Showing 126001 words to 129000 words out of 129261 words
raba lafiya abokina." Hammad ya saki murmushi kawai yana komawa b
akin gadon da kansa ya zira mata hijabinta har k'asa kafin ya ce "Taho mu tafi ko na Goya ki?" Ta girgiza kai kafin ta ce "Ka shirya goyo dai nan da three days ka san sabon amarci zan fara." Ya sunkuya yana lek'a fuskarta kafin ya ce "In ye amaryar ba, in
dai za'a jiyar da ni waccan harkar mai dad'in gaske ai kuwa zan yi goyo har da zani k'albeey ta." Ta saki murmushi had'e da mak'ale kafad'a "Ni wallahi sai na haihu laulayi fa nake." Hammad ya ware idonsa kafin ya ce "Ashe kuwa zan yi kwanan asibiti don ko
mai zai iya faruwa matuk'ar za ki min rowar abina bayan ga ni ga ki a gado d'aya tabbas a sume za'a kawo ni asibiti." Ta turo baki kafin ta ce "Na barwa Maman Khairi kai wallahi sai na haihu." Ya girgiza kai "Allah ya kaimu jibin idan na aikata miki wani a
bin da kan ki zaki kawo kan ki, Hajiyata."
★
𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍
✍
️
★
𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍
✍
️
★
ALKALAMIN JIKAR NASHE
📲
49.
*08033748387*
A cikin harabar 'Dan Borno family house ya yi parking, tana k'ok'arin fita ya yi saurin rik'e hannunta ba tar
e da jin kunyar su Sa'ada da suke baya ba, ganin hakan yasa suma da
Sauri Suka fice daga motar. Idanunsa ya shigar cikin nata sosai kafin ya ce "Remain 3 days dai a daina min rowar jikina." Da sauri ta janye hannun nata tana danna lock d'in motar ta fice,
ya bi bayanta da kallo yana sakin ajiyar zuciya Allah ne kad'ai ya san wahalar da yarinyar nan take ba shi. Kafin ya fito ya bi bayanta sai da ya ciji lab'b'ansa yana sakin murmushi.
A falo ta samu Didi a zaune kusa da KK da yake ta barcinsa cikin kwanciy
ar hankali, da alama ya da'de bai samu barcin irin haka ba, za ta yi magana Didin ta yi saurin saka yatsa a lab'b'anta alamar ta yi shiru, Hamda ta saki ajiyar zuciya tana bin bayan y'an uwanta su Sa'ada da suka shige cikin d'aki. Sai dai kafin ta kai 'dak
i ta jiyo atishawar KK da sauri ta jiyo shima Hammad daidai lokacin suka shigo da Kamla da Abulkhairi. Gabansa ne ya fa'di ganin KK 'din kamar mara lafiya ya shiga cikin sanyin jiki kafin Didi ta ja tsaki ta ce "Kun tashe shi hankalinku ya kwanta, haba ni
ban tab'a ganin jaraba irin wannan ba, kai mai ma ya shigo da kai nan?" Kk ya mik'e yana murmushi hannayensa rik'e da kansa da ya ji yana 'Dan sara masa ka'dan ya ce "Ki barsu Didi, ai na ma 'Dan samu sauk'i dama ciwon kaine ya matsa min." Ya zuba idanunsa
akan Hamda da ya ganta kamar mara lafiya ya ce da Hammad "Me ya faru da iyalinnaka na ganta so weak haka?" Tsagal Didi ta yi kafin ta ce "Me zai sameta banda ta sake kwasowa kanta ciki don tsiya irin ta Hamda sai da na ce kada ta sake ta saurari yaron nan
sai an danganata da 'dakin miji amma ta yi burus da ni ta nuna ban isa ba, ai ga shi nan ya kai ki ya baro za'a yi taron biki da ciki, dama idan za ki yi Amanki don Allah Hamda ki taimakeni kada ki yi shi kusa da ni." Kunyar duniya ta gama kama Hamda bata
san sanda ta mik'e tana hawaye ba ta shige 'daki KK dariya ya yi kawai yana bin cup 'din kunun da Didi take mik'a masa "Maza ka sha kunun tsamiya ne zaka samu afuwa in sha Allah." Gefe guda Kuma peppe soup ne na naman rago ta masa mai yaji mai yawa ganin
kamar mura yake. Sosai ya ji da'din kunun ya yi murna da shigowarsa cikin rayuwar su Didi ga shi yanzu ita yake gani matsayin mahaifiyarsa.
_____________________
Sosai babban hall 'din dinnerr ya cika kana ganin wajen zaka san Naira ta ci k'aniyarta.
Hamda da yayyanta ba k'aramin kyau suka yi ba, cikin tsadadden lace 'dinsu sea blue, Dinner ce ta mata zalla ba maza ko masu 'daukan hoto mata ne zalla kamar yarda KK da Abbu suka zartar ba sa son
caku'de'deniya tsakanin maza da mata sun kiyaye dokokin ub
angiji k'warai da gaske.
Yana mota yana jiranta kamar yarda ya yi alk'awarin a yau zai zarce da ita gidansa ba sai gobe ba kamar yarda aka tsara. Ya gaji da wa'dannan bidi'oin ba kuma zai tsaya sai wani gayyar y'an kai amarya sun kai masa matarsa ba, da
kansa zai kaita har gidanta, sai dai su shafa su ji ba amarya. K'amshi kawai yake zabgawa daidai lokacin da Ya ganta sun taho tare da Sa'ada kana ganinta ka san a galabaice take don da kyar ma take tafiya sosai take buk'atar hutu. Hannu yasa ya bu'de mata
gaban motar kafin ya kalli Sa'ada murya ba wasa ya ce "Please Sa'ada we need privacy ki koma motar su Munira." Sa'ada ta waro ido tana kallonsa ya 'd'aga mata gira cike da son tabbatar mata. Murmushi kawai ta saki ta juya shi Kuma ya shige motarsa.
Kyan d
a ta yi ne yake sake jan idanunsa yake kallonta yana sakin ajiyar zuciya yana k'iyasta da mai zai kwatanta yarda yake sonta a zuciyarsa. Da sauri ya ja motar ganin tana shirin kuka yana fara tafiya wani barci mai nauyi ya 'dauketa ya saki murmushi a hankal
i ya furta "Ki farka ki ganki a gadonki na gidan ki na aure haba wannan gantalewar ta yi yawa." Ya fa'da Yana shafa kumatunta masu sulb'i da wadataccen taushi. Hannun ta ta sa ta rik'e masa hannu ba tare da ta sani ba saboda barcin da yake idonta.
Bai tsa
ya ko ina ba sai a harabar katafaren gidansa da KK ya mallaka masa gari guda mai tsari da zubi irin na k'asar waje. Wani abu kawai ya danna a hannunsa mai kama da mabud'in mota kyakykyawan gate 'din ya bu'de shi kuma ya danna hancin motar ciki, yana bin ha
rabar wajen da kallo da k'amshin damuna da na bishiyoyin wajen suka gama hancinsa ya zuk'i k'amshi yana sakin murmushi ha'de da jaddada godiyarsa ga Allah mamallakin kowa da komai, mai ikon canja komai a duk lokacin da ya so kuma ya ga dama.
Tsayar da mot
ar bai saka ta farka daga nauyayyan barcin da ya yi awon gaba da ita ba, ya bi jikinta da kallo yana sakin murmushi musamman ganin bak'in hadarin da ya lullb'e sararin samaniya. Da kansa ya 'dauketa cak, kasancewar a gajiye take ya sa 'daukan ya mata da'di
ba tare da ta farka ba ta sake narke wa a faffa'dan k'irjinsa tana zuk'ar k'amshin turarensa da take jin sa tamkar a mafarki. Bai tsaya a ko ina ba sai da ya mata masauki a kan faffa'dar kujerar three seater da take parlourn. Sai sannan ta ware idonta a k
ansa, da sauri kuma ta mik'e tana dube-duben inda ya kawota. Tsararren falon da ya 'dau black tiles ta dinga bi da kallo kafin ta sauke ganinsa a kanta ciki kasalalliyar murya ta ce "Ina ne nan?" Murmushi yake saki yana bin ta da nasa idanun kafin ya ce "G
idanki na kawo ki mana." A firgice ta mik'e tsaye ta ce "Gida na kuma? Me yasa ina y'an kai amaryar?" Ya zare babbar rigar da ta bi ta addabeshi kasancewarsa ba mai son manyan kaya ba ya ce "Sun tafi tun kina barci." Bata yarda da maganarsa ba don kuwa ba
yau aka yi za'a kawota gidan ta ba don haka murya a raunane ta ce "Please Y. Hammad ka mayar da ni gida kafin ka sake jawo min maganar Didi dama ban tsallake wannan da ka jawo min ba kullum sai ta min gori a cikin mutane balle kuma ta ji da kaina na kawo k
aina gidan miji ai wallahi ta samu na yi." Bata ankara ba ta ji ya janyota jikinsa cikin wani irin lamari ya dinga gigita tunaninta har ya samu bakin nata ya yi tsit. Ta shiga amsar duk wasu sak'onni da yake aika mata ba tare da ta shirya hakan ba, tsawon
lokaci yana aika mata da wasu irin zafafan romance kafin ya sake ta yana mayar da ajiyar numfashi. Cak ya mik'ar da ita "Mu je mu yi Sallah K'albeey wannan daren bana son saurarar kowacce k'aramar magana ina son in nuna miki irin tanadin da na miki, ki dai
na min maganar
wannan magananniyar tsohuwar ta da'de ba ta yi surutunba b'acin ranta ba abinda zai ja miki kamar yarda nawa b'acin ran zai kai ki wuta." Da kansa ya kaita toilet ya ha'da mata ruwan 'dimi mai zafi so yake ta wargaje duk wata gajiyar biki da
ta kwaso kafin ya sake saka mata wata sabuwar gajiyar. Ta ji da'din ruwan sosai don tunda ta shige bathtub 'din ta samu wata irin gamsashshiyar nutsuwa tana bin toilet 'din da ya ji kayan alafarma da kallo komai black and white, ta shiga wanke dukka sassa
n jikinta kafin ta fito.
Tuni ya fito mata da wata Nighty gown ta alfarma da Ammi ta sa aka saka mata a wardrop wani irin k'amshi kayan suke fitarwa da ya ja hankalinsa har bai san sanda ya cafko rigar ba yana shinshina k'amshin turaren da yake sake birki
ta masa nutsuwarsa da kyar ya samu shima ya tafi na sa 'dakin don yin nasa wankan. Bayan ya shiga kitchen ya saka kaza a micro oven don ta 'dima ma.
Sai da ta sake turare gashinta da ha'din mutanen jordan gashin ya dinga ba da wani irin k'amshi kafin t
a janyo rigar ta saka, ita kanta ganin yanayin rigar a jikinta sai da ta ji wata irin kunya ta rufeta ga shi sai da Ammi ta mata garga'di akan dole ta saka rigar. Jin motsinsa ya sa da sauri ta zumbula dogon hijabinta na sallah kafin ta zauna ta takure a g
efen gadon kamar wata sabuwar amarya.
Tray 'din hannunsa ya ajiye mai 'dauke da Laban Almara'i na k'asar Saudia gefe guda kuma dabino ne na ajwa a cike a wani 'Dan bowl sai kazarsa da ya na'deta a wani tray daban. Bai bi ta kanta ba don ya tabbata idan ya
zare hijab 'dinnan ba zai iya tsayawa ya gudanar da Sallah a nutse ba, k'arshenta ma sallahr ta shiriri ce. Ya shimfid'a sallaya ya juyo yana kama hannunta murya can k'asa ya ce "Tashi Mu yi Sallah." Jikinta ba k'wari ta mik'e ta tsaya a gefensa suka kabb
ara Sallah.
************
Tun ana saka ran dawowar Hamda har hankula suka fara tashi ganin har lokacin ba labarinsu. Didi sai Addu'a take ja dafatan Allah yasa lafiya suke.
Sa'ada ce ta fito daga 'd'aki jin cigiyar ta yi yawa yasa ta kallesh ta ce "K'
alau fa su ke Y. Hammad da kansa ya je ya d'auketa amma ban san ina suka je ba." Didi ta 'dago tana mata wani irin kallo kafin ranta a b'ace ta ce "Kan Uba! Wannan 'da akwai jarababbe bayan ya 'dirka mata cikin ma har yanzu bai mayar da maitarsa ba sai ya
sake 'dauketa...."
Jikar Nashe ce
✍
🏽
✍
🏽
******************************
***** ALHAMDULILLAH*****
********MURFI**********
Komai ya yi farko yana da k'arshe banda ikon Allah. Ina godiya k'warai da had'in kan da kuka bani Ubangiji ya saka muku da alja
nna, masoya mabiya YA ABIN YAKE?
Na sadaukar da littafin nan kacokam da mabiya na group 'din Jikar Nashe Real Fans. Sai Allah ya had'amu In Sha Allah a cikin sabon littafina bayan sallah idan muna da yawan rai. Saboda watannin da za su shiga watanni ne m
asu alfarma da bai kamata bawa ya shagalta da abubuwan duniya ba, mu dage y'an uwa wajen ribatar watannin na masu alfarma. Bissalam. Jikar Nashe ke muku fatan alheri.
🙏😊😊😊
Ba wanda ya bi ta kan Didi illa 'daukacin mutanen wajen mamakin Hammad ya kusa
sumar da su a tsaye. Nanna jikinta ne ya yi la'asar ta fara rok'on Allah a ranta akan Allah yasa dai Hammad ya zamo mai adalci a tsakaninsu, saboda ayyukansa muraran suke nuna tsagwaron son da yake wa Hamda. Mahmah Sadiya ma a tsoracen take itama fatan ta
'daya kada soyayyar Hamda ta rufewa Hammad ido ya kasa kwatanta adalci kamar yarda mahaifinsa ya zama, duk da dai yanzu komai ya daidaita yana k'ok'arin gaske wajen kamanta adalcin sab'anin lokutan baya da suka shu'de, ga shi tana ganin nutsuwa da tarin l
adabi a wajen Hamdan ta nan kam bata da matsala da surikan nata shi yasa itama ta 'daukesu 'daya take jin su kamar y'ay'an cikinta. Ammi kuwa farin ciki ne ya lullub'eta ba don komai ba sai don ko anan aka tsaya Hammad ya nunawa duniya tsananin son da yake
wa Hamda tana fatan kuma hakan ta 'dore har abada.
*******
Lokacin da can a gidan ake cecekuce su b'angaren Hammad da Hamda ma ba su san me duniya take ciki ba a wannan lokacin wata iriyar soyayya suke yi cike da tsananin son juna da 'doki game da zakwa
'di kai kace first night 'dinsu. Hammad a gigice yake sosai jin yarda Hamdan ta sake canja masa bai san sanda ya dinga furta mata wasu irin kalamai na daraja wa da suke barazanar tarwatsa zuciyarta, saboda yarda ta dinga jin kanta yana girma ta tabbata a w
annan daren da kyar za'a samu wata mace mai sa'a irin tata. TA MUSU ZARRA. Sai mu ce Hamda Allah ya bada zaman lafiya.
_______________
Watanni sun shud'e kamar yarda kwanaki suka dinga tafiya suna zama satittika haka sati suka dinga zama watanni har zu
wa sanda Allah ya kawo Haihuwar Hamda. Gaba 'daya familyn 'dan Borno sun yi murna da haihuwar da aka yi musu. KK jinsa yake a wata irin duniya saboda
tsananin farin ciki. Yarinya kyakykyawar gaske mai kama da Uwa da Ubanta duka saboda yarda kamannin nata s
uka yi caku'de'diniya sai Kyan nata ya zama mai ban k'aye.
Didi ce a tare da ita a asibitin sai Mahmah da itama ta kasa tsare duk da Didi na ta mata shagub'e amma Mahmah ta yi funfurus kamar bata gane da ita take ba. Wata irin soyayya takewa Hamda musamma
n yarda ta kwantar da kanta take yi wa Nanna biyayya Duk wannan kishin ya ragu sai dai 'dan abinda ba za'a rasa ba. Yanzun ma da Nanna da yaran Nannan duka suna asibitin da su ake jegon Ammi kuwa bata zo ba, ta yi kara da alkunya. Hakan yasa lokacin da wat
a aminiyar Ammin ta zo bayan ta gaida Didi ta ce "Saknan bata zo ba ne Hajiya Didi?" Didi an tab'o mata inda take so ta gyara zama tana mele baki idanunta akan Sadiya ta ce "Ina za ki ga Sakna anan, ita da ba 'digon jinin fulani ma a jikinta ta yi kara da
alkuny duk da Hamdan ba 'd'iyar fari bace, wasu fulanin dai ai suna jawa fulani tsiya wallahi Allah dai ya yiwa Sakna Albarka, kuma ina nan in ga wanda zai canjawa yarinyar nan suna daga nawa da na ra'da mata, mutane ba Allah a ransu y'ar kujerar makka dai
ake wa to kuwa bana ko Kamalu ya bayar da kujerar sai na hana, naga dai mutum da ba son auren ya ke ba." Mahmah murmushi kawai take tana mamakin Didi haka kawai sai a tafi a barta daga ita sai Hamda Lauratu na wajen aiki sai yamma take zuwa ta tafi da saf
e ita kuma sai ta fansheta tunda Saknan ba wasu y'an uwa ba ne da ita anan. Ita kuwa Umma Asma sun koma k'asar su can inda suke dama hutu suka zo. Turo k'ofar da Hammad ya yi ne yasa Didi yin shiru don lallab'ashi take kada ya ce ya canja takwarar da ya ma
ta saboda ta san yarda baya son ko ka'dan a tab'a Sadiya. Idanunsa a cikin na Hamda da take bawa Babyn Nono hannunsa rik'e da na Kamla da Khairi, ya zauna a gefen gadon yana gaishesu 'd'aya bayan 'd'aya kafin ya juyo kan Didi ai kuwa tana washe baki ta ce
"Yauwa Hammadu ya kamata ka gayawa duniya sunan yarinyar nan." Hammad yana k'unshe dariya ya ce sunanta UMMA Asma mana. Wata zabura da Didi ta yi sai da kwanukan wajen suka tarwatse bata damu ba ta ce "Ai wallahi ka yi a banza ni zaka yaudara to ko Usmanu
Uban Umaru bai isa ba balle kai 'dan Umaru yarinya tilas sunana zata amsa ba fashi." "Tabbas kuwa Hajiya Didi" KK da yake shigowa ya sake tabbatr mata yana dariya don duk yana jin drammerr da ake yi ya ce "Hammad na fa lura ka raina min uwa zan maganinka y
arinya dai tabbas sunanta Hadizatul Kubra Didi ba, kuma ba wata inkiya da zamu mata Didi za mu dinga kiranta da shi don kada sunan ya b'ata." Didi ta ranga'da gu'da ta ce "Madalla da alherin ka gareni Kamalu D'an Kabiru jikin Mu'dallabi yaron albarka."
B
ayan fitar kowa daga 'dakin ya rage daga Hammad sai Hamdan ya k'arasa wajen ta ya zauna sosai a jikinta yana lek'en fuskar yarinya a kunne ya ra'dawa Hamda ba sunan Didin ne ake gudun sawa ba Allah yasa kada ta yiyo rigimar Didi da masifarta." Hamda ta sha
fa gefen kumatunsa tana murmushi kafin ta ce "In sha Allah komanta Halin Didi ba zata 'dauka jajirtacciyar mace mai son zumunci ibada ga kyauta Allah Ameen." Ya ja karan hancinta kafin ya ce "Jallah ya miki albarka ina jiran twins next year maza su ci suna
n Kamalu da Umarun Didi, Allah yasa Didin tana da rai a lokacin." Ya