Showing 9001 words to 12000 words out of 129261 words

Chapter 4 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

50

/>
Tafiyarsa da wata uku yayi mana aike akan ya samu mata zai yi aure a can. Ai kuwa na rufe idona na ce bai isaba, hakan ya tashi hankalinsa sai gashi ya dawo k'asar ba shiri lokacin watansa shidda da tafiya. Da Allah d

a annabi da saka malamai suyi mana wa'azi muka amince da yayi auren amma da sharad'in ni da kakanku zamu je muga tushe da asalin yarinyar. Bai wani damu ba ya ce mana ya yarda. Nan muka fara cuku-cukun tafiya kakanku ya siyar da gonarsa d'aya muka tafi har

da k'aninsa da suke ciki d'aya wanda kuke kira Baffa Mamman.

Mun samu tarba Ta mutunci daga iyayenta,babu aibu sam a tattare da su dattawa ne sosai, don shi kansa Umarun a gidansu yake zaune kuma yana d'an aiki a kamfanin mahaifinsu mutumin kirki shima

daga Nigeria yaje karatu sai ya had'u da uwarta mutuniyar Jordan d'in ta nuna bu'katar aurensa shikkenan zamansa ya koma can don haka da yaga Umar bahaushe ne ya ja shi a jikinsa,

ya shiga farin ciki, ko da yarinyarsa ta nuna tana sonsa take ya amince ya

bashi aurenta.

Hankalina ya kwanta da naga ubanta bahaushe ne, kuma har kwatancen gidan su yayi mana a garin Niger (Minna) cikin unguwar limawa nan ce mahaifar Kakanku na wajen uwa, ta daina muku fankamar wai asalinta balarabiya ce, asalin uwarta dai.Kak

anku ya ce zai bincika ya gani, ai Niger ba bak'on waje bane a wajensa.

Ba mu dawo ba sai da aka d'aura auren, amma jikina ya yi sanyi da na lura da uwar Sakina ce take kula da al'amuran gidan shi uban nasu ba shi da ta cewa sai abinda Ta d'aurashi a kai,

kuma yarinyar da naji suna kira Sakna ni ce nan na mayar mata da sunanta Sakina har yanzu a garinsu Sakna ake kiranta, kaf halayen uwarta ne a tare da ita bata ganin mutane da gashi. Gaisuwa kanta sai taga dama take min gashi iyayen suna ji da ita tamkar

masifa ko don itace babba.

Satinmu biyu muka baro garin daga nan umara muka wuce, na kuwa dad'e a d'akin Allah ina kaiwa Rabbil Izzati kukana akan aurennan na ubanki don sam zuciyata ba wai ta gama yarda da auren d'ari bisa d'ari bane, na yarda ne dai don

Malam yafi 'karfina.

Dawowarmu Nigeria muka dinga zuba idon ganinsu sai dai kamar mun shuka dusa ba amo ba labarinsu.

Hankalina ya tashi matuk'a da gaske ga gari ba kusa ba kuma lokacin wayar hannu bata zo ba iyakaci ta landline ce shima ba waje mai n

isa ake kira ba.

Ganin tashin hankalin  nawa ya yawaita hakan yasa Malam ya shiga addu'a da a lokacin ake kiranta addu'ar kiranye. A lokacin har aka yi bikin k'anwarsa amma bai dawo ba. Na haifi autata lauratu shima bai dawo ba.

Kwatsam wata rana mun

a zaune da hantsi sai ga sallamarsu ina d'aga Kai suna shigowa da hakimar uwarku tana wani cin magani tana yatsina kamar ta shigo gidan da ake tsubire himulin kashi, ba mu bi ta kanta ba muka shiga murnar ganin Umaru da duk yayi 'kiba ya zame min babban mu

tum kuma duk da a lokacin ko shekaru talatin bai rufa ba. Na shige rumfa ina musu lale marhabin ku shigo mana. D'aki na tsaf yake duk da dai ba kujeru amma malale yake da sabuwar leda sabuwa dal don mun fara shirin azimi daga gefe kuwa fanka ce Ta tsaye sa

i dadduma da tum-tum irin na gidan sarauta.

kuma bana mantawa a lokacin k'amshin turaren tsinke yake da na kukkunna a duk wata kusurwa da take d'akin, ya kuma sha Fenti da farar k'asa kamar yarda malam yake k'o'kari duk shekara a watan sallahr tsofi yak

e shafe gidan da farar k'asa.

Duk da wannan abin amma Sakina yamutsa fuska kawai take, ta d'ofana d'uwawunta akan tum-tum d'in da yake gefe sai sannan Umar ya kalleta ya ce "Ki gaisheta mana." Fuskarta kamar ta zunduma ihu cikin gwarin hausarta da ko fita

bata yi a lokacin ta ce "Ina kwana?" Ina murmushi na ce mata "Lafiya k'alau Sakina." Ji nayi tana masa magana da turanci ban dai fahimci abinda tace masa ba amma tabbas naji ta ce Sakna da Sakina a cikin zancen nata. Sai naga yayi murmushi ya ce "Didi sun

anta ba Sakina ba Sakna sunanta."

Na kuwa daddage na jefe shi da umbola na ce nak'i nace Saknan ka gaya mata ba zance ba Sakina zance Au nan k'arata Ta kawo don rashin Ta ido? gaisuwar ma ina ce sai da kace ta gaisheni, kai Umaru!ni dai ka tak'aitan da b

a ka auro mai jin  hausa ba balle ta fahimci masifar da nake mata ja'ira fuska kamar jan k'osai." Kallona kawai take tana ta'be baki ni kuwa na mik'e ina kallon Ummaru da yake ta guntse dariyarsa nace "Sai ka kawo mana bak'uwa ba sanarwa yanzu mai kakeso m

u bata? Ga d'akin naku ma ba a gyare yake ba."  Na k'walawa Ali kira yana zuwa nace "Gadanga sai ka tattara kayanka ka dawo d'akin nan na tsakargida sai a gyara musu can d'in tunda d'aki ne da rumfa har da makewayi a ciki." Ali cikin farin ciki ya shiga ai

ki ma'kota kuwa tuni aka fara shigowa ganin Amaryar Ummaru ana mamakin yarda ya auro balarabiya sai da nayi musu jan ido sannan suka fice na saka sakata a Zauren gidan ina sake tsinewa k'auyanci banda haka meye na dandazon zuwa ganinta abinda gobe zan saka

ta zaga gida-gida su gaisa dasu.

Abincin da muka yi na rana shinkafa da miya da salak na juye musu kaf na bawa gadanga ya siyo kifi sukunbiya na saka musu, har da dafaffen k'wai wai duk don na karramata. Na zuba musu zo'bo mai sanyi har da fura da yake

ina siyarwa k'aton firiza ne dani a tsakrgida, nake sararwa da mutane zo'bo da fura mai sanyi kuma cinikin ya kar'beni sosai.

Reras na jere musu langunan abincin har da cokula na sababbi gal dasu.

Umaru yayi saurin jan tray d'in abincin ya fara k'o'karin

zuba musu, gani nayi tayi wuf Ta ri'ke hannunsa tana girgiza masa kai sai kuma naji tana ambaton hotel da nuna masa lokaci ta hanyar kallon agogo. Sai naga ya mayar da abincin ya rufe yana sakar min murmushi ya ce "Didi ai wucewa ma masauki za muyi mun ri

ga mun kama d'aki a hotel." Ban san sanda bakina ya zunduma masa zagi ba nace "Ba Otel ba Otalo kai har kayi kud'in da ba zaka iya ajiye iyalinka anan ba? to wallahi baka isa ba nan d'in da take 'kyama anan zata zauna ba gidan uwar da zata je, ina kallo da

ma tun d'azu kallon rainin da take wa gidannan to ka gaya mata nan kwana nan yini don uwarta ba inda zata je ga d'aki can na saka gadanga yana gyara muku, kuma ko dawowa kayi gaba d'aya ga 'bangarenka can malam yasa ana gina maka anan d'in zaka zauna. Ni

za'a kawowa fi'ili da zancen banza." Ina kallo tana tambayar me nake cewa naji ya ja ajiyar zuciya yana mayar mata da harshen da tafi wayo a kansa kawai sai naga yarinya ta saka kuka ta mi'ke tana d'aukar jakarta tayi hanyar waje da sauri Umaru ya bita dai

-dai lokacin da malam yayi sallama ya shigo.. kamar zata bangaje Malam, Umar d'in yayi sauri ya rik'ota ai kuwa munyi kallo don fad'awa jikinsa tayi tana kuka sosai kamar yarinya cikin kukan babu abinda nake ji sai furucin Back da kuma Jordan sai kuwa wata

kalma da take yawan maimaita Ta wai now now. Malam ya saka salati tare da furta "Umaru saukar yaushe naji kuma amaryar taka tana ita Jordan zata koma? Ku muje ciki naji me yake faruwa a tsanake." Umaru ya ja hannunta ko kunyarmu bai ji ba ya saka ta a gef

en hammatarsa yana goge mata k'wallar idonta. Sosai takaici ya kumeni nama kasa magana zuwa lokacin da suka shigo Malam ya sake tambayata na bashi labarin kaf abinda ya faru. Take shima na ga fuskarsa ta sauya da yanayin 'bacin rai amma da yake namiji ne s

ai bai nuna ba kalmar Ashsha kawai yake fad'i sai kuma ya girgiza kansa ya kalli Umaru ya ce "Kai kuma don sakarci sai ka biyewa matarka ka 'batawa uwarka rai? Meye da gidannan d'in da ba zaku sauka ba? ka gwammace Ku kama Hotel ina ce kaima a gidan ka ray

u?" Kasa cewa komai yayi ganin ran mu ya 'baci ina kallo yana ta fama da hakimar tasa kan ta ha'kura amma taja ta turje akan sai ta tafi abincin da na kawo musu ma ko ci ba suyi ba. Bama ta kalleshi ba ran Malam a 'bace ya ce masa su wuce su tafi sa dinga

lek'omu kafin su tafi. Abin mamaki Umaru kuwa ko ja da lamarin baiyi ba yaja matarsa suka wuce ba abinda ya dameshi balle ya gane Malam gatse yayi masa.

Bayan fitarsu Mun dad'e muna ta'ajibin abin, mamaki kuwa kamar ya kashe mu haka yasa Malam yanke shaw

arar aura masa yarinyar mak'ocinmu Sadiya, Yarinyar da kowa ya shaida da nagartar halayenta ga son ibada kamar me. Ubanta Aminin Malam ne. Murna na shiga yi da shawarar Malam na karb'eta d'ari bisa d'ari muka kuma ce ba za mu sanar dashi ba sai dai yaji an

aura masa aure da ita dole kuma ya amsheta matsayin mata.

Malam bai bari sai kashegari ba a daren ranar yaje wa da Talle amininsa zancen, Talle yayi farin ciki sosai don babu wanda zai k'i had'a zuri'a da Malam sai marar rabo, take suka saka lokacin aur

e Sati biyu masu zuwa. Malam ya cigaba da ginin da yakewa Umaru a gefe guda a gidanmu. D'aki biyu ne da babbar rumfa sai makewayi 'd'aya da yake dangar rumfar daga can gefe.

Kashegari Umaru shi kad'ai ya zo don hakimar ta ce ba zata

Biyoshi ba, ban ko ta

mbayeshi ba shi yake rattabo min bayani, na ta'be baki na ce ta sha zamanta ai ni ba na nemanta, don na gane k'yank'yamun mu take kuma tayi Ta banza don kwanannan zata gane kurenta."

Bai wani da'de sosai ba ya tafi.

Da ku'dina da na Malam har da na g

adanga da Y'ar uwarsu da tayi aure muka ha'da aka yi lefen kishiyar Uwarki Sadiya.

Da yazo yaga ana had'a lefen bai kawo komai a ransa ba ranar ma bai dad'e ba kuma nan ma bata biyoshi ba sai wasu dogayen riguna na k'asar da Ta aiko min dasu da na k'ann

ensa ni kuwa duk na tattara na zuba a lefen Sadiya....

To fa!

Ko me Ummaru zai ce idan ya

Samu labarin aurensa da Sadiya? Shi da yake da tsaleliyar Balarabiya_~AL

Ƙ

ALAMIN JIKAR NASHE

YA  ABIN  YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387

Follow me

on wattpad

Nazeefah381

ELEGANT ONLINE WRITERS

(Ha

ɗ

in kai shine takenmu.)

Ya Abin Yake? Daban yake da sauran.



🏽



🏽



🏽📖📖📖📖



🏽



🏽



🏽

6

Duk tunaninsa lefen Gadanga ake ha

ɗ

awa, shi yasa bai damu ya tambayeni ba.

Sai ana gobe

ɗ

aurin au

re kamar an jefo su sai ga su sun zo da yamma. Fuskata babu wani alamun damuwa na tareta da murnata da komai, na malala mata tabarma a rumfa, ta kuwa zauna ranar kamar abin arziki har tana gaisheni cikin gwarancin hausarta. Lauratu da ta dawo daga islamiyy

a ganin ta yasa ta fa

ɗ

awa jikinta a guje sai naga ta tureta a fusace tana ka

ɗ

e jikinta, mamaki ya hanani cewa komai sai janye Lauratu da ta fara kuka nayi. Lokacin bata wuce shekara goma ba, cikin lallashi nace mata yi ha

ƙ

uri da

ɗ

in abin burinmu daf yake da

cika."

Sai naga ya kalleni da alamar neman

ƙ

arin bayani, ni kuwa na galla masa harara. Muna zaune Malam ya dawo fuskarsa fal

ɗ

auke da murmushi da katinan aure a hannunsa. Shi kansa Malam

ɗ

in ba fara'a ba girmamawa ta shiga gaisheshi, shi kuwa ya amsa ba

tare da komai a ransa ba. Ya mi

ƙ

e ya shige turakarsa yana fa

ɗ

in "Idan ka tashi tafiya ka sameni."

Ƙ

asa yayi da kansa kafin ya ce "Malam ai tafiya zamuyi jirgin dare yau zamu bi." Daga ni har Malam ba wanda bai firgita da jin zancen ba muka ji tamkar sau

kar aradu a ka. Ni dai har razana nayi.

Malam ya dawo da baya yana masa kallon tuhuma kafin ya ce "Da kazo mai kace min? Ca nake cewa kayi wata guda zaku yi?" Ya

ɗ

aga kai kawai, idanunsa sun nuna yana cikin wani yanayi na

ƙ

a

ƙ

a ni kayi. Malam ransa a

ɓ

ace

ya ce "To menene dalilin canjin zancen?" Daburcewa yayi sosai kafin ya ce "Kawai dai zafin garin ta ce ya isheta." "Shine kai kuma kabi abinda tace wajen ruguza shirinka kuka

ɗ

aura aniyar tafiya yau?"

Na fa

ɗ

a raina a

ɓ

ace da tunanin sun canja min ainahin

Ummaruna wannan ba nawa bane wani ne can daban. Zufa ya goge kafin ya ce "Duk ba haka bane,jarrabawa zata je ta zana." Malam Yaja ajiyar numfashi a kufule ya ce "Jarrabawo ba jarrabawa ba, ta bakin uwarka ne duk an canja maka

halaye, to albishirinka ungo

nan."

Ya fa

ɗ

a yana manna masa katin auren a tafin hannun da ya mi

ƙ

o "

Ɗ

aurin aurenka gobe da Sadiya, sai ka sanar mata idan taga zata tafi sai tayi gaba ita ka

ɗ

ai." Sam bamu san zufa bace take karyo masa, sai da na kai idona kansa sannan na ankare. Na kuwa

saka salati ganin yarda ya dur

ƙ

ushe a gaban Malam yana fa

ɗ

in "Kayi min rai wallahi ba zan iya ha

ɗ

a Sakna da kowacce mace ba."

A zafafe Malam ya ce idan an

ɗ

aura ka saketa, amma ka tabbatar in dai ni na haifeka to babu shakka aure ya

ɗ

auru." Yasa kai ya

fice Lauratu da take gefe sai dariya take zuciyarta fal farin ciki, duk da umbolar da nake mata bata fasa ba. A zuciye Ummaru ya jawota zai fara jibga. Na kuwa saka

Hannu na janyeta ina cewa kada ma ka fara, don wallahi ba zan

ɗ

auka ba. Ina kallo tana tamb

ayarsa daga yanayin fuskarta na gane tambayarsa take masifar mai muke? Sai naga ya saki murmushin dole ya girgiza mata Kai.

A daddafe ta bari suka cika awa guda cur, naga ta mi

ƙ

e hannunta

ɗ

auke da Jakarta ta kalleni a banzace naji ta ce "Good bayi." tana



ɗ

aga min hannu shima ya mara mata baya bayan ya ajiye min wata leda yasa kai ya fice da sauri.

Shikkenan daga ranar bamu sake ganinsa ba, amma haka Malam yasa aka d'aura auren kuma Sadiya ta tare a shiyyarsu da aka gina mata ita da Umarun da

Ya wuce ya k

oma

Ƙ

asarsu ko salaam babu.

Bai kuma dawo k'asar ba sai bayan shekara Guda, Ba ni kad'ai ba wannan karan hatta Malam sai da ya nuna masa 'bacin ransa.

Don muna zaune a tsakargida wannan karan ma muka ji sallamarsu. Nayi turus ina kallonsu, Allah yaso r

anar juma'a ce dama Sadiya ta saba duk sati a juma'ar take kitso idan kuma k'unshinta ya goge ta sake mayar da wani. Ranar ma haka ta kasance tsaf da ita tayi adonta cikin atamfa Diamond ta kada d'auri had'e da zubo himulin gashinta da ko balarabiyar ba za

ta nuna mata komai ba a gashi ko dirin jiki sai dai ta nuna mata hasken fata da santsin Gashi. Sadiya na da sirrin kyau da baya bayyana sai idan ta haske idanunka da murmushi anan zaka hangi zallar madarar kyau,

Sai dai bak'ace kamar yarda kika sani kuma b

ak'innata sam bai dameta ba balle tayi shafe-shafe kullum cewa take haka Allah yaso ya ganni.

Tayi karatu sosai duk da karatun nata yafi k'arfi ana addini na bokon kam ka'dan ta samu a k'aramar sakandire ta tsaya.

Murmushin dai ta haske shi da shi da ya

sakashi ya tsaya cak yana kallonta da alama addu'ar da muka duk'ufa yi ni da sadiya taci don kullum addu'armu Allah yasa ha'duwar farko ubangiji ya jefa k'auna mai girman dutsen dala a

Zuciyarsa, ba ta kowa ba sai ta Sadiya baiwar Allah da Sam

Duniya da a

binda yake cikinta ba su dameta ba.

Da fara'a ta na mik'e ina aukin fa'dar Ta'al Ta'al Ta'al! Wata irin dariya naji Sakina ta shek'e da ita har da dafa ciki. Raina a b'ace nake kallonta ganin kamar ta mayar dani mahaukaciya, Lauratu tayi kanta a zafafe t

ana fad'in Uwarki kike wa dariya?" "Uwar ki wannan nake wa." Ta fad'a cikin gwarin hausarta ina kallon Ummaru ya dafe kai cikin takaici ya  "Zagi fa kika yi!" Sai naga ta bud'e hannu tana girgiza kai, shi ma kansa a k'asa ya ce "Didi ba zaginki tayi ba, ba

mamaki jin kina yarensu ne abin ya burgeta kika ga tana dariya." Na girgiza kai ina fa

ɗ

in Yo ko da naji. Ku zauna" Sai naga wannan karan ta saki jikinta ta zauna har da d'an murmushinta tana kallon Laurat da ko kallonta ba tayi ba da alama bata manta abin

da tayi mata wancan zuwan da ta zo ba. Hannu ta mi

ƙ

awa Lauratu  amma Laurat tayi shigewarta d'aki bata fito ba. Shi kuwa Gogan idanunsa akan Sadiya, sai da na gaji da kallon da yake jifanta da shi baka ganeta bane? Sai naga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login