Showing 36001 words to 39000 words out of 129261 words

Chapter 13 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

68

akan wannan yarinyar ba, don haka ba shiga huruminta kad'ai ba daga nan

har Birmingham zan tafi da ita zata rayu da nine a k'ark'ashin inuwa d'aya har sai aurenta ya tashi, saboda duk duniya a yanzu ni ne gatanta don haka I

dan kin ga ba zaki iya zama da ita ba you are free to go, kada azo ana nayi ba daidai ba.."

Tsawon lokaci d'akin ya d'auki bak'uncin shiru baka Jin komai sai saukar numfashinsu da sautin kukan Nanna da furucin Hammad yazo mata a bazata ta kuma rasa a ma'a

unin da zata ajiyeshi tabbas idan ya kafe sai ya tafi da yarinyar nan Birmingham ya taro k'wallan masifa....



Jikar Nashe ce...ALK'ALAMIN JIKAR NASHE

NAZEEFAH SABO NASHE.

(Ga masu tambayar ko akwai complete book d



in? Yes akwai idan ba zaki iya jira ba

ki biya 500 kacal a baki complete don jin yarda Abin yake. Nagode da comments da soyayyar da kuka nunawa Book d



in nan.)

YA ABIN YAKE?

17.

08033748387



🏽



🏽



🏽



🏽📖📖📖



🏽



🏽



🏽



🏽

Ajiyar zuciya kawai Hamda take saki, jin zantukan Nanna da suka

zo mata a bazata, sam bata tsammaci haka daga bakinta ba, Lura da cewa ta nuna wa yaranta k'auna, amma a yau ta wanke idonta tana furta muggan kalamai a kanta tamkar ma bata tab'a saninta ba, kawai don k'addara ta hau mata. Me yasa ba za su yi mata uzurib

a? Dubi da cewa itama ba laifinta bane da bisa son ranta ne da bata amince ta zo duniya ta wannan k'azantacciyar hanyar ba. Ta sake rintse idonta gam jin cece kuce yana sake yawaita tsakanin Nanna da mai gidanta. "Wallahi Mahmah ki yi masa magana

muddin ya

ce sai ya tafi da ita to tabbas sai dai ya san yarda zai yi da ita ba zata zauna min a gida ba."

Fuskarsa a tamke ya dubeta had'e da furucin "San da na siyi gidan ko aurenki ban yi ba, balle ki ce da kud'inki na siya, idan kin san tashin hankali za ki kom

a min da shi you better stay at your father's house." Zata sake magana cike da zafin rai Dida ta daka mata tsawa "Nanna bana son rashin hankali ki bari a yi komai a nutse. Duk wannan maganar ba ta da amfani." Kuka ta sake fashewa da shi "To ku gaya masa ka

da ya tafi da yarinyar nan, wallahi zan iya aikata komai idan na ce komai ina nufin komai." Cikin b'acin rai ya mik'e zai fice har ya kai k'ofa ya ji Mahmah ta daka masa tsawa. Tsak ya tsaya had'e da juyowa yana facing d'inta. "Me kake nufi da tafiya da it

a? Ko kana nufin da gaske ka karb'eta a matsayin y'ar cikin ka, Hammad kada kace min da gaske yarinyar nan jininka ce?" Ya d'ago kai yana kallonta cikin tafasar zuciya sai dai lab'bansa sun gaza furta furucin komai illa idanunsa da suka jirkita launi zuwa

ja. Ya sunkuyar da kansa kawai. Har zuwa san da Dida ya fuskanci tabbas ba zaida ce komai d'in ba, ta dafa kafad'ar Sadiya cikin taushin murya ta ce "Yaya mu bi komai a hankali, insha Allah komai zai bayyana kansa, a yanzu na fuskanci halin da Hammad yake

ciki sam ba zai iya furta komai ba." Sadiya ta bud'e baki zata yi magana Dida ta yi saurin girgiza mata kai, don ta lura idan har aka cigaba da kucincina maganar tsaf Hammad zai iya datse igiyar auren y'arta, ko ba haka ba ita Hamdan ce ma ta bata tausayi,

ta lura ba a k'aramin rud'ani da firgici take ciki ba, kada a je ta rasa hankalinta ko zuciyarta ta buga haka kawai an saka ta a halin ban ji ba ban gani ba. Idan har Hammad ya matsa sai ya tafi da ita, ita zata rik'e ta madadin a had'a ta da Nanna a zo a

haifi d'an da ba shi da ido. Don haka ta girgizawa Sadiya kai alamar kada ta ce komai, ta kuma k'arasa gaban gadon murya a tausashe ta dafa kan Hamda da ya d'au zafi rad'au ta ce "Ki yi hak'uri kin ji, komai zai daidaita ubangiji Allah ya ba ki dangana, d

uk abinda kika ga ya faru ga bawa muk'addari ne daga Allah kuma bawa ba zai iya goge k'addararsa da Ubangiji yada rubuta masa ba, ki yi ta addu'a a zuciyarki ubangiji Allah ya baki ikon amsa jarabawarki Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahlan wa anta t

aj'alal Hazna iza shi'ita sahlan. Tana yaye duk wata damuwa da nauyi zuk'ata." Daga haka ta yi mata sallama suka fice. Hamda ta bi bayanta da kallo, tana jinjina kyakykyawan hali irin nawannan mahaifiyar Nanna, tunda abin ya faru ita kad'ai ce ta fad'a mat

a abinda ya kwantar mata da hankali kad'an, ita ce matar da ta lallasheta da furuci mai warware fushin zuk'ata, wani abu kad'an daga cikin abinda yaaka tokare k'irjinta ya sauka, a hankali wasu siraran hawaye suka fara biyo k'uncinta. Ta shiga nanata wacca

n addu'ar da Dida ta gaya mata. Sai ga shi a hankali barci duk da ba za'a kira shi mai dad'i ba yazo ya d'auketa. Tana sakin ajiyar zuciya akai-akai. Hammad da yake zaune ya zuba mata ido, wani abu mai kama da tausayi yana tsirga masa cikin zuciyarsa, da g

aske yana jin tausayinta, idan kuma ya tuna ta hanyar da aka sameta sai ya ji zai iya sadaukar da Duk wani farin cikinsa matuk'ar ita za ta yi farin ciki.

Kusan awoyi biyu yana zaune kamar maigadinta yana kallon yarda take sauke ajiyar zuciya cikin barci

. Ba ya son ya tasheta duk da kuwa za suje wajen passport, ya fi so ta tashi da kanta. Sai da ta k'ara mintuna talatin akan awa biyun sannan ta farka. Idanunta cikin nasa da ya kafeta da su, da sauri ta d'auke na ta idanun tana tattare gashin kanta da ya k

wanto a

Saman fuskarta. Da kyar ta mik'e zaune tana dafe pillow, tana mamakin yarda ta yi barci sosai haka. Fuskarsa a d'an d'aure ya mik'e yana gyara wristwatch da yake hannunsa "10 minutes na ba ki, ki yi alwala ki yi sallah za mu je wajen passport kuma

kada ki yi taking time sauri nake." Bai saurari amsarta ba ya fice da sauri. Sai da ta fi minti d'aya a zaune kafin ta mik'e cike da kasala ta

shige toilet d'in d'akin. Ita dai da zai bi ta tata da ya kyaleta ta shiga duniya tunda zamanta tare da su a gare

ta ba shi da wani amfani, musamman da matarsa ta nuna mata k'iri-k'iri bata son zamanta tare da su. Sam ba taga laifinta ba, dama y'ay'a irinsu haka mutane ke gudunsu ba sa son sam su rab'e su, duk da kasancewar ba laifinsu ba ne.

Mintuna biyar ta k'ara

akan lokacin da ya bata, tuni ya je wajen Doctor ya amshi sallama, bayan Doctorn ya tabbatar masa damuwa ce silar ciwon nata, da zarar an kwantar mata da hankali everything will be alright Insha Allah.

A rab'e ya ganta jikin bango, tana hangoshi ta fara

wasa da bakin hijabin da yake jikinta. Sai da ya isa gabanta sannan ya duba agogo hannunsa ya sauke kallonsa a kanta. Yana d'an girgiza kai, ba kuma tare da yace komai ba ya juya ya cigaba da tafiya. Ita kuma jin bai ceyi tazo ba kawai sai ta ja ta tsaya.

Har sai da ya yi taku goma sai yaga tamkar bata bin sa. Hakan yasa ya jiyo tsaki yaja kafin ya ce "Jira ki ke na zo na d'auke ki ne?" Ya yi furucin ba tare da ya juyo ya kalleta ba. Sai sannan ta bi shi tana mamakin yarda yake mata abubuwa tamkar ana tilas

ta shi, ya k'yaleta mana ya k'yaleta ta kama gabanta idan yana ganin kamar ta zame masa wani kaya ne. Bai san haushi yake bata ba, idan ta tuna yarda suka bi son zuciyarsu suka samar da ita tada gurb'atacciyar hanya ya zama dole ta samawa kanta mafita ba w

ani Birmingham da zata bi shi. Ya aura mata Zunnuraini kawai.... Da sauri zuciyarta ta buga ta tabbata da kyar idan zata auru idan har mutum ya san wacece ita? Dai-dai lakacin da ta ci karo da motar ba tare da ta sani ba, shi kuwa yana kallonta ya k'i mata

magana yana son ya ga yarda zurfin tunanin nata yaje.

Tsaki ya ja, a zafafe ya ce "Ki je ki bugar da zuciyarki a banza garin banzan tunaninki." Da kyar ta d'ago jajayen idonta tana so tayi masa tsiwa amma kwarjininsa yana hana ta. Musamman idan ya tsatsts

areta da idanunsa masu kaifin gaske." Sai kawai ta runtse idonta, hawaye na kwaranyo mata ta fad'a motar. Yana kallon yanayinta ta cikin motar har da murgud'a bakin da ta yi, murmushi kawai ya saki ya tabbatar da abinda take k'unsawa a zuciyarta.

Yana far

a driving taji ya ce "Idan kin gama tsara yarda za ki gudu ki sanar min na baki kud'in mota." Da wata irin razana ta d'ago tana dubansa ya aka yi ya San Sirrin zuciyarta? ya aka yi ya san abinda take shiryawa, kamar ta tambayeshi sai kuma ta yi shiru tana

cigaba da wasa da hannunta

Tsawon lokaci suna tafiya kowa da abinda yake sak'awa a ransa, da gaske ba ta son bin sa Birmingham d'in nan amma sam ta rasa k'warin gwiwar da zata kalli fuskarsa ta ce ba za ta je ba.

Sun kusa isa gurin ya dubeta ta side d'a

ya kafin ya ce "Idan ba ki bini Birmingham ba, kina tunanin akwai inda za kije ki samu peace of mind, kina ji dai Mai gidan ya ce Baya buk'atar ganinmu mu bar masa gidansa." Hawaye ta ji yana son zubo mata "Kada Ki fara min wannan kukan banzan, ki bani num

berr saurayinki na yi magana da shi idan yaga ya shirya aurenki ya fito nan da kwana biyar na aura miki shi a wuce wajen, amma idan aka zo bincike wajen su Abbu asiri ya tonu fa?" Rintse idanunta ta yi ita ma tana jin wannan fargabar amma tana tunanin ai b

a za su tona mata asiri ba, tunda idan sun tona kan su suka yiwa. "Ki ba ni numberrsa zan yi magana da shi." Wani dad'i ta ji ya tsarga mata duk da gefe guda tana jin Shakka da kasantuwar hakan, tun da dai an ce zancen duniya ba ya b'uya. Bai sake mata mag

ana ba har zuwa sanda suka isa

Immigration office d'in. "Dama da zarar sun tambayi sunanki, kice musu Hamda Hammad na gaya miki." Ta d'ago tana son tambayarsa ya tsatstsareta da idanunsa "Daga yau na canja miki suna, tunda ance ni ne Babanki, suma takardun

makarantar gobe za mu je court ki yi changing name d'inki kin koma Hamza Hammad UU d'an borno." Tsit ta yi saboda sam ba zata iya magana ba. Ya fice daga motar, kafin ya yi mata magana ita ma ta bi bayansa tana mamakin sunan da ya lak'k'aba mata.

****

***************

Cikin ikon Allah likitocin suka samu nasarar farkar da Hajiya Didi, ta hanyar gark'ama mata oxygen aka dinga zuk'o numfashinta. Ta farka sai dai sam magana ta d'auke tsaf daga bakinta, ga ta dai idanunta biyu amma ba ta uhm bata uhm-umm sa

i hawaye da suke kwaranya a idonta sosai musamman idan ta so yin magana ta kasa. Da k'afarta da komai kuma hannayenta suna aiki, bakin ne dai ya d'auke, amma likitocin sun tabbatar musu a kowane lokaci bakinta zai iya dawowa.

Hankalin D'an Borno family ka

m a tashe ya ke matuk'a da gaske, musamman Abbu da lokaci d'aya duk ya fita hayyacinsa, shima a lokacin da za'a aunashi tabbas za'a tabbatar yana buk'atar a yi admitting d'insa a hospital.

Ita kuwa Ammi hankalinta a kwance yake ko banza dai ta san ta ture

waccan matsalar, musamman ganin kowa hankalinsa ya kau daga kanta.

A kuma daren ranar ne Abbu ya turketa da tambayar me yasa sanda abin ya faru ba ta sanar da shi ba." Cikin muryar kuka ta tabbatar masa da cewa tsananin kunyarsa ne ya sa ta kasa gaya mas

a kuma da wani ido ma zata iya dubansa ta gaya masa wannan abin kunyar. Kamar zai sake mata wata tambayar sai dai ya ja bakinsa ya tsuke don sosai yake jin haushin tuna lamarin gaba d'aya.

Mahmah dai hankalinta ba a kwance yake ba, tana son ta hana Hammad

tafiya da Hamda amma Dida ta hanata, ta ce ta kyaleshi ba wani abu bane don ya tafi da itan, ta kuma ja kunnen d'iyarta Nanna akan ta kyaleshi kada ta sake yi masa maganar don a yanayin da yake tsaf zai iya sakinta idan har ta cigaba da jayayya da k'in bi

n umarninsa. Haka tilas ta hak'ura sai dai ta k'udirtawa ranta sam ba zata bar Hamda ta yi rayuwar jin dad'i ba, tilas sai ta bak'anta mata har ta gwammaci ta bar gidan da k'afafunta.

_____________________

Suna fitowa daga Immigration office d'in ta g

a ya d'auki hanya bai tsaya ko ina ba, sai wani k'aramin gida. Ba tayi magana ba har ya tsayar da motarsa ya fita ya bud'e k'aramin gate d'in. Ya

shigar da motarsa y'ar madaidaiciyar harabar gidan. Zama ta yi har sai da ya ce "Fito mana." Ta d'ago ido tan

a dubansa kafin cikin dauriya ta ce "Ya Hammad me zan yi?" Tsahon second yana dubanta kafin ya ce "Umarni na ba ki, ki fito kuma daga yau kada na sake jin kin kirani da Yaya Hammad ai ki na ji aka ce ni d'in ba wanki bane, Ubanki ne don haka ki dinga kiran

a da Daddy kamar yarda kika ji su Kamla na kira na. Ki fito na ce." Ganin yarda ya tsare gida ne ya sata saurin fitowa. Gaba yayi a zuciyarta ta ce "Ashe dai mutumin nan mafad'aci ne?" Sai kuma ta kama bakinta da sauri tunawa da ta yi matsayin mahaifi ya k

e a wajenta. Idan ta tuna hakan sai ta ji wani iri a ranta. Ya murza key ya tura k'ofar k'aramin parlourn. Sannan ya shiga parlourn tsaf da shi sai k'amshi yake. Tana so tambayeshi gidan waye sai kawai ji ta yi ya ce "Gidan abokina ne, mazaunin k'asar Birm

ingham, anan yake zama da matarsa idan sun zo hutu, shi yasa nima yanzu nake jin takaicin rashin gina gidan kaina, amma insha Allah soon zan gina ko don gudun kora daga gidan mutane." Ta juya tana k'arewa madaidaicin parlourn kallo kafin ta ce "To me zan y

i anan?" "Zama za kiyi kafin mu san abin yi, idan sauryin naki ya shirya auren sai na aurar da ke, ko ba shi da yarda zai ajiyeki sai na ba shi Aron nan, kafin ya samu inda zai ajiyeki." A raunane ta d'ago tana dubansa kafin ta ce "Amma Yaya Hammad ba ni k

ad'ai zaka bari anan ba ko? Ka kawo min ko Kamla ce." Tsaf ya tsaya ya k'are mata kallo kafin ya saki tsaki ya ce "Idan na sake jin kin kira ni da Yaya sai na murji bakinki, kuma ba Kamla zan kawo miki ba Kamlo zan kawo miki, ba kiji yarda mu kayi da uwart

a bane, ko ke kurma ce ba ki ji mai uwarta ta ce ba, idan za ki shirya rayuwa ke kad'ai ki shirya na gaya miki." Ya fad'a yana shigewa wani d'aki. Hamda ta bi bayansa da kallo hannayenta akan k'uncinta ta zabga uban tagumi, da gaske dukkan lamarinsa mamaki

suke bata, shi kamar ma babu abinda yake damunsa daga bayyanuwar Sirrin nan..... Allah dai ya sa Zunnuraini ya shirya aurenta, ta samu zuciyarta da addu'a.

To sai mu ce Ameen.

N

Jikar Nashe ce..ALK'ALAMIN JIKAR NASHE

NAZEEFAH SABO NASHE.

(Ga masu

tambayar ko akwai complete book d



in? Yes akwai idan ba zaki iya jira ba ki biya 500 kacal a baki complete don jin yarda Abin yake. Nagode da comments da soyayyar da kuka nunawa Book d



in nan.)

YA ABIN YAKE?

17.

08033748387



🏽



🏽



🏽



🏽📖📖📖



🏽



🏽



🏽



🏽

Ajiyar zuciya kawai Hamda take saki, jin zantukan Nanna da suka zo mata a bazata, sam bata tsammaci haka daga bakinta ba, Lura da cewa ta nuna wa yaranta k'auna, amma a yau ta wanke idonta tana furta muggan kalamai a kanta tamkar ma bata tab'a san

inta ba, kawai don k'addara ta hau mata. Me yasa ba za su yi mata uzuriba? Dubi da cewa itama ba laifinta bane da bisa son ranta ne da bata amince ta zo duniya ta wannan k'azantacciyar hanyar ba. Ta sake rintse idonta gam jin cece kuce yana sake yawaita ts

akanin Nanna da mai gidanta. "Wallahi Mahmah ki yi masa magana muddin ya ce sai ya tafi da ita to tabbas sai dai ya san yarda zai yi da ita ba zata zauna min a gida ba."

Fuskarsa a tamke ya dubeta had'e da furucin "San da na siyi gidan ko aurenki ban yi ba

, balle ki ce da kud'inki na siya, idan kin san tashin hankali za ki koma min da shi you better stay at your father's house." Zata sake magana cike da zafin rai Dida ta daka mata tsawa "Nanna bana son rashin hankali ki bari a yi komai a nutse. Duk wannan m

aganar ba ta da amfani." Kuka ta sake fashewa da shi "To ku gaya masa kada ya tafi da yarinyar nan, wallahi zan iya aikata komai idan na ce komai ina nufin komai." Cikin b'acin rai ya mik'e zai fice har ya kai k'ofa ya ji Mahmah ta daka masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login