Showing 24001 words to 27000 words out of 129261 words

Chapter 9 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

54

"Bani da waya." Ya kuwa dad'e da ido a bud'e bisa ga dukkan alamu tarin mamakinta ne yake nema ya karshi, a zamanin nan d

a waya ta zama ruwan dare ace zabgegegiyar budurwa kamarta da ta fito daga zabgegen gida bata da waya? Abin a jinjinawa lamarinta ne don kuwa yayi girman da ya kamata ya girgiza zuk'ata.

"Wasa kike amma?" Ya sake jefo mata tambayar, ta girgiza kai tana tu

ro baki kafin tace "Da gaske bani da ita, bata yarda za'a yi had'uwar farko na jaka da wasa alhali ba ban san ko kai waye ba."

Ya jinjina kai had'e da sakin murmushi, "Shikkenan, na yarda dama kamila kamarki bai kamata aji zance akasin gaskiya a bakinta ba

, zan dawo jibi da misalin takwas na dare, insha Allah zan taho miki da waya."

Tamkar tace masa  Ya barshi, sai dai ita kanta tana buk'atar rik'e wayar, kamar yarda taga k'awayenta na rik'ewa, Abbu ya tab'a siyo mata amma Ammi na kyalla ido ta k'wace ta,

taji ciwon hakan a ranta, sai dai bata damu sosai ba, saboda ta san hakan ce take faruwa a duk sa'ilin da Ammin taga abu mai mahimmanci da zai sata nishad'i a rayuwa, sai ta san hanyar da tayi ta k'wace.

"Ki shiga gida beauty, naga a gajiye kike sai Alla

h ya dawo dani."

Murmushi ta d'an sakar masa kafin ta tura wangamemen gate d'in gidan nasu, ta d'aga masa hannu kamar yarda shima yayi waving d'inta.

Da shigarta Kamla da suke wasa a harabar gidan ta taho ta d'aneta da gudu, haka kawai jininsu yazo d'

aya da yarinyar, kai gaba d'aya d'iyoyin Hammad ma suna sonta tamkar yarda take sonsu cikin tata zuciyar.

Peck ta bata a kumatu, a kunne kuma ta rad'a mata "My Kamlulu, dirar yaushe? Yaushe kuka dawo daga gidan Granny?" Kamla ta d'an cono baki had'e da cew

a "Ni nafi son nan gidan, can ba dad'i shine Mom tace a dawo damu ita sai jibi zata dawo." Hamda taja hancinta had'e da cewa to Parrot wa ya tambayeki, ina Khairi? Da Abul khair? Tayi mata pointing b'angaren Didi da hannu, "Suna can suna cin wani abu wai z

ogale, nifa na kasa ci amma Sis Khairi tana taci wai dad'i ita da Dad nifa idan naci am sure I will vomit it." Ta fad'a tana kakarin amai "Please Anty Hamda will

you cook noodles for me?" Hamda ta gyad'a mata kai, dai-dai lokacin da take tura k'ofar parlou

rn Didi.

A baje ta gansu duka akan carpet sun yi Baja-baja da tarkacen b'awon gyad'a ga kwanon da suka ci zogale, shi kuma yana saman three seater yana danna waya.

Sallamar da tayi cikin sanyin murya yasa shi d'ago kai, idanunsa akansu ita da Kamla, sa

i ya sake ganin zahirin kamanninsa ashe da ba abinda ya gani.

Bayan ta gaida Didi ta gaisheshi, suma su Khairi suka gaisheta, ta amsa musu cike da kulawa, ta fara harhad'a plates d'in wajen, Khairi ta sa hannu tana tayata. Didi sai mita take "Baiwar Alla

h daga zuwanki zaki fara gyara waje, ai wallahi wanda ya aureki ya more mace, ba dai tsafta ba abinci kuwa idan aka ci naki kamar kunne zai tsinke, to ba dole na soki a

Cikin jikokina ba, mai kula da kai ai

Shine abin martabawa, ba wanda ya mayar da kai d'

an iska ba, yanzu tunda nayiwa Hammad magana akan matarsa da taje ta rashe gindi ta zauna gidan iyayenta yake zaune nan yake ta cin magani ina ji ma har zagina yayi a zuciyarsa.."

Hamda ta ware ido tana kallonta kafin a hankali ta ce "Yaushe kika shiga zu

ciyar tasa kika gani? Ba fa kyau shaidar zur Didi?"

Sarai yaji abinda ta ce kafin Didin cikin kwararato ta fara masifa "Ubanki Damanga shine mak'aryacin, ban ga zuciyar tasa bane zance yace? Haka kawai mace don taga y'ar uwace ita sai ta zauna tayi ta ab

inda taga dama, ita kuma Sadiya da yake shashashace ko kuma kwad'ayin abin duniya oho mata? Taga uwarta tana auren maikud'i dad'in abin mun san komai ai ba shi ya haifi Nannan ba, nata uban da ya mutu matalauci ne sai bayan mutuwarsa sannan ta auri wannan

Alhajin, Allah na tuba mu za'a yiwa k'aryar arziki, kai Sadiya ba dai son abin duniya ba."

Wani kallo Hammad ya wurga mata kafin yayi k'wafa ya mik'e, murya a cunkushe ya ce "Kada ki sake jefa min mahaifiya cikin maganganunki balle ki jingina mata sunan b

anza."

Salati Didi tasa cikin k'ank'ance ido tace "Kiji min Annamimanci, yaushe na zagi Sadiya, Sadiyar ba don ni ba ai ubanka ba zai zauna da ita ba, balle har a d'au cikinka

A haifeka kazo kana min rashin kunya, kaje ka tambayi Sadiyar idan bani na din

ga banka mata magungunan mata ba, har ya mak'ale mata ya d'ura mata cikinka, ke bana baki labari ba?"

Hamda rintse idonta tayi, da sauri ta shige kitchen a zuciyarta ta ce "Kai lamarin Didi sai a addu'a kuma."

Cikin cunkushewar bak'in ciki Hammad ya zab

ga tsaki yasa kai zai fice sai ji yayi Didin ta ce "K'aton banza kawai dama kada na sake ganin k'afafunka anan balle kazo ka cinye mana abinci kamar da ubanka aka siya min, dad'in abin wannan karan ba Ummaru bane ya siya min, Ali k'usar yak'i ne ya siya mi

n, balle kayi fankama kace abincin ubanka nake ci."

Shi dai Hammad girgiza kai yayi ya fice a ransa yana cewa zan koya miki hankali wallah, kafin na bar k'asar nan, mata sai zaro zance tamkar ba a gasa miki baki ba.

***********************

Sai da ta g

ama gyaran gidan, sannan tayiwa Kamla da Abul khairi wanka ta dafa musu Noodles, Jallop tayi musu a abincin dare da taji alayyahu da

Naman rago da busassan Kifi, sannan ta yiwa Didi kunun zak'in da ta saba sha duk dare.

Tsaf ta sake gyara gidan sai fitar

da sihirtaccen k'amshi yake.

Wannan daren dai Hammad yayiwa Didi yajin cin abinci, duk da

Dai ya san duk inda yaje yaci dole sai ya tuna abincin Didi ko yace abincin Hamda.

Tun Didi na basarwa har ta fara damuwa da rashin bayyanar jikannata, mafi soyu

wa kuma a cikin jikokinta idan ka d'auke Hamda da ta biyo bayansa, bata jin ko y'ay'anta na cikinta tana yi musu soyayyar da takewa su Hammd d'in.

Gajiya tayi da jiransa ta sab'i gyalenta tana fad'in da kaina zanje bikonsa yanzu haka yana can Sadiya ta ta

sa shi a gaba, jarababbiyar yarinya ko kunyar d'an fari bata ji." (Kuji Didi da K'arfin hali, ita da d'anta.)

Har ta isa b'angaren Sadiyar mita take kamar taci babu, hannunta damk'e da Na Khairi take cigaba da fad'ar "Wallahi Idan naje na ganshi wajen Sad

iya ko abincin yake ci sai Na kifar, Allah Na tuba Matar da bata iya girki ba ma, ai kudai Ummal Khairi ba kiyi sa'ar Kaka ba, kamar yarda Hamda tayi sa'ata a matsayin kakarta ga shi babu ce kawai idan an bata ba zata girka ba." Khairi dai murmushi kawai t

ake wani zubin kuma ta tuntsire da dariya.

Danna k'ofar kawai tayi ba tare da sallama ba, a fusace ta shige d'akin idanunta cikin na Sadiya da suke zaune gaba d'aya da yaranta hud'u Hamid ne kawai baya nan,

Girgiza kawai Didi ta shiga yi ta zauna a kujera

tana kad'a k'afa.

A tsorace Sadiya ta fara shirin gaisheta, da sauri ta saka hannu alamar dakatarwa, "Yau kam na gane dalilin Sakina na son haihuwar maza ashe wannan take gudu, ke yanzu Sadiya ba kijidon kunya ba, ki tasa yara a gaba kina gayaa musu k'ar

ya da gaskiya wai ke mai y'ay'a, Ashe shi yasa naga Hammadu yau ya taho nan ya tare kin koya musu su raina mutane, Allah na tuba Banda na kasa na tsare ta ina zaki samu cikin Hammd d'in, kin san dai lokacin ko kallon arziki Ummaru ba yi miki yake ba, wato

yanzu yara sun girma zaki fara iko da su, to wallahi ahir ki fita ido na akan Hammad sai na ci uban kowa a gidannan, su dama wad'annan ai tuni na sallama miki su, don daga

gaisuwa ba abinda yake had'a mu da su, kin riga kin koya musu tsanata. Kai Hammadu t

ashi mu tafi." Fuskarsa ya d'aure tamau, alamar ba inda za shi har sai da Sadiyar ta dinga had'a shi da Allah sannan ya mik'e fuskarsa a had'e ya fice.

Sai da Mahmah tagais fitarsu sannan ta saki ajiyar zuciya Humaid kuwa sai dariya yake don shi ya mayar

da itabin comedian. Mahmah ta kai masa duka da pillow ganin yarda yake kwaikwayar Didin.

_____________

K'ememe ya k'i cin abincin har sai da Didin ta bashi hak'uri sannan yaci, don dama duk burga ce shi kansa yana son cin abincin ya kuwa ci da yawa,

musamman kunun zak'in da ya dinga shansa kamar ba gobe, ta kowanne fanni zai iya dakar k'irji yace matarsa Nanna tayi hundred percent, inda take da matsala kawai a b'angaren girki ne, sam bata iya girki sosai ba, duk da tana k'ok'ari matuk'a da gaske wajen

ganin ta iya d'in.

_____________________________

Cikin dare, don zai iya kiran lokacin talatinin dare, idan ya dinga jiyo motsin mutane kasancewar ba barci yake ba, yana ta duba ayyukan companyn su ta internet.

Motsin da yaji ya yawaita ne ya saka

shi fitowa da d'an hanzari, duk da matarsa batanan shi kad'ai ne a part d'in nasa, yaransa na can

Wajen Hamda da Sam suka k'i rabuwa da ita, musamman Kamla.

A hankali yake taku kafin ya k'araso parlourn.

Gabansa ne ya buga sosai, ganin mutanen zube a par

lourn nasa, sanye cikin bak'ak'en kaya, hatta da fuskarsu sun k'unsheta ba zaka tab'a shaidasu ba, idanunsu sanye da Glass.

Duk da ya tsorata da ganinsu,

Sam jarumtarsa bata bayyana hakan ba, sai ma b'ata fuska da yayi, ya kuma isa wajensu cikin takun sa

na gadara. Da ginshira da komai tamkar jinin sarauta ya ce "Lafiya?"

Mai suffar samudawan daga cikin su ya mi'ke tsam da niyyar kai masa duka, da sauri d'aya daga cikin su ya tare shi "Kada ka fara ka san ba abinda muka zo yi ba kenan, aiko mu aka yi mu

gusar masa da tunaninnasa na shekara da shekaru, ta hanyar wannan maganin da tabbas idan ya sha shi

ko kalar uwar da ta haifeshi ba zai sake tunawa ba, balle ubansa sunansa ma sai an masa Tarjama..." yana jin su suka shek'e da dariya had'e da Kai masa shak

'a........Alk'alamin Jikar Nashe

YA ABIN YAKE?

NAZEEFAH SABO NASHE.

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e

Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

On Wattpad @Nazeefah381

13



🏽



🏽



🏽📖📖📖



🏽



🏽



🏽

Kamar an farkar da Abbu cikin da

ren, akan idonsa Samudawan suka shiga sashen Hammad d'in bayan sun sumar da masu gadi har biyu da suke bakin gate d'in.

Hankalinsa a tashe ya kira y'an sanda kafin cikin sand'a ya nufi part d'in su Hammad d'in yana bin bango, akan kuma kunnensa suka yi wa

nnan furucin, da yayi barazanar hargitsa kayan cikinsa. Addu'a ya shiga yi akan Allah ya kawo police d'in da wuri.

Cikin hukuncin Ubangiji duk da dukan da suka yiwa Hammad d'in bai yarda ya sha k'wayar da suke tura masa a baki yana furzarwa ba.

Ance Sa

rkin yawa yafi sarkin k'arfi, don haka kafin kace me tuni sun wahalar da shi, duk da ya kafe akan k'in shan maganin.

A lokacin ne kuma y'an sandan suka bayyana cike da k'warin gwiwa suka danna kai sashen bisa jagorancin Abbu.

K'ok'arin gudun da suke ne y

asa police d'in danna musu harbi a k'afafunsu, sun yi nasarar kama mutum biyu, yayinda uku suka tsere.

Ba wani b'ata lokaci suka gark'ame su da ankwa, a kuma lokacin ne mutanen gidan k'arar harbin

bindiga ya farkar da su, Dama Didi da Hamda ba barci suke

ba, a razane suka fito duka d'aukacin jama'ar gidan suka nufi inda suke jiyo harbin.

Cikin tashin hankali Didi take kiran sunan Hammad "Ubangiji Allah kasa ba su kashe min jika na ba"

Ta fad'a idanunta akan Hammad d'in da yake kwance magashiyyan Abbu y

ana k'ok'arin d'aukansa don su kaishi asibiti amma ya kasa, ga shi gidan ba maza duk suna gidajensu shi kuma Hamood yana makaranta.

Mahmah kuwa kuka kawai take ta kasa katab'us, sai Ammi ce cike da kissa ta kama k'afafun Hammad d'in suka kinkimeshi da Abb

u don zuwa asibiti, hankalinta a tashe don bata san mai zai je ya dawo ba idan Hammad d'in ya farfad'o, ba mamaki a take a wajen ya tona mata asiri, da ta sani bata bi gurguwar shawarar kady ba gashi ta kaita ta baro. Dole ta nemi mafita a gaggauce kuwa ka

fin wankin hula ya kaita dare.

Bugun da suka yi masa a baya da gefen muk'amik'insa shine yake masa ciwo sosai sai kuma dukan da suka yi masa a kai da yayi sanadiyyar sumansa. Haka likitan yayi musu bayani kafin suyi masa allurai aka kuma jona masa drip b

arci mai nauyi ya d'aukeshi.

Dole Abbu da Didi ne suka kwana a asibitin don Sadiya bata zo ba bata son surutun Didi, shi yasa tayi zamanta a gida, Ammi ta so zama amma Didi ta ce a sabida me? Don kalan dangi, to ki fita idona wannan ba huruminki bane me k

ika had'a dashi? Banda auren ubansa da kika yi, maza-maza ki tattara komatsanki kiyi can wajen samudawan y'an matanki da

Kika ajiye kina adon d'aki da su."

Ranta a tunzire ta tafi, dama taso zama ne ko ta samu mafita, wannan karan yarda take jin zuciyart

a da tsoron tonuwar sirrinta, tana tunanin da kanta ma zata iya kawar da Hammad idan ta samu faraga sai gashi tsohuwa Didi tayi mata kanda garki, ta hanata sakat don haka jikinta a salub'e ta tafi, had'e da aniyar sake wani shirin ko da na zuba masa guba a

abinci ne, sai dai tana tsoron a kamata, don haka zuciyarta ta amince da shawara d'aya da zata zartar da ita da zarar ya warke ya koma gida.

____________________________________

Da sassafe Hamda ta gama duk wasu aiyakunta, har peppe soup da sinasir ta

yiwa su Didi da zummar idan tayiwa yaran wanka su tafi gaba d'aya su duba Babansu.

Tana cikin shafawa Kamla mai Mahmah ta aiko idan ta gama shiryasu suje gaba d'aya.

Tsaf ta shirya su cikin kayansu na yau da kullum English wears kasancewar har lokacin b

asu saba da kayan hausawa ba.

A zaune suka sameta a parlour da coolers a gabanta, ta zabga uban tagumi so take taje duba yaronta amma tana tsoron tijarar Didi, gashi wad'annan mutane na jiya sun tsaya mata a rai, ya kamata tabbas ta bincika wajen sanin ko

su waye, dole akwai wanda ya saka su ba zuwan kai bane.

Sallamarsu ce ta sata sauke wani dogon numfashi, idanunta akan Kamla da Hamda, da suka yi tamkar ya da k'anwa.

Har k'asa Hamda ta durk'usa ta gaisheta kafin su Kamla suma suyi koyi da ita. Mahmah t

a saki murmushi zuciyarta tana jin dad'in yarda Hamdan take kula da y'ay'an d'an uwanta ta ce "Masha Allah, inye yaran Anty Hamda har an shirya, to maza kuzo mu karya sai akaiku asibiti ku gano jikin Babanku ko."

Khairi ta zaro ido "Me ya samu Dad?" Kafi

n Mahmah ta bada amsa Hamda tayi saurin cewa "Fad'uwa yayi yaji ciwo kad'an, ai tafiya ma za muyi Mahmah saboda mun karya." Mahmah ta jinjina kai,

"Duk dai baki gaji ba, ga d'awainiya da su ga girki to ubangiji yayi miki albarka." Murmushi ta saki tana ams

awa cikin jin dad'i da gaske tana son jin wad'annan addu'ar abinda bata tab'a samu ba daga bakin mahaifiyarta, sai dai Mahmah Abbu da Didi sai kuwa Malaman islamiyyarsu da kullum suke sambad'a mata albarka kwando-kwando.

"Ku tashi maza ku shirya kuje, ga

driver can ya kaiku ga abinci ku kai musu."

Da sauri Hamda ta ce "Ai nayi musu sinasir, kunun gyad'a da k'osai naga Ya Hammad yana masifar son su."

Mahmah cikin sake Soyuwar yarinyar a ranta ta ce "Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari, ya fahi

mtar da mahaifiyarki tarin ni'imomin da Allah yayi mata da

Ya bata ke a matsayin y'arta, ba'a ja da lamarin ubangiji amma da nace dama nice."

Murmushi Hamda tayi hawayen idanunta na barazanar zubo mata, duk da k'ok'arin togacesu da tayi.

Mahmah jikinta y

ayi sanyi matuk'a tana tsaye har suka shiga mota suka fita daga gidan. Ta ja ajiyar numfashi tana sake jin tausayi da k'aunar Hamda a zuciyarta a zahirance jinta take tamkar jininta.

__________________________

Da sauk'i sosai jikinsa, ganinsu yasa Abbu

tafiya gida, Didi kuwa ta zubawa Hammad abincin a baki tana bashi kamar k'aramin yaro.

Sai da yaci ya k'oshi sannan ta gyara zama tana rik'e hab'a ta ce "Sadiya dai ta tabbata Asararriya, wallahi bana haufi Rashin ilimin nasara ke d'awainiya da Sadiya ta

ke yin wani abu tamkar zubin mutanen farko, to ko ni da nake y'ar zamnin da ai ba zank'i zuwa duba Ummaru idan lalura ta sameshi ba, balle har ta kai ga kwanciya asibiti, amma kuji min lusarar mace yarda ta bursune idanunta da toka tak'i zuwa dubata, Yanzu

ai ka tabbatar daga ni sai ubanka Ummaru ne muke sonka, Sadiya kuwa da kai da

Babu duk d'aya ne a wajenka, shashashar uwa kenan lamba d'aya Sadiya kenan, har yanzu ruwan Gwarzo bai bar jikinta ba, ai zamu koma gidan da ni take zance."

Hammad ya d'an bud'

e idonsa kad'an yana harararta k'asa-k'asa, shi surutunta ya fara isarsa, ta daddage sai magana take, ta barshi ma yaji da matsalarsa. Ya

Zama dole ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login