Showing 18001 words to 21000 words out of 129261 words
direct, yana fatan ya iya d
anne b'acin ransa idan yayi arba da fuskarta da kai tsaye yake kira bak'ar Fuska. Addu'oi ya fara yi a zuciyarsa kafin ya saka kai cikin sashen nata.
A zaune ya sameta saman kujera, gaba d'aya yanayinta zaka kalla ka tabbatarwa kanka da gaske yau bata ci
kin nutsuwar zuciya, don dai ko kallabin kanta bata d'aura ba balle akai tajallin gyaran gashi.
Idanunta k'ozai-k'ozai babu kwalli. Guri d'aya ta zubawa ido, da alama tayi nisa cikin zuzzurfan tunanin da ya ke mata kaikawo a zuciya.
Bata ji sallamarsu
ba sam, sai k'amshin turarensa da ya riga ya zauna rad'am a hancinta ba tun yau ba tun yana saurayi shine dai ainahin turaren da yake amfani da shi.
K'amshin ne ya farkar da ita cikin razani, idanunsa kuwa suka gauraya cikin nata.
Y'ar fara'ar da take f
uskarsa ya d'inke tsaf, tare da amsa gaisuwar su Najma da suke gaisheshi cikin mutuntawa, kasancewar sun san shi mutum ne da baya wasa da su tun suna yara balle yanzu
da ya mallaki hankalin kansa.
Shigowar Kamla ne yasa Ammi wani irin mik'ewa da sauri ci
kin razana tana dubanta. Ganin yarda idanu suka yi yawa a kanta sai kuma ta sunkuyar da kai ta waske tana jan hannun Abulkhairi.
Abin mamaki madadin shi da yake matsayin d'a wajenta ya gaisheta, itace take gaisheshi cikin basarwa da sunkuyar da kai tamka
r dai surikinta.
Mintuna uku cikakku bai k'ara a d'akin ba, ya mik'e da sauri ya fice, yana jin zcuciyarsa kamar ana hura masa wuta. Suma su Nanna suka d'unguma suka bishi.
Hakanne ya bawa Ammi damar shigewa d'aki a sukwane tana sake lalubar numberr way
ar babbar aminiyarta da tun safe take nema bata shiga. Wannan karan ma dai still wayar a rufe take kamar yarda ake ta sake jaddada mata a waya.
A kujerar parlourn Mahmah ya zube idanunsa a runtse kafin ya bud'e ya zube su cikin na mahaifiyrsa da take t
a kallonsa cike da murmushi. Rabin hankalinta kuma yana kan Nanna da y'an jikokinta da sam babu shakuwa a tsakaninsu. Taja hannun Abul khairi tare da fad'in "Maigidan da ba awo ba cefane."
Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya samu damar gaishe da Mahma
hn cikin k'arfin hali da dauriyar zuciya. Mahmah ta amsa masa zuciyarta cike da farin cikin zuwansa Nigeria.
Sun dad'e suna hira duk da shi rabin hankalinsa ba akan hirar yake ba, sau tari sai Nanna ta sako shi a zancen sannan yake ankarewa da nisan tuna
nin da ya lula.
Ganin da ya yi ya rasa samun nutsuwa ya mik'e ya nufi sashensa, don ya sake nazari sosai akan lamarin da kansa tsaye zai iya cewa ALMARA.
_____________________________
Cikin sa'a k'arfe sha biyun dare ta samu numberr aminiyarta ta ta
shiga ta saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya, duk wani abu da ya tokare mata na b'acin rai ya sauka daga k'irjinta. Gani take tamkar ta samu mafita ta gama.
Murya a cunkushe ta ce "Ke kuwa Kady ina kika shiga tun safe nake nemanki?"
Kady daga can taja aj
iyar zuciya "Ke dai bari, ya aka yi? Akwai matsala ne?"
Tsaki Nanna taja ta ce "Idan kin ji matsala d'aya kenan matsaloli dai yaronnan Hammad fa ya dawo k'asar nan."
"Innalillahi!" Daga can Kady ta zabga kafin ta ce "Yanzu meye abin yi?" Ammi taja tsaki
"Ke zan tambaya kady, wallahi kaina ya k'ulle kin jefa ni a matsala da na sani tun farko ban karb'i shawararki ba, takaicina d'aya ranar fallasuwar sirrina, ranar da za'a tono b'aragurbin k'wan da na burne, ranar da jama'a da dama za su......" kuka ne ya
kufce mata. Kady tayi tsaki "Yanzu na barki kiyi kukan kenan? Idan kin gama kukan sai na kiraki, tunda kuka ne zai mana maganin matsalarmu."
Had'iye kukan tayi da kyar ta ce "To yanzu ya kike so ayi?"
"Ki bud'e kunne da kyau ki jini, idan zai yiwu a s
alwantar da ran Hammad kawai idan ba haka ba komai na iya faruwa."
Ammi ta saki ajiyar zuciya a karo na biyu kafin Ta ce "Kina ganin haka ne mafita?" Tsaki kawai Kady ta ja tare da latse madannin wayar ta mutu ta san sarai Ammin yanzu zata waske zancen
kisan, duk da ita dai bata hango wata mafita bayan wannanba.
___________
Sai da ya yi wanka sannan ya samu nutsuwa, duk da har a lokacin yana jin yanayin yarda k'irjinsa yake duka, Kansa yana matuk'ar sarawa, a zahirin gaskiya ji yake ya
Kamata ya san
ar da mahaifiyarsa zancen nan, duk da muninsa ya kai muni amma bai kamata ya b'oye mata ba ba yanzu ake ji ba gaba ake ji, tunda ya tabbatar Hamda bata da gadon mahaifinsa, Bai kamata kuma ta cigaba da amsa sunan Mahaifin nasa alhali shi yasa ba ubanta ban
e.......
To fa! Wannan shine Ya Abin Yake?DON SAMUN WANNAN LITTAFIN KYAUTA NA YA ABIN YAKE SHIGA WANNAN LINK D
’
IN ZA
’
A DINGA TURASHI SAU UKU A RANA.
DAGA ALKALAMIN NAZEEFAH SABO NASHE
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.co
m/5Y2EmZDu7OvHg6iDTCY81D
Alk'alamin Jikar Nashe.
Ya Abin Yake?
08033748387
Follow me on Wattpad
@Nazeefah381
ArewaBooks
@Nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
Da safiyar ranar ta shirya tsaf, da azama ta ja motarta s
ai gidan Kady don sam kasa barci tayi jiya tambayar duniya kuma Abbu yayi mata sai ta ce Bata jin dad'i ne, shi yasa yau tana cewa zata Asibiti bai yi nawar hanata ba, don yanayin da ta kwana shi kansa abin ya yi matuk'ar rikitashi, sai ya ce tun bayan hai
huwar Hamda bai tab'a riskarta a yanayi kwatankwacin na jiya ba.
Daga jin yanayin horn d'in motar Kady Ta tabbatar mutuniyartace ita kanta sam bata cikin nutsuwa don haka yau da wuri ta sallami mai gidan, tana shirin kiranta a waya sai gata ta bayyana. D
a sauri ta bud'e k'ofar hasashenta kuwa ya yi dai-dai don Sakina ce cikin wani irin yanayi ta shigo parlourn, wullar da jakarta kawai tayi ta ce "Kina ganin kashe Hammad shi zai rufe b'aragurbin sirrina?
"K'warai kuwa." Kady ta masa mata cike da k'warin g
wiwa "Rashin salwantar da rayuwar Hammad shi yake nuni da fallasuwar b'aragurbin k'wan da zai girgiza ahalin D'an Borno."
Sakina tayi tsai da ranta, kafin ta saki gwauran ajiyar zuciya, ta ce "Bana son salwantar rai, zan saka dai a sake masa gargad'i had'
e da tabbatar masa da k'udirina na k'arshe idan har ya sake ya bayyanawa mutane gaskiyar lamari."
Kady tsaki ta ja, kafin ta ce "Ni ban ga dalilinki na rashin son kashe shi ba, mutumin da rayuwarsa kamar wata bala'i ce ga taki rayuwar, ke da kanki kince b
aya miki kallon mutunci balle ya girmamaki, kina tunanin idan ya cigaba da yi miki haka uwarsa ba zata so sanin dalili ba? Kina tunanin idan ya b'oyewa kowa zai iya b'oyewa mahaifiyarsa?"
Sakina ta share zufar da ta game goshinta. Hankalinta a tashe ta ce
"Tabbas zancenki na kan hanya, saboda yarinyarsa Kamla yarda kika san kaki yarinyar nan Hamda tayi saboda tsananin kamarsu, ni kaina har mamakin bayyanuwar kamar nayi, wallahi abin ya bani tsoro kamar dai wata ishara ce
Allah yake so ya nuna...."
"Shi na
ke so ki gane, ki cire duk wani shakku a kawar dashi daga doron k'asa, ina dalili? Tun ranar da abin ya afku na sanar da ke a kawar da shi kika wani ce a gargad'eshi, alhali kwalliya bata biya kud'in sabulu ba namijin dai da kike so baki haifeshi ba, kika
tsaya cewa wai yaro ne zai ji tsoron tona hakan ga kowa, to ga dai yaro nan ya girma kuma yana shirin bankad'a duk wani sirri idan ba kiyi wasa ba, haba idan da nice ai da tuni an wuce wajen."
Sakina ta ja ajiyar zuciya "Shikkenan, ki bari zan shigo yank
e shawara anjima insha Allah." Daga haka suka yi sallama, Sakina kam ta samu salama a zuciyarta ta kuma amince da shawarar Kady tana ganin hakan kawai shine mafita a gareta, da ahalin D'an Borno family gaba d'aya.
_____________________________
Tun asub
a da ta farka bata koma ba gyara sashen Didi tayi kafin ta tafi sashen Amminta nan ma ta gyara. Wanka kawai tayi ta dawo parlourn Didin ta zauna had'e da d'aukar Alk'ur'ani tana karatu, Didi kuwa lazimi take, da radio a gefenta tana saurarar labaran BBC Ha
usa.
Sai da Takwas ta cika sannan ta shiga kitchen don d'ora abin karyawa kasancewar juma'a ce Didin bata azimin tsofaffi don idan watan azimin tsoffin ya shiga sau hud'u take yinsa duk sati litinin,talata,laraba da Alhamis.
Kunun tsamiya da ta saka wadat
accen lemon tsami tayi musu, sannan ta soya musu k'osai da dankali da k'wai.
Kafin kace me? Har ta gama, ta kawo Daddumar Didin ta jeresu. Didin shi mata albarka kawai take tana fad'in Uwarki tayi farar haihuwa sai dai ita bata san haka ba shashasha, a z
amanin nan samun yarinya mai hali irin naki ai sai an tona." Murmushi kawai Hamda tayi. Dai-dai lokacin da aka yi knocking k'ofar sashen Didin.
Tsaki Didi tayi kafin ta ce "Jaraba, ko waye kuma da safiyar nan? Allah yasa dai lafiya."
Hamda ta kalli agogon
parlourn ta ce "Didi k'arfe 9:30, yanzu ai ba sassafe bane." "Gurinki ne ba sassafe ba wajen mutanen gidan nan kam ai ba mamaki yanzu suka yi juyin farko." Hamda dariya ta guntse kafin ta k'arasa bakin k'ofar. Cikin sanyin muryarta ta ce "Wanene?" "Bud'e"
kawai ya ce cikin dakewar tasa muryar.
Gabanta ne ya fad'i sanin cewa shine tun jiya ta haddaci muryar tasa, da zarar taji take riskar kanta cikin wata irin razananniyar fad'uwar gaba.
Hannunta na rawa ta murd'a handle d'in k'ofar bayan ta murza mukulli
n da yake jikin k'ofar.
K'amshin turarensa ne ya fara dokar hancinta kafin ya shigo idanunsa a kanta, yarda ta mak'ale jikin bangon ya tabbatar masa da yanayinta na rashin sabo da jama'a. Kamar a tsorace take da mutane bata sakewa da su, kullum yanayinta
na nuna kamar ace kyat ta zura da gudu.
Idanunta a k'asa cikin rawar murya ta ce "Ina kwana?"
D'auke idanunsa ya yi daga kanta kafin ya amsa da "Lafiya" ya shige ya barta a tsaye ta bi bayansa da kallo sanye yake da jallabiya mai gajeren hannu, wanda ta
bayyana damtsen hannunsa da gashi ya kwanta luf a jikinsa.
A gefen Didi ya zauna yana gaisheta cike da Kamala, idanunsa akan coolers d'in da suke zube bisa daddumar, dama ji yake kamar an wawashe masa kayan cikin sa kaf, ko don daga training wanka kawai
yayi ya taho nan wajen Didi, kamar yarda ya saba tun a da, in dai Didin tana nan da safe nan wajenta yake karyawa.
Cup kawai suka ga ya d'auka ya fara tsiyayyar kunun da yake cikin flask d'in sai zabga k'amshi yake na lemon tsami da kayan k'amshi. Da tu
ririn da komai ya kai bakinsa, har hakan ya ba Hamda mamaki ganin yarda yake cin k'osan da zafinsa cikin hanzari ko ta kan Irish d'in bai bi ba. Haka dama shi yake cin abincinsa a hanzarce musamman idan yana jin yunwa, shi yasa yake da k'akk'arfan jiki kum
a ginanne mai d'auke da murjajjiyar fata.
Tsaki Didi tayi tana harararsa "Ni fa Hammadu bana son iya shege, waye ya gayyato ka nan kake shirin cinye mana abinci? Shi yasa ga kanan a tsaye k'ik'am da kai."
Fuskarsa ya d'aure sosai kafin ya ture kwanan k'
osan cikin fad'in "Alhamdulillah" Didi ta saka salati bayan ganin ya wawashe k'osan tas guda biyar kacal ya bari.
Murmushi ya sauke a fuskarta ya ce "Kin san rabona da irin abincin nan kuwa?" "Ina zan sani tunda ni ba Allahn musuru bace, kawai ka zo ka w
awashe k'osan nan yarinyar nan ko ci ba tayi ba, tun safe take aiki akan digadiginta, ina ruwana y'ar uwarka ka cuta don wannan biyar d'in dai ba bata zan ba wallahi." Ta fad'a tana dangwalar yaji ta cinyeshi tas.
Hamda mik'ewa tayi ta shige d'aki don dam
a ita ba gwanar karya wa bace da wuri. Yabi bayanta da kallo cike da tausayinta sai ji Didi tayi ya saki ajiyar zuciya ya ce
"Har yanzu uwarta bata karb'eta a matsayin y'a ba tamkar sauran y'ay'anta?"
Tsaki Didi tayi ta ce "Yaushe zata karb'eta ai Umar
u ya cuceku da ya auro muku jahila, wannan zuwan ma da nayi haka na zo na tarar da ita a galabaice ciwon sanyi ya kwantar da ita, saboda tsabar aikin azaba da take bata. Allah wadaran dai Halin Sakina mai farar fuska bak'ar zuciya."
Shiru Hammad yayi duk
da fuskarsa ta nuna zallar b'acin rai bai ce komai ba, ya had'iye abinsa had'e da mik'ewa, ganin Didin na hamma alamar barcin hantsi take buk'ata.
Ko da ya koma sashensa, tararwa yayi su Nanna har sun shirya, gidansu zata je kuma ta rok'eshi kwana biyu za
ta yi da yaran gaba d'aya.
Mahaifiyarta Yayar Sadiya ce (Mahmah) uwa d'aya amma uba kowa da nasa. Ita dangin nata mahaifin a gwarzo suke ita kuma na Mahaifiyar Nanna anan Kano suke.
__________________________
Yana kwance a parlourn da yake b'angarensa
yaji ana buga k'ofar da k'arfi tamkar za'a cireta.
Rintse ido yayi sam baya son tashi daga kwanciyar da yake, amma ya lura koma waye a uzurce yake daga yanayin bugun na rashin nutsuwa.
"Waye?" Ya fad'a cikin cunkusashshiyar muryarsa daga can b'arin a
ka ce bud'e ka gani"
Ba zai manta muryar ta ba, muryar shaid'aniyar matar nan ce k'awar Sakina wato Kady, ba zai manta wancan lokacin ba, da tare suka aikata abinda har yau yak'i barin zuciyarsa ta huta , bisa son zuciyarsu suka kuma buk'aci tilas ya ruf
a musu asiri.
Fuskarsa ya tamke sosai kafin ya bud'e mata k'ofar, don a shirye yake wannan karan ko da mai suka zo ya shirya karb'arsa.
Kallon-kallo suka shiga wurgawa juna bayan ya bud'e k'ofar, Mamaki ne ya kama Kady ganin yarda Hammad d'in ya zama w
ani ingarman namiji, kamar ba yaronnan da shekarun baya suka.....
Tayi saurin katse tunaninta ta hanyar sake kallon fuskarsa, sai taji tana shakkar zancen da tazo masa dashi, da alama bata tsammaci ganin sa haka ba, cikakken namiji da yake tashe da k'arfi
da lafiya, daga yanayin fuskarsa ta san wannan karan ba zai d'au rainin hankali ba.
Da baya da baya ya juya cikin parlourn, wannan damar suka samu suka rufa masa baya.
Tuni har ya zauna kan kujera yana murza goshinsa da d'an yatsa, hakan ce take kasanc
ewa a duk sanda ya kai matuk'a a b'acin rai ko tashin hankali.
Tsawon lokaci parlourn ya samu bak'uncin shiru, su sun kasa magana saboda yarda yayi musu kwarjini a parlourn, shi kuma ya runtse idonsa saboda sam baya son yayi ido da ido da su, ji yake tamk
ar ya shak'esu ya kashe su ya huta.
Idanun nasa a runtse ya ce "Me ke tafe da ku? Ko kuma kun zo kuyi abinda kuka saba ne?"
Da sauri Ammi tace "Subhanallah, ko d'aya wallahi, wancan karanma kamar yarda na gaya maka wallahi sharrin shaid'an ne. Don Alla
h ka manta ka d'auka ma kamar ba a yi ba wallahi rud'in zuciya ne da son haihuwar d'a namiji ta kowane hali."
Idanun nasa a runtse yake sakin wani murmushi da kai tsaye zaka kira shi na takaici murya a kaurare ya ce "In manta da abinda ya faru fa kika ce?
To idan na manta ita kuma yarinyar a wani mizani kuka ajiyeta? Ya zaku yi ku fahimtar da mutane cewa bata da gadon Abbu, a lokacin da ya rasu? Ko kuwa kuna son nayi shiru Allah ya kamani da laifi?
Dole ne ko ba yau ba in sanar da duniya wannan bak'in lab
arin." Har zuwa lokacin da ya kai aya, idanunsa still a lumshe suke amon muryarsa ne kawai yake tashi a parlourn cikin isa da ginshira. Ammi ta kalli Kady kafin tayi mata alamun kinga taurin kansa ko? Jin shiru basu ce komai ba, ya bud'e idanunsa ya sauke
su akan Ammi. "Yanzu yarinyar nan kina so kai tsaye na b'oye gaskiyar lamari a dinga kiranta y'ar Abbu alhali ni da ke mun san ba haka bane. Wannan karan a shirye nazo zan fallasa sirrinki, in huta da abinda ya tokare min k'irji shekaru da shekaru ko da ku
wa Abbu ba zai yafe min ba........
Da sauri Ammi ta katseshi ta hanyar durk'ushewa a gabansa gwiwa bibbiyu "Don Allah kada kayi min haka Hammad, kamar yarda kace yarinyar zaka duba, zaka shafa mata bak'in paint mai wuyar gogewa." "Kina son kice min kina
son yarinyar da tun farkon haihuwarta kika nuna mata tsana muraran, yarinyar da kika so hallakarwa banda da kwananta a gaba, yarinyar da kike gallazawa tamkar ba jininki ba? Yaushe kika fara Sonta? Yaushe kika daina cutar da ita? Yarinyar da tun tana jarir
iya kika so mutuwarta akan wanzuwarta a duniya, yarinyar da ba kya son farin cikinta, ko ba ke na kama da shinkafar b'era zaki bata a tea ta mutu ki huta ba, saboda nayi shirin fallasa sirrinki kika min asirin da na gwammace nayi rayuwa a birmingham fiye d
a k'asata Nigeria Am sorry to say wannan karan ba gudu ba ja da baya wajen bankad'uwar sirrinki ko da hakan yana nufin kaf zuri'ar D'an Borno zasu d'ora min laifin akan rashin sanar da su da wuri, na kuma shirya karb'arwa yarinyar nan y'ancinta ta kowane h
ali."
Ya fad'a yana bud'e idanunsa da suka kad'a suka yi jajir, ya zuba su akan fuskar Sakina da take durk'ushe a gabansa, idanunta ta sauke k'asa ruwan hawaye na ambaliya a saman k'uncinta.
Kady ce ta ja wani wawan tsaki ta mik'e had'e da janyeta. "Mik'e