Showing 114001 words to 117000 words out of 129261 words

Chapter 39 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

89

ki ba ni?" Kan kace me Sa'ada ta bi bayan Munira da sauri da taga

ta yi gate, ita ma ta saka k'afa zata bi su ya mata wani irin ja da yasa ta tsayawa ba shiri idanunsa cikin nata tsawon lokaci yana yawo da su a jikinta kafin ya ce "Na haramta miki fita daga yau, lalle kuma na yafe shi kin ji na gaya miki." Wata irin

jan

yewa ta yiwa jikinta da ya saka su gogar k'irjin juna duk da k'ok'arin sa na kaucewa hakan da sauri ya runtse idanunsa yana turata gefe ya ce "Malama kada ki b'ata min azimi." Ta watsa masa kallo kafin ta d'aga k'afa zata tafi ta ji yace "Kunun gyad'a da k

'osai nake so na shan ruwa." Wannan karan cak ta tsaya murya a cunkushe cike da tsiwa ta ce "Ka saka Sa'ada ta maka." Yana murmushi ya ce "Kin san kuwa ina cewa zata min, wallahi kada ki saka na auri yarinyar nan da gaske." Tana harararsa ta ce "Allah ya b

ada sa'a." Ta shige sashen Didi hawaye na zubo mata ba na hanata lallen da yayi bane na zallar takaicin cewa zai auri Sa'ada ne, sharrin shaid'an sai ta ji zuciyarta na ingiza ta da tabbatar mata ba mamaki ma yana son Sa'adan saboda ya ga ta sallama masa j

ikinta ta dantse leb'enta tana jin takaicinsa har tsakiyar k'ok'on zuciyarta, ta tabbata da itace Nanna aka mata kishiya kai tsaye zuciyarta zata buga.

Umma Asma cike da mamaki take kallonta, "Ke kuma ina Lallen?" Murya a cunkushe ta ce "Ya hana." Umma ta

waro ido "Ya hana? Ban gane ya hana ba? Shi da za'a wa kwalliya shine mai hanawa, ai shikkenan ya yiwa kansa." Didi kuwa tab'e baki ta yi tace "Jarabbaben kishinsa shi zai sa ya hanata." Ita dai Hamda d'akinta ta shige dama barci ne a idonta lalle kuwa duk

ranar da yaga dama ya barta ta yi.

________________

Yana zaune a falonsa Nannan ta kira wayarsa, mamaki ya kamashi ya mayar da kallonsa kan wayar a zuciyarsa ya ce "Mhmn ta daina fushin kenan?" Yana d'agawa ya ji tana gaisheshi da waccan kammalalliyar

muryar ta Nannan da da ya sani mai cike da nutsuwa da kwantar da hankalin mai sauraro ya ji ta ce "Habibi kazo ka d'auke ni." Wata irin sanyayyar ajiyar zuciya ya saki, ya tabbatar Nannan yau ta huce daga fushin da take murya a tausahshe da son nuna d'aki

nsa ya ce "Okey Madam on my way In sha Allah." Ta saki shashshek'ar murmushi kafin ta ce "Take care, bye-bye." Ya zare wayar a kunnensa yana sake ware idonsa akan screen d'in yana son tabbatar da gaske Nannan ce ko kuma wata daban?

Wanka kawai ya yi ya z

ura jallabiya ya fice zuwa d'auko tan.

Koda ya shiga gidan Didi gaba d'aya ta saka su a gaba da yi musu nasiha, ta kuma ja kunnensa da ya aikata adalci matuk'ar baya son tashi da shanyayyen b'arin jiki ranar alk'iyama Hammad kada ka wulak'anta uwargidanka

akan amarya, saboda uwargida itace tushen gidan idan ka darajata ka daraja gidanka idan kuma ka wulak'anta tabbata ka wulak'anta gidanka, idan ka ga ana zaman lafiya a gida mai gidan ne ya so, idan ka ga ana tashin hankali a gida mafi rinjayen laifin Yana

wajen mai gidan don haka sai ka jajricewa zuciyarka wajen tabbatar da adalci da son ranka ko ba so a tsakanin matanka, Allah ya had'e maka kansu ya baku zaman lafiya mai d'orewa. Ka ji ka k'i ji ka gani ka k'i ka gani sai ka ga kun zauna lafiya." Daraja k

'ima da mutuncin surukartasa ya sake bunk'asa a zuciyarta ya tabbata samun irinta a rayuwa yanzu matuk'ar dace ne. Sosai ya mata godiya suka mik'e shi da Nannan zuk'atansu fes ba kamar sanda Nannan ta taho gida ba zuciyarta na zafi da k'una.( anan na ke so

n jan hankalin iyaye mata don Allah mu zama masu k'arfafa zuk'atan iyayen mu a zaman rayuwar aure ba masu ruguza musu tarbiyya ba da zubar da mutuncin kansu a idanun surukansu k'ima da darjarsu ta zagwanye madalla da samu iyaye na gari.)

Ko a mota kallont

a kawai yake yana sakin murmushi ganin yarda ta kwantar da hankalinta murya

a sauk'ak'e ya ce "Dida uwace ta nunawa sa'a ki godewa Allah da yasa kika fito a tsatsonta." Ta saki murmushi kawai kafin ta ji ya ce "Yanzu da wata uwar ce daga fuskarta Zan ga b'

acin ran na yiwa y'arta kishiya wata ma daga nan zata d'ora y'ar a hanyar bin malamai shikkenan sai komai ya kacame k'arshe a kai ga saki Allah ya Yi mana tsari." Ta lumshe ido kawai Kafin ya sake Cewa "yanzu gimbiyar a ina take son Zama Abuja ko kano?" Ta

na murmushi ta zube idanunta a cikin nasa Kafin ta ce "Abuja mana, na fi son na ganni ga katara ta ga taka. Tunda a can zaka fi zama." Wani irin taratsatsi ne ya shiga zuciyarsa har ya kusan sakin sitiyarin kafin ya jiyo ya ce "Abuja kuma Madam?



𝕹𝖆𝖟

𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍





[



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

*08033748387*

YA ABIN YAKE? 45.

Ya ABIN YAKE complete @Arewa books

Danna wannan link din, kada a manta da follow

Arewabooks. @NazeefahSaboNashe.

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc

8a75f51b283a378e

1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Cikin son k'ara tabbatar masa ta d'aga kai tana lumshe ido, daga cikin k'wayar idanun nata ya tabbatar babu maganar wasa a cikin furucin nata, jan ajiyar numfashi ya yi yana tuno irin dangerr da Hamda zata ma

sa tunda ta ce tafi son Abuja, a wannan gab'ar ba shi da ta cewa tunda dole ya bawa uwargidansa zab'i haka shari'a ta amince. A kasalance ya dinga jan motar har suka isa gida ya rasa hukunci d'aya da zai zartar.

Tana tsaye a harabar gidan ta hango sun fit

o daga mota, fuskokinsu d'auke da walwala ranta ne ita kuwa ya sake b'aci musamman yarda ta hango yana cikin matuk'ar farin ciki ita kuwa ya k'unsa mata bak'in ciki ta hanyar hana ta zuwa lalle duk da ga shi nan ta hango lalle rad'am a hannu da k'afar mata

rsa ja da bak'i, yanzu haka ma lallen ya kaita a kayi mata ita kuma ya mayar da ita sha ka tafi. Ido biyu suka yi da Nanna, sai ta ga ta sakar mata murmushi duk zuciyarta na tsananin takaici haka ta hak'ura ta sakar wa Hamda murmushin amma Hamda ta zuba ma

ta ido cike da

b'acin rai kafin murya a cunkushe ta ce "Ina wuni Maman Khairi." Bata jira amsarta ba ta shige sashen Didi, idanuwan Hammad zube a kanta yana hango tsagwaron jin haushin da take nasa. Ya saki murmushi kawai yana sosa k'eya musamman da ya han

go Nannan ta kama shi dumu-dumu da kallon Hamdan, basarwa kawai ta yi itama don ta d'au alk'awarin ba zata sake bayyana b'acin ranta ba zata yi ta rok'on ubangiji ya yaye mata kishin da yake cunkushe a zuciyarta. "Amaryarmu na ga ta sake kyau, sai wani has

ke ta ke." Ta fad'a tana jin k'unar furucin da yake fitowa daga bakinta, sai dai har k'asan ranta tana mamakin yarda Hamdan ta sake kyau cika da gogewa tamkar mai shigar yaron ciki. Hammad bai amsa mata ba illa shigewa da ya yi b'angaren su shima a zuciyar

sa yana ganin kyan da Hamdan ta sake.

______

Sai da aka sha ruwa sannan ya shiga b'angaren Didin duk yawancin suna zaune a falo har yaran Umma Asman, ya sannu waje daga gefe yana hararar Hamda k'asa-k'asa ganin yarda take zaune ko mayafi babu hular kant

a ma ta zame sai zuba zance take da su Sa'ad d'in Umma Asma. Sam bata ankare da dalilin hararar tasa ba, itama tunzira baki take tana watsa masa nata idanun, Hammad ya ciji leb'ensa na k'asa kafin ya mik'e ya shiga kitchen d'in Didi, Didi ta bi bayansa tan

a k'wala masa kira "Ba fa na son rashin arziki Hammad, kada ka kwashe min naman miya na ga dai yanzu rowar tsiya ce da kai, yaushe rabon da ka kawo min naman." Mahmah da Umma Asma suka tuntsire da dariya ganin kallon da Hammad d'in ya watsa mata kafin ya c

e "To kura, ni tea zan zubo. Ke Hamda zo ki zubo min black tea." Kunyar Mahmah ce ta sata mik'ewa, Mahmahn na kallonta k'asa-k'asa ta na godiya ga Allah da ya bawa yaronta lafiyayyiyar yarinya tabbasa ta so ta tafka wa Hammad asara. Hammad ya bi bayanta da

ma ba wani tea da yake so so yake ya bud'e mata ido ya ja mata warning ta daina masa wasa da halittun jikinta kowane banza yana gani bata san zuciyarsa zata iya bugawa a duk lokacin da ya fuskanci wani namijin yana sha'awarta. Suna shiga kitchen d'in ya ja

ta jikinsa ya mata wata irin runguma kamar zai tsaya jikinsa ya mayar da ita, wata irin kewarta ce take katantanwa da rayuwarsa, gaba d'aya yake lalubeta yama manta a inda suke burinsa ya kai ga can ta yi saurin tureshi ganin hankalinsa yana shirin gushewa

ita kanta muryarta a cakud'e ta ce "A kitchen fa mu ke." Lumshe idanunsa ya yi yana jan hannunsa ya d'ora saman k'irjinta murya a dashe kamar mai rad'a ya fara magana a kunnenta "Hamda ya kike so na yi? Ke kika jawo komai ma, gudu na kike kamar ba ni da h

a'k'ki a kanki sannan ina shigowa kika haske ne da wad'annan abubuwan kin zube su kowane banza yana gani, wallahi koma cikin gida kike na sake ganinki ba hijab gaban maza sai kin gane baki da wayo, kina ji na." Ya fad'a yana wata irin lasa a wuyanta, gaba

d'aya ji ta yi tana shirin shid'ewa da sauri ta ja jikinta ta zame ta zauna a k'asa ba tare da son ranta ba ta fara fad'in "Please Yaya Hammad, ka fita kada wani ya zo ya ganmu." Bin ta ya sake ya sai gani kawai ta yi ya d'auke ta cak ya d'ora akan working

space d'in kitchen d'in yana kai mata sumbata a baki, sosai ya sumbaceta kafin ya saketa yana mayar da wani irin numfashi ya ce "Duk wanda ma ya gani shi ya jiyo wa yace su hana ni mata ta? Gaskiya ana d'aukan hak'kina da ma ban d'and'ana bane da sauk'i t

o ni na san mai na jiyo." Hamda da sauri ta Durga daga wajen tana shirin fita ta ji ya ce "Nanna ta zab'i Abuja, don haka ki gayawa su Didi a kano za'a miki jere don na san may be kafin ku wuce Saudiya za su buk'aci zaman gida, sannan jibi insha Allah za m

u wuce Birmingham da Nanna." Wani irin Burki ta ja kafin ta juyo ta zube idanunta cikin nasa, k'una take ji sosai a ranta "Ita zai raina wa hankali kawai ya fito ya gaya mata

ya fi buk'atar matarsa a kusa da shi fiye da ita, meye na mata k'umbiya-k'umbiya

idanunta na zubar da hawaye take k'ok'arin furta masa ko Kamla d'aya amma ta kasa, yana k'ok'arin janta jikinsa ta fincike cikin ajiyar numfashi ta ce "Jikina kawai kake buk'ata, soyayyarka da kulawarka gaba d'aya ka bawa matarka, to wallahi matuk'ar haka

ne ba zan tare a gidanka ba, kuma na fasa aurenka ko ma me zai faru ya faru." Daga haka ta ja wani abu muk'ut da ya tokare mata wuya ta juya da sauri ta fice daga kitchen d'in, Hammad ya ja ajiyar zuciya don ya hango abinda ta fad'a d'in da gaske take har

k'asan zuciyarta, gabansa ne ya fad'i yana hasashen ranar da za'a ce ya rabu da Hamda wani banza can ya aureta ya tabbata a ranar ajalinsa ya zo, amma ya zaiyi da Nanna ai da kunya ya nuna mata ba ya buk'atar zamanta a Abuja ya fi son zaman amaryarsa ya ru

ntse ido yana tuno yarda Hamda take magana cikin tsagwaron b'acin rai.

Ita kuwa tana fita ba wanda ta bari ya ganta d'akinta kawai ta shige ta mayar da k'ofa ta rufe har da murza key kafin kuka ya k'wace mata, gaba d'aya haushin kanta take ji da har ta ba

ri zuciyarta ta rinjayeta ta so mai mata duk da ta san tsagwaron kishinta, kukanta ta sha sosai kafin ta yanke shawarar zuwa gobe ta rok'i Abbu ya saka Hammad ya sahhale mata auren da gaske ta fasa ba zata iya zama da mai mata ba, zuciyarta tana sake tabba

tar mata da wata rana tsananin kishinta zai iya kaita ga hallaka ko aikata aikin da na sani koma zuciyarta ta buga gaba d'aya.

Hammad ya dinga k'ok'arin kiranta a waya tana rejecting k'arshe ma sai ta yi blocking d'insa ta barsa da waya a hannu yana zuba i

danunsa cikin hotonta da yake kan phon book d'inta, lallai ya san ta yi fushi don bata tab'a masa rejecting kira ba ko fushi take da shi sai dai ta d'aga wayar ta saka a kunne ta yi shiru maganar duniya da zai yi ba zata furta ko da kalmar 'A' ba. Ya saki

ajiyar zuciya yana tunanin yarda zai iya zuwa ya tunkari Nanna ya ce mata ita ta hak'ura ta zauna a kano da kunya, ita kuma Hamda Son da yake mata shi zai hana ya iya yi mata jan ido ya ce ta zauna dole a kano, ya saki ajiyar zuciya kawai yana sake kiranta

amma still ta k'i shiga.

__________

Kashegarin ranar ya kama sallah ce, kowa da farinciki ya tashi idan ka d'auke Hamda da Hammad da suka ta shi zuciyarsu a cusgune musamman Hamda da bata san sanda barci ya d'auketa ba saboda tsananin b'acin rai ruwan

kunun gyad'a ne kawai a cikinta, Hammad a ranar dama ya ajiye wa zuciyarsa za'a kai lefe don shi da Mami Lauratu suka had'a kayan lefen akwatina 2set ita kuma Nanna kud'i zai bata ta siyi nata, sanda ya yiwa KK waya ya sanar da shi fad'a KK ya hau shi da

shi yana fad'in "Wa yace Ka wahalar da kanka Hammad? Na Riga na bada a had'a mata lefe, amma tunda ka yi ba zan hanaka ba, ka je ka samu Abbunku sai ya gaya maka inda za'a kai lefen tunda y'arsa ce ni kaine nawa d'an, idan ya gaya maka ka gaya min Zan turo

mutanen da za su kai lefen naka sai a had'a da na wajena da key na mota guda biyu ta ta d'aya ta Nanna d'aya, akwatinan da na musu nata set biyu na Nanna set d'aya, don itama dole a mata adalci." Hammad yana farin ciki ya dinga masa godiya "Ha'k'ki na ne

Hammad, ina jinka kamar ni na haifeka fiye da yarda nake jin Hamda da Kamla Allah ya yi muku albarka. Don haka kada na sake maka abu ka min godiya ka d'auke ni kamar Abbu tunda ni ba ni da wani d'a namiji kai nake gani na ji dad'i." Hammad murmushi ya saki

bayan ya sauke wayar a kunnensa ya sake gwada kiran Hamda still wayar a kashe take, saboda tana fushi da shi ko kwalliyar sallahrta bai gani ba, sallahr idi ma da

zata can ya hangota sanye da nik'ab, bugun da zuciyarsa take masa ne kawai ya tabbatar masa

itace don in dai tana waje sai ya ji wannan bugun k'irjin.

Direct wajen Abbu ya wuce ya isar masa da sak'on KK farin ciki ya cika zuciyar Abbu da wannan daraja da k'ima tawa da KK ya masa ya ji duk duniya ya daina jin haushin wancan lefin da KK ya masa cik

in fara'a ya ce "Kira min shi." Yana d'agawa Abbu suka gaisa ya ce "Na ji sak'onka nagode k'warai a kawo nan gidan zuwa magriba insha Allah."

KK cike da jin nauyin Abbu ya ce "Ba godiya tsakaninmu Ai Hamda y'arka ce, ba ni da hurumi a kanta yarda ka yi wah

ala da ita kad'ai ya isa a jinjina maka, alfarma d'aya zaka min ka bar min yaro na Hammad a daina shiga huruminsa ya zama ni ne Babansa please!" Abbu yana murmushi ya ce "Na bar maka dama naka ne Allah ya taya mu rik'onsu." KK ya ce "Ameen ya Allah, yau za

su zo insha Allah." Daidai lokacin Ammi ta shigo idanunta zube cikin na Abbu ta ce "Su waye za su zo? Na ga sai zabga fara'a kake?" Yana murmushin ya ce "Masu kawo lefen Hamda, sai ku fara shiri ko da yake ba huruminki bane bari na je na gayawa Didi." Jik

in Ammi ne ya yi sanyi jin abinda Abbun yace wai ba huruminta bane, kawo lefen y'arta shine ya zama ba huruminta bane, har wata k'wallace ta fara son zubo mata ganin da gaske Didi ta mata fashin y'a tana ji tana gani. Hammad da ya lura da ita murmushi kawa

i ya saki ya mik'e yana ficewa daga d'akin ko da wannan kad'ai aka barta ya tabbata ya isheta takaicin da zai saka mata hawan jini.

-

__________

Abbu na gayawa Didi ta rangad'a gud'a fad'i take "Lokaci ya zo abu na mu maganin a kwab'emu, ai sai a zo a

fara shiri a musu orderr kayan ciye-ciye a kuma tanadar musu kud'in tukuici don na san kaya ne za'a kawo ba na wasa ba." Abbu murmushi kawai ya saki yana kallon Umma Asma ya ce "A yi abinda ya dace, sai ki turo min Zan tura miki ta account d'in ki." Tana

murmushi ta ce "To" Hamda da take d'aki tana jiyo Abbu ta yi saurin fitowa idanunta fal k'walla ta zube a gaban Abbun, gaban Hammad ya fad'i ganin yarda duk ta bi ta birkice da sauri ya hau girgiza mata kai, ita kuwa dafe cinyar Abbun ta yi murya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login