Showing 39001 words to 42000 words out of 129261 words

Chapter 14 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

77

tsawa. Tsak ya

tsaya had'e da juyowa yana facing d'inta. "Me kake nufi da tafiya da ita? Ko kana nufin da gaske ka karb'eta a matsayin y'ar cikin ka, Hammad kada kace min da gaske yarinyar nan jininka ce?" Ya d'ago kai yana kallonta cikin tafasar zuciya sai dai lab'bans

a sun gaza furta furucin komai illa idanunsa da suka jirkita launi zuwa ja. Ya sunkuyar da kansa kawai. Har zuwa san da Dida ya fuskanci tabbas ba zaida ce komai d'in ba, ta dafa kafad'ar Sadiya cikin taushin murya ta ce "Yaya mu bi komai a hankali, insha

Allah komai zai bayyana kansa, a yanzu na fuskanci halin da Hammad yake ciki sam ba zai iya furta komai ba." Sadiya ta bud'e baki zata yi magana Dida ta yi saurin girgiza mata kai, don ta lura idan har aka cigaba da kucincina maganar tsaf Hammad zai iya da

tse igiyar auren y'arta, ko ba haka ba ita Hamdan ce ma ta bata tausayi, ta lura ba a k'aramin rud'ani da firgici take ciki ba, kada a je ta rasa hankalinta ko zuciyarta ta buga haka kawai an saka ta a halin ban ji ba ban gani ba. Idan har Hammad ya matsa

sai ya tafi da ita, ita zata rik'e ta madadin a had'a ta da Nanna a zo a haifi d'an da ba shi da ido. Don haka ta girgizawa Sadiya kai alamar kada ta ce komai, ta kuma k'arasa gaban gadon murya a tausashe ta dafa kan Hamda da ya d'au zafi rad'au ta ce "Ki

yi hak'uri kin ji, komai zai daidaita ubangiji Allah ya ba ki dangana, duk abinda kika ga ya faru ga bawa muk'addari ne daga Allah kuma bawa ba zai iya goge k'addararsa da Ubangiji yada rubuta masa ba, ki yi ta addu'a a zuciyarki ubangiji Allah ya baki iko

n amsa jarabawarki Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahlan wa anta taj'alal Hazna iza shi'ita sahlan. Tana yaye duk wata damuwa da nauyi zuk'ata." Daga haka ta yi mata sallama suka fice. Hamda ta bi bayanta da kallo, tana jinjina kyakykyawan hali irin

nawannan mahaifiyar Nanna, tunda abin ya faru ita kad'ai ce ta fad'a mata abinda ya kwantar mata da hankali kad'an, ita ce matar da ta lallasheta da furuci mai warware fushin zuk'ata, wani abu kad'an daga cikin abinda yaaka tokare k'irjinta ya sauka, a han

kali wasu siraran hawaye suka fara biyo k'uncinta. Ta shiga nanata waccan addu'ar da Dida ta gaya mata. Sai ga shi a hankali barci duk da ba za'a kira shi mai

dad'i ba yazo ya d'auketa. Tana sakin ajiyar zuciya akai-akai. Hammad da yake zaune ya zuba mata

ido, wani abu mai kama da tausayi yana tsirga masa cikin zuciyarsa, da gaske yana jin tausayinta, idan kuma ya tuna ta hanyar da aka sameta sai ya ji zai iya sadaukar da Duk wani farin cikinsa matuk'ar ita za ta yi farin ciki.

Kusan awoyi biyu yana zaune

kamar maigadinta yana kallon yarda take sauke ajiyar zuciya cikin barci. Ba ya son ya tasheta duk da kuwa za suje wajen passport, ya fi so ta tashi da kanta. Sai da ta k'ara mintuna talatin akan awa biyun sannan ta farka. Idanunta cikin nasa da ya kafeta

da su, da sauri ta d'auke na ta idanun tana tattare gashin kanta da ya kwanto a

Saman fuskarta. Da kyar ta mik'e zaune tana dafe pillow, tana mamakin yarda ta yi barci sosai haka. Fuskarsa a d'an d'aure ya mik'e yana gyara wristwatch da yake hannunsa "10 m

inutes na ba ki, ki yi alwala ki yi sallah za mu je wajen passport kuma kada ki yi taking time sauri nake." Bai saurari amsarta ba ya fice da sauri. Sai da ta fi minti d'aya a zaune kafin ta mik'e cike da kasala ta shige toilet d'in d'akin. Ita dai da zai

bi ta tata da ya kyaleta ta shiga duniya tunda zamanta tare da su a gareta ba shi da wani amfani, musamman da matarsa ta nuna mata k'iri-k'iri bata son zamanta tare da su. Sam ba taga laifinta ba, dama y'ay'a irinsu haka mutane ke gudunsu ba sa son sam su

rab'e su, duk da kasancewar ba laifinsu ba ne.

Mintuna biyar ta k'ara akan lokacin da ya bata, tuni ya je wajen Doctor ya amshi sallama, bayan Doctorn ya tabbatar masa damuwa ce silar ciwon nata, da zarar an kwantar mata da hankali everything will be alr

ight Insha Allah.

A rab'e ya ganta jikin bango, tana hangoshi ta fara wasa da bakin hijabin da yake jikinta. Sai da ya isa gabanta sannan ya duba agogo hannunsa ya sauke kallonsa a kanta. Yana d'an girgiza kai, ba kuma tare da yace komai ba ya juya ya ci

gaba da tafiya. Ita kuma jin bai ceyi tazo ba kawai sai ta ja ta tsaya. Har sai da ya yi taku goma sai yaga tamkar bata bin sa. Hakan yasa ya jiyo tsaki yaja kafin ya ce "Jira ki ke na zo na d'auke ki ne?" Ya yi furucin ba tare da ya juyo ya kalleta ba. Sa

i sannan ta bi shi tana mamakin yarda yake mata abubuwa tamkar ana tilasta shi, ya k'yaleta mana ya k'yaleta ta kama gabanta idan yana ganin kamar ta zame masa wani kaya ne. Bai san haushi yake bata ba, idan ta tuna yarda suka bi son zuciyarsu suka samar d

a ita tada gurb'atacciyar hanya ya zama dole ta samawa kanta mafita ba wani Birmingham da zata bi shi. Ya aura mata Zunnuraini kawai.... Da sauri zuciyarta ta buga ta tabbata da kyar idan zata auru idan har mutum ya san wacece ita? Dai-dai lakacin da ta ci

karo da motar ba tare da ta sani ba, shi kuwa yana kallonta ya k'i mata magana yana son ya ga yarda zurfin tunanin nata yaje.

Tsaki ya ja, a zafafe ya ce "Ki je ki bugar da zuciyarki a banza garin banzan tunaninki." Da kyar ta d'ago jajayen idonta tana so

tayi masa tsiwa amma kwarjininsa yana hana ta. Musamman idan ya tsatstsareta da idanunsa masu kaifin gaske." Sai kawai ta runtse idonta, hawaye na kwaranyo mata ta fad'a motar. Yana kallon yanayinta ta cikin motar har da murgud'a bakin da ta yi, murmushi

kawai ya saki ya tabbatar da abinda take k'unsawa a zuciyarta.

Yana fara driving taji ya ce "Idan kin gama tsara yarda za ki gudu ki sanar min na baki kud'in mota." Da wata irin razana ta d'ago tana dubansa ya aka yi ya San Sirrin zuciyarta? ya aka yi ya

san abinda take shiryawa, kamar ta tambayeshi sai kuma ta yi shiru tana cigaba da wasa da

hannunta

Tsawon lokaci suna tafiya kowa da abinda yake sak'awa a ransa, da gaske ba ta son bin sa Birmingham d'in nan amma sam ta rasa k'warin gwiwar da zata kalli f

uskarsa ta ce ba za ta je ba.

Sun kusa isa gurin ya dubeta ta side d'aya kafin ya ce "Idan ba ki bini Birmingham ba, kina tunanin akwai inda za kije ki samu peace of mind, kina ji dai Mai gidan ya ce Baya buk'atar ganinmu mu bar masa gidansa." Hawaye ta

ji yana son zubo mata "Kada Ki fara min wannan kukan banzan, ki bani numberr saurayinki na yi magana da shi idan yaga ya shirya aurenki ya fito nan da kwana biyar na aura miki shi a wuce wajen, amma idan aka zo bincike wajen su Abbu asiri ya tonu fa?" Rint

se idanunta ta yi ita ma tana jin wannan fargabar amma tana tunanin ai ba za su tona mata asiri ba, tunda idan sun tona kan su suka yiwa. "Ki ba ni numberrsa zan yi magana da shi." Wani dad'i ta ji ya tsarga mata duk da gefe guda tana jin Shakka da kasantu

war hakan, tun da dai an ce zancen duniya ba ya b'uya. Bai sake mata magana ba har zuwa sanda suka isa Immigration office d'in. "Dama da zarar sun tambayi sunanki, kice musu Hamda Hammad na gaya miki." Ta d'ago tana son tambayarsa ya tsatstsareta da idanun

sa "Daga yau na canja miki suna, tunda ance ni ne Babanki, suma takardun makarantar gobe za mu je court ki yi changing name d'inki kin koma Hamza Hammad UU d'an borno." Tsit ta yi saboda sam ba zata iya magana ba. Ya fice daga motar, kafin ya yi mata magan

a ita ma ta bi bayansa tana mamakin sunan da ya lak'k'aba mata.

*******************

Cikin ikon Allah likitocin suka samu nasarar farkar da Hajiya Didi, ta hanyar gark'ama mata oxygen aka dinga zuk'o numfashinta. Ta farka sai dai sam magana ta d'auke t

saf daga bakinta, ga ta dai idanunta biyu amma ba ta uhm bata uhm-umm sai hawaye da suke kwaranya a idonta sosai musamman idan ta so yin magana ta kasa. Da k'afarta da komai kuma hannayenta suna aiki, bakin ne dai ya d'auke, amma likitocin sun tabbatar mus

u a kowane lokaci bakinta zai iya dawowa.

Hankalin D'an Borno family kam a tashe ya ke matuk'a da gaske, musamman Abbu da lokaci d'aya duk ya fita hayyacinsa, shima a lokacin da za'a aunashi tabbas za'a tabbatar yana buk'atar a yi admitting d'insa a hospi

tal.

Ita kuwa Ammi hankalinta a kwance yake ko banza dai ta san ta ture waccan matsalar, musamman ganin kowa hankalinsa ya kau daga kanta.

A kuma daren ranar ne Abbu ya turketa da tambayar me yasa sanda abin ya faru ba ta sanar da shi ba." Cikin muryar k

uka ta tabbatar masa da cewa tsananin kunyarsa ne ya sa ta kasa gaya masa kuma da wani ido ma zata iya dubansa ta gaya masa wannan abin kunyar. Kamar zai sake mata wata tambayar sai dai ya ja bakinsa ya tsuke don sosai yake jin haushin tuna lamarin gaba d'

aya.

Mahmah dai hankalinta ba a kwance yake ba, tana son ta hana Hammad tafiya da Hamda amma

Dida ta hanata, ta ce ta kyaleshi ba wani abu bane don ya tafi da itan, ta kuma ja kunnen d'iyarta Nanna akan ta kyaleshi kada ta sake yi masa maganar don a yanay

in da yake tsaf zai iya sakinta idan har ta cigaba da jayayya da k'in bin umarninsa. Haka tilas ta hak'ura sai dai ta k'udirtawa ranta sam ba zata bar Hamda ta yi rayuwar jin dad'i ba, tilas sai ta bak'anta mata har ta gwammaci ta bar gidan da k'afafunta.

_____________________

Suna fitowa daga Immigration office d'in ta ga ya d'auki hanya bai tsaya ko ina ba, sai wani k'aramin gida. Ba tayi magana ba har ya tsayar da motarsa ya fita ya bud'e k'aramin gate d'in. Ya shigar da motarsa y'ar madaidaiciyar

harabar gidan. Zama ta yi har sai da ya ce "Fito mana." Ta d'ago ido tana dubansa kafin cikin dauriya ta ce "Ya Hammad me zan yi?" Tsahon second yana dubanta kafin ya ce "Umarni na ba ki, ki fito kuma daga yau kada na sake jin kin kirani da Yaya Hammad ai

ki na ji aka ce ni d'in ba wanki bane, Ubanki ne don haka ki dinga kirana da Daddy kamar yarda kika ji su Kamla na kira na. Ki fito na ce." Ganin yarda ya tsare gida ne ya sata saurin fitowa. Gaba yayi a zuciyarta ta ce "Ashe dai mutumin nan mafad'aci ne?"

Sai kuma ta kama bakinta da sauri tunawa da ta yi matsayin mahaifi ya ke a wajenta. Idan ta tuna hakan sai ta ji wani iri a ranta. Ya murza key ya tura k'ofar k'aramin parlourn. Sannan ya shiga parlourn tsaf da shi sai k'amshi yake. Tana so tambayeshi gid

an waye sai kawai ji ta yi ya ce "Gidan abokina ne, mazaunin k'asar Birmingham, anan yake zama da matarsa idan sun zo hutu, shi yasa nima yanzu nake jin takaicin rashin gina gidan kaina, amma insha Allah soon zan gina ko don gudun kora daga gidan mutane."

Ta juya tana k'arewa madaidaicin parlourn kallo kafin ta ce "To me zan yi anan?" "Zama za kiyi kafin mu san abin yi, idan sauryin naki ya shirya auren sai na aurar da ke, ko ba shi da yarda zai ajiyeki sai na ba shi Aron nan, kafin ya samu inda zai ajiyeki

." A raunane ta d'ago tana dubansa kafin ta ce "Amma Yaya Hammad ba ni kad'ai zaka bari anan ba ko? Ka kawo min ko Kamla ce." Tsaf ya tsaya ya k'are mata kallo kafin ya saki tsaki ya ce "Idan na sake jin kin kira ni da Yaya sai na murji bakinki, kuma ba Ka

mla zan kawo miki ba Kamlo zan kawo miki, ba kiji yarda mu kayi da uwarta bane, ko ke kurma ce ba ki ji mai uwarta ta ce ba, idan za ki shirya rayuwa ke kad'ai ki shirya na gaya miki." Ya fad'a yana shigewa wani d'aki. Hamda ta bi bayansa da kallo hannayen

ta akan k'uncinta ta zabga uban tagumi, da gaske dukkan lamarinsa mamaki suke bata, shi kamar ma babu abinda yake damunsa daga bayyanuwar Sirrin nan..... Allah dai ya sa Zunnuraini ya shirya aurenta, ta samu zuciyarta da addu'a.

To sai mu ce Ameen.

N

Jikar Nashe ce..ALK'ALAMIN JIKAR NASHE

YA ABIN YAKE?

NAZEEFAH SABO NASHE

18.

08033748387



🏽



🏽



🏽



🏽📖📖📖



🏽



🏽



🏽



🏽

(Akwai complete book din nan akan naira 500 kacal ga wanda ba zai iya jumurin sauraro ba.)

Yau Didi jikin sosai ta mik'e id

anunta sosai akan y'ay'anta da suka baibayeta zagaye da ita a gadon asibitin.

Gwaggonsu Amina ce har a lokacin ba ta iso daga Dubai, don ta ce musu tana hanya a cikin satin mai zuwa.

Didi so take ta yi musu maganar Hammad amma ba baki, sai da dabara ta f

ad'o mata sannan ta duni gadanga ta yi masa alamar ya samo mata abin rubutu. Shi kad'ai take wa fara'a bayan shi ko kallon arziki ba ta yiwa Abbu da Lauratu.

Gadanga ya fita zuwa motarsa, ya samo mata littafi sabo da biro yana jin dad'in yau za su San abi

nda yake ranta. Sam ya mance da wannan hanyar ta rubutu.

Yana komawa d'akin ya manna mata biro da takardar. Ta amsa sannan ta fara rubutun duk da dai ta fi ganewa Ajami amma haka ta dagura Hausar. Ina Hammad da Hamda? Shine abinda ta rubuta ta mik'awa Gad

anga, ya yi tsai da ransa saboda bai San abinda zai ce mata ba, shi kansa bai ji dad'in hukuncin da Yayan nasu ya zartar be. Sai da ta sake tab'o shi ta tsatstsareshi da ido sannan ya saki ajiyar zuciya a hankali ya ce "Yaya ya kore su." Didi ta mai da kal

lonta kan Abbu kafin ta mik'awa Gadanga hannu ya bata takardar da rubuta kalmomi guda uku ta mik'a masa "Ka yi gaggawar dawo da su, kafin na wa ran ya b'aci." Daga haka ta mik'awa Gadanga takardar ta mayar da kanta Ta kwanta zuciyarta ce ta ke suya Idan ta

tuna da lamarin.

Abbu kam Shiru yayi fuskarsa a d'aure saboda umarnin Didin ya zo masa a bazata. Sam ba ya jin zai iya yafewa Hammad wannan gungumemen laifin, ita kuma yarinyar da zarar ya cigaba da ganinta tsanarta ce zata dinga hauhawa a zuciyarsa. Sai

dai ya san sarai ba shi da ja akan umarnin Didi musamman da ya lura ko son had'a ido da shi bata yi.

Ammi kuwa dama ba zuwa take ba, sabida tasirin idanun Didin a kanta yarda take k'in kula ta da banzan kallon da take mata dalilin kenan da yasa ta bi sha

warar Kady aka kai Didin wajen malami

ya d'aure mata baki, la'akari da duban da take mata ta san zata iya tona mata asiri. Shi yasa a daren ranar ta nemi shawarar Kady ita kuma ta bata shawarar a mannewa Didin baki, ba sai tana magana ba balle ta k'aryata

Ta. Shi yasa Ammin take shan shatafinta ko bakomai ta cusawa Sadiya bak'in ciki goma da ashirin, dama ta tsaya mata a rai bata son ganinta burinta bak'in cikin Abin nan ya kashe su ita da Didin idan yaso ta mallaki gida ba wanda zai saka mata ido.

Budiri

nta take sosai, musamman na shirye-shiryen auren y'ay'anta Najma da Nasma, ba ta damu sam da halin da ahalin d'an borno suke ciki ba, cafkar naira take a wajen angwayen son ranta irin surikan da take so kenan, y'ay'anta su samu mazaje na kece raini ba ta d

amu da wa za su aura ba? Menene halayyarsa? Burinta kawai su samu Hamshak'an masu kud'i wanda suka ci suka tada kai ba matasan masu kud'i ba, shi yasa ba ta kyashin fitar da ko nawa ne akan y'ay'anta don tabbas ta san kwalliya zata biya kud'in sabulu.

*

*****

Tsawon mintuna Ashirin yana zaune cikin motar yana jiran Hakimar tasa Nanna kenan, bai d'auka har a lokacin fushin take da shi ba da bai wahalar da kansa ya zo ba, da sai ya turo mata text ya ce mata jibi za su tafi. Dama yazo ne su fahimci juna ita

kuma ta zauna ta na b'ata masa lokaci. A d'abiarsa shi mutum ne da ba ya son rainin hankalin y'a mace sam ba ya jura. Wa la Allah ko don ya taso da taurin zuciya tunda abin ya faru ya dainewa mata uzuri a rayuwarsa. Gani yake duk halinsu d'aya, shi yasa k

o da aka ba shi zab'in aure ya ce su zab'a masa ko ma wacece ba shi da lokacin soyayya da y'a mace, shi yasa Sam fushin Nanna ba ya tasiri Akan sa. Sau tari da kanta zata yi fushin da kanta kuma zata sharewa kanta hawaye ta sauko ta zo tana neman sulhu a w

ajensa. Duka mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login