Showing 45001 words to 48000 words out of 129261 words
dai tana tsoron fita parlourn, ta ci karo da Nanna, bata san wannan kallon da take jifanta da shi.
Da kansa ya mik'e ya fito tunawa da yayi haka t
a kwanta bata saka komai a cikinta ba, gwara ma
su sun ci abinci a cikin jirgin. A kitchen ya taradda Khairi da Nanna suna dafa noodles don ita kad'ai ce da su a gidan komai sun fitar da shi kafin su tafi. Ya lek'a tukunyar sannan ya juya ya fice.
Direct
d'akin da take ya nufa har ya murd'a zai shiga sai kuma ya tsaya ya d'an k'wank'wasa. Da sauri Hamda ta zari veil d'in da yake gefenta ta nad'e himulin gashinta da shi. Har yanzu ta k'i amincewa zuciyarta cewa muharraminta ne. Ya tsaya daga bakin k'ofa yan
a nazarin fuskarta, gaba d'aya yunwa ta riga tasa ta fara fita daga hayyacinta. Ya ja tsaki yana sakin handle d'in k'ofar "Kina jira a zo a baki abiinci ne? Ba zaki zo ki samu abinda zaki ci ba." Da kyar ta mik'e jiri na d'an d'ibarta kad'an ta saka k'afa
zata fito daga d'akin sai gani ya yi tayi baya ta fad'i.
Da hanzari ya juyo ya d'aga cak yana mamakin wauta irin tata. Fuskarsa a d'aure ya ce "Wai ke wace irin shashashace? Kin san ba zaki iya tafiya ba wa yace ki taso?" Ya zaunar da ita a gefen gadon san
nan ya fice. Tea mai madara had'ad'de Nanna ta ga yana had'awa mamaki ya kusa kasheta a tsaye don dai ta san baya shan irin wannan tea d'in zallar black ko green tea yake sha. Ta kuwa tsatstsareshi da ido "Me zaka yi da shi?" Bai kulata ba ya fice da mug d
'in a hannunsa da sauri ta bi bayansa sai taga ya shige d'akinsa, wani irin tuk'ukin b'acin rai ya shigeta. Da sauri ta juya d'aki tana lalubar wayar aminiyarta da take zaune a garin Uk.
A tsaye ya mik'a mata mug d'in hannunta na rawa ta saka hannu ta ka
rb'a ta kai bakinta da sauri take zuk'a alamar tana jin yunwa sosai. Juyawa kawai ya zari key d'in motarsa gwara ya je ya samo solution akan Hamda don ya lura zamanta da Nanna ba abu ne mai yiwuwa ba. Shopping zai yi saboda ba su da komai a gidan, zai biya
kuma wajen abokinsa Mustafa da suka fara maganar Hamda da shi a waya su yanke shawarar yarda za su b'ullowa Ammi. Da safe kuma yaje makarantar da ya riga ya samar mata admission.
__________
Cikin dare Gwaggo Asma'u jirginsu ya sauka daga k'asar Dubai
. Duk da gajiyar da tayi amma a daren ranar ta matsantawa mijinta Sheikh Abdallah akan sai sunje sun ga jikin Didi.
Ba kowa a wajenta sai Sadiya da Lauratu. Da murna suka tareta bayan an gaggaisa Sheikh Abdallah ya tambayi yanayin ciwon nata. Don ya ga D
idin bata magana sai dai kallo da ido. Sai da suka bashi labarin kaf abinda yake faruwa sannan suka ga ya saki murmushi kasancewarsa masani akan cutittuka na shafar jinnu ya tabbatar musu ciwon Didin bana asibiti bane da safe a neman mata sallama shi zai s
ake dubata. Daga haka ya yi musu sallama ya tafi ya bar matarsa a wajen. Suka cigaba da jajanta lamarin. Asma'un ce ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce "Amma Sakina an yi y'ar banza, su kuma su Yaya fisabilillahi ya aka yi suka yarda da wannan tatsuniyar da ta
shirga. Duk ma ba wannan ba yanzu ina Hammad da yarinyar me yasa ba'a gwada k'wayoyin halittarsu ba a tabbatar shin y'ar da gaske tasa ce ko sharrinta ne." Mahmah ta ja mayafi ta goge hawayen fuskarta kasa magana ta yi sai Lauratu ce tace "Ai zancen da na
ke miki Hammad ya tafi da y'ar Birmingham bayan da Yaya ya koresu."
Rik'e kai kawai Asma'u tayi kafin ta ce "Kash Na so Na zo na sameshi amma bakomai idan ta san
wata ai ba ta san wata ba da kaina zan nemo gaskiyar lamarin."
Tun bayan da ya kawo mata a
binci da kansa cikin d'aki bai sake waiwayarta ba har safiyar Ranar.
Ya shigo fes da shi cikin shigar bak'ar Rigar Hilfiger da brown trouser. Sai jibegegiyar rigar sanyi bak'a a jikinsa kansa kuma sanye da bak'ar hular sanyi da ta rufe masa har kunnensa.
Yana shiga tana share hawayen da yake sauko mata. Ya san kukan me take kukan maganganun da Nanna ta dasa mata take, yana jin su. Sharewa ya yi kamar bai gani ba "Mik'e mu je makarantar da za ki fara zuwa." Ta mik'e cikin sanyin jiki suka fice daga gidan.
Sai da suka isa harabar makarantar Aston University da ke Birmingham cikin wata irin murya ya ce "Saura ki shiga kina wannan sussunne kan, kuma kin iya turanci ko?" Sunkuyar da kanta kawai tayi tana jin takaicin maganarsa. Ya fice daga motar ita kuma ta
bi bayansa.
A hanyarsu ta dawo ya kalleta yana reverse da mota zai shiga layinsu ya ce "Zamanku da Nanna ba zai yiwu ba, don haka na yanke shawarar aurawa Amini na ke.... kin amince?" Da sauri ta d'ago tana kallonsa kafin ta ce wani abu yace "Shine abind
a yafi kamatarki a halin yanzu."
Jikar Nashe
✍
🏽
ALKALAMIN JIKAR NASHE..
YA ABIN YAKE?
NAZEEFAH SABO NASHE.
08033748387.
(Ga mai son complete akwai shi a k
’
asa akan ku
’
di Naira 500 kacal.)
20. _____________________
Kallonsa kawai take tana mamak
in furucinsa, shin da gaske auren zai yi mata, me yasa ya taho da ita k'asar da bata san kowa ba alhali ya san matarsa ba zata iya rik'eta ba? Aure dama an tab'a aure haka ba tare da matar ta san mijin ba, ko kuwa don k'addara ta hau kanta sai a samu koma
waye a lik'a mata shi a matsayin miji? Shikkenan ita bata da damar soyayya kenan? Ta ina mijin zai ga k'imarta da mutuncinta. Hannu tasa ta share hawayen da ya kwaranyo kan fuskarta da gaske
lamarin ya yi mata zafi k'warai da gaske. Shikkenan duk mafarkint
a na tsalelen mijin da take so ta aura ya bi iska, ko zunnuraini da ta amince zata aureshi ne kawai ba don ya zama irin mijin da take so ba. Irin mijin da take so sirri ne a zuciyarta da kuma tunaninsa take kwana a koda yaushe.
A fili ya ja tsaki "Idan b
a kya son auren ba sai ki fad'a ba me ye na zama kina min kuka. Kin san da yaya ya amince zai aureki ma tukun?" Ya fad'a daidai yana parking a k'ofar gidansa "Aurenki shine abinda yafi alheri a yanzu a rayuwarki, ko bakomai za kiyi karatunki cikin nutsuwa
, don haka ki share wannan hawayen idan kin amince gobe zai zo ku ga juna zai kuma kawo miki sadakinki da duk wani abu da za ki buk'ata, Nan da kwana biyar za muje masallaci da su a d'aura miki aure ki tare a gidan sa." Tana shashshek'a ta share hawayenta
had'e da d'aga kanta cikin wata irin murya ta ce "Shikkenan bakomai Allah yasa haka ne yafi alheri a gareni" idanunsa cikin nata ya ce "Haka ne ma insha Allah, kina da suffa da halayen da za ki saka namiji ya so ki ko bai shirya ba, don haka ki k'addara za
ki zama star a zuciyar abokina." Yatsun hannunta kawai take wasa da shi kafin ya mik'a mata jakarta ya ce "Mu je gida." Ta fita daga motar jikinta a salub'e haka kawai kuma gabanta yake dukan Tara-tara. Tana mamakin yarda lamarin auren nata ya zo kamar au
ren y'ar tsana.
A parlour Nanna take zaune cikin hamshak'iyar shiga, fuskarta sam ba walwala take jifansa da wani kallo ganin yarda suka shigo gidan. Ba tare da ya kalleta ba ya zauna yana d'iban lemon tataccen inibin da yake gabanta a jug. Ta d'ago tana
kallonsa kafin ta ce "Ban da dai yarinyar nan y'arka ce da sai nace ko soyayya ku ke?" Fuskarsa a had'e ya d'ago tare da zuba mata wani matsiyacin kallo, sai kuma ya girgiza kai kawai ya cigaba da kurb'ar juice d'insa "Ka kalleni ka yi shiru, na lura kula
r da kake bawa yarinyar nan ta na nema ta wuce muhallinta don ko ni matarka ban samu kwatankwacin kular ba, kada dai bayan an gama da uwa a zo a koma bibiyar y'a." Ji ta yi kawai ya yi cilli da Glass tumbler d'in hannunsa cikin matsanancin b'acin rai ya du
beta "Na rantse da Allah idan kika sake min kwatankwacin wannan furucin I will show You who I am. Wani irin iskanci ne wannan kawai don na zuba miki ido kina duk abinda kika ga dama doesn't meant kin fi k'arfina ne." Daga haka ya fice daga gidan zuciyarsa
a tunzire har hakan ya d'an firgitar da Nannan ta tabbatar yau ta kaishi mak'ura amma zuciyar shaid'an na sake tunzirata. Ta mik'e da sauri ta nufi d'akinsa inda Hamda take.
Tana zaune a gefen gadon hannayenta zube a k'uncinta, gaba d'aya zuciyarta ta ru
ga tunani. Mamakin yarda rayuwa ta yi mata juyin waina take. Turo k'ofar da aka yi da k'arfi ne ya sata saurin d'aga kai, idanunta suka sauka cikin Na Nanna da take tsaye tana huci tamkar zakanyar da ta kwana da yunwa "Ki tattaro duk wani kayanki ki koma
d'akin yara, duk da babu space ki dinga bajewa a k'asa, haba yarinya kin shigo rayuwata kin zame min bala'i ina zaman lafiya da mijina yanzu abu ya gagara shegiya kawai, na tabbatar uwarki ce ta yiwa mijina fyad'e saboda jarabarta ta son haihuwa d'a namiji
amma aka tattare laifin duk aka jibge masa." Ganin Hamda ba ta ce komai ya sa ta cigaba da zabga mata masifa "Kuma last warning da zan miki ba ke ba shirgin yara ne ki tsaya a matsayinki na shegiya su ma su tsaya a matsayinsu na y'ay'an Sunna da aka haifa
da aure. Sai na bi na sanar da kowa matsayinki wallahi idan ba ki bar gidan nan ba, sai na goga miki bak'in fentin da zaki kasa auruwa ki fito yanzun nan na gaya miki." Daga haka ta fice daga d'akin ta bar Hamda tana wani irin kuka tabbas Yaya Hammad ya y
i gaskiya da ya ce aurenta shine abu
mafi alheri a gareta. Ta lura idan har zata cigaba da zama a gidan nan Nanna sai ta saka mata ciwon zuciya da bak'ak'en kalamanta. Ta rasa me ta yi mata da har ta tsaneta haka? Duk abinda ya faru itama fa ba laifinta ba
ne.
Tsaf ta had'e kayanta ta mayar da su d'akin su Khairi. Gado uku ne a d'akin daidai kwanciyarsu don haka dole ita a k'asa zata dinga kwanciya ba bak'on abu bane a gurinta, amma ya zama dole ta amince da mijin da Hammad ya zab'a mata ta huta.
______
__________________
Cikin farin ciki Sakina da yaranta suke, saboda yau aka kawo kud'in auren yaranta su biyu Najma da Nasma kuma gaba d'aya aka had'a har saka rana. Duk da k'annen Abbun sun nuna a bari Didi ta samu lafiya amma Sakina ta ce Sam ayi kawai
ko Didin da zata iya magana ai cewa kawai za tayi ayi tunda ta fi kowa son yaran su yi aure. Nan fa shirye-shiryen biki ya kankama don bayan Sallah da sati biyu za'a yi bikin. Lokacin kuwa Azimi saura kwana goma aka saka ranar. Bakin Ammi yak'i rufuwa sabo
da ba k'ananan kud'ad'e take shak'a a wajen Angwayen da uban gayya Abbu ba. Don sosai ta sake samun kansa ta hanyar bankawa kanta magungunan mata da suke sake zautashi. Dole wannan karan ma Sadiya ta sake zama y'ar kallo don ko ranar girkinta sau tari ya s
ha kiranta da sunan Sakina ta. Sakina kaza Sakina kaza. Tun abin baya damunta har yanzu ya soma damunta don da tayi masa k'orafi ma cewa ya yi "Ki yi hak'uri Na rasa yarda zan yi na kwatanta adalci tsakaninku, amma ke ma da laifinki ko y'an dabarun nan na
mata ba kya yi." Ranta a b'ace ta fice masa daga d'akin tana ayyana in dai ba shi ya nemeta ba ba zata sake kawo kanta gareshi ba. Ranar ku san kwana ta yi b'acin rai na nuk'urk'usar zuciyarta. Sai daga baya ta ja tsuka don ta bawa kanta a haushi a yanayin
shekarunta ma ya kamata ace ta tattara wannan matsalar ta saka ta a gefe tunda tun a lokacin yarinta ma ba ta tata yake ba ta Sakinarsa y'ar Gold k'irar diamond. Dama haushinsa take ji tun akan maganar Hammad don dai su Asma'u da Gadanga sun ce ta saka ma
sa ido ne su ga iya gudun ruwansa.
Didi kuwa tunda aka dawo da ita daga asibiti ake ta abu d'aya duk malamin da yazo sai ya ce Sammu ne amma insha Allah bakinta zai bud'e kuma suna ganin alamun nasara. Don haka su Lauratu suka sake dagewa da tsare sashen
Didin don sam ba sa haufi akan cewa Sakina ce ta yi mata asiri. Ko abinci ta kawo ba bu mai ci don lamarinta yanzu tsoro yake ba su.
_____________
Sai dare ya dawo gidan, Hannunsa d'auke da takardun makarantar ta ya nufi bedroom d'in sa. Don ya san ace
zai sameta. Yana murza k'ofar d'akin ya ji wani k'amshi ya doki hancinsa, ba ya haufi k'amshin turaren Nanna ne. Mamaki ya kamashi da ya kunna fitila ya ga Nannan kwance akan
gadonsa cikin wata fitinanniyat rigar barci da duk ta bayyana surorin jikinta. A
tunaninta ta yi kyau sai dai ina shi bai gani ba muninta kawai ya gani da bayyanar halittunta da suka sauya sabida haihuwa kasancewr Nannan mai teb'a da zubabbun Mama. Tsaki kawai ya ja ya shige toilet kamar ya tamabayeta ina Hamdan? Sai dai ya kyaleta do
n ya san rigima take nema. Wanka ya yi da brush ya fito sanye da kayan barcinsa pyjamas samfurin ck ya tsaya gaban mudubi ya taje sumar kansa sannan ya feshe jikinsa da turare. Duk abinda yake tana kallonsa tana wani sake birgima duk don ta ja hankalinsa t
saki ya ja a zuciyarsa ya ce "In an girma a san an girma wannan rigar ai bata dace da ke ba, da suturce jikin kika yi may be da na fi sha'awarki. Duvet ya d'auka had'e da kashe mata wutar d'akin ya fice. In dai shine ba zai kulata ba sai ya koya mata hanka
li ta fannin da ya san bata iya jurewa sai ta kusanceshi. Sau tari yana mamakin yanayin halitta irin ta ta. Tana da zafaffiyar sha'awa.
Kwanciyarsa ya yi ana parlourn zuciyar Nanna a tunzire ta biyoshi don ba k'aramin shiri ta yiwa wannan daren ba ta bank
i magunguna son ranta duk don ta kautar da hankalinsa tasa ya mayar da Hamda campus. Yana jin motsinta ya rufe idonsa ruf tamkar mai barci. Ga mamakinsa sai ya ji ta yaye duvet d'in rufe jikinsa da shi. Tana tsaye daga ita sai banzar rigar da ta k'ak'aba w
a kanta. Ya so tuntsirewa da dariya sai ya gimtse bakinsa "Lafiya?" Ya furta yana tsatstsareta da ido "Anan zaka kwana?" "Eeh" ya amsa mata direct "Amma fa kai nake jira." "Sai ki daina jiran nawa ki je ki yi barcinki tunda ni ai ba kiga ina jiran naki ba.
" Ya sake mayar da kansa ya rufe. Gwiwa a salub'e ta juya ta koma d'aki hankalinta a matuk'ar tashe. Da kyar ta samu barci ya yi awon gaba da ita. Shima d'in ba wani barci yayi ba tunani sun sha masa kai ta yarda zai yi da matsalar Hamda.
______________
____________
Kamar yarda ya ce mata kashegari da kansa ya kawo mata envelope shak'e da dollars a ciki. Ya mi'ka mata "Ga sadakin ki don zuwa yanzu na tabbatar kin gamsu da cewa auran da zan miki shine gatanki. Ango kuma zai zo anjima." Shiru ta yi tana j
uya kud'in a hannunta kafin ta mik'a masa "Ka ajiye min a wajenka zan karb'a" ya karb'a kafin yace "Be ready around 5:00 pm idan ya dawo daga office zai zo." Ta gyara zamanta had'e da d'aga masa kai.
Tunda k'arfe biyar d'in ta kusa ta ji k'irjinta na sa
ke nauyi fargabarta na k'ara yawa, da gaske tana jin tsoron had'uwa da mutumin da aka ce shi zata aura. Ta dai yi wanka amma ko mai da kyar ta shafa ta zira wata simple gown had'e da mayar da gashinta baya ta yi rolling kanta. Yanayin garin da alama zai ka
rb'eta don ta sake wani fresh fatarta ta sake bayyana taushinta. Tana zaune a k'asan carpet Kamla a jikinta, don ita sam ta kasa rabuwa da ita duk da jan kunnen da Mom ta yi mata tana son Hamda sosai. Ya turo k'ofar ya shigo idanunsa a kansu sai ya gan su
tamkar wasu ya da k'anwa. "Fito ga bak'on ki can a garden, ki kuma kiyaye mutuncinki bana son zubar da martabar d'iya mace." Hannunta cikin na Kamla suka fito kirjinta na sake nauyi tamkar an d'ora mata dutse.
Tun daga nesa ta hangoshi zaune akan kujerar
da take gark'ame a garden d'in. Sanye yake cikin
farar shadda k'al da ita kansa da hula zubin zannan bukar. Ta sake damk'e hannun Kamla a karo na biyu jikinta ya fara rawa ji take tamkar ta juya sai dai juyowar da ya yi ya sata saurin k'arasawa ba shiri, s
aboda ya riga ya ganta ba amfanin guduwar.
Bak'i ne sosai sai dai ba za a ce masa mummuna ba.
Yana da kyansa da kuma kamalarsa ji ta yi Kamla ta ce "La Uncle Musty." Suka had'a ido ba shiri ta ce "Ina wuni?" Yana murmushi ya ce "Lafiya lau Amarya ya shir