Showing 57001 words to 60000 words out of 129261 words
sark'afe ya ce "Ki daina min wannan kallon Idan Ba so ki ke ta karb'i hak'kina ba ga tsoro ga neman magana." Ta turo bakinta tana juya masa baya. Murmushi ya sakar mata a wuya yana mik'ewa da sauri ya fice daga d'akin don idan ya b
iye ta tata sai yara su yi late a school.
Ita kuwa Hamda gabanta ne yake fad'uwa tsoronta d'aya kada suje Nigeria a raba su. Don tana jin sanda Mahmah ta kirata da shegiya! Shi yasa k'irjinta ya yi nauyi ta fara jin tsoro a ranta. Sam bata tunanin zata iy
a sake rayuwa a duniya ba tare da Hammad mahad'in zuciya da gangar jikinta ba. Musamman a yanzu da suka zauna na kwana biyun ta tabbatar da shi a matsayin lafiyayyen namiji abin alfaharin kowacce mace. Dama can a mafarki shine burinta balle yanzu da ya sha
yar da ita zumar k'auna ya lula da ita duniyar dad'i a zahirance. Ba ta jin akwai mahaluk'in da zai raba su.
Ya dad'e a bakin k'ofa yana knocking kafin Nanna ta mik'e zuciyarta a tunzire ta bud'e k'ofar. Idanunsa cikin nata ya hango tsananin b'acin rai kw
ance a fuskarta.
Ko kallo na biyu bata sake yi masa ba ta juya da sassarfa zata shige ciki da sauri ya jawo hannunta ya damk'e sosai ta yarda ba zata iya gudu ba. Ya rutsa ta a bango sosai ta yarda ba zata iya wani motsi ko gudu ba. Ya kuma kakkafeta da id
o kaifin idanunsa da suke yawo a jikinta ya sa ta runtse idanunta tana jin hakan yana tasiri a ranta ya kuma sauya bugun zuciyarta a lokaci guda. Hammad ya san ta kan zuciyar mata yana siye zuciyar mace ko bata shiryaba balle ita da soyayyarsa ta
game zuci
yarta gaba d'aya bata jin zata iya sharing d'insa da ko wace mace shi yasa da ta kwana ita kad'ai a gado d'aya lamarin ya gigita ta dan hakan sabon abune a wajenta. Bai tab'a faruwa ba a tsawon zamantakewar su ta aure. Ganin ya kwantar da b'acin ranta ta h
anyar da ba ta zata ba ya sashi sakinta yana mayar da
Numfashi kad'an ya ce "ina yaran su fito na yi dropping d'in su kada su yi late." Ta so ta sake yi masa mita sai dai ta san shi mutum ne da baya son ya lallab'aka ka botsare don shi idan ya tashi rigima
rsa ta fi tata. Jikinta a sanyaye ta juya duk da hancinta ya juyo mata k'amshin turaren da ba nasa ba a jikinsa. Amma ta bar abin a ranta don ba yanzu bane lokacin magana zata yi bincike da kanta idan kuwa ta tabbatar da wata ce take tarayya da mijinta a w
aje tabbas mai raba da ita sai lahira. Ta fad'a zuciyarta na matsanancin bugu saboda tsananin kishi. Ganin irin kallon da
Take masa ya tabbatar masa rigimar tana nan jira take ya dawo ta sauke masa ita kwando-kwando murmushi kawai ya saki a zuciyarsa ya ce
dama kin adana rigimarki nan gaba kad'an zata yi miki amfani.
____________________
Cikin dare ta gama shirinta tsaf cikin wasu irin sihirtattun turaruka masu gigita d'a namiji ko bai shirya ba. Wani chewing gum mai masifar k'amshi ta cilla a bakinta t
a tsaya gaban mudubin d'akinta tana sake turare sussulb'an gashin kanta da abin turara ga shi. Ita kad'ai take sakin murmushi bayan ta bi jikinta da kallo ta ga irin yarda yauk'akkar rigar barcin ta bi lafiyar jikinta ta kwanta luf iya kacinta gwiwa ta kum
a fitar da duk wani shape d'in ta na halittun Y'a mace. Har a wannan lokacin saboda gyara da take wa jikinta halittunta suna nan tsaf kamar na wata budurwar shape d'inta da surarta sam ba su jirkita ba saboda yarda take maintaining d'in su.
Tattausan sili
fas d'inta ta saka sannan ta kawo dogon hijabi ta saka tana murmushin mugunta don tabbas yau mai kwatar Abbu a hannunta sai ya shirya. Ita kad'ai ta san bam d'in da ta had'a masa ta yarda duk umarnin da ta ba shi zai bi ba wani musu.
A falo ta sameshi ya
na kallon BBC london. K'amshin turarenta ne ya sanar da shi zuwanta ya d'ago yana sakar mata tattausan murmushi. Kafin ya yi aune ta cire hijabin ta hullar guntuwar rigar barcin da kad'an ta wuce gwiwa ta bayyana Santala-santalan cinyoyinta. Abbu kusan sum
ewar zaune ya yi don ta dad'e bata yi masa wannan shigar ba sai ya ganta tamkar ranar da suka fara tarewa a matsayin amarya da ango. Cikin tafiyar jan hankali da lank'wasa jiki ta k'arasa wajen sa tana sakar masa wani irin murmushi had'e da kallo mai rikit
ar da y'an maza sam bai san sanda ya yi mata masauki a cinyarsa ba bayan ya ji sunan da ta rad'a masa a kunne k'albeey barka da dare.
Karfe biyun dare ta sake gyara kwanciyarta a jikinsa tana rik'e da hannunsa ta ce "K'albeyy akwai fa abinda yake damuna.
" Gashinta ya shafa sosai yana jin kamar ya mayar da ita cikinsa "Gaya min damuwarki ko ta mecece kin ji Dearling." Ta sake narkar da idonta cikin nasa "Kalbeey me yasa Asma'u ta takurawa rayuwata? Ban san me nayi mata ba yanzu fa zuga Didi take a zuwan ni
na yi mata asiri. Fisabilillah in rasa wacce zan yiwa asiri sai matar da nake wa kallon mahaifiya. Ni ban san me yasa y'an uwanka basa sona ba ko don na zamo bare a cikinku ni ba k'abilarmu
d'aya ba." Ta fad'a tana sakin wani irin kuka na tashin hankali.
Ran Abbu kam ya kai k'ololuwar b'aci. Don ba abinda yake d'aga masa hankali irin ya ga Saknansa tana kuka. Ji yake kamar ya mik'e a daren ya je ya ci mutuncin Asma'u. Cikin takaici ya sake janta jikinsa sosai ya fara aikin lallashi ita kuma ta samu abinda
take so ta shiga jera ajiyar zuciya a hankali tana sake masa mita da yi masa famfo akan y'an uwansa tuni ya hau kai ya zauna ya k'addara tilas ya yi maganin Asma'u da safe. Murya a k'asa ya rad'a mata a kunne ki yi hak'uri dearling da safe zata tattara ta
tafi gidan mijinta ai Didin ta samu sauk'i. Babu mai tab'a min ke wallahi na k'yaleshi yau na sake amicewa da har abafa kece mahad'in zuciyata." Dad'i ya shigeta da farinciki ganin yarda ta juya shi ba boka ba malam sai zallar iya sarrafa shimfid'a ta shig
a wasa da gemunsa tana jaddada fad'in "Thanks Kalbeey zaman Asma'u ai masifa ne a gidannan." Burinta ya cika Asma'u na tafiya zata zuba guba a abincin Didi kuma a na gidan Sadiya zata zuba mai aikinta zata siye da mak'udan kud'i ta bata ta zuba gubar. Ta s
aki murmushin tarin farin cikin samun nasara a lokacin da ta sare.
Dama sau tari shi yasa bata fiye yarda da malamai da bokaye ba da kanta take sarrafa mijinta son ranta.
_________
Da sasafe suna gama shiryawa da Abbun ta had'a masa lafiyayen breakfast
cikin tarairaya ta dinga bashi abincin a baki tana yi tana sake ingiza shi game da Asma'u da Lauratu k'annensa. Shi kuma hakan yana sake tasiri a ransa ya tabbatar shine basa so tunda ba sa son Saknarsa mai ba shi farin ciki a ko da yaushe. "Tashi muje de
arling a yi komai a gabanki." Ta mik'e cike da farinciki ta manna masa sumbata a gefen kumatu ya saki murmushi ya ja hancinta a cikin kunne ya rad'a mata "Shi yasa a ko ina nake alfahari da samun mace kamar ki." Ta lumshe idanunta suka fita tana sakin shas
hshek'ar dariya ta tabbata yau lamarinsa da Asma'u ba mai kyau bane.
A falo suka samu su Didin da Asma'u suna karya wa. Abbu cikiciki ya yi sallama ita kuwa Sakna da alamar shak'iyanci a muryarta ta yi sallamar tana jifan Asma'u da kallon mugunta. A gefe
n Didi ta durk'usa murya cike da ladabi ganin Abbun ta shiga gayar Da Didi shi kuma Abbun yana lura da kallon banzan da Asma'u da Didin suke jifan Saknarsa da shi. Ya tabbatar da abinda Saknan ta ce don haka ransa ya yi k'ololuwar b'aci ya kalli Asma'u a f
isge ya ce "Ashe abinda ake gaya min gaskiya ne, nema kike ki haddasan wutar masifa a gidana. Idan banda haka me baiwar Allahn nan ta yi miki tunda ta shigo kike wurga mata harara." Asma'u da Didi suka saki baki suna masa kallon mamaki ganin yarda yake mas
ifa da kumfar baki son ransa. "To ni ba zai yiwu ba gaskiya Didi ta tattara ta koma gidan mijinta ai suna da masauki anan garin. Tunda dai Allah ya baki lafiya kuma zan samo miki abokiyar zama ko a cikin dangi ne amma dai Asma'u ta bar gidannan." Didi ta g
yara zamanta ranta a b'ace tana girgiza kai da gaske lamarin nasa ya fara fitgitata ta shak'a sosai kafin ta gama jin tijararsa "Ba Takka, to tannu Utmanu don dai a wannan jallin ka wuce d'a te dai miji ko uba. To bud'e kunnenka da kyau ka ji babu inda Atm
a'u zata je har te tun tati tafiya, te dai idan har ni zaka had'a ka kora tatata kawai da mace ta riga ta gama da ti. Ina jiye maka lanal da na tani Ummaru ko hakkin Tadiya kawai ya iteka ya hanaka kwanciyar kabali." Didi ta dinga masifa sosai ya dad'e ma
bai ga b'acin rai kwatankwacin wannan a fuskarta ba. Ta wurgawa Sakina harara
a zafafe ta ce "Munafuka lana dubu da ta b'alawo ce lana d'aya ta mai kaya." Sakna ta fice jikinta a sanyaye idanunta suna Kawo ruwan hawaye na rashin samun nasara. Asma'u kuwa t
ana zaune mamakin d'an uwanta ya hanata magana ji take kamar ta fito da recording d'in nan amma tana tunanin akwai sauran lokaci.
______________
Yana zubesu a makarantar ya jiyo, ji yake kamar ya koma wajen Hamda amma ya San bai Isa ba. Dole ya koma w
ajen uwar gida sarautar mata ya goge mata abinda ya tsaya mata a zuciya.
Tas ya sameta ta yi wanka ta tsuke cikin kananan kaya. Gidan sai zabga k'amshi yake. Ga chicken peppe soup ta yi masa da chips da egg. Tana zaune zuciyarta sam babu dad'i saboda yard
a take jin tamkar zargin mijin nata yana nema ya d'arsu a ranta. Ta sake bin jikin ta da kallo ta ganta tsaf a hasashenta.Tana son saka wando da riga sai dai k'ira da dirin jikinta ba na wando da riga bane. Kallonta yake sosai ganin duk don shi Tayi wannan
kwalliyar sai dai da zai bata shawara da yace ta dinga shigar hausawa sun fi yi mata kyau akan wad'annan matsatstsun kayan da take sawa. Ganin kallon da yake wurga mata ne ya sata murmushi a tsammaninta ta gama gigita tunaninsa ne. Don haka ta mik'e tana
kashe masa ido d'aya duk da tana jin haushinsa amma tana kewarsa sosai ta fad'a jikinsa had'e da sakar masa kyakykywar runguma cikin wani irin zak'uwa take furta masa "Me yasa kake neman canja mana farin Cikin da
Muka rayu da shi ne, kasan jiya kuwa a yand
a na kwana jina ni kad'ai a gadonmu sai turarenka da ya bi ya addabeni please me yasa ka kwana a wajen aiki?" Kokarin zame jikinsa yake amma tak'i ba shi damar hakan sai sake narke masa take don dole ya biye mata a ransa yana ayyana ta matsanta masa.
Sai
da ta samu nutsuwa sosai sannan ta bi shi da kallo suna kwance a gadon ta ce masa "K'amshin turaren da na ji a jikinka ya barranta da naka,Kayan da ka dawo da su ba da su Ka fita ba. Menene dalili?"
Ta fad'a tana jifansa da kallon da tuhuma.."ALKALAMIN JIK
AR NASHE
✍
🏽
YA ABIN YAKE?
25.
(Yau ba posting da daddare saboda 2pages na had
’
a muku. Sai kuma gobe In sha Allah. Ga mai buk
’
atar littafin complete akwaishi a kan 500 Naira kacal.)
08033748387.
ArewaBooks.@nazeefah
Sosai hantar cikinsa ta kad'a d
a tambayar k'wakkwafin da ta jeho masa. A hankali ya yi k'ok'arin matsewa ta hanyar jan hancinta "Idonki bai lura bane, sau tari ina tafiya da kaya office na dawo da wasu musamman idan lokacin damuna irin wannan ya kama lokacin ruwan sama. Turare kuwa may
be hancinki ne ya ji." Ta d'an saki ajiyar zuciya kad'an duk da ba wai ta amince da abinda ya ce bane zuciyarta tabbas tana wasiwasin lamarin. Cikin tsare gira sosai ta ce "idan ma wani abu ne a ranka ka tattara shi gefe ka ajiye don ba zan amince ka yi Au
reba balle na yarda da kwamacalar had'a shimfid'a da
Wata mace." Ya bi idanunta da kallo ya tabbatar iya zallar gaskiyarta ta fad'a tabbas nan gaba kad'an ashe za a kwashi drama don ruwa da iska ba mai saka shi rabuwa da Hamda ko a da ma balle yanzu da ya
kwankwad'i zallar madarar dad'i daga gareta.
Murmushi kawai ya sakar mata yana sauka daga gadon. Burinsa ya je yaga Hamda sai dai ya san bai isa ba a wannan lokacin don haka tilas ya hak'ura.
Sai yamma bayan ya d'auko yara daga makaranta. Sannan ya sake
shirinsa bayan ya yi wanka ya sameta a d'akinta. Zaune take a gaban mudubi tana sake tsantsarawa kanta kwalliya sam Nanna bata gajiya da kwalliya lamarin son kwalliya a jininta yake. Ya saki murmushi yana k'arasawa bakin mudubin. Ta jikin mudubin ta dinga
masa kallon mamaki. Yana k'arasawa ya dafa kafad'unta yana kallon kansu ta jikin mudubin murya a raunane ya ce "Kin yi kyau sosai M. Khairi." Bakinta ta d'an turo kad'an kafin ta tab'e bakin ta ce "Sai ina kuma naga ka fece wanka?" Ya shafa gefen kumatuns
a ya yi kalar tausayi "Am sorry dear, kin san abinka da d'an k'wadago yau ma kwanan office d'in Zan yi." Wani kallo ta jefe shi da shi na kada ka raina min hankali sannan ta d'auke kanta fuska a d'aure ta ce "Dear bana son fa rashin gaskiya, shekararka naw
a a office d'in baka tab'a aikin kwana ba sai yanzu ka tsiro min da zancen aikin kwana." Wuyanta ya murza a hankali cikin kwantar da murya ya ce "To ya zan yi? May be nextweek ma za mu wuce Nigeria insha Allah, ina tunanin su Khairi ma a gidan Musty zan ba
r su."
Baki sake take kallonsa ta ce "Nigeria kuma? For what reason duka-duka how many days rabonmu da k'asar ni sam wallahi ko sunanta bana son ji balle shiga cikinta nan kwana kusa." Ya girgiza kai cikin mamakin furucinta ya ce "Me yasa? Ke da k'asarki t
a haihuwa?" Ta girgiza kai "Abinda ya faru ba k'aramin girgiza ni yayi ba shi yasa sam bana son sake ziyartar k'asar nan kwana kusa" yana jan jelar gashinta mai tsananin sulb'i da k'yalli ya ce "Ya zame miki dole ki je don kira ne daga Umma Asma'u na gagga
wa akan wancan maganar da kike gudu, na fi son a yi komai a gabanki ki zama ready nan da 5 days." Daga haka ya saka kai ya fice yana fad'in take care. Idanu kawai ta bishi da shi zuciyarta cike da d'imuwa gani take kamar a tsukun lokacin a canja mata shi g
anin yarda yake walwala da farin ciki tamkar sabon Ango da sauri gabanta ya buga da tsoro dafatan kada Allah ya k'addara mata ganin ranar da za'a yi mata kishiya. Ta girgiza kai tare da runtse ido ita kanta bata hasasho kalar haukan da zata yi ba.
____
______________
Cike da nishad'i da walwala ya kutsa kansa cikin falon. Bakinsa d'auke da wak'ok'in soyayya na larabci. A kwance ya ganta fuskarta a had'e duk da ta sha kwalliya cikin wasu matsatstsun English wears da suka bayyana tsantsar kyawun dirin jik
inta. Amma sam fuskarta ba walwala idanunta kuwa sun nuna alamar ta sha kuka don sun d'an kumbura. A tunaninta tunda ta ji shiru ba zai dawo ba duk da dagewar da tayi ta tsantsara masa girki mai rai da motsi. Amma ta ji shi shiru tun safe daga cewa bari ya
kai y'an makaranta ya dawo. Zama ya yi daf da ita sosai yana janta saman jikinsa "Me ya faru Nuri?" Ya rad'a mata a kunne "Ko missing d'ina kika yi?" Samun kanta ta yi da d'aga masa kai tana k'udundune kanta a jikinsa. Ya saki murmushi yana k'ok'arin d'ag
a fuskarta ta runtse ido kafin ta ce "Ni ka kyaleni bayan ba ka damu da ni ba ka yi tafiyarka ka bar ni." Murmushi ya ja yana kaiwa lab'b'anta sumbata tuni ya kashe bakin tsiwar ta yi muk'us kafin ya d'ago yana jifanta da murmushi "Tarbar da ya kamata ki y
i min kenan, amma kin tsaya shagwab'a. Idan mace ta yi missing mijinta kyakykyawar runguma take kai masa ba k'ananan mita ba. Ni haka matata ta saba min." D'if ji da ganinta suka d'auke saboda tsananin kishi ta zare jikinta a hankali ta koma gefe idanunta
na shirin zubar da ruwa. Yana murmushin ya sake damk'ota, tana tirjewa ya d'aga ta cak "Bari na je na baki hak'uri a d'aki mana. Kin ga idan na tada miki da mikin jikinki kya tuna ni mijinki ne ki dinga girmamani." Bakinta ta turo tana kicinyar k'wace jiki
nta ta sauka da kyar tana tirjewa da bubbuga k'afa "Haka kawai sai ka dinga min zancen matarka ka san yarda zuciyata take ji." Kallon mamaki yake binta da shi ya kuma tabbatar iya gaskiyar furucinta kenan. A yarda yake hangowa ma kamar Hamda ta fi Nanna ki
shi ashe akwai aiki ja a gabansa. Cikin tsokana ya ce "Tab, amma fa Nuri kin d'auko da zafi ki aure mata miji kuma ki dinga kishinta? Ita kuma ya kike so ta yi? Da