Showing 21001 words to 24000 words out of 129261 words
/>
yaje ya gayawa duk uban da zai gayawa, sai me? Idan kika tubure ubansa ne yayi cikin akwai yarda za'ayi dake ne? Idan ma ya fad'a dole shima Za'a tuhumeshi...." haka tayi ta masifa kafin su bar parlourn da sauri, kana ganinsu ka san a hassale suke. Allah
yaso gidan ba kowa Mahmah tabi su Nanna gidan iyayenta, ita Didi sun tafi asibiti ita da Hamda. Don haka suka samu wannan damar suka shiga wajen nasa.
Ya dad'e yana cizar leb'ensa na
K'asa kafin ya furzar da wani hucin numfashi ya mik'e. Wanka ya shiga ya
na fitowa kuma yayi shirin zuwa gaida surikansa, Gidan su Nanna.
_______________
Kady a zafafe ta sake duban Sakina kafin ta ce "Wallahi kina so ko ba kya so sai an kawar da wancan banzan a doron k'asa, don na lura da shirin tozartaki yazo, kina gani
n yarda yake cika yake batsewa idan ya san wata ai bai san wata ba shashashan banza, ba dai kince yarinyarsa da ita take kama ba?"
Sakina ta runtse hannayenta kawai kafin ta ce "Ban so zata kaimu ga jallin kisan kai ba, amma idan haka ne mafita ba yarda
zamu yi, sai dai zamu aikata hakan ta hanyar da ba za'a saka mana zargi ba, wacce hanya kike ga zamu bi."
"Kunce burkin motarsa da k'usoshin tayar motar ta hanyar had'a baki da ma'aikatan gidan nan ko mak'udan kud'i sai mu shak'a musu.........DON SAMUN W
ANNAN LITTAFIN KYAUTA NA YA ABIN YAKE SHIGA WANNAN LINK D
’
IN ZA
’
A DINGA TURASHI SAU UKU A RANA.
DAGA ALKALAMIN NAZEEFAH SABO NASHE
Open this link to join my WhatsApp Group: https://
chat.whatsapp.com/5Y2EmZDu7OvHg6iDTCY81D
Alk'alamin Jikar Nashe.
Y
A ABIN YAKE?
08033748387
Wattpad muna page 13
Follow me on Wattpad
@Nazeefah381
✍
🏽
✍
🏽
✍
🏽📖📖📖
✍
🏽
✍
🏽
✍
🏽
11
*******************************
Idanunta jajir ta sake zubesu a fuskar kady "Wallahi har ga Allah bana son kalmar kisan nan ba
yarda zan
yi ne tunda ya riga ya kafe ne, tun yana shekarun yarinta dama yaron nan kafiya ce da shi da d'an banzan taurin Kai." Kady ta ja tsaki kafin itama cikin takaici ta ce "D'an banza kina kallon yarda ya rufe ido yana magana a gadarance alamar ko son magana d
a mu baya yi, ni fa da zaki bar ni da kaina zan aika da shi lahira amma tunda kina tsoron kisan bari mu bi ta yarda kike so, zan
Aiko masa da fataken dare su ja masa kunne na k'arshe idan ya k'i yarda kuwa wallahi zai gane kurensa."
Sakina ta d'an ja fasa
li kafin ta ce "Shikkenan, Allah yasa mu samu nasarar hakan, matsaloli sun yi min rufdugu a kaina, ga matsalar yarinyar nan da matar can ta saka musu ido akan lallai sai sun fitarda
miji, ga matsalar nan da muke ciki.
Kady ta dafa kanta murya a
raunane c
ike da tausayinta ta
ce "Komai zai daidaita Insha Allah, su yaran ki bar lamarinsu a hannuna zan samo musu mazaje na kece raini, tunda kyawawa ne ba zasu yi wuyar shigaba, nayi mamaki ma da har yau ba wani k'usan Gwamnati da yazo ya kawo musu hari, sai kac
e wad'anda aka yiwa asirin bak'in jini."
Ajiyar zuciya Sakina taja kafin ta ce Allah ya shige mana gaba, zan saka su tura hotunansu sai ki watsasu a status k'ila ta wajenki a dace tunda kina huld'a da manyan k'asar nan, da kuwa ranar nayi rawa da tsalle
idan senator ko minister suka taya." Kady murmushi ta saki kafin ta ce "Ai
ba abin mamaki bane, kyawun da
suke da shi kad'ai ya isa yaja hankalin maza kansu, ki saka dai suje ayi musu makeup na
kece raini, sai a kira FARISH yayi musu hoto, don naga ya iya
fidda
hotuna masu kyau." Ammi cike da
murna ta ce "Haka ma za'ayi wallahi kin kawo idea"
__________________________________
Daga ita sai Didi a parlourn, Didin tana taje mata dank'ararren gashin kanta da bata son gyarawa sai dai ta wanke, mita take tay
i mata "Ke sai kace ba mace ba a haka zaki samu mijin aure, naga ko y'ar powderr nan ta y'an mata ba shafawa kike Ba kullum idanuwa a kod'e kamar nama, ai gwara ki dinga gyara jikinki ko kya samu saurayi kiyi aurenki ki huta da masifar Uwarki. Gobe zan bak
i kud'i dama ki siyo kayan kwalliya har da gazal da jam baki, don ance ko kana da kyau ka k'ara da wanka, amma lamarin tsoro yake bani ace har yanzu ba wanda yazo yace yana sonki, ko kuma don ana ganin y'an uwanki masu kalar larabawa, kema ai ba mummuna ba
ce kawai da duhun fata ne da ke na kuma tabbata da rashin gyara."
Shiru Hamda tayi mata, zuciyarta ta lula can tunani, sai yanzu da Didin tayi mata maganar sannan
ta ankarar da ita, da sam ta manta a irin shekarunta ya kamata ace tana da saurayi ko da ku
wa ace na wasa ne, ko me yasa ita bata da saurayin a tsayin rayuwarta ba wanda ya tab'a cewa yana sonta, ba mamaki rashin kwalliyar ne kamar yarda Didi tace idan kuwa hakane ya zama wajibi ta fara kwalliya, don da gaske itama tana son tayi aure ta bar gida
nnan fatanta da burinta ma bai wuce ta auri d'an wani garin ma, ta yarda zata dad'e bata zo gida ba.
Dai-dai lokacin da Didin take kame mata k'ak'k'arfan gashin nata ya turo k'ofa ya shigo, idanunsa a kanta, da tayi saurin sunkuyar da kai. Ya d'an tab'e b
aki had'e da zama gefen Didin.
Ta kuwa washe masa baki ganin ya turo mata leda shak'e da kaya gabanta. Kaya ne fal na ciye-ciye a ciki sai kayan tea da k'unshin ledar gasassun kaji a ciki, ga yoghurt masu sanyi.
Fara'ar Didi ta yawaita cewa take "Yanzu
na san Hammadu ya dawo k'asar nan, wallahi da a zuciyata har na fara tunanin ko ka zama zumbuli ne kakan marowata, har na fara tsinewa Ingila gaba d'ayanta don na tabbatar su suka koya maka rowa, kai da kake kyauta kamar baka so, Ina matar taka ta dawo kuw
a?" Ya d'an girgiza kai yana sakin murmushi ganin yarda take cin naman kamar wacce a shekara sau d'aya take ci. Tsaki taja kafin tace "Zancen banza zancen wofi, to zaman me take a gidan nasu? Ta barka anan wa zai kula da kai, idan kazo nan kaci abinci, cik
in dare kuma wa zai gyara maka shimfid'arka, fisabilillahi A'a nifa bana son shegantaka daga kwana biyu shine za'a tafi har hud'u, ina ce tuni aka yi sadakar bakwan uban nata, wanda ya mutu ba ya mutu ba fisabilillahi na meye kuma zata rashe waje ta zauna
kai kuma ta barka da rungumar filo cikin dare da mafarkai barkatai"
Tsaf ya had'e fuskarsa ganin zata yi masa b'aranb'arama a gaban Hamda, itama Hamdan kunya ce ta d'an kamata don sarai ta san inda zancen Didin ya dosa, ta mik'e ta shige kitchen gwara ta
tsiri wanke-wanke akan ta zauna jin hirar Didi marar kan gado.
Tana jiyoshi yana yiwa Didin sababi, da sanar da ita shi ya amince matar tasa taje a zafafe yace "Kuma ni nace miki idan bana tare da matata ina rungumar pillow da mafarkai cikin dare?da zak
i bani kunya gurin k'aramar yarinya."
Tsaki Didi tayi ta ce "Zancen banza Zancen wofi Hamdan ce yarinya? Allah na tuba itama tun yaushe na gama gane aure take so, ai Ina lura da mafarkan da take yi da matse filo a k'irji, don haka ma zan sanar da ubanku a
yi mata aure."
Hamda da take kitchen ji tayi kamar ta nutse cikin k'asa saboda bala'in kunya da gaske yau Didi ta shammace ta ko a ina ta tab'a kamata tana rungumar pillow? ita ina ruwanta ma da wata soyayya, don takaici har wata y'ar k'walla ce ta zubo m
ata, yanzu wani kallo Didi take so Yaya Hammad yayi mata?
Shi kuwa don takaici kasa ce mata komai yayi, a fusace ya mik'e ya fice daga d'akin yana mamakin tsofaffi yarda ba ruwansu suke sakar zantukan da suke so son ransu ba tare da sun tauna abinda zasu
fad'a d'in ba. Ya tabbata Hamda tana can tana jin takaicin furucin Didin. Shi kad'ai kuma sai ya saki murmushi ya girgiza kai kawai ya fad'a sashen mahaifiyarsa.
_____________________________
Hamda kuwa cikin takaici ta amsa kiran Didin da take ta k'w
alla mata.
Ta fito daga kitchen d'in fuskarta a had'e tana cono baki, ji take kamar ta rufe Didin da duka.
Didin data lura da b'acin ran kan fuskarta taje Tsuka ta ce "Kamar kumbo kamar katanta, shima haka ya fita yana muzurai dad'in abin dai a dake ba
zan daku ba, a zage ba zan zagu ba sai dai a zageni a zuciya, wannan kuma mutum shi ya jiyo, k'arya aka yi miki ba auren kike so ba ranar fa ina kallonki kina barci kina faman matse k'afa."
Hamda ta d'ago ta watsa mata wani kallon takaici kafin ta ce "Wal
lahi Didi ba kyau, Allah fa yana kallonki, ki ji tsoron Allah yanzu me kike so Yaya Hammad ya d'aukeni?"
Dariya Didin tayi ta ce "D'an nema, yazo da k'warin gwiwarsa da alama yunwa yake ji, anzo cinye min abinci,daga maganar gaskiya kuma ya fice, ba don
halinsa ba d'auki abincinsa ki kai masa ko don himulin siyayyar nan da yayi mana."
Hamda ta waro ido kafin ta ce "Ni zan kai masa abincin? Cabd'i ai kam ba dani ba. Da wani idon Zan kalleshi bayan kin gama kwaye min zani a wajensa."
Didi ta zabga mata h
arara "Ni kike so in tashi in kai masa kenan ko? Da yake ni marainiyar wayonki ce, idan da Uwarki ce ai da ba ki fad'a mata haka ba, sai ni da kika ga na sakar miki ko? To ko ki d'auka ki kai ko nayiwa Gadanga waya yazo shi ya kai masa. Hammadun bai fi min
uban kowa ba, duk cikinku wa ke kula da ni yarda shi yake yi, to wallahi ko ubanki sai na kira na saka shi ya kai masa abicin nan, tunda ke ban isa dake ba."
Jin haka da sauri Hamda ta sunkuci tray d'in ranta fal da takaicin Didin.
Tana fita kuwa Didi
n ta saka dariya ta ce "Ja'ira y'ar nema banda nayi mata haka, ba zata je ba."
Dai-dai zata shiga k'ofar sashensa shima ya sawo kai, ya dawo daga b'angaren Mahmah. Da sauri taja gefe kanta a k'asa murya na rawa tace "Didi ce tace a kawo maka abinci." Ban
za yayi mata yana bud'e k'ofar. Ganin bai kulata ba ya sanya kanta cikin parlourn, da ba abinda kake ji sai k'arar Ac da sautin karatun alk'ur'ani daga bakin Sudais cikin suratul wak'ia, sai kuma sanyayyen K'amshin turarukan wuta, da suka gauraya da nasa t
uraren.
A dininig ta ajiye, cikin sauri har ta murza handle d'in k'ofar "Hamda" ya kira sunanta cikin ginshira wanda direct zata iya cewa shine karo na farko da taji sunan nata akan harshensa a dai yanzu da ta manyanta.
Kamar ba zata jiyo ba sai kuma ta
juyo a hankali ta k'arasa inda yake zaune, tsawon seconds yana danna waya bai ce mata komai ba har ta ji ta gaji da tsayuwar sai taji yace "Aure kike so kamar yarda Didi tace?" Da wani irin shock take kallonsa kafin ta russunar da k'wayar idonta, duk da C
ewa idanunsa ba akanta yake ba Ta k'asan ido yake kallon duk halin da ta shiga, yana cigaba da danna wayarsa ya ce "Ina jin ki, ke nake saurare, kina da tsayayyen saurayin da ya shirya maganar aure ne?" Wannan karan ba jikinta kad'ai ba har k'afafunta rawa
suke mata ta rasa me yasa yake mata kwarjini ta fi jin shakkarsa fiye da Abbu mutumin da ta kwana da sanin cewa shine mahaifinta. "Ba fa na son rashin hankali, na miki magana kin mini banza, nace kina da tsayayyen saurayin da zuciyarki ta amince zaki iya
aurensa ko Babu."
Maganar ce ba zata iya ba, ta tabbata idan ta bud'e baki tayi magana muryarta rawa zata yi bai zama lallai ma ya fahimci me ta ce ba. da dai ace zai kalleta ne to da sai ta girgiza masa Kai, amma magana yake yi hankalinsa baya kanta, ka
mar yarda take hasashe, sab'anin haka tar yake kallonta ta yanayin da bai zama lallai ta fahimci ita yake kallo ba.
"Kurma ce ke?" Wannan karon a zafafe yayi maganar da alamun b'acin rai cikin maganar tasa ji yake tamkar ya kai mata mangari. Idanu ya tsa
tstsareta da su. Hakan yasa ta shiga wasa da yatsun hannunta kafin cikin dakiya ta ce "Bani da saurayi, kuma ma ni ba'a tab'a cewa ana so na ba, sannan ni ba ni na gayawa Didi ina son aure ba." A rarrabe tayi maganar kamar mai in'ina amma tsaf ya had'e ka
laman nata ya fahimcesu don haka ya saki wata ajiyar zuciya kafin ya ce "Auren naki kuma shi zai sama miki kwanciyar hankali ba, ya fitar dake daga k'angin bautar ba gaira ba sabar da kike ciki ba, don haka ki saka a ranki kin kusa aure, na baki sati guda
jal ki fidda gwaninki kafin Na bar k'asar nan zan miki aure Na gaji da ganinki a wannan bak'ar rayuwar, da ba abinda zai samar miki y'anci sai aure. Kije kiyi k'ok'arin kawo min miji nan da sati guda, 3 months kawai zan yi a garinnan hakan yana nuni da cew
a ana sallah cewa zan tafi, kafin nan insha Allah zan aurar dake."
Wani irin bugun k'irji ne ya Sameta, kafin ta runtse ido cikin wani yanayi da kai tsaye ba zata bashi suna ba, abu d'aya Ta sani kamar yarda ya ce Aure ne mafitar ta,
Abin tambayar wa zata
kawo nan da sati guda kacal? Ita da ba'a tab'a cewa ana sonta ba.
"B'ace min da gani"
Taji muryarsa daga sama, hakan yayi saurin dawo da ita cikin hankalinta, duk da ba kallonta yake ba ta tabbata da ita yake, don haka da sauri ta juya har ta na yi kam
ar zata kifa.
_____________________________
Ko da tazo barci, kasa barcin tayi tana kallon Didi da take sallolin Nafilfilunta hakan yasa itama ta mik'e a fili ta furta Barci ba nawa bane gwara na kaiwa Rabbi Kuka ne yayi min maganin damuwata sannan ya
kawo min Mijin Aure Kwana kusa.
⭐
️
Sanye take da Hijabin Islamiyyarsu da yazo mata har k'asa, fuskarta d'auke da nik'af sai dai ta d'age shi sama.
Yau kam har da y'ar powderrta da jambakinta light pink ta goga. Dai-dai bakin gate zata shiga taji ance "Y
'an mata salamu Alaikum." Da sauri ta juyo tana amsa sallamar duk da ta d'an firgita a karon farko sai dai bata bayyana hakan ba.Matashin da zai kai shekaru Arba'in ko kusa da haka ya jefeta da wani murmushi da yasa ta saurin d'auke ido daga kansa "Kiyi ha
k'uri na tsayar dake a hanya, sunana Zunnurain idan ba damuwa numberr wayarki zaki bani, nafi awa biyu anan ina jiranki tunda zaki shiga islamiyyarku Na ganki,kwarjininki ne ya hanani yi miki magana...." Hamda da kyar ta d'ago kanta tana masa kallo na biyu
, kafin ta daure ta nuna masa wajen zama da yake gefe kad'an a kuma daidai lokacin Motar Hammad ta danno Kai, har ya yi parking ya fito idanunsa ya na kansu, kana ganinsa kaga matashin Dattijo da ya kusa cika shekaru Arba'in cif, wannan karan sanye yake ci
kin farar shadda fara tas sai zabga k'yalli take, kansa sanye da zanna bukar da tayi masa kyau sosai cikin takunsa na isa da ginshira ya isa wajen da suke zaune, cikin wata k'aramar bukka.
Tunda ya nufosu gaban Hamda ya ke dukan Tara-tara, da sauri ta sunk
uyar da kanta, tana gani ya mik'awa mutumin hannu da a shekaru zasu iya kai d'aya. Suna gama gaisawa ya shige gida sai sannan Hamda ta samu salama ta d'ago idanunta cikin na Usman tana murmushi shima murmushin ya sakar mata, a hankali ya furta "Yayanmu ko?
" Ta d'aga kai tana wasa da zoben hannunta. Shikkenan tashi ki shiga gida, sai na dawo insha Allah don naga ba ki sake da ni ba sosai, kuma ma ya kamata na fara neman iso kafin na zo wajenki..."Follow me on ArewaBooks
https://arewabooks.com/book?id=635c
58dc8a75f51b283a378e
Follow me on Wattpad
@Nazeefah381
12
✍
🏽
✍
🏽
✍
🏽📖📖📖
✍
🏽
✍
🏽
✍
🏽
Tunda ya fara maganar tayi k'asa da kanta sai da taji yayi maganar neman iso wajen Iyayenta sannan ta d'ago tana masa wani irin duba
A tsorace take kallonsa, kasantuwa
r ba'a tab'a tareta da magana kwatankwacin wannan ba.
Taji zuciyarta na wani irin bugu kamar yarda dai hakan take faruwa ga tarin y'an mata, a karo na
farko da saurayi ya taresu da kalmar Na gani Ina so.
"Kin amince min?" Ta jiyo maganarsa daga sama tamka
r dirar mikiya. Da sauri ta d'aga kai, don bata da zab'in da ya zarta hakan, Wa take da shi bayan shi? Da zata ce bata amince masa ba?
Ta tabbata Allah ne ya kawo mata mafita a lokacin da ta kai kukanta garesa cikin sakankancewa da cewa Jallan ya amsa ma
ta. Sai ga shi a cikin lokacin da bai gaza kwana biyu ba kacal Allah ya aiko mata da Zunnurain ya aureta, ashe dai ba zata bawa Yaya Hammad kunya ba, kamar yarda yace ya bata kwana bakwai, zata je masa da labari mai dad'i Samun Miji a gab'ar data dace.
"
Kisa min digit d'inki" Ta sake jiyo maganarsa wannan karan ma a bazata. Da sauri ta kalli wayar hannunsa tana girgiza kai tare da cewa