Showing 87001 words to 90000 words out of 129261 words
kafin yace "Ina zuwa, idan na dawo zaki ga ko wacece duk da baki santa ba." Daga haka ya yi saurin ficewa a gaggauce kamar ya fad'i. Mamaki ya kamani da tunanin wacece a garin wacce ba santa ba, sai kuma na tab'e baki na mayar da kaina barc
i ya sake kwasheni.
Cikin barcin na ji yana bubbuga kafad'ata "Nanna Nanna tashi mu yi magana." Cikin idanuwan barci da suka min nauyi na bud'e idanun ina kallonsa mamaki ya kamani ganinsa da jaririya a hannu. Na murza idanuna sosai ina jifansa da ayar ta
mbaya, murmushi ya sakar min had'e da saka min y'ar a cinya "Ki yi hak'uri kyauta Allah ya bamu don Allah kada ki tambayeni alfarma d'aya za ki min ki sanar da duniya ke ki ka haifeta." Tsananin firgita ya sa saura k'iris yarinyar ta sub'uce daga jikina a
tsorace nake kallonsa, kafin da kyar na had'a kalmomin "Ban gane ba?" Ya girgiza kai sai na ga ya d'an saki ajiyar zuciya ya ce "Shi yasa tun farko na had'aki da Allah akan kada ki tambayeni ki k'addara kyauta ce Allah ya ba mu." Dangwara masa y'ar na yi a
cinya fuskata da mabayyanin b'acin rai na ce "Wallahi sai ka gaya min y'ar waye? Kuma ta wace hanya aka haifeta? Kafin ka saka ni rik'eta dole." Ya girgiza kansa yana murza goshinsa kamar yarda ya saba idan ransa ya b'aci murya a shak'e ya ce "Y'ata ce Na
nna, kuma ta hanyar halak aka haifeta Wallahil azeem." Takaici na ya girmama jin ya alak'antata da y'arsa na ware idona ina kallonsa kafin na ce "In dai har y'arka ce to sai dai idan ba ta hanyar halak ka samar da ita ba, don ban san sanda aka d'aura auren
ba." "Ba ku ma za ki sani ba, tunda ba huruminki bane" Na ji ya fad'a cikin wata irin kaurin murya da ya saka na kalleshi kafin na d'ora wani abin cewa na ji yace "Wallahi, idan ba ki rik'e y'ar nan ba, ina tabbatar miki a satin nan zan auri wacce zata ri
k'e min ita, kuma idan ki ka
bayyana sirrin nan ga wani ina tabbatar miki a bakacin aurenki matuk'ar ke kika furta ba ni na fad'a da kaina ba." Hanjin ciki na ya hautsina ganin cewa ya riga ya yi min dabaibayi da duk abinda nake tsoro sakin aure da kishiya
. Hawaye ya b'alle min na shiga tambayarsa "Amma Abban Khairi me yasa zaka min haka? Hakan ya yi min tsauri." "Hakan kad'ai zan miki na samu kan ki, gobe zan sanar da dangi cewa kin haihu, kuma uwarta ta saka mata suna Kamla." Kuka nake kawai takaicinsa da
bak'in ciki na nuk'urk'usar raina. Na zame na kwanta ba tare da na karb'i yarinyar ba. A daren ya gaya muku wai na haihu, kwana ya yi yana kula da yarinyar don na k'i yarda na karb'eta. Kashegari da na tashi da safe ya sake turkeni a d'aki ya tabbatar min
idan ban amsheta ba yana tabbatar min a yau ba sai gobe ba zai je jami'ar Birmingham ya samu bahaushiya ya aura, bisa tilas na amince muka je asibita aka bani magunguna na samu ruwan Nono yazo haka kawai sai na tsinci kaina da son yarinyar kamar yarda nak
e son Khairi, na kuma ja baki na k'ulle ba wanda na bayyanawa don ina tsoron saki da kishiya, wallahi Mahmah wannan shine abinda na sani, kuma har yau bai gaya min gaskiyar magana akan Kamla ba ni kuma ban sake tamabayarsa ba, ko su Khairi ba su san ba cik
in su d'aya da Kamlan ba."
A gigice Sadiya ta watsa mishi mari, cikin b'acin rai take tabbatar masa ba zata bar d'akin ba sai ya sanar da ita Wacece Kamlan?" Rik'e yake da k'uncinsa ya kasa fitowa ya mata magana sai ajiyar zuciya yake, don shi dai zai iy
a cewa tun tashinsa bai tab'a ganin Mahmahn ta mareshi ba sai yau, kuma yana hango tsananin b'acin rai a idanunta, amma ya gaza furta mata wacece Kamlan? Alk'awari ya d'auka, abinda shi kansa ya san a yau ya kamata ya sauke alk'awarin amma ina? Ya riga ya
d'au alk'awarin ba zai furta da bakinsa ba har sai lokacin bayyanuwar hakan ya yi.
Durk'ushewa ya yi a gaban Mahmahn cikin tashin hankali ya rik'o hannayenta ya saka fuskarsa a tafin hannayen "Allah ya huci zuciyarki Mahmah bakina ba zai iya gaya miki ba.
" Cikin b'acin rai ta janye shi daga jikinta murya a raunane ta ce "Idan baka gaya min ba, ai zaka gayawa Didi da ubanka don a yau ba sai gobe ba zan sanar da su." Ya dinga rok'onta tare da neman ta bashi kwana biyu zai sanar da ita wacece Kamlan, da kyar
ta amince da hakan, shima don bata son ta tara masa jama'a ne ta fi son ta ji ta yarda ya samu Kamlan kafin ta san ta yarda zata b'ullowa lamarin. Cikin sanyin jiki ta fice daga d'akin tare da tabbatar masa kwana biyun jal da ya buk'ata ta bashi yazo mata
da cikakken bayani.
Tana fita ya saki ajiyar zuciya ransa a b'ace ya dubi Nanna ya ce "Hankalinki ya kwanta..." bakinta na rawa ta dubeshi "Me kake nufi Abban Khairi ka san dai ba ni na gaya mata ba." Ya zuba mata narkakkun idanunsa kafin cikin b'acin ra
i ya ce "Ni na gaya mata kenan? Ba zan ce miki komai ba a yanzu amma ina tabbatar miki sai na d'au zazzafan hukunci a kanki." Daga haka ya yi k'wafa ya fice, Hamda kawai yake son gani a lokacin amma Didi ta yi masa katangar k'arfe da ita, ita kuma da yake
mashiririyace ko ta neme shi, ya cije leb'ensa ya na son tattaro duk wata nutsuwa ya sawa kansa amma abu ya faskara, ya dinga zabga tsaki kafin ya isa Sashen Didin yana fatan ya tarar ta yi barci ko zai samu ganin Hamdan.
Umma Asma ce kawai a falon hannun
ta rik'e da waya da alama waya take da mijinta, ta ji ya turo k'ofar ya shigo, da hannu ta dinga nuna masa lafiya? Ya girgiza mata kai shima da hannun ya nuna mata wajen Hamda ya zo. Ta ware idonta kafin ta yi saurin katse wayar tana rik'e hab'a "Rufa min
asiri Hammad, kada kasa Didi ta fige ni, baka ji me tace maka bane d'azu?" Idanunsa ya marairaice da son ta tausaya masa "please Umma mana, ko nan ta fito ni ba abinda zan mata zance na zo tunda ance sai na sake neman auren daga tushe." Ya fad'a yana murmu
shi. Asma'u ta girgiza kai "Zancen ne da Sha d'ayan dare? Duk zancen arziki ai da yamma ko magriba ake yin sa." Ni dai don Allah ki taimaka min wallahi akwai abinda zan tambayeta." Ta bishi da kallo tana hango fitina kwance a idanunsa ita ba ruwanta ba zat
a d'au hak'kkinsa ba kan wani zancen Didi mara tushe, ta mik'e had'e da cewa "Bari na turo maka ita, amma ka tabbata daga zancen ba a zarce k'aida ba?" Murmushin gefen kumatu ya bita da shi a zuciyarsa ya ce "Wasa kenan ni da Halak d'i na."
A zaune ta s
amu Hamdan hannayenta zube a kuncinta, sai ta ga ta mata haske ta sake kyau duk da ramar da ta yi. Ta zare mata hannun tana sakar mata murmushi "Ba kyau dogon tunani, ki je mijinki yana kiranki, kada dai ki sake ya wuce gona da iri Didi gata zata miki don
ban tab'a jin irin aurenku ba ko a labari. Ki bari a kaiki gidansa cikin mutunci a kuma gyara miki jikinki ta yarda zaki martaba fiye da yanzu a idanunsa, kin ji na gaya miki, idan ki ka bari ya moreki ina tabbatar miki ba zai miki lefe mai nauyi ba, haka
kawai ya sameki a araha." Sunkuyar da kanta ta yi tana jin zuciyarta tana amincewa da duk abinda Umma Asman ta ce mata. Ta tabbatar soyayyar da suke mata ita da Didi sam ba algus a ciki, dole ta siyawa kanta mutunci.
Hijabi ta saka zunbulele a jikinta. S
annan ta fita.
Tun daga nesa yake jifanta da kallo yana jin takaicin dogon Hijabin da ta zumbula, yaushe rabon idanunsa su ga halittun jikinta? Amma yau da ya samu dama ta wani saka dogon hijabi ta k'dudundunesu. K'aramin tsaki ya ja, yana mata kallon k'as
an ido, cikin wata irin murya da bata san shi da ita ba ta ji "You better takeoff your Hijab, before coming here." Turus ta yi tana mamakinsa "Ina ruwansa da Hijabinta da zai ce sai ta cire sannan zata zo, ba ta cire d'in ba ta cigaba da isa inda yake. Tsa
m ya mik'e tsaye yana manna ta da jikinsa, sanin cewa ba wanda zai gansu "Ba ki ji me nace miki bane? Amma kika min kunnen uwar shegu." Ya fad'a yana k'ok'arin cire Hijabin ita Kuma ta k'i ba shi damar hakan, har sai da ya saka hannu ya doke hannunta sanna
n ya samu damar zare Hijabin. Saura k'iris ya yi suman tsaye kasancewr rigar barci kad'ai a jikinta, yana k'ok'arin manna ta da jikinsa ta yi saurin durk'ushewa tana duk'unk'une jikinta murya na rawa ta ce "Please mana Yaya Hammad don Allah ka bari." Ganin
bashi da niyyar bari ya sa ta d'an saki kuka da ya saka shi k'ara mannata da jikinsa yana lalubar bakinta. Daidai lokacin da ya ji muryar Didi tana fad'in "Wani Kwalton ne anan cikin dare? Muhammadu rasulillahi." Zuciyar Hamda ta buga.. amma shi ko gezau
bai yi ba....Hamda na k'ok'arin tureshi ya manna bakinsa a cikin nata, suman zaune ta kusa yi, tana nuna masa Didi da take kusan tosu hannun ta d'auke da sandan mopper...
★
𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍
✍
️
★
𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍
✍
️
★
ALKALAMIN JIKAR NASHE
📲
YA ABIN YAKE? 3
9.
*08033748387*
K'ok'arin tureshi take yi, amma bai bata damar hakan ba, duk da ya ga Didin na kusanto su sake manna bakinsa ya yi cikin nata, fatansa Didin ta gansu ina ruwansa tunda ya san ba haramun ya aikata ba, ya manna ta da jikinsa sosai ta yard
a ba zata samu damar tserewa "Nutsu Malama, kada ki sake tureni da fushin Didi da na mala'iku wanne ki ka fi tsoro?" Hawaye kawai ta ji suna zubo mata ganin Didin dab da su, cikin gigita ta runtse idanunta tana jiran jin saukar sandar mopperr a jikinta. Sa
i ta ji Didin ta saka salati "Innalillahi, wace jalaba ce wannan cikin dalennan kazo kana lalubeta kai dai an yi tanbad'adde k'warai da gaske." Bai kulata ba, ya mik'e da Hamdan a jikinsa ya sake rik'ota sosai idanunsa cikin na Didin ya ce "Haramun na aika
ta?" "K'anin haramun ka aikata tunda ni ban amince da wannan tambad'adden auren naka ba." Ciki-ciki ya yi da idonsa kafin ya ce "Kada ki sake tambad'a min aurena, aurena na halak ne da shaidu da komai.." Didi ta wurgi Hamda da take k'ok'arin k'wace hannun
ta daga nasa da harara "Munafuka da kika ganni ba, ke wato har kin iya biyo dare ki samu namiji saboda kina jin dad'in tumurmusaki da yake yi, tun kina budurwa ai na san kema jalababbiya ce yadda kike kwana kina matse filo a jiki, ba zaki wuce ba tai na ma
ka miki tandan nan." Da sauri Hamda ta fincike Hannunta ta shige d'aki wata kunya da bata san daga inda ta taho ba ta had'u ta rufar mata. Didi ta bi shi da kallon banza kafin ta ce "Wallahi Hammad na sake ganin k'afafunka a nan tai na taka Umalu ya yi man
a tsakani da kai." Shiru ya yi mata don gaba d'aya Hamda ta tafi da duk wata nutsuwarsa jin sa yake da kyar yake mayar da numfashinsa ga Didi na neman sake caza masa kai, ya mik'e cike da k'warin gwiwa yake kallonta "Saboda lefe kika rik'e min mata? Idan n
a yi lefen a gobe za ki bani Matata?" Kallon banzan ta sake watsa masa kafin ta ce "Ai idan kaga na baka ita, an had'a an yi bikinta da na y'an Uwanta da za'a yi ana tallacewa tannan za'a kaita d'akinka, don ban yarda ka sameta a gantale ba." Kallon baki i
sa ba yake mata kafin ya yi k'wafa ya sa kai zai fice ya jiyota tana fad'in "Ni Za'a kawowa itkanci wallahi ka take zuwa ma tai na fad'awa Tadiya ta titseyeka ka taketa ai dama ba son Auren takeba, na ma
Yi mamaki da hal yanzu bata take tada balli ba." Jik
insa a mace ya wuce sashensa gaba d'aya jallabiyarsa ta nad'e k'amshin jikin Hamda tsaf,
K'amshin da yake sake tada masa zafaffiyar sha'awarta. Wanka ya shiga kafin ya fito ya kwanta gefen Nanna da ta juya masa baya, zuciyarta cike taf da jin haushinsa don
ta tabbatar daga gurin Hamda yake tunda ya shigo ta ji k'amshin turaren mata a jikinsa, tsaki ta ja a hankali ba tayi zaton zai ji ta ba, ga mamakinta sai ji tayi ya birkitota yana jifanta da kallo da manyan idanunsa "Allah yasa dai tsakinki ba dani kike
ba?" Tsoro ne fal ya cikata shi yasa ta k'i biyewa zuciyatta da take ingizata tace Da shi d'in take sai me? Amma madadin haka sai ta girgiza kai cike da tsoronsa "Magana za ki min, Bana son raini." Murya a shak'e ta ce "Ba da kai nake ba, kaina ne ya ke mi
n ciwo." Ya sassauta rik'on da ya yi mata ta hanyar shafa kan sai ya ji da d'an zafi da alamar da gaske ciwon kan take, sauka ya yi ya samo ruwa da paracetamol ya b'alla yana cusa mata bakinta ta samu ta had'iye da kyar, suka kwanta yana d'an murza mata ka
nta yana k'okarin yakice tunanin Hamda da ya tsaya masa a k'irji.
Hamdan kuwa fad'a ta sha gurin Umma Asman sosai akan yarda ta yi kunnen uwar shegu da jan kunnen da ta yi mata. "Ba zaki bari a siya miki mutuncinki na y'a mace Ba? Ba zaki bari ya dinga d
'okinki Ba, zuwa kika yi kika sake sakar masa jiki, kin kyauta to." Kunya ce ta kamata sosai har ta ji takaicin yarda ta fita ta sameshi ta tabbata rigar da take jikinta ce ta janyo ya kasa hak'uri sai da ya jata jikinsa, tunda idan har zai ganta a haka ta
tabbata Ba zai iya d'auke kansa ba, dama ya lafiyar giwa, dole kuwa ta ja jikinta da shi, musamman da bata san makomar auren nasu ba, daga yanayin yarda Mahmah take amsa gaisuwarta ta tabbata ba tayi na'am da aurensu da Hammad d'in ba, za kuma ta iya dats
e shi a duk lokacin da ya yi mata. Ba zan sake kusantarka ba har sai Mahmah ta amince da aurenmu shine tunanin da take a zuciyarta.
__________________
Duk fushi take da Ammin amma tana jiyo muryarta falon Didi sai da ta ji zuciyarta na son ta ganta, tan
a son Ammi fiye da kowa a rayuwarta, zuciyarta na son fita ta ganta ko da zata yi mata hararar da ta saba, amma tana tunanin lokutan da Ammin ta d'auka tana wahalashsheta akan laifin da Ba nata ba, ashe duka kuskuren ma idan za'a tankad'eshi a taskaceshi n
a Ammin ne kacokam ba nata ba, ita tabi son zuciyarta Allah kuma ya nuna mata ikonsa ba dai d'a namiji take so ba, to shi kuma Allah bai so ta haifa ba. Kasa jurewa ta yi sai da ta mik'e ta fita jin kukan Ammin a gaban Didi kamar ranta zai fita tana jiyo s
autinta tana fad'in "Don girman zatin Allah Didi ki yafe min, Umar ya ce ba zai cigaba da zama da ni ba har sai idan ke kika amince masa, wallahi zan gyara kuskurena zan zauna da kowa Lafiya, zan yi biyayya a gareki Didi ki tuna ko Allah muna masa laifi ya
yafe balle d'an Adam, Didi watan azimi muke ki dubi girman Allah alfarmar watannan ki yafe min." Yawan magiyar ya sa Didi taji tausayinta da sauri ta d'aga mata hannu "Ya ita Takina, dama ni ban tab'a k'ullatarki ba, kuma sai a godewa Allah da ba ta hany
ar banza kika samar da cikin nata ba, Zan yafe miki amma tai kin ja y'alki a jiki kin nuna mata soyayyar da duk bata samu ba, kin wanke mata wancan bak'in painting da kika goga mata a zuciya, daga yau kuma nake ton na fala ganin canji shima Umalun zan gaya
mata. Abu na gaba ki zauna da kowa lafiya, mu nan da kike gani ba wanda yake k'ullatarki kowa son ki yake, ke ki ke ganin kamal ina fifita Tadiya a kanki ko d'aya ba haka bane, Idan kin gyala halinki za mu zauna da ke k'alau. Allah ya take tiltyal da ke a
lfalmal muhammaduna manzan Allah." Murna da tsananin farin ciki ne yasa ta fara kwararar da hawaye tana furta "Nagode Didi Asma'u ki taya ni godiya." Murmushi Umma Asma'u take ta kuma k'walawa Hamda da take tsaye a bayan k'ofa kira. Farin ciki yasa Hamda t
ahowa a guje ta zube a gabansu tana sakin hawayen murna, bakinta ya kasa rufuwa wani kallo kawai takewa Ammin tana kallon hannayen da Ammin ta bud'e mata alamar ta taho, Ba tayi wani jinkiri ba ta fad'a cikin k'irjin da ta dad'e tana son jinta kwance a cik
insa tana kuka har mafarkin hakan take, cikin wata iriyar soyayya mai zafi Ammin ta rungumeta tsam a k'irjinta hawayen farin ciki yana zubar musu, tana jin kuma yarda zuciyoyinsu suke bugawa kusan lokaci d'aya. K'aunar nan ta tsakanin uwa da d'a ta taso ta
lullub'e zuk'atansu. Daidai Lokacin da Abbu da Hammad suka shigo kamar had'in baki farin cikinsu ya yawaita ganin Hamda rungume a jikin