Showing 117001 words to 120000 words out of 129261 words

Chapter 40 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

56

rawa t

a ce "Abbu ina da magana." Gaba d'aya Abbu ya tattara nutsuwarsa kanta yana shafa kan nata ya ce "Maza Hamda gaya min me ya faru?" Kuka ta saka tana jin nauyin furucin da zata furta amma ya zama dole don bata san jefa kanta a hallaka "Abbu na fasa aurensa

don Allah ka saka ya rabu da ni..."

[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Gaba d'aya falon Didin ya Samu bak'uncin shiru, dukkansu a razane suke Kallon ta cikin mamakin furucinta da ya zo musu tamkar dirar aradu, Ammi ma zancen ya dirar mata a nata kunnen daidai

lokacin da ta sawo kai zata shigo falon Didin, tuni ta ja jikinta baya ta koma ta jingina da bango tana mayar da numfashi takaici da haushin wautar maganar Hamdan ya sata runtse idonta. Ban da wauta wace irin magana ce Hamda take yi bata ji kunyar Abbu ba

, bata ji ta Didi ba balle ta uwa uba Hammad da yake zaune a wajen. Ta ja tsaki kafin ta juya ta fice daga sashen Didin tana ayyana yarda zata samu damar ci mata mutunci yau. Sa'ada kanta ta ga ragon azancin Hamda sosai ta ga wautarta musamman ganin yarda

Hammad d'in idanunsa suka kad'a suka yi jajur alamar ransa a matuk'ar b'ace yake. Didi kuwa k'ank'ance ido ta yi tana k'arewa Hamda kallo tana son ta gano shin a cikin hankalinta take. Abbu ya ja ajiyar

zuciya kafin ya ce "Me yasa ki ke son ya sake ki?" Wa

nnan karan hawayene yake kwaranya akan fuskarta kafin ta mayar da kallonta kan Hammad da ta ga ya sunkuyar da kansa wani Abu mai kama da tausayinta yana son tsirga mata, sai ta maze tana tuno Yarda ta hangoshi da matarsa suna cikin farin ciki da walwala ki

shi ne yake damunta sosai ta runtse idonta kafin ta ce "Abbu bana son mai mata, ina da tsananin kishi ina tsoron fad'awa halakar ubangiji." Tsit falon ya sake d'aukan bak'uncin shiru Abbu ya shiga tunanin mafita don ya hango tabbas Hamda tafi Sakna kishi,

haka ya yi fama da Sakna kafin ta saba duk da har yanzun ma ba gama sabawar ta yi ba, ya dafa kanta kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shikkenan za'a san abinda za'a yi. Ta shi ki je ciki." Ta mik'e jikinta a sanyaye ta shige d'aki, Hammad kuwa ya bita da

kallo cikin tsananin takaicin ta da mamakin yarda har ta ke neman ya saketa, Hamdan Sa dai da suke matuk'ar son Juna sai ya ga kamar an jirkita mata tunaninta. Ya runtse idanunsa yana jin yarda bugun zuciyarsa ya canja lokaci guda, zuciyar ta cunkushe waje

d'aya sai wani irin zafi k'irjinsa yake masa, maganar da Abbun ya yi masa ita ta dawo da shi cikin hankalinsa "Me ka yi mata da har take neman saki a wajenka?" "Me kuwa Zai yi mata shak'iyanci ne irin na y'ayan zamani da kuma ganin yana nuna mata soyayya,

mama kuwa in dai ina raye Ai ba mai raba Aurennan. Ehe sai da zuciyarta ta buga ta mutu." Abbu shiru ya yi jin abinda Didin ta ce ya mik'e kawai ba tare da ya sake cewa komai ba, sai da ya kai k'ofa ya kalli Hammad d'in ya ce "Ka sameni a sitroom d'ina."

Hammad da duk hankalinsa ya jagule ya mik'e ya bi bayan Abbu. Yana jin kamar zuciyarsa ta fito don tsananin b'acin ran Hamda.



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍





I



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

YA ABIN YAKE?



46.

*08033748387*

A falo zaune shi da Abbu ya kalleshi "Matarka kishi ne yake damunta, kai kuma baka san ta yarda zaka tafiyar da lamuran mata masu tsananin kishi ba, ita mace mai kishi a duk sanda kake tare da ita bata son ta ji kana ambaton ko da sunan

y'ar uwarta ce, menene musabbabin dalilin da ya sa take neman saki?" Idanunsa sun kad'a sosai ya d'ago ya dubi Abbu "Akan mun yi magana da ita ta fi son zaman Abuja, ita kuma Nanna ta ce min itama tafi son zaman Abujan shine na ce tunda itace k'arama ta ha

k'ura ta zauna anan, abinda ya jawo ta ji haushi kenan." Abbu ya saki murmushi kafin ya ce "Dole zata ji haushi, ka san me yasa? Saboda ka mata baki biyu, me ya sa ka bata zab'i kafin ka bawa Nannan da take gaba da ita zab'i? Kuskuren da maza ku ke yi kena

n a yayin neman aure idan baka jajirce ba zaka zama lusarin namiji yanzu dai ka ga gaba d'aya abin ya b'aci, shawarar da zan baka tunda gidajen masu girma ne kowacce  ka bata part d'aya wata sama wata k'asa idan yaso idan kuka zo sallah Ku zauna a gidanku

na Kano Abuja ma kuna tare." Hammad ya yi shiru,

duk da yana tunanin hukuncin Abbun shine daidai amma shi sam bai masa ba, baya son had'a su waje d'aya don ba abinda hakan zai haifar illa tashin hankali ya san Hamda da d'an banzan kishi. Ya ja ajiyar numfa

shi kafin ya ce "Please Abbu ka dai rarrasar min ita, amma wallahi had'a su akwai matsala don Hamda tana da kishi." "Raba su ma akwai matsala don matuk'ar kana can da Nanna anan ma Hamda rigimar zata ta yi maka." Abbu ya fad'a cike da son tabbatar masa. Ha

mmad ya sake sakin ajiyar zuciya kafin ya ce "Hakan shine masalaha Abbu, idan yaso zan dinga tahowa every thursday da yamma na hak'ura da aikin friday d'in sai na koma monday da safe kaga na raba musu kwanakin kenan." Abbu ya jinjina kai kafin ya ce "Hakan

ma dabara ce amma fa sai uwar gayyar ta yarda tukun na ka san yarda zaka shawo kanta ta amince." Ya d'an saki ajiyar zuciya kafin ya ce "In sha Allah, zan bi da ita ta yarda zata amince." Ya mik'e a zuciyarsa yana tunanin ya zama dole ya fitowa Hamda a na

miji kafin raini ya shiga tsakaninsu. Abbu ya bi shi da kallo cikin murmushi yana tunanin tabbas Hammad shima ya d'aura k'afa a irin tasa wahalar da alamar Hamda ma Sakna ta d'auko mai gigita kwanyar d'a namiji lokaci guda.

______

Ammi kallon Sa'ada kaw

ai take tana mamakin kaifin basira irin na Sa'adan "Wallahi Didi na nema ta lalata Hamda Ammi, idan ba kiyiwa tufkar hanci ba, duk wani rashin mutunci da takewa mijin ta da d'aurin k'afar Didi, ita take sata raina mijinta wallahi, shi kuma soyayyarta ta ru

fe masa ido baya gane rashin daidanta sai nan gaba idan yana son ya juyata ta ce bata san zancenba." Ammi ta ja ajiyar numfashi kafin ta ce "Maza Sa'ada je ki ki kira min ita, duk abinda ta yi ina ji akan kunnena ta yi shi, kada kice ni nake nemanta." Sa'a

da ta d'aga kai ta fice da sauri. Tana shiga taga Hamdan kanta akan cinyar Didi tana taje mata gashi tana ji Didin tana sake  zugata "Kin ji na gaya miki wallahi ki kafe ke Habuja ki ke so haka kawai ga garin shugaban k'asa bak'in ciki zai min don kada na

je wani azimin na tare a gidanki, banda ma haka ke da gidan ubanki ba ubanki bane ya bada gidan ai sai inda ki ka zab'a za'a ce miki wai ki zauna a kano gari duk hayaniya ita ga y'ar mai ya kaita Habuja, mata sai uwar k'ibar tsiya da kyar fa take juya maza

unanta." Sa'ada tana hararar Hamdan ganin yarda take tuntsira dariya ta ce "Hamda d'an zo ki ga wani abu." Hamdan ta mik'e tana zura hula ta bi bayan Sa'ada, ba su dire ko ina ba sai falon Ammin. Tun daga kallo d'aya da tayiwa Ammin ta tabbatar yau lamarin

Ammin ba wasa, nan kuwa Ammin ta shiga surfeta da masifa "Don ubanki da kika kalli idon ubansa kika nemi saki baki ji kunya ba, ke shashashar ina ce idan banda Lusaranci uban me ya yi miki da za ki nemi saki, kin san hukuncin macen da ta nemi saki wajen m

ijinta kuwa? Balle ki kalli idon mahaifinsa ki ce wai d'ansa ya sake ki." "Ni yaushe na kalli idon Babansa na ce ya sake ni, ai Babansa bai zo gidannan ba, Abbu ne kuma Baba na ne shi da kansa ya fad'a kuma ni Ammi kin san me ya min na ce ya sake ni?" "Uwa

rki ya miki, kin ji na ce Uwarki ya miki, ba baki na miki ba idan kika bari Hammad ya sake ki ba za ki samu wanda zai maye miki gurbinsa ba, don yana da duk qualities d'in duk wani mijin da ake kira na k'warai na sake jin kalmar saki a bakinki wallahi sai

ranki ya b'aci, shashashar banza ko da yake ban ga laifin ki ba rainon Kaka ce haka za ki je ki yi ta shirme a gidan miji." Sunkuyar da kanta ta yi kawai tana sauraran fad'an Ammin da daga baya ya juye ya koma nasiha zuciyarta ta yi sanyi musamman da Ammin

ta saka tattausan hannunta tana share mata hawayen da suke kan fuskarta. Ta sake saka ta a hanya sosai da yarda zata yi ta mallaki zuciyar mijinta "Kishiyarki tana da wayo Hamda dole sai kin dage dantse idan ba haka ba ki ji a salansa Allah ya muku albark

a gaba d'aya."

A daren ranar masu kawo lefen suka kawo, gida ya kacame da ganin lefen Hamda, akwatina set hud'u kowanne dank'am da kaya na alfarma, da mukullin motarta, ita kuma Nanna nata set biyu itama da nata key d'in motar galleliya irin ta Hamda s

ak, Hamda kanta da ta ga kayan sai da ta jinjinawa Hammad tunda bata san wasu kayan Daddynta bane ya yisu ya shige d'aki zuciyarta cike da farin cikin ganin kayan wai ita Hamda ita ta rikid'e ta koma y'ar gata haka, Hamda dai da take a wulak'ance banda a w

ajen Didinta itace yau Ta zama abar so a wajen kowa ta kuma zama sanyin idon mahaifiyarta, duka dai dalilin Hammad, sai ta ji tana son ta ji muryarsa duk wancan fushin ya kau, ta shiga kiran wayarsa sai dai bugun duniya bai d'aga ba, sai ga Hamda tana hawa

ye tana sake kiransa sak'o ya turo mata "Na aiko da takardar ne?" Ras gabanta ya fad'i ta shiga duba sak'on tana zaro ido ga zuciyarta ta kasa fassara mata sak'on daidai da sauri hannunta na rawa ta rubuta masa "Takardar me?" Wannan karan bai jima ba ya am

sa mata da "Saki mana, ba shi ki ke so ba?" Hamda ta runtse idonta tana jin nauyin k'irjinta yana k'aruwa kada Fa Hammad ya ce zai ji haushin abinda ta masa ya saketa, da ina zata saka kanta bata jin zata iya rayuwa ba Hammad, daman duk kurari ne irin na y

'ay'a mata, sak'onsa da ya shigo ne ya sake tarwatsa mata zuciya don tsananin bugun da take gumi gaba d'aya ya jik'eta ta shiga k'ara ware ido tana nazarin anya da gaske yake abinda ya rubuta.....

Jikar Nashe ce!

[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Idan kin

amince za ki zauna a kano shine muradina idan kuma ba haka ba, ki zab'i abinda ya yi miki saboda na lura don kin ga Daddynki ne ya bani gidajen ki ke neman yi min iko a kansu..." wannan ne sak'on da ya turo mata tsananin mamakin sak'on ya sa ta shiga ware

ido tana nazarinsa ne Hammad yake nufi  itace zata masa gorin gida shikkenan zata amince ta zauna a duk inda yake so, ta runtse idonta zuciyarta na wani irin zafi da gaske dama haka auren mai mata yake? Sai yarda matarsa ta juya shi. Sam bata san hawaye na

sauka daga kwarmin idonta ba har sai da ta ji d'imunsu akan lab'b'anta jiki a sanyaye ta saka hannunta ta share hawayen haka kawai ta ji tana jin haushin aurenta da Hammad d'in tun yanzu har matsaloli sun fara samun mafaka. Shigowar Sa'ada ce ta sata tatt

aro nutsuwar dole ta saka a fuskarta don bata son kowa ya san sirrinta da mijinta. Sa'adan ma maze wa ta yi bata nemi ta ji ba musamman dama ita can haka take rayuwarta bata damu da sanin abinda ba - saka ta a ciki ba. "Kai Hamda lefenki ya yi Kurt ko y'ar

shugaban k'asa ai sai haka." Hamda tab'e bakinta ta yi tana cigaba da danna wayarta haka kawai ta samu kanta da gushewar murnar lefen daga zuciyarta. Ganin bata son magana ya sa Sa'ada ficewa daga d'akin.

Didi ta ja kayan fad'ar kishiyar Nanna gabanta a

kwatina set biyu ga mukullin dank'arareyar mota tab'e baki ta yi kafin ta ce "Ni fa ban ga dalilin wad'annan kaya da za'a laftawa waccen matar ba, yo fisabillahi ai ba son Hamdan take ba, yanzu kuma don rashin kunya sai ta saka hannu ta karb'i kyautar uban

ta." Ba wanda ya kulata sai bambamin fad'a take kafin ta ce "Ke Sa'ada tafi ki kira min ita na kafa mata sharad'ai idan ta amince falillahi hamdihi idan bata amince ba kuwa

wad'annan kayan ba rabonta bane."  Lauratu ta ware ido kafin ta ce "Wani sharad'i k

uma Didi ai ita kamata ya yi a lallasheta musamman an mata laifi wallahi." Didi ta watso mata harara kafin ta ce "Lauratu ki fita idona mutuniyar banza laifin uban me aka mata? Auren da ya yi ne laifi?" Shigowar su Nannan ce ta sa Didi jan tsaki murya a k'

asa ta ce "Haka kawai mata tana zaune shirin a wani bata kaya." A fili kuma sai ta washe baki "To zauna ki ga kab'akin arziki Uban Hamda dai ya k'watarwa y'arsa y'anci don haka kada in ji kada in gani wallahi kin wa Hamda wani abu irin wannan dukiya da ya

narka miki na tabbata don ki zauna da y'arsa lafiya ne, idan kuma ba kya son zaman lafiyar a mayar masa." Nanna fuska a had'e take kallon kayan kafin ta ja ajiyar numfashi ta ce "Allah ya bamu zaman lafiya ya kawar da y'an ba ni na iya a cikin lamarin." Di

di ta kalleta shek'ek'e "Su waye y'an ba ni na iyan? Eeh lallai wuyanki ya isa yanka. Ta wulleta da mukullin kafin ta ce "Kin yi da uwarki Sadiya da Maryama da kuke kira Dida. Rasa kunya." Murmushi Nanna ta yi kafin ta ce "Ni fa Addu'a na mana Didi." Daga

haka ta mik'e tana bud'e kayan ta yaba k'warai da karamci KK ta masa addu'a sannan ta saka su Sa'ada su tayata kwasar kayan.

__________

A kashegari Hammad suka tafi da matarsa Birmingham don su tattaro kan iyalinsu zuwa gida Nigeria. Ba k'aramin kai zu

ciya nesa ya yi ba, da ya k'i neman Hamda so yake ya d'orata akan saiti ta san zaman aure suke yanzu ba zaman saurayi da budurwa ba, hakan da ya yi kuma ba k'aramin hassala zuciyar Hamda ba, ta tattara lamarinsa ta watsar suma suka fara shirin tafiya Umara

.

______________

Tsawon sati biyu suka yi a Umarar a wannan gab'ar kuma a hanyar dawowa Hamdan ta fara wani irin zazzafan zazzab'i da haraswa ta galabaita sosai don komai bata son ci sai Apples da grapes hakan ya sa ta yi guzirinsu da yawa daga Saudi. D

uk da Asma'u da Amminta sun gane ba su furta mata ba su tsoronsu d'aya ma

Ranar da Didi zata fuskanci akwai cikin sun san akwai tab'argaza don haka suka yi shiru, Ammi dai ta mayar da hankalinta sosai kan kula da autarta gaba d'aya yanzu burinta ta ga Hamd

a ta kama zuciyar Hammad yarda ya kamata don ta lura kamar har yanzu basu kai matakin da take so ba, tunda har zasu iya d'aukan lokaci Suna gaba, don tana d'aukar wayar Hamdan ta ga ko Hammad d'in sun yi waya sai ta ga ba kiransa haka nan

Text messages sai

abin ya fara bata tsoro ya zama dole ta sanar da Hamda sirrin kame zuciyar d'a namiji. Tun a daren ranar da suka dawo ta rutsata a d'aki "Hamda me ke tsakininku da mijinki?" Hamda idanunta ya kawo ruwa ta d'ago tana kallon Ammin kafin murya a dashe ta ce

"Ni ma fa Ammi ban sani ba haka kawai ya daina min magana." Ammi ta girgiza kai "labari kike Hamda ta yaya kina amarya miji zai yi wannan dogon fushin da ke? Ki fito ki gaya min gaskiya ni mahaifiyarki ce." Kuka ne ya fara zuwa mata cikin muryar kukan ta s

higa ba wa Ammin labari. Ammin tana gama jinta ce "bud'e kunnenki ki ji da kyau ba 'a kama zuciyar miji ta hakan da kika b'ullo na tabbata k'in bari ya kusanceki kike shi yasa ya yi wannan dogon fushin dake idan kika

bari ya saba da kusantar jikinki shine

ba zai iya dogon fushin da ke ba, saboda ko ya yi dole ya sauko ba 'a wa miji rowar kai kina ji na?" Tana hawaye ta d'aga kai "Yauwa Yanzu na ji ance gobe zai dawo kuma saura kwana biyar a fara biki ban ce ki bari ya kusanceki yanzu ba, ki bari akwai had'i

n da zan miki da zarar an kaiki gidansa ya kusanceki ina tabbatar miki ba  zai sake iya d'aukan ko awa biyu yana fushi da ke ba, ki kuma dage da

Shan zuma da tsumin da na baki turaren tsuguno kada ki yi wasa dashi kin ji ai." Hamda a kunyace ta d'aga kanta

duk da ta ga ita Ammin ba abinda ya dameta kamar ma da k'awarta take magana.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login