Showing 111001 words to 114000 words out of 129261 words
alama ta nuna Sa'ada
ta rufe ta da key, Umma Asman ta ce "Ki kyaleta Didi ba mamaki barci ya d'auketa ki je ki d'an runtsa kema, kin ga dai kwana mu ka yi muna tahajjud" Didi ta d'aga kai tana cewa "Bari na je don kuwa barcin nake ji sosai, amma na so na duba na ga ko lafiya?"
Umma Asman ta ce "Jeki dai ki kwanta ni anjima kad'an Zan dubata." Didi ta ja jikinta ta shige d'aki don kuwa barci ne sosai a idanunta. Umma Asma ta saki ajiyar zuciyar samun mafita, don ta tabbatar yau da Didi ta san Hamda a wajen Hammad ta kwana duk gi
dan sai sun sani, ya kamata dai a gaggauta ba shi matarsa don tana hango kalar kallon da yake jifanta da shi mai nuna zallar yarda yake missing d'inta. Ta dawo falon tana jifan Hamda da Sa'ada da wani kallo ganin yarda suka yi tsumu-tsumu mamakin y'ay'an z
amani ya gama cikata, kasa musu magana ta yi ta juya kawai ta shige d'aki to me zata ce musu? Ta ce kada ta je wajen mijinta? Alhali da ta tare da shi har da guzirin ciki kafin ya zube, Ba ruwanta da shiga hurumin ubangiji bata san mai Allah ya b'oyeba. Ku
nyar Duniya ta game dukkansu Ba ma Hamda kad'ai ba, har Sa'adan sa ta bada goyon baya.
Suka shige d'aki suka yi tsumu-tsumu kafin Sa'adan ta tuntsire da dariya ta ce "Ke sharesu kawai, ai Ba haramci muka aikata ba, ba ni labarin na san dai jiya abin ba dam
a ko?" Hamda ta jefa mata harara "Ai duk ke kika jawo min ga shi nan duk jikina ciwo yake banda barci da yake walagigi da rayuwata." Sa'ada tana murmushi tace "Ai dole ki ji barci tunda an sha ibada an yi k'iyamallaili, yau da Didi ta ganki wallahi ba ke k
ad'ai ba da ni kaina na kad'e har ganyena." Hamda ta ja wayarta da ta ji tana k'ara alamar sak'o ya shigo murmushi ta saki ganin Sak'on Hammad ne.
Nagode Sweety, kin shayar da ni wata iriyar zuma da ban tab'a d'and'anar kalarta ba a ratuwata. Ni na san wa
cece ke na san kuma tarin ni'imomi da Allah ya wadata ki da su, Ubangiji kada ya bawa wani damar d'and'anar zumarki sai ni kad'ai, please kada ki sake nisa da ni don Allah, a yau na yi burin ace ke na fara aure tabbas da ba ni ba sake k'ara aure don na tab
bata cikin mata dubu da kyar za'a samu goma masu taste kwatankwacin naki ba ma irin naki ba, daga yau kin zama Honey ta."
Murmushi ne ya kasa barin fuskarta tana jin wani irin nishad'i da ya kusa fasa k'irjinta. Ta rungume wayar a k'irjinta tana jin haus
hin sa da ta taho da shi yana zagwanyewa yana zama wata iriyar k'auna mai wuyar fasaltawa, Hammad shine zab'inta har ila yau zab'in Allah, madallah da miji nagari Ya Allah. Ta furta a hankali tana kallon Sa'ada da ta karb'i wayar tana karanta sak'on, ita k
anta abin ya matuk'ar burgeta har ta fara jin kewa da tunanin nata saurayin tana burin yazo nan kwana kusa su yi aure, tabbas a yau Hamda ta tabbatar da soyayya ruwan zumace. Sa'ada ta bugi cinyarta ganin tana lumshe ido had'e da matse filo a k'irji ta waf
ce filon kafin ta ce "Maza ki karya azimin ki." Hamda ta yi saurin jan ista'aza lamarin ne mai tsayawa a zuciya mai shiga rai kuma.
___________
Daga ranar bata sake ganinsa ba, saboda kunyar Umma Asma da take ji, ga shi tana son zuwa saloon da kitso ita
da Sa'ada da Munirat, tana son ta tambayeshi tana jin tsoron kiransa kada ta jangwalowa kanta don ta san fushi ya yi ya daina nemanta, don ma kullum ta kan tura masa text, tsawon kwana biyar sai yau d'in da suka fito ana gobe Sallah za suje saloon. Ta sas
hen Ammi suka bi don su kira Munira, suna shiga Hamda ta rakub'e daga gefe tana gaida Ammin da ta zuba mata ido tana ganin yarda Hamdan ta sake zama cikakkiyar mace ba zato ta ji Ammin ta ce "Auta ina zaku?" Ta d'ago ido tana dubanta tana son ta gasgata ku
nnenta, Ammi tana murmushi ta d'aga mata kai "Akwai wata autar bayan ke, kuma kin tambayi Hammad d'in da zaki saka k'afa ki fita?" Hamda ta girgiza kai, Ammi salati ta saka ta ce "Wani irin shashanci ne zai saka ki fita baki tambayi miji ba ba fa na san wa
uta kin san adadin zunubin da za ki jibga idan kika fita ba da saninsa ba?" Hamda ta sake girgiza kai, cike da takaici Ammi ta ce "Bud'e baki ki min magana bana son maganar bebaye." "Zan tambayeshi" ta fad'a a tsorace kamar yarda ta saba yiwa Ammin magana,
cike da takaicin yarda take mata Ammin ta zuba mata ido tana sakin ajiyar zuciya ta ce "Kirashi ki gaya masa, duk duniya yanzu shine zai baki izinin fita, kuma gobe jibi, gata mai gyaran jiki zata fara muku tunda saura sati hud'u ya kama bikin, na so a ce
kunje Jordan to komai ya zo a k'uratccen lokaci sai dai su suzo kawai." Hamda wasa kawai take da wayarta a zuciyarta ta raya ina ruwanta d wasu mutanen jordan, da ai ba su damu da ita ba suma sai yanzu da suka ji ubanta wani ne. Munira na fitowa ta mik'e
Sa'ada ma ta bi bayanta, Ammin ta bisu da kallo
zuciyarta na rawa, sosai yarda Hamdan take mata take jin haushin abin har kasa barci take sau tari tana tunanin yarda zata shawo kan Hamdan su dawo yarda aka san kowace 'Ya da Uwa. Amma abin ya ci tura. Ta d'
auke k'wallar da ta zubo mata da yatsunta tana addu'a a ranta "Ya Allah ka cusawa yarinyata soyayyata ta daina gani na kamar wata bak'uwa a wajenta.
A ranar KK ya sake zuwa ganinta, wannan karan fuskarta a d'aure shima ta gaisheshi, don shi d'in ma sau
tari tana jin haushinsa dalilin da yasa ya barta ita sam bata yarda da wancan dalilin da ya bayar ba, shekarunta fa sha takwas sai yanzu zai bayyana kansa a matsayin mahaifinta. Ya kalli Didi yana murmushi ya ce "Zancen tafiya Umara ina ganin ana sallacew
a sai a samu mutum takwas a family a tafi da su, a had'a da Hamda da ke kinga goma kenan, shi kuma Hammad da Matarsa za su wuce Birmingham su had'o komai na su su dawo, yaushe Babansu ya saka bikin?" Didi tana washe baki tace "Yanzu dai muna zancen saura s
ati hud'u insha Allah, Kai madallah ke Hamda sai ki fad'I da wa za'a je?" Hamda ta girgiza kai "Ni Didi ban sani ba, ni za ki tambaya." Didi ta ce "Tabbas ba ke Zan tambaya ba, mantawa na yi kaf familyn D'an Borno ni ce da zartar da hukunci a kuma bi ko An
a so ko ba'a so. Za'a tafi da Asma'u da Lauratu sai k'awarki gata nan Sa'adatu a had'a da Sadiya..." KK ne ya katseta da sauri ya ce "A had'a da kowa na cikin gidan nan, har Gadanga da matarsa, sai Baban nasu da yaran duk da suke cikin gidannan." Cikin far
in ciki Didi ta dinga zuba masa godiya ta kalli Hamda ta ce "Maza ki kirasu suji wannan abin arzikin." Da sauri KK ya girgiza kai ya ce "Ba sai an Kira su ba don Allah Didi, sai zancen kayan d'aki ina da Show room Hamdan da y'an uwanta da za'a yiwa aure ha
r matar Hammad su je su zab'i abinda suke so, duk da dai ita Hamda akwai wad'anda na mata order daga turkey nextmonth za su zo, Didi Kemal za'a zo a miki gyaran d'akin saboda biki." Didi ta ce "Masha Allah, yanzu magana d'aya ta rage yaushe zaka kai Hamdan
danginta su ganta, kuma har yau Uwar Kamlan bata zo an sada zumunci ba." Yana murmushi ya ce "zata zo insha Allah, tana Ethiopia ne, na bata numberr Hamdan ta ce min abin yafi k'arfin waya so take kawai ta zo ta ganta, ai y'an k'asar tamu ma suna nan tafe
za su zo bikin." Ya mik'e idanunsa cikin na Hamdan ya ce "Hope dai ba matsala ko daughter na?" Ta d'aga kai kafin ya ce "To taso ki rakani in baki goron Sallah, don gobe a athiopia Zan yi idi daga nan ma airport na nufa." Nan Didi ta shifa zabga masa addu
'ar isa lafiya da dawowa lafiya. Hamda kuma ta bi bayansa ya dawo ya ri'ko hannunta suna tafiya yana tambayarta bai ga Hammad ba.
__________________
Anty Salman a d'aki ta saka Nanna tana sake hure mata kunnenta "Ina tabbatar miki Sadiya ba zata k'wat
ar miki y'ancinki ba sai kin tashi tsaye d'azunnan fa baki ji abinda ta gaya min a waya ba, wai ita ta barwa Allah komai, to bud'e kunnenki da kyau na koya miki dabara, a fuska ki nunawa duniya kin karb'eta bakomai ki nuna mata soyayya a zahirance ta haka
zamu samu damar cutar da ita, idan ba haka ba ina tabbatar miki yarda Sadiya ta zama bora haka kema zaki zama amma idan kin san abinda hausawa su ke kira kisan mummuk'e haka zamu yi mata. Ta yarda duk abinda zai faru daga baya ba mai ganin laifinki..
(Kw
ana biyu zaku ji ni shiru, ku min afuwa biki ne gagarumi a gabana insha Allah ranar litinin za mu d'ora dafatan ba ku ji haushi ba,dole ce ta sa hakan. Nagode remain few pages insha Allah.)
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Nannan kasa'ke ta yi tana sauraran
ta, daidai lokacin da Dida ta bankad'a labulan d'akin idanunta kafe akan na Salman,
Cikin matuk'ar b'acin rai take harararta kafin ta furzar da hucin bakinta na tsabar bak'in ciki ta ce "Madallah da samun Uwa irinki, ke kuma Salma taki tarbiyyar kenan, mad
adin ki lallasheta ki bata baki da nasiha da lallami sai ki ka b'uge da d'orata akan keken b'era, kin bani mamaki ina ilimin islamiyyar ta ki da har kika manta cewa ubangiji ne ya bawa namiji damar k'ara aure, idan har kuna ja da haka tabbas da ubangiji ki
ke jayayya, babu dad'i da kuma matuk'ar ciwo ka wayi gari kana zaune da mijinka k'alau rana d'aya ya sako wata a tsakiyarku babban lamari ne ga mata amma fa mai sauk'i a wajen wanda ya yarda da ayar da Allah ya ce 'Fankihu ma d'aba lakum minannisa'i Mathna
wa sulatha wa rubaa' ashe k'in yarda da hakan kina haramta abinda Allah ya halatta ne, idan ka daure komai mai wucewa ne har ya zamo kamar ba 'ayi ba, haukan ba ya maganin komai sai hasara da nadama, babu abinda wacce za'a aura ta fiki idan har kin cika m
ace sai dai ma ki fita ta b'angarori da dama, abu d'aya za kiyi ki hak'kake za ki zauna da ita da zuciya d'aya sai ki ga Allah ubangiji ya lamunce miki kaidinta ya zama duk sharrin da ta nufo ki da shi yana jirgewa a kanta, idan ba'a yi sa'a ba anan bigire
n sai ki ji ana yamad'id'i da ke ana kin asirce miji wance bata da katab'us a gidanta sun manta ubangiji ne yace idan bawa na ya zama mai kusanta ta a koda yaushe sai na zama jinsa da yake ji da shi, na zamo ganinsa da yake gani da shi na zamo hannunsa da
yake damk'a da shi na zamo k'afarsa da yake taku da ita, kin ga kuwa ta ya duk ubangiji yana kula da wannan b'abgarori na ki zai bari wani abu ta sameki na daga sharri. Har ila yau sun manta Ubangiji da kansa yace duk wanda ya dogara ga Allah hak'ika ya is
ar masa, shine isashshe akan duk al'amari yake kuma da iko akan k'addaruwar komai, 'Waman yatawakkal alal Lah fa huwa hasubuh Innallaha baligu amrih k'ad Ja'alallahu li kulli shai'in k'adra' don haka don girman zatin Allah Salma ku yarda makaman yak'inku i
ta kanta yarinyar idan ta ga kin ja girmanki sai ta fi daraja ki sab'anin ki tayar da hankalinki raini ya shiga tsakaninku, shi kansa mijin daraja da k'imarki zata k'aru a wajensa.(anan na ke jan hankulan y'an uwa na mata da cewa a duk lokacin da muka yi s
allah mu dinga rok'on ubangiji ya sauk'ak'a maka kishin da yake zuk'atanmu, ya bamu abokan zama na gari ya bawa mazajenmu ikon aikata adalci a tsakaninmu) Dida bata gushe ba tana cigaba da jan hankalin Nanna da Salma ta hanyar nasiha da misalai iri-iri har
sai da zuk'atansu suka yi la'asar nadama mai tsanani ta shiga tsakaninsu, daga lokacin Nanna ta janye duk wani mugun nufi a zuciyarta ta shiga addu'ar samun sauk'in zuciya 'Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahlan wa anta taj'alal hazna iza shi'ita sah
lan. Tunaninnika suka shiga zuciyarta tabbas shaid'an yaso wasa da zuciyarta sai dai tana godiya ga ubangiji da ya bata jajirtacciyar Uwa mai k'ok'arin d'orata bisa turbar gaskiya, ta runtse idonta tana jin wasu hawaye masu sanyi suna kwaranyo mata da tun
faruwar lamarin sai yanzu zuciyarta ta samu salama daga takaicin da take ciki, banda sharrin zuciya idan ba'a auren ta ya wad'annan tarin matan da suka baza gari za su auru idan ta tuna itama tana da y'ay'a mata tana da k'anne wanda ta yi imanin da wani ma
i mata zai zo ya so su ba zata hana ba, ashe kuwa ba ta bi fad'ar manzon Allah (s.a.w) ba da yace ka sowa kanka abinda ka sowa d'an uwanka, sosai ta fad'a jikin Dida hawayen na sake kwaranyowa take furta Astagfirullah ya Allah, ina rok'on afuwarka da gafar
arka, ubangiji ba ni da ja akan duk wata k'addararka Allah ka bamu zaman lafiya ka kawar duk wata fitina da zata wanzu a tsakaninmu."
Salman ma d'an hawaye take tana jin takaicin yarda ta zama uwar banza take zuga y'ar yayarta. Dida ta saki Hamdala a zuciy
arta da Allah ya farkar da su daga barcin asarar da ya d'abesu ta shafa kan Nanna ta ce "Ki godewa Allah da ubangiji ya baki miji irin Hammad masu wuyar samu a wannan zamanin ki kuma jajirce wajen biyayya da kyautata masa ki kuma sawa zuciyarki don Allah k
ike wannan biyayyar ba don ki fi waccan kishiyar ta ki a wajensa ba, ki sha mamakin yarda ubangiji zai d'aga martabarki da k'imarki a wajensa ba boka ba malam, Allah yasa mu dace. Zan kuma cigaba da miki addu'a akan samun sauk'in kishi." Nanna murya a dash
e tace "Nagode Dida madallah da samun uwa ta gari ya Allah." Dida ta lumshe ido kafin ta janye Nannan a jikinta ta ce "Ina son na ga canji daga yau, don haka ki tashi ki tarkata komatsanki ki wuce d'akin mijinki a can duk wata martaba taki take." Nanna tan
a murmushi ta d'aga kai, had'e da mik'ewa ta fara tattara shirginta don haka kawai da ta fice daga gidan Hammad d'in tana jin haushinsa.
__________________
Tun daga nesa ya tsura musu ido, duk da hijabi ne a jikinta bai hana bayyanuwar tudun k'irjinta
da faffad'an k'ugunta ba mai d'auke da tsukakkiyar mara. Takaici mara misali ya kamashi ganin ita a cikin Hijabin ma sai surarta ta bayyana, kishinta sosai ya tokare masa numfashi yana jin anya kuwa zai iya barin Hamda ta dinga fita ba bisa k'wakkwaran dal
ili ba, ya tabbata duk namijin da ya yi katarin ganin surarta sai ya ji wani abin ya tsarga masa zuciyarsa. Ya lumshe ido yana ganin yarda take taku kamar bata so. Ba tayi niyyar tambayarsa zuwa gidan lallen ba, amma Ammi ta tilasta ta sai ta tambayeshi gu
dun fad'awa fushin ubangiji. Yana zaune suka k'araso idanunsa na kan tattausar k'afarta mai kama da ta jarirai da ta yi kyau a cikin bak'in flat shoe d'in da yake saye da k'afar harta k'afarta ta kishin wani ya gane masa ita yake.
Fushi yake da ita don hak
a ya tattare fuskarsa ya k'unshe duk wata walwala da take cikinta, yana wurginta da kallo kafin ya mayar da idanunsa cikin na Sa'ada yana sakar mata murmushi a wasance ya ce "Amaryata sai ina?" Wani irin kallo Hamda ta jefeshi da shi da ya kusan saka shi d
ariya, Sa'ada kuwa murmushi ta saki ta ce "Y. Hammad tsokana ko?" Ya girgiza kai "Ba wani tsokana ai ba haramun zan aikata ba, na lura k'awarki ba zata iya d'auke hidimata ba, kin ga gwara na had'a da ke tunda ita lazy ce. Ina zuwa?" Ya fad'a idanunsa ciki
n na Hamda da take had'iye wani irin yawu mai matuk'ar d'aci wanda ta tabbata na zallar kishi ne ji take kamar ta kai masa duka. Sa'ada na murmushi ta ce "Gidan lalle za muje to Ammi ta takura sai munzo mun tambayeka." Ya girgiza kai "Ke dai ki je ki yi la
llenki, amma ita na yafe in dai ni zata yiwa." Ya fad'a yana k'issima yarda lallen zai zauna rad'am ya yi mata kyau a tausashahiyar k'afarta shikkenan maza sun samu na kallo ina ba zai iya ba, duk sanda ta tare a gidansa ya tabbatar ba wanda zai ganta ta d
inga masa lallen ba yanzu ba da kare da doki za su iya ganinta." Idanu ta zube a kansa kamar ta yi kuka kafin ta ce "Ban gane ba zan yi lallen sallah ba?" Ya tsai da idonsa a kanta yana d'aga mata gira cikin wani irin kallo da ya tabbatar da zai gigita zuc
iyar y'an matan ya ce "Eeh haka nace, ba za kiyi lalle ba, don ban ga amfanin lallen ba, duk wata matar aure tana yin lalle ne don ta ja hankalin mijinta ke idan kin ja hankalin nawa mai za