Showing 15001 words to 18000 words out of 129261 words

Chapter 6 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

58

zai birge

ka balle idan ka shiga cikin ainahin building d'in.

Nanna ce zaune gefe guda da waya a hannunta tana kuka sosai bayan samun sak'on mutuwar Babanta.

Ta sake kallon Hammad mijinta a karo na biyu kafin ta ce "Kayi wa darajar girman Allah ka bini mu tafi t

are har yarannan, yanzu fa Khairi shekararta Sha d'aya amma bata san danginka ba balle nawa, sannan yanzu ma Baba na ya mutu kace ba zaka ba, wannan wace irin masifa ce wai me aka yi maka a Nigeria?" Ta fad'i furicin hawayen na sake kwarara a fuskarta na z

allar b'acin ran mijin nata wanda wani lokacin idan ya rikid'e mata sai ya zama kamar bak'in kumurci don fad'a da b'acin rai, wani lokacin kuma suyi zamansu gwanin sha'awa.

Wannan karan ma ya rikid'e d'in, don runannun idanunsa ya d'ago ya zuba su a kan

ta, wanda ya sata had'iye kukan babu shiri. Tayi saurin mik'ewa zata shige d'aki da azama ya fincikota, rintse idanunta tayi tana jiran taji saukar mari kamar yarda ya saba a duk sanda ta kawo masa zancen zuwan Sa Nigeria.

Madadin marin wannan karan hank

ad'ata kawai ya yi ya mik'e da sauri ya shige bedroom d'insa ya kulle k'ofar har da murza key.

Nanna ta runtse idanunta, don ta San tabbas abinnasa yazo, idan abin ya tashi zame mata yake

kamar mahaukaci, sai kace mai aljannu. A hankali furucin Ya Allah

ya fito daga bakinta.

Ba zata bishi ba don ta san ko zata shekara tana bugu ba zai bud'e ba a wannan bad condition d'in da yake. Allah ma ya taimaka yau baya zuwa aiki da bata san yarda zata yi da shi ba.

Wayarta ta shiga lalube ta fara danna kiran Mah

mah, gwara ta gaya mata tayi iya yinta ya ce Ba zai zo ba.

Bugu biyu Mahmah ta d'au wayar, dafatan Allah yasa surukartata taci nasarar shawo mata kan d'annata. Madadin daddad'an labarin sab'anin haka ta samu. Mahmah ta runtse ido zuciyarta na karyewa bata

san dalilin yaronta Na rashin son zuwa inda suke ba, ko su suke son ganinsa sai dai yayi Musu Visa suyi tattaki su je. Gashi wannan karan Didi ta takura ta gaya musu dole su saka Hammad d'in yazo gida musamman da surikinsa ya mutu.

Ta ja aijyar zuciya ka

fin ta ce "Shikkenan, ki kyaleshi zuwa anjima zan kira shi, dama har yanzu yana shiga wannan condition d'in?"

Nanna ta ja ajiyar zuciya kafin ta saki kuka na nuna alamun zallar damuwa ta ce "In dai zan masa zancen da ya shafi Nigeria sai yayi." Mahmah ta

yi jim kafin ta ce "Kin ga kuwa dole yazo ko dan na nema masa Magani, zuwa yanzu kam na tabbata ba k'alau tabbas akwai wani k'ulli da Allah ne kad'ai ya barwa kansa sani."

Daga haka suka yi sallama, Mahmah ta lalubi numberr Hammad ta tura masa text.

Slm.

     Ya zama dole ka taho Nigeria a wannan gab'ar idan ba so kake na bayyana maka b'acin rai na ba ta hanyar sallamaka a cikin zuri'ata.

Daga haka ta ajiye wayar, ta jingina kanta jikin kujera wannan karan zuciyarta ta kasa sukuni har sai da ta zubar d

a wasu tarin ruwan hawaye. Rashin gane takamaimai matsalar d'annata abin yana ci mata tuwo a k'warya kullu yaumin da abin take kwana ta tashi kuma, don dai ta kasance mace mai juriya ba kasafai take bari b'acin rai ya bayyana k'uru-k'uru a fuskarta ba.

Ta

haddaci k'unshe b'acin rai tun farkon aurenta da mijinta, da ta tabbatar ba sonta yake ba yana zaune da ita ne kawai don itace zab'in Didi mahaifiyarsa, amma soyayyarsa kam tana ga Sakinah Balarabiya da soyayarta yake kwana yake tashi sau tari ya sha kira

n sunan Sakina a cikin barcinsa ko a yayin da suke saduwar aure. Duk ta danne take zaune da shi da zuciya d'aya, ta kowane hali kuma burinta yi masa biyayya ko ta samu rahmar ubangiji tunda dai shi yayi umarni abi su.

Ta share hawayen da ya zubo mata a fi

li ya furta YA ALLAH ka kawo mana d'auki akan bawannan naka ka sanyaya zuciyarsa ka dawo min da hankalinsa gida.

____________________________________

Farkawarsa daga nauyayyen barcin da ya sureshi yaci karo da sak'on mahaifiyarsa. Zuciyarsa ce ta buga

ya tabbata yau Mahmah fushinta ya kai mak'ura, don bata tab'a nuna masa b'acin ran wanzuwarsa a Birmingham ba sai yau. Shi kuwa ya tabbata idan yaje Nigeria ya sake ganin yarinyar nan ba abin mamaki bane zuciyarsa ta buga. Shi a nasa tsarin yayi sallama da

k'asar sa ta haihuwa babu abinda zai sake mayar da shi. Me yasa Mahmah zata yi masa wannan furucin bata san zamansa anan shine kwanciyar hankalin kowa a zuri'arsu ba. Cikin wani irin yanayi ya murza goshinsa tare da furta Oh Allah.

Ya sake duba agogonsa

sai yaga har lokacin dawowar yara tuni ya shige ya tabbata zuwa lokacin Nanna ta d'aukosu.

Wanka yayi kafin ya fita parlourn.

duk da zuciyarsa a tunzire take bai hanashi shafa kan yaran nasa ba da suke zaune suna buga ps game a tv. Idanunsa akan Yarinya

rsa ta biyu Kamla, yana mamakin sake bayyanar kamatarta da waccan yarinyar Hamda da gaske suna kama sosai yarda take black beauty haka Kamla take da eye shape da mouth d'insu duk d'aya.

Cikin k'udirar Ubangiji sam ba banbanci a zubin a halittarsu, ba zai

mance kamannin k'anwar tasa ba a idanunsa. Da sauri ya rik'e kansa yana tuhumar kansa da zamantowarta k'anwar tasa a zahiri take k'anwarsa amma a bad'ini shi da uwarta sun san sai dai su kira ta........

Ya runtse idanunsa baya son tuna matsayin yarinyar,

abu ne da zai iya kiransa direct ABIN KUNYA da Allah Wadai.

Murmushi ya sakarwa Nanna da take tsaye da cup d'in coffee tea a hannunta tana mik'a masa, duk da ranta a b'ace yake kuma idanunta sun nuna ta sha kuka bata fasa kyautata masa a kowanne yanayi y

ake. Da gaske Nanna ta cancanci kansa tsaye ya kira ta da suna MACE TA GARI. Ta kowanne fanni ta cika ta tumbatsa bata da makusa ko kad'an.

Hannunta ya ja ya zaunar a gefensa bayan ya lura hankalin yaran su yana kan t.v game, don duk kasancewar suna rayu

war turai suna matuk'ar jajircewa wajen tarbiyyar yaransu.

Ya rungumota jikinsa sosai, kafin a kunne ya rad'a mata  "Am very much sorry, zamu wuce Nigeria within this week Allah yaji k'an Baba." Wani irin tsalle tayi tare da rugumeshi, wanda har sai da ya

ja hankalin yaransu. Abul khair ya ware ido yana furta What?" Nanna ta jashi jikinta had'e da cewa "Uban masu gida zamu je Nigeria k'asar da kuke son zuwa gashi har Babana ya mutu bai sanku ba." Da Hausa tayi masa maganar kasancewar sosai suke musu Hausa s

hi yasa

yaran suka iya yaren Hausa tunda nan ne asalinsu da tushensu.

Yaran ma sosai suka shiga murna

Musamman Khairi da burinta dama taje Nigeria. A ranar ya fara nema musu booking flight kafin kashegari yaje ma'aikatarsu ta Miller Hughes construction Bu

ilding contractor ya sanar musu yana buk'atar d'aukan hutu. Bai sha wahala ba wajen amincewarsu musamman sani ba tab'a nema yayi ba.

Daga nan ya tafi makarantar yaransa Junior league of Birmingham sunshine school suma ya fad'a musu, suma suka nuna masa ba

komai zasu bawa yaran kayan karatun da zasu dinga yi kafin su dawo.

Shikkenan suka fara shirye-shirye yayi waya ya sanar da Mahmah da Abbu zuwansu in the next four days. Gaba d'aya gidan murna aka d'auka na zuwan Babban Yaya.

_________________________

____

Gefe guda kuwa Sakina hankalinta a tashe yake da zuwan nasa, a zuciyarta ba sak'e-sak'en da ba tayi ba, wato bai ji abinda tace masa ba akan sake dawowarsa Nigeria shine zai sake dawowa, sam bata san wanzuwarsa a gidan gudun bankad'uwar sirrinsu. Sh

i yasa ma take ta bankawa Malamai kud'i akan a cire masa son gida gaba d'aya a ransa.

Hanakalinta ba k'aramin tashi yayi ba ta shiga suntiri cikin bedroom dinta cikin mummunan b'acin rai tabbas lokaci yayi da zata san mataki na k'arshe da zata d'auka aka

n Hammad, duk da dai ta san ba zai tab'a fitowa ya gayawa duniya wannan sirrin ba tunda shina kamar ya d'au wuk'a ya dab'awa kansa ne.

_____________________________

Gidan a hargitse yake sosai da shirin dawowar Hammad d'in. Abbu yasa an fitar da kayan

da yake sashensa tun yana saurayi gaba d'aya, akayi fenti tare da canja komai Na toilet da furnitures d'in ciki. D'aki biyu ne da parlour kawai a ciki sai wani k'aramin kitchen. Guri ya d'au harami sosai sai jiran dawowar Babban Yaya.

Y'ayan su Gadanga

k'annen Abbu duk Didi tayi musu waya akan su zo. Musamman kasancewar

lokacin hutun second term ne anan k'asar mu ta gado Nigeria.

Yaran Gadanga Ali k'usar yak'i hud'u: Salima Salima Salman sai Salma.

Ita kuwa Asma'u yaranta uku Sajeed, Sajida sai Sajjad

.

Lauratu tana da hud'u: Sa'ad,Sa'adatu sai Sadik da Saddik'a.

Nan kuwa gidan Umaru Usman Dan Borno da aka fi sani da UU D'an Borno kamar yarda kuka sani Sadiya Na da yara biyar Hammad Humaid  Sai Hamidan da Abdul Hameed da Humaid.

Ita kuma Sakina (

Ammi Na da Biyar) Najwa ce babba sai Nasma da Ahlam sai Muneerat da Hamda. Wad'anna sune jikokin Didi tsohuwa mai ran k'arfe, mai tsage gaskiya duk d'acinta. Manyan duk an aurar dasu idan ka cire d'akin Ammi da mace d'aya jal ta aurar. Inda ta auri wani ha

mshak'in d'an kasuwa suke zaune a can k'asar ibadan yanki yarbawa duk da bahaushe ne ya zab'i zaman ibadan a can ya ke duk wasu kamfaninnikansa saboda rashin kishin arewa.

_____________________________

Da k'arfe hud'u na yammacin ranar ta juma'a suka S

anka a airport d'in Malam Aminu Kano international airport da ke birnin kano.

Kaf k'annensa maza da cousins brothers d'insa ne suka zo tararsa.

Suka fara saukowa daga jirgin, ransa ya b'aci lokacin da ya fara shak'ar iskar Nigeria.

Sanye yake cikin

black jeans na companyn Gucci, Sai casual T.shirt Na companyn Tommy Hilfiger dake U.S da rigar sanyin Tomford Bumber a jikinsa sai zabga k'amshin turarensa na kullum yake Emporio armani oud. K'afafunsa sanye da takalman Dolce and Gabbana logo embossed leat

her slippers, bak'ake Wanda suka haskaka kyakkyawar tausashshiyar fatar k'afarsa. Idanunsa kuwa cikin black glass suke Na companyn Gucci. Hannunsa da yake d'aure da agogo k'irar Gucci bracelet watch ya kalla. Yana sauka daga matattakalar jirgin fuskarsa a

d'an d'aure yana sakin tsaki akai-akai musamman ganin arnen zafin da ake kwararawa a k'asar Nigeria mai barazanar dafa fatar mutum, musamman Su da suka dad'e basa k'asar. Ya ilahil Alameeen' ya fad'a murya a cunkushe.

Daga kallon farko idan kayi masa zata

zaka yi saurayi ne da ba zai haure matakin shekaru takatin ba ba zaka Ta'ba bashi shekaru har talatin da takwas ba.

Da gudu k'annesa suka rungume y'an cutest yaransa. Idanun Hamood cikin na Kamla da sauri ya bud'e baki yace "Masha Allah Hamda's carbon

copy." Da sauri sauran ma suka kai dubansu kanta suna ta'ajjabi da mamaki a zahirance suka ce "Wannan dai Hamda ka haifo y'a." Gabansa ne yake fad'uwa a duk sa'ilin da suka had'a Hamda da y'arsa, duk da zahiran shima ya san suna kama irin kamar nan da dole

idan Na gansu ka san JININ SU D'AYA.DON SAMUN WANNAN LITTAFIN KYAUTA NA YA ABIN YAKE SHIGA WANNAN LINK D



IN ZA



A DINGA TURASHI SAU UKU A RANA.

DAGA ALKALAMIN NAZEEFAH SABO NASHE



Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/5Y2E

mZDu7OvHg6iDTCY81D

Alk'alamin JIKAR NASHE

Ya Abin Yake?

Page 9.

08033748387

Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care

Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana

gyara fata tayi kyau

Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo

Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861

Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya af

arashin company

Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd

_________________

Haka suka d'unguma zuwa ainahin main House d'in su da ke unguwar Hotoro G.R.A.

Mutanen

gidan suna jin shigowar motocinsu suka fita a guje domin tararsa.

Sakina ce kawai bata fito ba, da yaranta masu bak'in hali Najma da Nasma. Amma hatta da Muneerat sai da ta fito a guje duk da kiran da Ammin take zabga mata.

Tunda ya fito ya zubawa k'

annensa ido yana mamakin yarda suka girma lokaci guda. Har zai shiga sashen mahaifiyarsa Hamood ya kama hannunsa had'e da fad'in "Big Bro rufa mana asiri idan ba so kake Didi tasa ayi yak'in duniya na biyu ba."

Ya d'an bud'e ido yana kallon k'aninnasa, s

aboda sam ya manta a irin wannan lokacin Didin tana kasancewa ne a gidansu.

Ya juya direct ya nufa sashenta, yaransa da matarsa suna bin sa da sauri. Mahmah da take tsaye a window Ta saki Hamdala don farin cikin ganin yaronta, duk da kawaici da Alkunya y

a hanata fita ta ganshi.

Didi da azama ta mik'e tana janye k'afarta da Hamda take shafawa Man zafi. Cikin fara'a kamar bakinta zai yage take fad'in Maraba lale, Oyoyo da mutanen Birmingham Masha Allah tubarakallah. Ta rungumeshi cikin tsananin farin cik

i.

Hamda kuwa idanunta cikin na Kamla tana mamakin tsananin kamarsu. Su kansu su Khairi kallonta suke musamman Nanna da ta kasa janye idanunta daga kallon yarinyar mai kama da tata d'iyar Kwabo da Kwabo. Saboda duk zuwan da take Hamda lokacin tana makaran

ta shi yasa basu tab'a had'uwa da ita ba.

Hamda cikin ladabi ta durk'usa ta gaida Nanna, ita kuwa ta jata a jiki tana kallon Didi da Hammad da ya rintse idanunsa yana mamakin yarda yarinyar ta sake girma, da gaske kuma tsananin kamanninsu ya sake bayyana

da Kamla musamman yanzu da suke zaune waje d'aya.

Cikin Masifa Didi ta dinga korar mutanen da suka yi dandazo a falonta. "Haba yau naji masifa, a bar mutum ma ya huta da jikokinsa ba za'a bari an zo an zuba musu ido kamar me? Ni jaraba ta yaran gidannan

ta fara isata, mutane ga ido k'wala-k'wala, duk sun bi sun gado manyan idona na masifa."

Ta dinga mita bayan sun tafi sun barta da jikokinnata sai kace su ba jikokinta bane, ko da yake su kansu sun san soyayyar da takewa Hammad daban ce, ko kuma don kasa

ncewarsa shine Jikanta Babba a maza tunda Najwa da suke kira Yana ta girme masa.

Sai da suka tafin sannan ta zuba idonta akan Hamda ta saki baki tana kallon kamanninsu da Kamla.

Gaza shiru tayi har sai da ta magantu "Ikon Allah, ikon gaske kai kuma Ham

madu sai ka haifo mai kama da Hamda kwabo da kwabo, ko wa suka yo a dangi don mu dai kaf danginmu ba masu kama da mutanen itofiya (Ethiopian).

Idanunsa ya zuba yana kallonsu, a duk sanda kuma ya kallesu sai gabansa ya buga fad'uwar gaba ta sameshi, baya

son ana yawan ambaton kamanninsu haka ne yake sawa yaji k'irjinsa kamar ya tarwatse.

Nanna ta ce "Ai haka lamarin ubangiji yake, ba abin mamaki bane musamman kasancewarsu Jini d'aya, ai k'arfin jini ya zarce haka." Hammad ya sake jin dukan da k'irjinsa y

ake ya tsananta musamman da ake ta nanata kalmar Jini d'aya. Anya kuwa wannan sirrin da suke k'ok'arin k'udindunewa nan gaba kad'an kuwa ba zai fallasu ba.

A sama ya jiyo muryar Didi tana tsaki "Ayi mace lusara, kina girma kina cin kashi abincin ma jira

kike nace ki d'ebo ki kawo musu? Bayan tun safe muke tsaye akan digadiginmu muna aikinnan amma ba zaki tashi ki kwaso su ba."

Ita dai Hamda bata bari ta k'arasa mitar ba, sai tsintar ta suka yi a k'ofar kitchen, Nanna Ta sake binta da kallo tana yaba kyau

da tsarin halittar zubin jikin yarinyar, farin ciki ya cikata da ta tuna itama Kamlanta haka zata dawo mai kyau idan ta girma.

Shi kuwa Hammad tunaninsa daban yake ta yarda yake mamakin  girmanta, duk da ba wata k'iba bace da ita amma duk wasu halittu na

y'an matancinta a cike taf da albarkatun ubangiji. Yayi ta'awwizu da tunanin hakan da yayi don ya San sarai ba shi da hurumi anan.

K'ememe Didi ta hanasu tafiya wajen Mahmah da ta kasa zuwa ta gansu, anan suka zube akan daddumar Didi mai taushin gaske s

uka ci abincin mai dad'I don Didi gwana ce wajen girki shi yasa Hamda ita ma ta koya. Ta iya girkuna kala-kala.

Shigowa U U D'an Borno ya yi yana fara'a, da farin cikin ganin yaronsa da familynsa.

Da sauri Hammad da Nanna suka durk'usa don gaisheshi ha

ka nan su Khairi da Abul khair ma suka gaisheshi.

Idanunsa akan Kamla yana dafe da kan Abul khair ya ce "Didi kin ga ikon Allah ko? Tunda naje barkar yarinyar nan na ce miki kamar su d'aya da Hamda, don har hotonta Na d'auko a waya Na had'a da Na Hamda wa

llahi ba banbanci ko kad'an banbancin d'aya ne wannan lotsawar da Hamda take da shi a k'asan hab'a ita Kamla a gefen Hanci take da shi. Tabbas kun haifawa Hamda y'a don nan gaba ko guduwa tayi da ita ba wanda Zai ce ba y'arta bace."

Gani suka yi kawai Ha

mmad ya rik'e kansa ya mik'e, had'e da cewa "Godiya nake Didi, bari naje na gaida iyalan Abbu" daga haka yasa kai ya fice da sauri bai saurari surutun Didi ba.

Su Nanna ma suka bi shi suna dariya.

B'angaren Ammi ya fara shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login