Showing 75001 words to 78000 words out of 129261 words

Chapter 26 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

87

kuwa don in sake tunzira shi na ce "Wallahi ka ban mamaki, daga gwaji ta yaya kake zaton ni zan k'i ka? Alhali saboda kai na rabu da dangina da k'asata na zo nan inda ban san kowa ba. Na

tabbata yanzu Ummeey ta ji labari ba zata bari mu komawa auren mu ba, cewa zata yi na tattaro na taho. Haka kaima idan Didi ta ji labarin shikkenan ta samu abinda take so." A gigice Umar ya rungumeni k'am a kunne ya dinga rad'a min "Me yasa kika min irin

wannan wasan Sakna? A lokacin da kika san ba zan iya controlling kaina

ba, kin san rashin kusantarki babbar masifa ce a wajena, please ba wanda za mu gayawa ya zama sirri a tsakaninmu, idan kin gama idda a sirrance zan d'aura miki aure da mutumin da na tab

bata a ranar ma zai iya sakin ki na mayar da aurenmu ba tare da kowa ya sani ba." Na yi d'an jim har farincikin da yake cikin zuciyata ya bayyana b'aro-b'aro akan fuskata na k'ank'ameshi sosai a kunne na dinga rad'a masa na amince ya zama sirri a tsakaninm

u amma ranar girkina ya zaka yi?" Ya runtse idanunsa yana dafe k'irjinsa kafin ya ce "Dole zan nisanci garin nan har ki ka gama idda, ina dawowa a d'aura mana aure, don ba zan iya controlling kaina idan ina ganinki ba Allah ya sani. Auren kisan wuta ba bu

kyau amma da mu aikata Zina gwara mu aikata waccan b'arnar. Allah ka yafe mana don girman zatinka." Ya fad'a yana saka kansa a cikin tafukan hannayena sai ga shi na ji yana wani irin gigitaccen kuka, mai tada hankali. Kafin ya mik'e cikin kasala da mutuwar

jiki ya fice daga d'akin yana waiwayena. Nima hawayen ne suka zubo min masu zafin gaske sai na ji kamar ban kyauta ba dama ban aikata son zuciyata ba, amma buk'ata ta da haihuwar d'a namiji shine ya janyo komai. In dai Zan samu cikar muradina to komai na

yi gani nake dai-dai ne a lokacin.

Daga ranar muka shiga wata irin rayuwa ni da Umar, ya zama ba shi da walwala ko kad'an. Sannan ya shiga neman visa ba ji ba gani. Idan ba ku manta ba shine lokacin da ya tafi Dubai ya yi zaman sa a can sai dai ya aiko d

a kaya a siyar masa idan an had'a kud'in a aika masa. Tsawon watansa hud'u a can.

Ni kuma a lokacin ni da Kady muka shiga farautar mai gadi duk da jira nake na gama idda sannan na bayyana masa k'udirina. Amma fa ina yawan yi masa d'inki sannan na dinga sa

nar da shi bana son k'azanta. Don haka ya rage k'azantar.

Daren da na gama idda, a daren na kira shi na bijiro masa da buk'ata daga ni sai Kady a zaune a falon har rufe k'ofa muka yi." Tsawon lokaci ya d'auka shiru kafin ya d'ago ya yi min kallon cikin i

do. Kady ta kafeshi da ido cikin tsare gira ta ce Saduwa d'aya za kuyi ka zabga mata saki uku bayan mun tabbatar da cikinka a jiKinta." Na gyara zama kafin nima na d'ora da cewa " Tun bayan da ka sanar min, yawaitar maza a zuri'arku, na tabbata Allah ne ya

kawo min kai don na samu namijin da nake so, amma fa ta hanyar aure ba hanyar zina ba." Kady ta sake tsareshi da ido kafin ta ce "A gobe muke so komai ya wakana saboda nan da sati biyu Alhajin zai dawo, ban dama an rufe dubai d'in da tuni a yau zai dawo a

mayar musu da aurensu. Abinda muke so kafin ya dawo ya zama da tayin cikin namiji a mahaifarta, inda da zarar ya bijiro mata da maganar auren kisan wuta zata sanar da shi ai da cikinsa a jikinta, ka ga ba aure kenan har sai bayan ta haife. Amma fa duniya

zata d'auka yes cikinsa ne. Tunda ba kowa ya san da sakin ba, kai ma kuma ya zama sirri a wajenka, don bayyanar sirrin kamar fansar da ranka ne, kuma tunda muka gaya maka sirrin mu ya zama dole ka yi mana abinda muke so. Sannan albishir d'in da zan maka ba

yan kwasar ganimar jikin tsaleleliyar mace akwai kyautar miliyan biyu cus da zamu maka ka tattara ka koma garinku." Ya share zufar goshinsa kafin ya d'an saki murmushi ya tabbatar mana da ya amince. A daren ranar Kady da ni da wasu maza a wani k'auyen k'ar

amar hukumar k'araye aka d'aura mana aure. Sai da muka amshi sunayen shaidun saboda ko nan gaba magana za ta tashi sannan muka taho.

Na biya da shi yarda zai dinga zuwa gyaran kai da hak'oransa. Kady sai tsiya take min.

Bayan kwana biyu Buzu ya dawo ta

s da shi. A kuma lokacin ne aka yi wata mutuwa a Gwarzo duk gidan suka tattara suka tafi. Na had'a musu har yara na suka tafi da su.

Wannan damar na samu na kira buzu mai gadi na muka keb'ance a d'akina. Bayan na saka shi ya datse gate d'in gidan. Sai dai

a rashin sani da tsautsayi sai ga Hammad ya dawo ranar kamar an turo shi sabida ba ya dawowa daga kasuwa da rana. Shi kuma ya riskemu a d'akin wanda ban san dalilin da ya kai shi d'akina a ranar ba. Sai ganinsa kawai muka yi, a lokacin ya turo k'ofar d'aki

n. Cikin gigitaccen yanayi ya saki ihu, ihun da yaja hankalinmu muka mik'e a firgice ina jan bargo. Buzu yana neman hanyar guduwa....

Jikar Nashe taku ce





















🙏

ALKALAMIN JIKAR NASHE

YA ABIN YAKE?



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍





08033748387.

33.

D

a sauri Hammad ya fice jikinsa na rawa. Na mik'e ni ma da sauri ina nunawa buzu hanya. Cikin rawar jiki ya ce "Hajiya kada ya illatani." Cikin masifa na ce masa "Ka wuce ka tafi, ba ni abinda zai maka zan yi maganinsa." Ya fice da sauri jikinsa na rawa a m

atuk'ar tsorace yake.

Na kasa samun nutsuwa bayan na yi wanka na kira Kady da sauri cikin matuk'ar damuwa ba ce mata an yanka ta tashi, Hammad dai babban d'an gidannan ya kama mu dumu-dumu da Buzu." Cikin k'arami Kady ta ce "Innalillahi, ya aka yi wannan

katob'ara don Allah?" Na runtse idona kafin na ce "Tsautsayi, ni dai ki gaya min mafita." Ta ja ajiyar numfashi kafin ta ce "Shikkenan, akwai mafita amma dole sai mun saka Hammad ya shiga d'akin ki. Mun d'ana masa tarko mai zafi tukun na inda tilas ma ya

ja bakinsa ya tsuke, idan ba haka ba tabbas kina ruwa." Na amince da shawararta, kuma na karb'eta d'ari bisa d'ari tunda ba ni da wata mafita da ta zarce wannan.

A ranar muka d'ana masa wannan tarkon, na isa d'akinsa da yake Boys Quaters, yana zaune

hanna

yensa dafe da k'uncinsa, na kira sunansa ya k'i ya d'ago ya kalleni illa had'e fuska da ya yi, kansa a k'asa. "Ka taso mu je akwai bayanin da zan maka." Funfurunfus yaron nan ya min banza. Ko kallona bai yi ba.

Jikina a sanyaye na bar b'angaren nasa, ina

mamakin kafiya da taurin kai irin nasa, duk da lallashinsa da na yi. Ina zuwa na cewa Kady "To ya k'i zuwa, don ba kiga ba ko kallona bai yi ba, balle ya san ina wajen, kady ina tsoron kada yaron nan ya tona min asiri." Ranta a b'ace ta ce "Tunda mun biyo

masa ta sauk'i ya k'i, dole mu bi da shi ta zafi, kin ganni nan dama na shirya masa idan har ya yi kafiya, kuma kin tabbatar min ba kowa a gidannan bari na kira yaran da za su kawo shi nan ko bai shirya ba." Ta d'auko wayarta tana kiran yaran da ta sabawa

sawa su yi mata aiki. "Ku zo yanzun nan, aikin nan na ga dole sai da ku." Ta katse wayar tana cewa "Ba su mintuna goma, za su kawo shi nan ta k'arfin tuwo, zai gane kafiyarsa ba ta da amfani."

Muna zaune kuwa suka yi mata waya sun zo, da kaina na je na bu

d'e musu gate d'in, suka shigo kasancewar Buzu yana d'aki cikin tashin hankali, ya yi k'ok'arin ya tafi kuma na hanashi, na tabbatar masa ba abinda zai faru.

Su biyu ne, k'arfafa da su. Na kai su har d'akin Hammad. Duk da gani na da ya yi da su bai saka z

uciyarsa ta rusuna ba, sai ma wani irin hucin b'acin rai da yake yi, yana jifana da kallon tsana. Da naga ba zai tafi ta dad'i ba da kaina na ce su d'aukeshi ko a kaine su kai shi d'aki na.

Haka kuwa aka yi, aka shimfid'e shi a gadona, su da kansu suka ci

re masa kaya, aka kuma d'aukeshi a haka yarda ya ke akan gado bayan sun shak'a masa abinda ya saka shi suman dole.

Bayan farfad'owarsa muka saka shi a gaba ni da Kady, anan nake sanar masa Ba zina nake ba da aurena da maigadi. Na ba shi labari tas tare da

nuna masa vedion d'auren auren a camera Kady. Fuskata a d'aure bayan na gama gaya masa na ce "Kuma ka ga idan wannan maganar ta fito, to tabbas zan alak'antaka da wanda yayi min fyad'e har cikin d'akina. Na nuna masa hotunan da muka d'aukeshi rabin jikin

sa akan cinyata. Ya tsorata sosai da ganin hoton ya dinga jifana da wani irin kallo na tsana muraran kafin mu ga wasu k'walla sun zubo masa idanunsa suka yi jajazur. Ya dinga fitar da wani irin huci kafin ya mik'e ya fice. Wannan shine dalilin da yasa bai

fad'a ba ya ja bakinsa ya tsuke, sai dai sam ba ya yarda mu had'a inuwa d'aya da shi, ya tsaneni sosai kuma ya zama silent ya dinga wasu irin abubuwa kafin a tattara shi ya bar k'asar gaba d'aya. Lokacin Hamda tana da shekara biyu.

Bayan faruwar wannan a

bin, da sati biyu Umar ya dawo da zakwad'insa ya shigo d'akina sai dai murnarsa ta koma ciki bayan na sanar da shi d'an tayin cikin da yake kwance a marata. Ya d'ago yana kallona a firgice cikin sagewar gwiwa ya ce "Yanzu har sai kin haife cikin nan kafin

a samu wani ku yi auren kisan wuta a sirrance a mayar da auren mu, anya kuwa zan iya jurewa?" Ya fad'a hankali a tashe..

Na raunana ganina a kansa sosai, bisa son tilas na nuna masa ni d'in ma a cikin matsananciyar kewarsa nake "Ka yi hak'uri Umar, kamar

yau ne zaka ga na haife cikin nan mun komawa auren

mu cikin yardar ubangiji." Ya girgiza kai cike da sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya ce "Shikkenan, Allah ya raba lafiya, yasa wannan karan ki haifi namiji tunda na san shine burin zuciyarki." Na amsa

da ameen cike da farin cikin jin addu'ar da nake so daga bakunan mutane masu albarka.

Daga lokacin na shiga rainon cikina, duk da kullum Umar a lissafe yake da watannin cikin, ganin yana son ya titseyeni akan ya kamata cikin ya isa watanni bakwai amma ya

ga baya girma." Hankalina tashe na samu Kady da zancen ita ta ba ni shawarar mu samu wani likitan mu siyeshi ya gillara masa k'aryar cewa akwai matsalar da tasa dole watannin cikin suke komawa baya, don haka zai iya k'ara watanni uku ko fi akan lokacin ha

ihuwarsa. Likitan ya tsara shi sosai ta yarda ba ta inda zai yi ya musa tunda ba aikinsa ba ne. Kady duk da haka ba ta amince ba, sai da tasa muka dangana gidan Malamai ta sa aka rufe bakin Umar akan zancen cikin, sannan aka rufe bakin Hammad ta yarda duk

sanda ya tashi tona asiri zai ji ya kasa. Na amince da shawararta da tunanin duk duniya ba ni da aminiyar da ta zarce Kady, a dai wannan lokacin.

Tun cikin yana wata uku na je scanning, sai dai likita ya tabbatar min bai zama lallai a wannan lokacin a ga

abinda Zan haifa ba, ma'ana jinsin mace ko namiji, na bari ya shiga wata na biyar tukun.

Munafukin likita shi ya dinga shirga min k'aryar namiji zan haifa tun bayan da yaga zuciyata ta d'anfaru da son haihuwar namijin. Na dinga shirye-shirye na sakankan

ce da hakan a zuciyata. Har mafarki nake da suffar jariri namiji mai kyau da zan haifa.

Abin haushi, mamaki da takaici, ranar haihuwa da na tashi sai na haifi mace, duk da Didi ta b'oye min a sanda aka yi haihuwar. Sai cikin dare lokacin na farka daga bar

ci ta isheni da kuka na yi tunanin pampers ne ya dameshi, ina zare masa na ga mace ce, Allah ne shaida ta k'iris ya rage ban yi cilli da ita ba. Zuciyata ta tunzira ban san sanda na saki wani irin kuka ba. Hankalina tashe na tafi da ita wajen Didi don bana

jin zan shayar da ita.

Daga wannan ranar na tsani mai gadi na ji babu amfanin zamansa a gidan tunda ya kasa ba ni farin cikin raina, tabbas idan ina ganinshi wata rana zuciyata zata iya fashewa musamman idan ina tuno yarda muka had'a jiki da shi. Sai na

ji na tsani kaina. A kashegarin ranar da na haihu ne na samu Umar da zancen mai zai hana a sirrance mu yi auren da Buzu sai ya sake ni a take a wajen ko kashegari idan ya so sai a sallameshi ya koma garinsu da alheri mai tarin yawa.

Abbu kuwa babu ja ya

amince da buk'atata, dama yana tunananin wanda zai aura min a sirrance kuma ya amince ya sakeni ba tare da duniya ta ji ba.

Suka keb'e da Buzu ya sanar da shi k'udirinsa, Buzu ba wani jainja ya amince suka wuce masallachi na can wani gari aka sake mayar

da auren mu da buzu, duk da dama da aurensa a kaina.

Kashegari kuma ya dank'ara min saki Umar ya sallameshi ya tafi ba mu sake ganinsa ba, kuma ba mu san inda za'a same shi ba, abu d'aya na sani ya ce min shi mutumin Ethiopia ne wato k'asar Habasha. Ina ro

k'onku don girman zatin Allah ga duk wanda ya ji haushi ya yafe min sharrin zuciya ne da na shaid'an."

Ta na gama bada labarin ta saka wani irin kuka. Duk jikin mutanen wajen saki ya yi, tsananin mamakin cukurkud'dden lamarin ya sa suka gaza cewa komai ill

a sakin ajiyar zuciya. Hamda kuwa kuka take sosai kamar ranta zai fice, duk da ta ji dad'i da ya kasance ita d'in halastacciya y'a ce ba shegiya ba kamar yarda take tunani. Amma tunaninta ya fi karkata akan ta yaya zata ga mahaifinta, mutumin da a labarin

da Ummanta take bata bata ji ta anbaci sunansa ba, sai kiransa da Buzu da ta ji ana yi, buzaye nawa ne a Habasha in dai haka ne? Didi da ranta ya gama dugunzuma da ta'ajibin labarin Sakna ta dinga dubanta tana jijjiga kai, ta kasa furta furucin bakinta, l

amarin ba k'aramin girgizata ya yi ba, wacce irin soyayya ce ta rufewa Umar d'inta ido har haka? Da ya kasa bayyana mata ya tab'a sakin Sakna tsahon wannan lokacin. Ji take tamkar ta shak'o shi ta yi ta jibga, ta fi jin haushinsa fiye da Sakina da dama bat

a amince da tsarin tarbiyyarta ba, idan ban da haka ta ya za'a yi ace, kai zaka zab'a ma kanka abinda ka ke so ka haifa sai kace a lokacin jaliyya. Hammad ma ya shiga jerin mutanen da Didi take jin haushi sosai ta yaya zai b'oye wannan babban abu haka? Duk

da dai da yarinta a lokacin amma me yasa da ya girma bai fito ya bayyana musu gaskiyar lamari ba, ai akwai hanyoyin da za'a gane tabbas Hamda ba y'arsa ba ce, ya ja bakinsa ya tsuke ya barsu suna bulayi cikin duhu.

Fuskar Didi a had'e sosai ta zubawa Nan

na da take ta kuka a wajen ido, duk da ta bi ta cika wajen da kwakwazon kukanta, cikin takaici Didi ta ce "Ke da halla yi mana shilu, mu ji da abinda ya damemu ke me ye ma na ki a ciki da za ki zauna ki b'are mana baki kina kuka? Wad'anda kuka ya kama ai b

ayan mu ne, da aka mayal y'an itka ba a damu da mu san komai a cikin gidan ba, kai Umalu ai te ka ja Takina ku yi gaba, a je a cigaba da Toyayya tunda Takina ta fiye maka ni Uwalka da na kawo ka duniya. Allah na gode maka da ka nuna min wannan lana tun kaf

in mutuwata. Ga dai Takina ga kuma tsiyal da ta shuka maka k'alshen Toyayya kenan, wanda na tabbata ba na haufi hak'kin Tadiya ne tun yanzu ubangiji ya fara mata takayya. Kai kuma Hammad ba abinda zan ce maka te Allah ubangiji ya yi maka abinda ka yi mana

da ni da Uwalka, ka b'oye mana abinda ya kamata ace tun tuni mun tani ka bar mu muna ta yawon bin malamai muna a yi maka addu'a ashe kai lamalin da yake filgita ka kenan? Kai ka jiyo ka je kai da halinka."

Ta juya ta kalli Ammi da take ta kuka kamar ranta

da zai fita, musamman ganin har a lokacin Umar bai ce komaiba, tun da ya d'ago kai ya kalleta da jajayen idanunsa sau d'aya, ba bu kuma abinda ta gani a cikin kallon sai tsantsar tsana da bata tab'a gani a cikin idanunsa ba, tsawon zamansu a matsayin ma'a

urata.

Didi ta yi tsaki "Kuka ma ai yanzu ki ka fala shi Takina? Kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login