Showing 96001 words to 99000 words out of 129261 words
ta yi wannan tunanin ba. KK ya saki murmushi kawai yana girgizawa Didi kai a hankali kuma ya ce "Duk abinda ya wuce ya wuce Didi a daina tayar da shi." Didi ta jinjina kai kafin ta ce "Amma kuwa tabbas ka jawa Hammad kunne dama kada
na ji kada na gani don ban shirya makanta ba, ya bari Idan tare a can ya je su ci tsiyar da za su ci, idan ya so ma ya gutsire bakin nata k'arewa tand'ewa." Gaba d'aya gurin ba wanda bai ji kunyar furucin Didi ba, kada Hamda ta ji labari ji take da da hali
da ta narke ta bi k'asa akan wannan kunyar da Didi take bata. Shi kansa Hammad d'in sai da ya gallawa Didi harara ta k'asan ido. Har waje ya raka KK kafin ya dawo wajen su Abbun, idanunsa na laluban inda zai gano Hamda sai dai sam bata wajen da alama ta s
hige d'akinta, ya ciji leb'ensa na k'asa yana takaicin yarda Didin take so ta saka masa shamaki tsakaninsa da matarsa.
Cikin kamala ya durk'ushe a tsakiyar falon, idanunsa a k'asa muryarsa ta raunana sosai kafin ya ce "Don Allah Abbu ka yafe min, na Dan a
n aikata maka ba daidai ba, ta hanyar b'oye maka
wad'annan sirrikan wallahi ba yarda Zan yi ne.." Tsawon lokaci Abbu yana masa wani irin duba kafin ya saki murmushi ya dafa kafad'arsa yana girgiza masa kai "Da fari kam na ji haushinka Hammad, amma yanzu na
gane dalilinka na aikata haka Allah yayi maka albarka." Ameen ya amsa a hankali idanunsa cikin na Mahmah da itama ta kafa masa na ta idon tana mamakin zurfin cikinsa ta yarda ya iya b'oye wannan sirrin mai girma cikin zuciyarsa shekara da shekaru. "Mahmah
kema ki yi hak'uri please!" Ya fad'a yana dunk'ule hannayensa waje d'aya alamar rarrashi, kafin Mahmahn ta ce wani abu Didi ta ce "Zancen banza, zancen wofi to ita kuma hak'urin me zaka bata? Me ka yi mata? Ai itace ma taso cutarka ta raba maka aure da y'
arnan kaga samu ka ga rashi haka kawai." Ya d'ago a fusace har zai mata rashin kunya sai kuma ya ga fuskar yaranta a wajen don haka ya gintse abinda ya so fad'a mata, ya kama hannun Mahmahn kawai yana matsawa idanunsa cikin na Nanna da ta rasa yarda zata s
aka kanta saboda tsananin takaici, idanunta ya yi jazur dalilin tashin hankalin da take ciki da matsanancin ciwon Kai, take a wajen wani irin tausayinta ya kamashi ya ji k'aunarta na d'an tab'a shi kad'an da gaske bai tab'a jin tana burgeshi ba, yana zaune
da ita ne kawai saboda itace zab'in mahaifiyarsa amma yau ya d'an Ji wani Abu mai kama da k'auna da yake so ya yi tasiri a zuciyarsa. Nanna bata da laifi ko kad'an tana kuma kyautata masa fiye da zaton mutum a rayuwarsa tana gudun b'acin ranta, yana kuma
ganin kima da mutuncinta musamman da ta rik'e masa Kamla tsakani da Allah duk da bata da tabbacin ba y'arsa bace, sau d'aya ya tab'a ganin laifinta Akan Hamda da ta kafawa d'anban tsana tun ma bata san wacece ita a wajensa ba. Shi kansa ya san mai laifi ne
a wajenta ya kuma wajaba k'warai da gaske ya amsa laifinsa ta hanyar kyautata mata da gudun b'acin ranta ko zai samu zaman lafiya a gidansa. Murmushi ya sakar mata yana d'aga gira d'aya, inda bata kula ba, hakan da ya yi bai yi tasiri a zuciyarta ba, ko k
ad'an bata ji sauk'i daga rugugin bak'in cikin da yake addabar zuciyarta ba, da gaske tana takaici tana kishi tana kuma bak'in cikin zamowar Hamda d'iyar KK, a da tana tunanin bata da asali har tana shirin goranta mata idan ta tare a gidan mijinta sai ga s
hi ashe ta fita asalin ma, hawaye ya silmiyo mata tana jin tsana da Kishin Hamda matsananci, a lokaci d'aya kuma tana jin k'aunar mijinta ba ta ga kuma wanda zata barwa mijinta ba wallahi, zata zauna da shi za kuma su goga kishin a ga wa ke da nasara? Ita
ko Hamdan?
Ganin tana jifansa da wani irin firgitaccen kallo ya sa shi d'auke kallonsa daga kanta, shi da kansa ya san yanzu aka fara? Kishiya itace yak'in mata ya tabbata ba aure ba.
Haka duk jama'ar wajen suka watse ganin dare ya lula. Shima Hammad haka
ya fita jikinsa a salub'e duk da yana son ganin Hamda ya san Didi ba zata ba shi wannan damar ba, ko ba haka ba bai shirya janyowa kansa idanuwa ba, zuciyar kowa fes ya tafi gida yau dai k'udundunenen Sirri ya fashe kowa ya ji asali da tushen komai.
Ha
mda tsaye ta yi a gefen mudubi hannuta d'auke da towel tana goge sumar kanta, ta saba duk dare sai ta yi wankan take jin dad'i. K'amshin turarukan wanka kawai take zabgawa a jikinta. Umma Asma ta shigo da cup a hannunta ta mik'a mata "Maza kafa ki shanye s
hi tas, don wannan mijin naki ban hango wasa a lamarinsa ba duk da dai yana da wata Matar. Matsananciyar kunya ce ta sa hannunta ya fara rawa duk da tun farkon aurenta bata tab'a sha ba ta san menene ta kuma san amfaninsa, tabbas ita kanta ta san lamarin H
ammad ba wasa dole ta tashi tsaye wajen gyara kanta. Umma Asma ta sake jan kunnenta sosai akan kada ta sake ta sake rab'arsa har sai an gama shiryata sosai. Ta amince da hakan kafin ta kulle d'akin ta juyo tana daka uban tsalle, murna fal cikinta da
ta tab
batar ko wanene mahaifinta. Ta lumshe idanunta tana hango yarda Hammad yake sakar mata murmushi kafin ta ja filo ta rungume a jikinta. Asuba ta gari Hamda.
_____________
Tunda ta shiga d'akinta take zagaye tsakar d'akin cikin tashin hankali zuciyarta c
e kawai take duka, neman mafita kawai take mafitar da zata hana Hammad auren koma wacece ba ma Hamda ba da take ganin ta zarceta a komai, kyau dirin jiki kyawun fata abu d'aya zata bugi k'irji ta ce tafi Hamdan shine kyawun gashi don ita ko relaxing kanta
ba tayi saboda tsabar santsi da yauk'insa, kuma sarai ta sani Gashi yana d'aya daga abinda yake burge Hammad a sasan jikin y'a mace. Ta runtse idanunta da zuciyarta ta hasasho mata yarda Hammad d'in yake maitar k'irjin y'a mace anan kam Hamda ta mata zarra
don a cike take taf daga saman ta har k'asanta, tashin hankalinta ya k'ara hauhawa har ta ji kamar ta kurma ihu da ta tuno yarda Mahmah ba kunya ba tsoron Allah ta yi mubaya'a ga auren duk da cika bakin da ta dinga yi a kwanakin baya, itace hope d'inta it
a kuma take saka ran za ta tirje ta k'i amanna ga auren sai ga shi a lokaci guda fuskarta ta nuna tana farin ciki da hakan, hawaye na ziraro mata cikin buga katifa ta ce "No No No Mahmah dole ke za ki yi min maganin abin nan, ko kina so ko ba kya so." Ta z
aro wayarta ta shiga kiran Anty Salma da ta zamo k'anwar su Mahmahnce ta kuma san ita kad'ai zata iya lankwasata ta saka Mahmahn ta yi abinda I take so ta shirya ko ba ta shirya ba, duk da ta ga dare ya tsala bai hanata doka mata kiran ba, tunda ta san dar
e ne na azimi goman k'arshe kuma ta tabbata kowa idonsa biyu.
Zatonta kuwa ya yi daidai don bugu biyu Anty Salman ta d'auka cikin tsoro ta ce "Nanna lafiya?" Kuka ne ya k'wacewa Nannan, kukan da take neman inda zata saukeshi sai yanzu ta samu. Anty Salma t
a saka salati ta ce "Lafiya Nanna?" Nan Nannan ta shiga bata labari da k'arya da gaskiya. Anty Salman ta dakatar da ita ta hanyar cewa "kan uban can, ita kuma Yayar ta amince? Hamda fa kika ce ya aura jjnin Sakna? Saknan da ta mayar da ita bora a gidan mij
i to wallahi ba zai yiyuba da safe Zan zo gidan, ki ma share hawayenki ba y'ar KK MuD'allab ba ko d'iyar shugaban k'asan Amuruka ce sai ya saketa, da ni ake zancen ban da abin Yaya ba yanzu bane zata nunawa Sakna kuskurenta.."
Farin ciki da murna ya cika z
uciyar Nanna, ta tabbata Anty Salma zata aikata duk abinda ta saka kanta, don haka barcin za tayi har da munshari....
1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Turo k'ofar da Hammad d'in ya yi ne, yasa Nanna bud'e idanunta da barci ya fara fusga a kansa, ta bishi da
kallon sama da k'asa tana jin yarda haushinsa yake sake dabaibaye zuciyarta. Shi d'in ma jikinsa a sanyaye ya k'arasa wajenta, ba shi da bakin da zai fara furta mata kalmar hak'uri shi kansa ya sani, kunya ce ta kamashi irin kunyar da take kama duk wani N
amiji mai kamala idan ya yiwa matarsa kishiya. Cikin sanyin jiki ya zauna a gefen gadon yana k'ok'arin ganin ya kawar da tasirin da kunyar ta yi a zuciyarta "Barci ki ke?" Ya furta a hankali ba tare da shi kansa ya san zata ji maganar ko ba zata ji ba, sab
'anin hasashensa sai ya ji ta ce "Ba barci nake ba, menene? Ka zo ka sake saka min wani b'acin rai ne?" Ya girgiza kansa yana fad'in "Ko d'aya na zo na kawar miki da b'acin ran ne." Ta saki wata dariya mai bayyana ainahin takaicin da ya cika zuciyarta kafi
n ta ce "Ai ka gama ba ni farin ciki a rayuwa, na tabbbata da bak'in cikinka zan mutu Hammad, Kishiya fa? Ban tab'a zaton zamanmu akwai cin amana irin
haka ba, me na rageka da shi da har na cancanci d'and'anar bakinciki irin wannan? Ka yi aure ban sani ba,
ka d'auko min d'iyar wani k'ato na rik'e ban sani ba, ashe k'anwar kishiyata na rik'e, duka saboda kana son mutumin can ya narka ka da Naira ba ka gode Arzikin da Allah ya baka ba, har sai ka jingina jikin mutumin da ba'a san inda yake samo arzikinsa ba,
ba zan fasa gaya maka ba, ba zan zauna da ita ba saki na ke so idan ya so ta cigaba da shayar da kai abinda ba na baka." Ta fad'a wasu hawaye masu k'una na karakaina akan k'uncinta. Sosai kukanta yake d'aga masa hankali ya kamo hannunta cikin alamar rarras
hi yana matsa shi a hankali, harshensa gaba d'aya ya yi nauyi ya kasa d'aga shi wajen furta mata kalmar hak'urin, gwara kawai ya aikata mata a aikace abinda bai tab'a yi mata ba ranar ya yi mata wani irin zazzafan romance yake sakar mata mai tafi da duk im
anin y'a mace ta mutu akan ko ma waye mai yi mata irinsa. Bakinta luf ya yi tun bayan da ta fara amsar sak'onsa da gaske lamarin ya gigita ta, ta fara tunanin ashe Hammad d'in gwani na wajen nuna soyayya amma bai tab'a nuna mata ba sai yau, lallai kuwa ba
zata yi saken da wata mace zata k'wace mata shi ba, musamman yau da ya shayar da ita wata zuma da bata tab'a kwankwad'aba.
____________________
Ammi kuwa tunda ta shiga d'aki gaba d'aya notunan kanta suka kunce ta rasa ta yarda aka yi wancan lamarin ya
juye haka, KK fa? KK Mud'allab da take yawan ganin ana hira da shi a tashoshin yad'a labarai shine Uban Hamda, mutumin da yake da arzikin da shi kansa bai san yawansa ba, mutumin da yake da farin jini a wajen al'umma fiye da shugaban k'asa saboda yarda ya
ke kyauta tawa talakawa shine Uban Hamda, Hamda dai d'iyarta, yarinyar da ta wulak'anta ta banzagatar da lamarinta, ashe da ita zata zo ta yi tink'aho kwana kusa, don ta tabbatar Hamda ta azirce ta gama, su wad'annan d'in da ta saka rai da su ta tabbata wa
d'anda za su aura ba su isa su had'a kafad'a da KK ba sai dai su zame masa yaransa, me yasa idanunta suka makance ta kasa gano kamannin KK da Hamda, ta runtse idanunta tana jin dana sani yana kanainaye zuciyarta, ji take tamkar ta dawo da rayuwar baya ta g
yara kuskuren da ta aikata, ta hanyar nunawa Hamda k'auna da soyayya fiye da duk yaran da ta haifa, ba mamaki da KK yafi ganin kimarta da mutuncinta har ma ya yaga mata wani kaso daga cikin dukiyarsa kamar yarda ya yiwa Hammad. "Yanzu ma lokaci bai k'ure m
iki ba Ammi, kina da damar da zaki gyara kuskurenki duk da na tabbata duniya zata zageki, tace don kin san wanene ubanta yanzu ne, amma ai ba tun yanzu kika sakawa zuciyarki salama ba kika karb'i Hamda a matsayin y'arki tun kafin bayyanar KK d'in." Ta tsin
ci muryar Munirat ta na bata shawara sai a lokacin ta san duk abinda take fad'a ashe a fili take fad'arsa tsabar rud'anin da ta shiga ne yasa bata gane ba. Idanunta zube a cikin na Munirat kafin ta saki ajiyar zuciya, tana tuna tsawon lokacin da Muniran ta
d'auka tana mata nasiha akan ta so y'ar uwarta amma ta yi burus da shawararta ta k'i ji gani take bayyanawa Hamdan k'auna zai saka ta samu ingattaciyar lafiyar da za tayi tsawon rai har asirinta ya tonu. Sai a lokacin ta fad'a jikin Munira tana sakin kuka
kukan da ta dad'e tana neman inda za ta saka kanta ta yi kuka ko ta samu k'uncin da nadamar ta jawo mata ya sauk'ak'a a zuciyarta, Muniran ta rungumeta itama nata hawayen suna sauka tausayin Ammin take ji tausayin da yake nad'e duk wani k'arfin zuciya, Uw
arta mai kyawun zuciya ce ta tabbatar kuma ba don gado take son ta haifi namiji ba, don dai ta sharewa Umminta bak'in cikin rashin haihuwar d'a namiji da har aka dinga mata gori a rayuwa.
Sun dad'e a haka kafin Ammin ta d'ago tana matsa hannun Muniran kafi
n ta ce "Ta wace hanya kike ga Zan ja Hamda a jikina? Da sam ba zata kawo zargin Dan naga ubanta da kud'i bane." Munira ta girgiza kai "Wannan zargin ba zai kau daga zuciyarta ba har abada, haka nan daga zuciyar mutanen gidan nan, abu d'aya da zaki tuna ki
kwantar da hankalinki shine idan kika tuna don Allah ki keyi ba don jama'a ba, to sai ki samu sauk'in zuciyarki, abu na gaba ki d'auke kai daga dukiyar KK kada ki sake ki nuna zalamarki a kansu." Amma ta girgiza kai tana jin zuciyarta ta samu nutsuwa daga
shawarwarin da Munirat d'in ta bata, duk da ta bi ta Munirat d'in da abin bai kai tsawon haka ba, to sharrin shaid'an duk shi ya jawo mata komai. Munirat ta sake share mata hawayenta had'e da cewa yanzu ki je ki sake bawa Abbu hak'uri na tabbata zai hak'u
ra duk da ya sakko dama." Ammi ta d'aga kanta alamun amsar shawarar y'ar ta ta.
Tsaf ta yi wanka, kamar yarda ta saba bata tunkarar tirakrshi sai da daddad'an k'amshin da ita kanta ta san yana wargaza tunanin Abbu, a wannan turbar take son saka duk yarant
a har Hamda kuwa daga gobe zata fara koyar da ita karatun mallakar miji, ta yarda ba zai iya rayuwa idan ba bu ita ba, harta da gashin kanta sai da ta turara shi sannan ta zumbula dogon hijabinta ta fice zuwa b'angaren Abbun.
Lokacin yana zaune jikinsa ya
ke jin ya masa nauyi, sosai yake son a mammatsa masa, ya san kuma Sadiya ba zuwa zata yi ba musamman sanin cewa ba girginta ba ne. Sakna ta tura k'ofa ta shiga da sallama. Abbu ya saki ajiyar zuciya yana amsa mata sai dai babu yanayin walwala a tare da shi
. Bata damu ba ta k'arasa ta zauna a gefensa fuskarta d'auke da murmushi burinta ta gusar masa da wannan fuskar da ta gusar masa da duk wani kyansa. Ta saka kanta a kafad'arsa yana jin yarda numfashinta yake hawa da sauka a kunnensa "Ka yi Hak'uri Faruk'u
na please ka yafe min mu koma kamar yarda muke a da, wallahi ba na jin dad'in yanayin nan sam." Ta fad'a tana matsa masa cinyarsa a hankali ta bi duk wata hanya da zata bi na ganin ta shayar da shi duk wani farinciki a wannan daren kafin ya sauko bisa tila
shin zuciyarsa ya fara mayar mata da martani gangar jikinsa na nuna mata yarda ya yi bala'in missing d'inta ta hanyar rawa da jikinsa yakeyi, tsammaninsa zai iya rayuwa ba Sakna sai dai yau jikinsa da ruhinsa sun k'aryata tunaninsa kansu tsaye, don idan a
zahiri ya nuna mata ya bazangatar da lamarinta sai dai yau bad'ininsa ya nuna mata itace dai mahad'insa itace Saknansa da duk wani numfashinsa da d'igon k'aunarta yake dira. Shikkenan zancen ya mutu murus ya koma tamkar ma ba ayi ba, madadin jin haushinta
wata sabuwar k'aunarta ce ta sake maye gurbin tsanar a zuciyarsa ko bakomai yau ta bashi wata irin zuma mai wuyar fasalta zak'inta a harshe, yana jin tamkar ya sake mayar da ita ciki. Ba boka ba Malam Sakna ta sake dawo da martabarta a zuciyarsa, ta hanyar
da mata da yawa kunya ba ta barinsu aikatawa JIKAR NASHE zata sake fad'a babu kunya a rayuwar aure da haka matan waje suke janye muku hankalin maza, ko a auro wacce take da masters a wannan fannin ta samu kan miji sai ki ji ana ta mallakeshi, ta asirceshi
alhali ita kad'ai ta san yarda take sarrafashi a gado ta yarda zai zame mata rak'umi da akala wannan ake kira 'Karuwar Gida'
😆
.
___________________
Babu komai a ranta ta tashi da safe, kafin Salma k'anwarta tazo ta wargaza mata duk wani tunani mai ky
au na zuciyarta, ta kuma amince da gurguwar shawarar da