun shiga jirgi sai hankalinki ya kwanta ko? Zan zo ki jini manne a jikinki kamar yarda ki ke so." Baki sake take kallonsa kafin ta ciji gefen d'an mitsilin leb'enta ta furta "Allah ya kyaut

a." Bai amsa mata ba ya yi sauri jan trolley d'in sa mik'e mu je an fara boarding." "Kada ka bata maganin nan. In dai nice ka je ka ji da matarka matsalarkuce muna zuwa Nigeria za ka sakeni nima na auri mijina ba mijin wata ba." Ya juyo da niyyar murzar le

b'enta ya hango Nanna sai kawai ya waske yana jijjiga kai alamar za mu had'u da ke."

Bata sake magana ba har suka shiga jirgin tana kuma kallon sanda ya turawa Nanna lemon a bakinta lokacin suna layin boarding ta tab'e bakinta in dai nice ka bata a banza

don na daina yarda ka mori jikina har sai ka sanar da kowa ka aureni"

Allah ya taimaketa ma ba wajen zaman su d'aya ba ita a can gefen window take su kuma suna d'ayan side d'in. Haushi kamar me ya kama Hammad ganin yarda wani bature ya zauna a kusa da i

ta. K'okarinsa kawai barci mai nauyi ya d'auke Nanna ya je ya tashi baturen daga kusa da matarsa. Allah ya taimkeshi ma sai ya ga baturen ya mik'e ya canja wajen zama. Hammad ya sauke ajiyar zuciya kawai yana takaicin yarda maganin yak'i d'aukar Nanna ball

e barcin ya kwasheta.

Sai bayan kusan mintuna talatin sannan barci mai nauyi ya yi awon gaba da Nanna. Lokacin kuwa Hamda wani irin amai da tashin zuciya ne kawai yake turnik'ota, ga wani sanyi mai kama da zazzab'i da take jinsa har cikin jikinta. A takur

e take sosai ga shi ba mataimaki ta ji kamar ta saka hannu a kai ta yi ta kurma ihu. Yawunta gaba d'aya ya tsinke ya zama wani marar dad'i ita sai ta ji ma kamar k'arni yawun yake mata. Tun tana daurewa har ta mik'e a gigice ta yi hanyar toilet d'in jirgin

. Hammad da ya ganta shima da sauri ya bi bayanta bayan ya zame Nanna da ta narke a jikinsa. Kafin ya isa har ta fara kelaya aman kamar zata kelayar da duk abinda yake cikinta. Ta galabaita sosai. Hammad bai tsaya sanya ba ya sanyata a jikinsa ya rungume h

ankalinsa a tashe jin yarda jikinnata yake b'ari ga zafi ya d'auka. Ganin k'afarta tana rawa ya ciccib'eta kawai yama manta da wata Nanna can baya inda ba kowa ya nufa da ita. Direct a cinyarsa ya yi mata masauki

ya rungumeta sosai, kamar zai mayar da ita

ciki. Abinka da turawa ba wanda ma ya kalli abinda suke. Jikinta kawai yake murzawa da tattausan hannunta ta cikin rigarta. Gaba d'aya jikinta ya gama saki hakan da yake mata sai ta ji tana samun sau'kin wasu abubuwan duk da dai tarin haushinsa take ji. Ya

nzun ma k'ak'arin zamewa take a jikinsa amma ya k'i bata damar hakan ya manna k'irjinta a nasa yana jin yanayin yarda zuciyarta take bugawa Ta hanyar d'aguwa da saukuwar k'irjin nata. A kunne ya rad'a mata "Ki bari mu samu nutsuwa mana rashin jin mahad'ins

a ne fa ya saki zazzab'in." Ta girgiza masa kai "Ni dai ka k'yaleni tunda muka taho fa baka kulani ba sai yanzu da ka bankawa matarka maganin barci. Ni baka damu da b'acin raina ba kenan idan na ga kuna had'a jiki itace ka damu da na ta b'acin ran. Ni muna

zuwa Nigeria zaka sake ni nima na auri mijina ba mijin wat...." Ji tayi kawai ya cafki lab'banta yana bata wata irin zafaffiyar sumba kamar zai cire leb'en.

Son ransa ya yi da lab'ban kafin ya saketa cikin wani irin yanayi ya ce "Hamda so kike son ki ya k

ashe ni? Ba ki san yarda nake jin kaina ba ko a duk lokacin da kika had'a kanki da auren wani. Please ki daina." Turo bakinta ta sake yi zata sake masa tsiwa still ya sake kame bakin yana tsotsa yana d'ago kansa ya ga Nanna ta nufo wajen tana daf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login