Showing 123001 words to 126000 words out of 129261 words

Chapter 42 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

92

ne, to za dai mu gani idan ita kuma Nannan zata yi sake a k'wace mata miji, don wasu matan haka suke zama sakarka

ru idan an musu kishiya sai kishi ya rufe musu ido su rasa kula da mijin har wacce ta shigo ta yi wuf ta mallake musu shi. Don haka Mata mu dage, Soyayya fa ba k'arya ba ce kuma So ba ya tsufa kullum ki dinga updating soyayyarki a zuciyar mijinki ta yarda

ko ya auro wata zai raina ta ta kulawar har ki ji yana fad'in me ma ya kai shi auren?

😀

)

Shigowarsu Kamla ne ya sa ta bud'e idonta da suka mata nauyi ta zubesu a kansu, cikin farin ciki ta dinga ware musu hannayenta tana hugging d'insu d'aya bayan d'aya.

Musamman Kamla da tun lokutan baya take jin tana mata wata iriyar k'auna da bata san dalilinta ba, ashe ita d'in jininta ce. Sosai ta rungume ta tana shafa kanta "Welcome Iyalan Birmingham ya kuka baro garin naku?" Khairi da bata cika son magana ba murmus

hi ta yi tana shafa gefen kumatunta "Anty Hamda are you married? Da gaske ne Daddy ne Husband d'inki." Hamda ta lumshe ido zuciyar ta na tsoron amsawa Khairin bata sani ba ko ta taya uwarta kishi. Idanun Khairin cikin nata tana sakin murmushi ta ce "Am ver

y much Happy Anty Hamda ke da Daddy kun dace sosai perfect match." Ta fad'a tana rungumeta a gefen jikinta. Itama Hamdan rungumeta ta yi kafin Abul Khairi ya ce "And now is my turn, Anty Hamda and Kamla siblings ne da gaske haka Daddy ya ce mana, gobe Momm

yn Kamla zata zo gari from turkey." Tsit d'akin ya d'auka Hamda tana mamakin yarda yaran suka sake abinsu da alama duk Babansu ya zauna ya warware musu komai. Ta shafa kansu murya a sake ta ce "Allah ya yi muku albarka." Ta fad'a tana sakin ajiyar zuciya m

ai k'arfin gaske, da ta tafi da duk wani tsoronta da shakkar yarda yaran za su d'auketa idan sun ji maganar, suma murmushi suka saki zuk'atansu fal da murnar dawowarsu cikin ahalinsu gaba d'aya.

___________

Rashin sukunin zuciya ya haifar mata da zazzaf

an zazzab'i cikin dare ga haraswa da take yi akai-akai musamman abin ya had'u ya had'ar mata da rashin cin abinci sai ta galabaita sosai.

Tun Sa'ada na ganin kamar hakan ragwanci ne da lalaci har ta tabbatar da tabbatuwar ciwon. Ganin tana shirin shid'ewa

ya sa Sa'ada ta fita a kid'ime kiran su Didi. Duk da barci ne a idanunsu bai hana su tahowa da sauri ba. Suma ganin yarda yanayinta yake ya tashi hankalinsu da sauri suka shiga kiran Hammad don ya kawo musu agaji.

Shima a lokacin ba barci yake ba gaba d'

aya hankalinsa a tashe yake ga wata iriyar zafaffiyar sha'awarta da take neman kassara masa garkuwar jiki. Duk da ga Nanna a gefensa amma gaba d'aya ba tata yake ba, gangar jikinsa Hamda take muradi abin tamkar wani maganad'isu tabbas d'iyar Ammi ta yi gad

on Ammi abin a jininsu yake, kishi da irinsu kuwa akwai tashin hankali don kullum sababbi suke komawa dal da su da zarar miji ya d'an yi kwana biyu bai kusancesu ba sai ki ga sun koma sun rufe ruf kamar ma ba'a tab'a aikata komai da su ba, samun irinsu k'a

lilan ne a cikin mata, don haka da zarar mutum ya auri irinsu to fa kowace irin mace zai aura ba zai tab'a kwatanta ta da wannan matar tasa ba, ki dage ki zama irinsu y'ar uwa.

😀

Wayar ya kara a kunnensa kafin ya ji kwararaton Didi tana sanar da shi rash

in lafiyar Hamdan. Ai kafin ya k'arasa ji ya yi wurgi da wayar da sauri ya mik'e ya fice ba tare da ya amsa kiran da Nanna take masa ba. Gabansa ne kawai yake fad'uwa yana fatan kada wani abu ya samu Hamdan. Kafin ya isa sashen Didin kuwa ya saka mai gadi

ya bud'e masa k'ofa.

A tsakiyar gadon take zube, numfashinta yana fita sama-sama, wannan karan idanunsa rufewa ya yi ruf ya ma manta da wata Didi tsam ya rungume Hamdan a jikinsa yana manna mata kiss kafin

ya sunkuceta bayan ya zira mata dogon hijabi da s

auri yake furta "please Hamda bud'e idonki don Allah kada ki rufe..." wasu irin maganganu ya dinga furtawa da har ya bawa Umma Asma kunya. Didi kuwa bud'e baki kawai ta yi tana kallonsa rud'anin da take ciki game da ciwon Hamdan ya sa ta kasa furta ko da k

almar 'A' sai mayar da ajiyar zuciya kawai take.

Sosai asibitin suka yi iya bincikensu kafin su sanar da su cikin jikinta ne yake galabaitar da ita ga shi ta saka damuwa a ranta, tun a gaban likitan Didi ta fara furta "Subhanallahi, ciki kuma to a gidan

uban wa hakan ta faru?



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

YA ABIN YAKE?

PAGE 48.

*08033748387*

Yanzu fisabilillah yaron nan sai da ka bi yarinyar nan ka turmishe ka mata ciki? Ni dai ban tab'a ganin ja

rababbe irin ka ba wallahi Hammad. Allah yasa ba a gado na aka je aka aikata wannan ta'asar ba. Masifa!" Didi ta furta tana watsa masa kallo. Hamda kuwa wata irin kunya ce ta kamata da sauri ta lumshe ido tana jin kunyar duka mutanen wajen Tabbas Hammad ya

kaita ya baro yanzu kuma kowa ya san ta yarda ta je ta samo cikin. Didi ta k'arasa bakin gadon idanunta akan Hamdan ta ce "Munafuka bud'e idonki da kyau ki kalleni ashe kin san ciwon da kike yo ni da na san laulayin ciki ne da mai zai saka na rakoki da lo

kacin da ne dai da an saka miki wak'a a dandali ace kin samu ciki ba'a kaiki d'akin mijinki ba. Jarababbu ku dai ku je ku nanik'i miji ku samu ciki mhmmn za ki dawo gidan ki sameni." Ta juya ta fice tana ta sababi. Umma Asma dai dariyarta kawai take shek'a

wa ganin yarda Didi ta d'au lamarin.

_______________________

A zafafe ya mik'e a d'akin taron yana watsa idanunsa cikin nasu, idanun da suka kad'a suka yi jajur tamkar garwashi." Mutumin nan ya yaudaremu tsawon lokaci muna fama da yarda za mu kawar d

a shi a doron k'asa sai ga shi ya zo mana da wata maganar banza wai yana da zuri'a, to ya zama dole a wannan karan mu kawar da KK daga doron k'asa kafin mu bi ahalin nasa suma mu

murk'ushesu." Yarda yake maganar a hassale zai tabbatar maka abin ya dad'e ya

na ci masa tuwa a k'warya. D'aya daga cikinsu shima ya mik'e kafin ya ce "Ya zama dole kuwa Yaya, amma ta wacce hanya kake ganin za'a bi?" Ya ja ajiyar numfashi kafin ya ce "Duk da gidansa akwai security ya zama dole mu samu wata daga cikin y'an uwa ta kom

a gidan ta tare ta yarda za mu samu mu cimma burin mu kai tsaye, ko da ta hanyar gubar iska ne da za'a saka a d'akinsa da zarar ya shak'eta zai shek'a lahira ko kuma mu kashe duk wasu cameras na d'akinsa ta saka masa wuta a d'akin cikin dare....

Tsayuwa

rsa a gabansu shi ya bawa cikinsu damar sakin wani irin rugugin sauti na razana da kid'ima. Daga yanayin kallon da yake musu tabbaci ne na cewa ya ji duk manak'isar da suke shirin k'ulla masa. Murmushi kawai yake saki mai nuna tsananin takaicin kasancewars

u zuri'ar mahaifinsa. Idan wani ne ya gaya masa hakan zata iya faruwa a rayuwa zai iya k'aryatawa sai ga shi zahirin lamarin kacokam ya faru a kansa, y'an uwansa da ya sani wanda suke uba d'aya su suke neman rayuwarsa bayan sun gama neman ta y'ay'an cikins

a duk akan wani banzan lamari wai dukiya da take k'arewa a duniya duk kud'in mutum bai isa ya tafi da shi lahira ba sai dai ya tafi da aikin ladan da ya yi ta sanadiyyar kud'in. Ya lumshe idonsa wasu hawayen bak'in ciki suka shiga zubo masa, bai san me yas

a y'an uwansa suke k'insa har haka ba, duk da tarin kyautatwar da yake musu ba wanda ba ya cin moriyar arzikinsa mazansu da matansu, kai har ma da yaransu, akwai albashi da yake marasa k'arfin cikinsu duk wata ban da zakka da yake dunk'ulewa ya basu, hidim

ar biki shine kai komai ma shi d'in dai KK shine mai d'aukar kaso mafi tsoka a hidimar ahalin K. Mud'allab sai ga shi zuri'arsa ce ba sa so da shi kansa suke neman hanyar hallaka shi, anya kuwa ubangiji zai barsu da alahakin wannan bawa nasa, kaico wannan

zamanin da son zuciya ya yi bake-bake a zuk'atan al'umma. Kukan ya ke sosai kukan da ya karya zuk'atan tsirari daga cikinsu suka riski zuk'atansu a cikin tarin da na sani, kunya matsananciya ta yi musu dabaibayi a zuciyoyinsu suka fara tunanin ta yarda zuc

iyarsa ta dinga ingiza su da bin son zuciyar wasu daga cikinsu.

Lamarine mai girma a wajen KK don haka ya kasa furta musu komai illa jan sawayensa da ya yi ya fice daga bigiren da suke. Zuciya bata da k'ashi a yau duk hak'urinsa zuciyarsa ta karye ba ya

jin har abada zai sake dubansu da idanun rahma, bai tsanesu ba amma ya zama dole ya nisanci mu'amala da su, duk kuwa da yake musu zahirinsa da bad'ininsa Allah ne shaida amma tunda su sun kasa fuskantar haka ya zama dole ya bi da su ta hanyar da karatun ra

yuwa zai fahintar da su, shima d'an zamani ne mai kuma madafan iko tunda yana da kud'i ya tabbata ko k'ara zai kaisu shine a sama, amma ba zai aikata haka ba, ko bakomai suna amsa sunan mahaifinsa ne K. Mud'allab albarkacin wannan sunan da yake rab'e da na

su ba su cancanci tozarci ba, sai dai zai bar su da halinsu ta hanyar yanke duk wata alak'a da su. Alhamdulillah tunda yanzu yana da zuri'a yana kuma da Ahalin Didi da ya mayar da su tamkar nasa ahalin madallah da ubangiji buwayi gagara misali. Da kansa ya

fisgi motar da mugun speed ya bar harabar gidan, don dole escort na sa suka bi shi suma a guje, zuk'atansu cike da tunanin dalilin tashin hankalin da

Suka ga uban gidansu a ciki, fatansu dai ya zama komai lafiya.

Bai tsaya ko ina ba, sai a gaban Didi. Ci

kin tashin hankali ya shiga falon Didin. Idanunsa sun kad'a sun yi jajir ya zube gwuwoyinsa a gaban Didin ya dafa cinyoyinta yana sakin wata irin ajiyar

zuciya mai bayyana mad'aukakin tashin hankalin da yake ciki. Didi addu'a kawai take ja a zuciyarta don

idanun KK kawai zaka kalla ka san zuciyarsa a turnik'e take da tashin hankali. Ta hau shafa kansa tana bubbuga bayansa had'e da jawo masa addu'oin samun sauk'in zuciya 'Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahlan wa anta taj'alil hazna iza shi'ita sahlan.'

A hankali ya dinga maimaita wa kafin ya saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya zame ya kwanta a k'asan carpet d'in Didin had'e da yin matashin kai da hannayensa. Nauyayyan barci ne mai k'arfin gaske ya d'aukeshi. Didi ta saki ajiyar zuc

iya had'e da zuba masa ido cike da tausayawa ta tabbatar duk abinda ya gigita shi mai girman gaske ne tausayinsa ya kamata, ganin duk tarin dukiyarsa shima akwai ta yarda Allah ya jarrabeshi don haka duk wanda ka ganshi kada ka yi addu'ar zama irinsa sabod

a baka san tarin matsalolinsa da suke bad'inance ba, kowa da inda yake da nak'asu a rayuwarsa. Didi ta saki ajiyar zuciya had'e da Kunna masa sautin Alkur'ani a gefen kunnensa sannan ta mik'e ta shige d'akinta, jin KK take kamar jininta a zuciyarta take ji

nsa kamar yarda take jin dukkan ahalinta.

____________________

Sai Azahar Umma Asma ta bar asibitin ita da Ammi da ta zo duba Hamdan bayan bayyanuwar ciwonta, suka bar Sa'ada da Munira a wajenta, sabida jikin nata da sauk'i su kuma akwai abubuwan da za

su yi masu mahimmanci tunda bikin dai saura kwana uku kacal.

K'amshin turarensa ne ya sanar da su wanzuwarsa a asibitin tun bai kai ga bud'e k'ofar ya shigo ba. Hamda ta runtse idonta don ita ta san shine, duk da tana jin haushinsa hakan bai saka ta k'i

d'akin ganinsa ba, sosai take son ganinsa idanunsa suna bayyana mata zahirin k'aunar da yake mata.

Jallabiya ce fara tas a jikinsa mai gajeran hannu sai hula da ake kira hana sallah da ya saka a kan nasa. Idanunsa sanye ciki. Kyakykyawan farin glass. Da

sallama ya shiga d'akin yayin da ya zube idanunsa a kan Hamda, da take sanye cikin tausassar doguwar Riga kalar ruwan hoda, ta tufke gashinta a tsakiyar kanta fuskarta ta sake haske ta yi fa yau da ita. Sa'ada da Munira gaishe shi kawai suka yi suka fice d

aga d'akin. Ya saki ajiyar zuciya kafin ya k'arasa gadon ya zauna sosai ya na k'ok'arin jan ta jikinsa, duk da burinta ne hakan ta jita kwance a jikinsa bai hanata janye jikinta ba fuskarta d'auke da wancan fushin da yake tsammanin ya wuce ashe da saura. Y

a saki ajiyar zuciya had'e da kwanciya sosai a cinyarta ya lumshe ido kafin cikin kasalalliyar murya ya fara fad'in "Tarin laifi na a wajenki shi yasa na kasa furta miki kalmar hak'uri gani nake ba ni da wannan kalmar ki barni na nuna miki a aikace please

my Hamda, wallahi bana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ko barci bana iya yi." Ya fad'a yana bud'e idonsa ya ware su a cikin nata idon, kallon da ya yi mata tasiri mai girman gaske don duk wani sassa na jikinta sai da ya amsa wannan kallon, soyayyarsa ga

ba d'aya ta yi hank'oro ta taso mata, ba zata iya cigaba da fushi da shi ba ko da tana son aikata hakan zuciyarta ta k'i bata dama shi d'in dai shine mahad'in zuciyarta da gangar jikinta gaba d'aya, tun bata san so ba take hasasho shi a matsayin mijinta, t

un kafin ya furta mata kalmar so gangar jikinta da nasa suna gauraya a cikin barci suke gudanar da wata iriyar gugitacciyar soyayya. Bata san sanda ta d'ora hannunta a zagayen lab'bansa ba ta shiga kewaye leb'en dasu. Lamarin da ya dinga d'imauta shi da ma

a kusa yake sai ga shi tana sake hura masa

wutar abin ya dinga jin duk wata garkuwar jikinsa tana motsawa, gaba d'aya ya wargazota jikinsa ya bata wata iriyar kyakykyawar runguma gaba d'aya ya manta ma a gadon asibiti yake sai da ta ankarar da shi, ta han

yar nuna masa cannular da take hannunta. Bakinsa kawai ya cije yana mayar da wani irin numfashi yanayin da yake jin jikinsa ji yake tamkar bai tab'a kusantar wata mace ba. Ya dad'e idanunsa a lumshe kafin ya bud'e idanun da suka jirkice cikin wahalalliyar

murya a kunnenta ya rad'a mata kalmar da ya saka ta runtse ido ba shiri saboda girma da kunyar kalmar kafin ya kamo hannunta yana wasa da shi murya a k'asa ya ce "Am serious Hamda wallahi idan ba a yi wasa ba son ki zai hallaka ni, yanzu fa bana ji bana ga

ni, wata irin baiwa ce da ke da wani irin taste mai gigitarwa don Allah kada ki yi amfani da wannan damar ki dinga wahalar da ni." Idanu ta zuba masa kafin a hankali ta janye jikinta idanunsa akan k'irjinta ta ce "Ni da ba ka so baka damu dani ba ka d'auke

matar so ka wuce da ita sannan da ita zaka tare a Abuja ni ka bar ni a kano mai yasa baka had'amu ba?" Ya dad'e yana kallon bakin da ta turo tana masa shagwab'a kafin ya kaiwa bakin cafka ya shiga tsotsarsa tamkar ya samu alawar yara yana yi yana mata wa

su irin sabgogi a sassan jikinta "Ba zan iya adalci tsakaninku ba Hamda, shi yasa ba zan had'aku ba, saboda in dai idona zai gan ki ba Zan iya yiwa Nanna adalci ba, ki barta ta zauna a can bana son kowa ya rab'eni a loakcin da nake tare da ke shi yasa, duk

Thursday da magriba ina kano kuma ba zan wuce ba sai monday early in the morning ai kin ga kamar ma kwanakin ki sun fi yawa saboda you are the best among the best." Tsit ta yi tana samun sukuni a zuciyarta jin bai shirya wulak'anta ta ba, ya dinga aika ma

ta wasu irin sak'onni da itama ta shiga mayar masa da martani ta manta da batun ciwo sai dai bata barshi ya zarce zuwa can ba ta dakatar da shi daga zafafan romance. Knocking d'in da ake ne ya saka shi dawowa cikin saitinsa da kyar ya mik'e yana gyara mata

rigarta ya bud'e k'ofar ya san dai koma waye dole ya san a halin da suke amma bai dameshi ba, yana bud'e k'ofar yaga Doctor Najeeb ne abokinsa murmushi ya d'an saki yana sosa k'eya. Doctor Najeeb ma murmushin ya yi ya ce "Haba H. D'an Borno a asibitin ma

ba zaka barta ta huta ba, bayan gadon Didin ma." Hisham ya kai masa bugu kafin ya ce "Malam ka sallameta ko na samu a kai min matata wannan jan ran ya yi yawa mata da ciki ace sai an mana wani biki zata tare." Doctor ya girgiza kai "shi yasa jiya na ga ka

kasa cewa hakan a gaban Didi, ai na san tana nan tana jiranku." Hamda dai lumshe ido ta yi cike da kunyar Doctorn. Bai d'au lokaci ba ya yi discharging d'in ta ya mik'awa Hammad Hannu "Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login