Showing 12001 words to 15000 words out of 129261 words

Chapter 5 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

82

matarsa tayi saurin kallon Sadiy

a da alama wannan karan ta fara

Jin yaren Hausa don haka don kar nayi

ɓ

aran

ɓ

arama nace masa ta fata jin yaran Hausa ne? Ya girgiza kai ya ce "Ta fara ji Didi kawai dai ba sosai ta iya mayarwa ba"  nace "Hakan yayi kyau, kada kace m



n baka gane Sadiya ba?"

Girgiza kai yayi "Wallahi Inna ban Wanye da ita ba."  raina a bace nace Ai kuwa naga alama to tashi muje waje zan yi magana da Kai." Ya kuwa bini muka shiga madafa. Idanuna cikin nashi na rik'e kunne nace "Ka jini da kyau Sadiya 'yar gidan Baba mak'oci CE,

ba zaka santa ba tunda ba anan tayi wayo ba daga yaye yar uwarta ta tafi da ita can Zariya sai da ta girma baka ma k'asar aka dawo da ita, itace matar da muka aura maka kashegarin ranar da ka gujemu." Ji nayi kawai yana jan Innalillahi kamar na watsa masa

wuta a jiki. Cikin wata iriyar murya ya ce "Yanzu Didi sai da aka yi aurennan?"  Tab'e baki nayi ina kallonsa nace "Aure kam an yi shi yau shekarata uku kenan da aurenta akan ka, baka kuma isa ka saketa ba wallahi ka saketa sai na d'aga maka Nono, ko Baya

n raina ban amince ka saki Sadiya ba. Ga can shiyyarku an gama d'aki biyu ne da parlour sai bayan gida a rumfa ta d'au d'aki ciki d'aya Sadiya dama an Zuba mata kayan a d'ayan ita kuma ta d'au d'ayan kuyi maleji kafin ku tattara ku koma." Hawaye sosai ya z

ubo masa takaici yasa na fice daga madafar Na shige Rumfa.

Idanuna a kanta tana ta faman yatsina tana kurb'ar zob'on da na kawo musu, nace "Kinyi ta banza ke Sadiya zo kije ga shi can ki kai musu abincin su k'arata a can yasan yarda zaiyi ya sanar da ita

ke a matsayin kishiyarta, na san dai yau akwai dambarwar tsiya, da kinji taga-taga ki gudo suje can su k'arata ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka. Sadiya murmushi tayi tana yafa mayafinta idanunta akan matar tana fatan bata ji abinda na fad'a ba.

Tsaki nayi nace "Duk iya hausarta ai bata isa ta kamo nan a Hausaba."

*********************************

Kai ranar mun ga abinda ake kira tashin hankali, ashe hausawa duk haukan da suke idan an musu kishiya na su Lami ne akan na Balarabiya Sakina, k'iri

-k'iri ta fito daga ita sai d'an tofi da vest tana cilli da duk abinda ta samu a tsakar gidan tana sai ta tafi, idan kuma ya k'i barinta ta tafi sai ta kasheshi ta kashe Sadiya sannan ta kashe kanta. Duk ta jijjiwa kanta ciwo da kyar ya turata a d'aki

ya g

ark'ame da d'an mukulli yana sakin ajiyar zuciya, murya a raunane ya ce "Didi kinga abinda na gaya miki ko? Su k'asar su wallahi basu san kishiya ba, kuma duk abinda ta fad'a zata iya aikata shi ba burga bace irin ta Malama Bahaushiya, don Allah a raba aur

ennan." Na ce "Wallahi ba za'a raba ba sai dai ita ka saketa ta tattara ta koma k'asarsu don ni yanzu ba zan ma amince ka bita ba, balle su kashe min kai a can."

Da kyar da sid'in goshi Malam ya rarrasheta, yayi da guntun larabcin sa ya ha

ɗ

a da guntun t

urancinsa sai ga shi tayi luf wallahi ta yarda ta amince zata zauna zuwa lokacin da zasu tafi. Tunda ta tabbata idan sun tafi da kyar zata barshi ya dawo nan kusa.

Ni kuwa gefe guda, na dinga tsuma Sadiya da kayan magunguna kala-kala da na tanada saboda

irin wannan ranar, har gyaran jiki nake mata a b'oye. Sai gashi kafin suyi shirin komawa Sadiya ta fara kwarara amai a bakin rariya da alama dai ta k'unso. Itama Sakina sai gashi ta fara nata laulayin. Hakan yasa ta uzzira masa sai sun koma can inda suka f

i wayo.

Ya lallab'a Malam aka siyar da wata Babbar gonar Malam d'in, ya bashi kud'in da niyyar zai je can ya kafa bisiness d'insa. Wannan kud'in shine silar arzikinsa.

Basu tafi da Sadiya ba amma yayi mata alk'awarin ba zai kai shekara ba zai dawo da z

arar ta haihu. Don kam ya karb'i Sadiya hannu bibbiyu ya tabbatar da zancen da nake gaya masa na kasancewarta yarinya mai hak'uri mai kuma ibada.

Duk wani abin buk'ata na haihuwa sai da ya dire mata shi. Tun farkon cikin matarsa ta k'wallafawa ranta haih

uwar namiji don kullum sai ta fad'a idan muna hira cikin gwarancin Hausarta zata ce "Insha Allah Sadiya na mata zata haifa ni kuma na maza." Dariya muke mata Sadiya ta ce Allah dai ya kawo mai albarka.

Ita ta fara haihuwa ta haifi Mace, suna yin arba'in

da kwana biyu suka zo Nigeria Sadiya ta dinga murna da ganin y'ar nan ita da Lauratu, yarinya jajir kamar Balarabiya Ta d'auko uwarta Sak.

Zuwansu da kwana goma Sadiya ta zankad'o namiji sak mahaifinsa tun a ranar Sakina ta fara bak'in ciki kuma ta kasa

dannewa har sai da ya fito fili. D'an shirin da aka fara yi da ita duk ta watsar, ta janye y'arta ba ta barin kowa ya d'auketa. Kullum rayuwarsu suke yi a d'aki. Ko Na aika nace ta bani yayarku Najwa sai ta hana,

Har na hak'ura na tattara ta na zubar.

Ranar suna yaro yaci sunan kakanku muna kiransa Hammad shine a can k'asar waje sanda ya tafi baki fi shekara hud'u ba har yau kuma baiyi sha'awar dawowa ba.

Ko shekara ba suyi da komawa ba suka dawo Nigeria gaba d'aya, don lokacin ubanku arziki ya zauna

masa har ya siyi gida Anan cutar da Malam yake yi ya buk'aci ya dawo ya fara kula da k'annensa don ya tabbatat ciwon ajali yakeyi.

Kamar yarda Sadiya take da tsohon ciki, wannan karan ma Sakina cikin ne da ita sai dai nata karami ne.

Ranar da Sadiya t

ake nak'uda na lura Sakina a k'age take taga abinda Sadiyar zata haifa, don dama kaf nice nake karb'ar haihuwarsu. Abin ikon Allah sai ga Sadiya ta haifi santalelen yaro wannan karan ma namiji.

Sakina kuma da ta tashi haihuwa itama ni na karb'i haihuwart

a sai ga shi ta haifi mace.__~AL

Ƙ

ALAMIN JIKAR NASHE

YA  ABIN  YAKE ?

LIttafin Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

Follow me on wattpad

Nazeefah381

ELEGANT ONLINE WRITERS

(Ha

ɗ

in kai shine takenmu.)

********************************

Hankalinta

a tashe take duban yarinyar kafin ta ce "Wannan karan ma Mace ce?"

Ina murmushi na amsa mata Macece kyakykyawa kuwa har tafi Najwa kyau." Wani tsaki tayi, kafin k'wallar da ta taru a idonta ta zubo mata cikin muryar kukan ta ce "Ya Allah yaushe Zaka cik

a min burin da na dad'e ina fata."

Da sauri na janyo  ista'aza raina a b'ace na ce "Sakina me kenan? Shin ba zaki godewa Allah ba da ya baki kyautar yara matan? ki kuma yi addu'a Allah yasa su zame miki sanyin Idaniya."

Hawayen fuskarta ta d'auke kafin

Ta ce "Ni ban ta'ba son haihuwar mace ba, kullum burina da tunanina a haihuwar yara maza yake, sai gashi Sadiya tana samu ni ban samu ba."

A zafafe nace Allah ne yaso ya jarrabeki, sai kiyi ta istigfari, da kika samuma kike haihuwar wasu suna can suna r

ok'on Allah ya basu yaran ma kowane jinsi ne amma bai basu ba, Sai ke da kika samu har kike k'ok'arin tantance jinsin da kike so, ki tuba ga Allah kafin yayi fushi dake."

Na mik'a mata yarinyar ta karb'eta cikin halin ko in kula sai kuma ta saki d'an mur

mushi ba mamaki na ganin yarinyar kyakykywar gaske ce.

____________________________________ Bayan sunan yarinyarta ta biyu da sati biyu Najma Allah ya karb'i ran Malam bayan ya sha doguwar jinya, tabbas mun shiga alhini da tashin hankali kuma mutuwar t

a shiga jikin mu sosai bare ni da nake ganin mutuwar tasa ni aka yiwa. Haka Rabbi yake baya barin wani don wani yaji dad'i.

A tsukun lokacin bayan na fita daga takaba mahaifinki ya kammala wannan ginin da muke ciki Muka tattara muka dawo, cikin birnin Ka

no.

Anan aka yi bikin Lauratu da Gadanga da ya auri k'anwar Sadiya Murjanatu.

Anan kuma iyayenki suka ta hayayyafa har zuwa sanda aka zo kan cikinki, Sakina ta dinga murna da fallasuwar cikin, mu dai bamu san dalili ba.

Wata rana taje asibiti ta dawo

sai gata ta shigo d'akina da sauri ta zauna a saman kujera takarda a hannunta tana ta jifan Yayanku Hammad da murmushi, wanda bamu san dalilin da yasa ya tsaneta ba, duk da a lokacin bai zarce shekaru sha tara ba, yaro ne shi mai Kazar-kazar da fara'a ga

son mutane amma tashi d'aya gaba d'aya halayensa suka canja ya zama mafad'aci, miskili da son kad'aicewa shi kad'ai ba kuma ya san ganin matar Babanku,

Ko me yake da zarar ya ganta yake barin wajen.

Kamar a tsorace yake da ita. Kuma tambayar duniya an ma

sa ya ce "Bakomai" Ganin lamarin nasa kamar ya fara girmama Babanku ya tasa shi a gaba akan lallai sai ya fad'i dalilinsa, take ya sanar dashi son fita waje karatu aka ce ya zab'i k'asar da yake so ya ce "Birmingham" dake can a k'asar England.

Nan kuwa aka

fara yi masa shirye-shiryen tafiya wajen.

Da murmushin ta mik'o min takarda tana cewa "Didi Burina zai cika, wannan karan cikin namiji nake d'auke da shi, bayan na k'i haihuwa har shekaru biyar saboda ina tsoron sake haihuwar mace sai gashi Allah ya cik

a min burina a wannan karan namiji zan haifa." Ta fad'a idanunta cikin na Hammad, gani kawai nayi ya mik'e da sauri ya fice daga sashen nawa.

Nima cikin murna nace mata "Masha Allah, abin Allah kenan da har kina cewa kin daina haihuwar?"

Da murna ta mi

k'e ta fice ni kuma na bi bayanta ina taajjibin lamarinta.

Duk cikun-cikun da akayi na son Hammad ya tafi karatu Allah bai yi ba, sai da aka ja lokaci. A tsukun wannan lokacin ina hankalce da shi tsana mai tsanani ta shiga tsakaninsa da mahaifiyarki sam

baya son ganinta. Sau tari na sha kama shi yana kuka amma tambayr duniya sai ya ce "Bakomai." Har raina ya b'aci na tattara lamarinsa na watsar.

Cikin Sakina ya isa haihuwa, ta fara d'igimi da shirye-shirye, d'aki guda ta ware a b'angarenta aka zuba kay

an yara maza, komai fari da kalar shud'i, kalar maza kenan a lokacin naji suna fad'a. Duk wani tattalin arzikin Sakina akan cikin nan  ta k'arar dashi, har shirin Suna duk tayi.

Wannan karan ma, cikin dare ta fara nak'uda aka kira likita, da ni da likita

r muka karb'i haihuwarta.

Tun da tayi nishi ko zafin nak'udar bata ji ba ta zuba ido tana son ganin mai ta haifa.

Nice Na zaro ki, gabana ya fad'i ganin dai wannan karan ma an kuma macece ta haifi mace, tun kafin a yanke cibiya Sakina ta cire kunyarta,

cikin gwarancin hausarta take cewa na mik'o mata shi

ta ganshi, gaba na ya dinga luguden daka ganin mace ce ban san kalar haukan da zata yi ba idan ta ganki, ban da kasancewarki mace duk a yaran da take haifa ke kika zo da duhun kala. Murmushin yak'e Na s

aki.

"Bari ki shirya a tsanake sai ki ga babyn, ki shiga ki gasa jikinki tukunna, Ai ba gudu ake ba."

Bata min musu ba, ta mik'e ta shige toilet, ni kuma na fice da jaririyar nayi mata wanka tas a falo. Na sink'eta cikin kayan sanyi burina ta bata Nono

a karan farko kafin ta san abinda ta haifa. Zai ma yi wuya na gaya mata yau.

A bakin gado na tarar da ita, tayi kyau sosai cikin shigar atamfarta England y'ar Ghana. Na mik'a mata Babyn bata kawo komai a ranta ba ta fidda wankakken Mamanta ta bata ta sh

a sosai ba tare da sanin me ta haifa ba.

Likitar naja gefe nace ta ja bakinta tayi shiru kada ta sanar da ita.

Amma me? Cikin talatainin dare na dinga jin wani irin bugu kamar za'a jijjige min k'ofa a razane na farka ina fad'in wanene?" Muryarta a shak

'e ta ce "Ni ce" Na bud'e k'ofar gabana na fad'uwa ina fad'in Sakina Lafiya?" Duk da Na San dawar garin. Mik'o min jaririyar tayi fuskarta a had'e ta ce "Wallahi, ba zan shayar da ita ba, wallahi asiri aka yi min kuma bani da haufi Sadiya ce tasa matsafa s

uka canja min yaro na, namiji aka nuna min har a scanning a mafarkina kuma namiji na gani."

Tsananin mamaki yasa na kasa ce mata komai sai karb'ar yarinyar da take shirin yar da ita nayi, ko pampers babu a jikin yarinyar sai tsala ihu take.

Raina a b'

ace nace "Yanzu Sakina wannan wani shirme ne? A darennnan zaki kawo min yarinya ya kike so nayi da ita? Ina da abin bata ne? Kina ganin tana Kuka."

"Wallahi sai dai ta mutu, in dai da Nono na zata rayu wanda na bata ma don ban san mace bace."

Daga hak

a ta juya a fusace ta shige sashenta, duk da kiran da nake k'wala mata amma tayi burus dani.

Tilas na juya da ke cikin d'akina, Na jik'a dabinon ajwa a ruwan zamzam shi na dinga baki har aka wayi gari.

Da Asuba Babanku ya shigo b'angarena kamar yarda ya

saba shigowa duk asuba.

Mamakine ya kamashi gani na da yarinya a zaune na zuba uban tagumi. Hankalinsa a tashe ya dinga tambayata "Lafiya?" Na ja ajiyar numfashi idanu na cike da kwalla Na fara gyara zama ina Bahijja

labarin abinda ake ciki, Salati ya sa

ka. Dai-dai lokacin da Hammad ya shigo, Babanku ya mik'a masa yarinyar ya ce "Karb'eta kaje falo ina fitowa." Wata irin zabura yayi yaja baya yana girgiza Kai, kamar yaga abin tsoro sai kuma ya fice da sauri cikin tsananin b'acin rai.

Mamaki ya kama mu ni

da Babanku, sai dai ya girgiza kai ya fice da yarinyar a hannunsa.

Dambarwar tsiya aka kwasa, tsakaninta da shi akan sai ta shayar dake amma ta k'ek'asa k'asa ta ce sam ba zata yarda ba sai dai ya saketa.

Ganin lamarin ya ta'azzara yasa naje nace ya fi

ce na karb'i yarinyar da zummar na bawa Sadiya da ta nuna tana sha'awar rik'eki, amma nan ma ta k'ek'asa k'asa Ta ce bata amince a bawa Sadiya ke ba, ta karb'eki a hannuna sai dai sam ta k'i yarda Ta shayar dake sai dai madara haka kika tashi a gantale waj

en y'an aiki, wani lokacin na karb'oki wani lokacin ta bani haushi na k'yaleki.

A tsukun lokaci abin Hammad ya ta'azzara dole aka sadashi da asibiti nan ya fara ganin likita, aka d'ora shi kan magani muka samu ya samu lafiya ya tattara ya tafi karatu.

Bai sake waiwayar garin ba sai bayan shekara hud'u lokacin da ya dawo sai kuma yazo da sabon salo ya dinga janki a jiki, yana nuna miki Soyayya da kulawa, kuma ko Uwar da ta kawo ki duniya ma bata isa ta dokeki ba matuk'ar yana wajen, sai muka lura a loka

cin ma kamar wani shakkarsa da tsoronsa take ji.

Bana manta wata rana kin dawo daga Islamiyya baki fi shekara biyar ba shi kuwa a lokacin shekararsa ashirin da hud'u,kika yiwa Amminku laifi ko sugar kika zubar mata ta dinga jibgarki sai ga shi Allah ya k

awo shi, ya dawo daga companyn mahaifinku da yake tab'a aiki a can, yana ganinki kina kuka yaja hannunki, kuka nufi wajen da take ya shiga surfa mata masifa abin har mamaki ya dinga bamu ganin yarda yake surfeta da masifa amma tayi shiru har ya gaji ya taf

i.

Shine fa bayan kwana biyu ya gama shirinsa, sai gashi yaje Gwarzo yake gaya min zai koma Birmingham, hankalina ya tashi nace bai isa ba ya bari a masa aure.

Girgiza kai yayi ya ce "Ba zan iya k'ara ko kwana guda ba akan jibin da zan tafi idan kun s

hirya auren ku samo min matar a d'aura auren zan mata visa aka kawo min ita ina maraba da zab'inku ko wacece.

Shine fa muka sama masa Nanna y'ar yar Babarsa, aka yi auren aka tura masa ita.

shi kam  bai sake dawowa ba amma ita Nanna tana zuwa hutu duk K

'arshen shekara yaranne dai baya bari tazo dasu saboda makaranta.

Wannan shine abinda na sani na dangane da labarinki da dalilin tsanar mahaifiyarki gareki, a zahiri dai wannan shine bamu san bad'ininta ba, sai ki cigaba da hak'uri har Allah ya nuna ma

ta ikonsa a kanki ba mamaki kece wacce zata zo tayi alfahari da ita nan gaba kad'an ki zame mata Sanyin idaniya."

Tuni hawaye ya gama b'ata mata fuska, a yau ta tabbatar ba laifin da tayiwa mahaifiyarta laifinta d'aya da tazo a jinsin Mace, menene laifi

nta anan? Me yasa kuma bata tsani sauran y'ay'anta ba sai ita? Ko don ita bak'a ce? Tabbas hakane aka amsa mata daga can k'asan zuciyarta, ya zama lallai ta nemawa kanta mafita kafin ciwon damuwa (Depression) ya kamata._~AL

Ƙ

ALAMIN JIKAR NASHE

YA  ABIN  Y

AKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387

Follow me on wattpad

Nazeefah381

ELEGANT ONLINE WRITERS

**********************************

                   BIRMINGHAM

Dake k'asar England.

Unguwar padstow Road Birmingham B24.

A ciki

n d'aya daga cikin gidajen rent d'in masu bala'in kyau. Gida ne mai d'auke da 3 bedrooms da 1 parlour sai kitchen da dinning area.

Kamar yarda aka san gine-ginen turawa wannan ma gini ne da yake d'auke da tsari, da zarar ka kalleshi tun a waje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login