Showing 51001 words to 54000 words out of 129261 words

Chapter 18 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

66

YAKE?

22.

Har bakin k'ofa ya ja hannunta ta raka shi sannan ya nuna mata yarda zata kulle k'ofar kasancewar ta mai password ce. Yana murmushi ya fice daga gidan da d'an sauri nishad'i fal zuciyarsa

Na mallakar matar da yake buri.

Ko da ya isa gidansa ya dad'e tsaye a k'ofar gida cikin mota yana tunanin yarda za su kwashe da Nanna dama danginsa gaba d'aya idan aka gano ya aure Hamda. Tabbas ya san sai Nanna ta kusa zaucewa kasancewarta a bigiren mata

masu d'an banzan kishi. Ya lumshe idanunsa yana sakin murmushin hango tak'addamar da za'a buga, hakan kuma shine hanya d'aya da Ammi zata fito ta fad'i sirrin da take k'udundunewa.

Ya fice daga motar yana sakin ajiyar zuciya. A falo ya ga Nanna zaune ta

ci kwalliya kamar bata so da gaske ta yi kyau sosai ya d'an zuba mata ido ita kuma sai sakin murmushi take don yau dai kam hankalinta a kwance yake kamar tsumma a randa. Tana murmushin ta ce masa "Har ka dangana ta ga gidan mijin?" Ya d'aga kai yana jifant

a da na sa salon murmushin da kai tsaye za'a kiransa na mugunta. Ta mik'e ta koma hannunsa had'e da zaunar da shi kusa da ita ba k'aramin missing d'insa ta yi ba d'an kwanakin da suka yi ba sa tare. Shiga jikinsa ta yi sosai kafin ta ce "Yanzu hankalinka y

a kwanta ka aurar da y'ar so. Na san zan samu kulawa da duk ka banzatar da lamarina." Ta fad'a tana wasa da sumar kansa. Ta nan ta ke karya lagonsa ya kuwa hau lumshe ido yana amsar sak'onta. Har cikin ransa tunanin Hamda yake ina ma itace zaune daf da shi

haka tana wasa da sumar kan sa. Ganin ya amshi sak'onta kamar yarda take so ya sa ta sake ba da k'aimi kasancewar yara basa nan sun yi barci yasa ta samu sake ta dinga yi masa abubuwan da suka lula shi duniyar Hamda. Da sauri ya mik'e suka shige bedroom.

________________

Hamda kuwa tana jin tashin motarsa ta rufe k'ofar tana sakin wata irin ajiyar zuciya had'e da zubowar wasu siraran hawaye da zata iya kiransu kai tsaye na zafin kishi. Tana da tsananin kishi ita kanta ta sani shi Yasa sam bata so auren

mai mata ba. Amma ba zata ja da hukuncin ubangiji ba za ta yi ta addu'ar Allah ya sauk'ak'a mata. Jikinta a sanyaye ta shiga ta gyara kitchen d'in da komai na cikinsa ya zama fari. Tsaf ya fito yana walwali tabbas Hammad ba k'ananan kud'ad'e ya kashe a gi

dan ba, gaba d'aya ya d'auke mata nauyin komai da ya kamata ace uba ne ya yi.

Parlourn ma komansa fari ne da adon black kad'an. Ta sake gyare parlourn sannan ta koma d'aki wanka ta yi ta tada sallolinta nafiloli kafin ta yi shirin barci ta kwanta. Sai d

ai me tana kwanciya tunanin Hammad ya fad'o mata yanzu haka yana can sun tsunduma wata duniyar shi da matarsa hakan ya sa ta runtse ido zuciyarta ta yi nauyi saboda b'acin rai. Addu'a kawai take akan Allan ya sauk'ak'a mata.

*******************

An c

i nasara sosai Bakin Didi ya bud'e bayan yawan addu'oi daga bakin manyan malamai na karya sihiri sai dai harshen ya d'an karye kad'an maganar bata fita yarda ya kamata. Mijin Asma'u ya tabbatar musu komai zai daidaita insha Allah.

Da asuba kawai suka ji D

idi tana kiran Atma'u wai Asm'au. Mama Asma'u ta yi saurin bud'e ido cikin farin ciki take duban Didi tana fad'in Alhamdulillah Didi na ke ce kika yi Magana." Didi ta d'aga mata kai tana sakin murmushi ta ce "Ni te Atma'u Alhamdulillah Na ta mu lafiya." Di

di dai (s) d'inta ta d'auke gaba d'aya shi yasa take mayar da ita (t) Asm'au ta kama hannunta tana dariya Alhamdulillah Didi ta lumshe ido tana farin ciki itama da maganar da ta fara. Ashe ba k'aramar k'una wad'anda ba sa magana suke ji ba tabbas ta na tau

saya musu a kuma yanzu take sake jajanta musu ubangiji ya sa hakan ya zama kaffara a garesu kuma sanadin shigarsu aljanna. A tsawon lokacinnan tana da abubuwan cewa da yawa sai dai ba halin magana rubutun kuma ba wai ta k'ware a hausan bane.

Ta mik'e sosa

i ta gyara zamanta "Atma'u kira min d'an Ki Hammad a waya, tun da abin nan ya faru nake cewa a kira min shi a waya tun k'i" Asma'u ta d'au waya ta shiga kiran layin Hammad a waya da layinsa na Birmingham.

Tsawon lokaci yana jin kiran idanunsa sauke akan w

ayar sai dai ganin daga family ake kiransa ya gagara d'aukar wayar musamman ganin Gwaggo Asma'u ce take kira daga layinta na Nigeria ya tabbatar ta je Nigeria kenan. Kimarta da take gani yasa ya kasa burus da kiran a karo na uku da ta sake kiran ya janye N

anna daga jikinsa had'e da kara wayar a kunnesa murya can k'asa ya ce "Hello Mama ina yini?" Asma'u ta saki ajiyar zuciya yau da aka ci sa'a ya d'aga wayar "Mun wuni lafiya? Yau ka ga damar d'aga wayar kenan? Yanzu Hammad yaushe ka zama yaro mara jin magan

a har haka? Ka

Saka k'afa ka yi tafiyar ka ka bar mahaifiyarka cikin damuwa ka kyauta mata kenan?" Tsit ya yi da wayar a kunnensa gabansa yana wani irin duka sai yanzu ya tuna irin b'acin ran da ya baro Mahmah a cikinsa "Ka kyauta ina tabbatar maka idan Sa

diya ta rasa ran ta to bak'in cikin ka ne ya kasheta ga Didi zata yi maka magana." Ta fad'a tana manna wayar a kunnen Didi "Hello Hammadu a duk inda ka ke ma kayi gaggawar dawowa gida ka warware k'ullin da bahaguwar matar uban ku ta k'ulla maka don na tabb

atar akwai lauje cikin nad'i." Murya a cunkushe ya ce

"Insha Allah zan zo ko next month amma kin san fa Abbu ne ya kore ni ba tare da ya ji ta bakina ba." "zancen banza zancen wofi, zancen Umaru har wani abin kamawa tallamamme da mace ta riga ta gama da sh

i. Ai ni na tabbatar da cewa Takina na haifawa Umaru Allah ya taimaki Utmanu kakanku ba ya raye balle bak'in cikin Ummaru ya kashe shi. Ka zo idan ka ta mu hutu don Tadiya ma uwarka a cikin matsananciyar damuwa take." Ya ce "To Didi zan zo, amma ya naji ma

ganarki kamar ta y'an koyo kin mayar da S T?" Ya fad'a yana tuntsirewa da dariya daga can Didi ta ce "Ai tuni na tan Umaru ya haifi d'an banza to Tadiya ka yiwa dariya ba ni ba."

Shi dai katse wayar ya yi yana sakin murmushi tare da kallon Nanna da ta tsat

stsareshi da ido saboda tana cikin morar jikinsa wayar ta dameshi da kira fuska a d'aure ta ja blanket ta d'an rufe jikinta don tana lura da kallon da yakewa k'irjinta ita kanta sau tari tana jin haushin yarda k'irjin ya zube ya lalace tilas ma ta nemi mag

ani, don ta lura hakan na son jawo mata matsala da ai ba haka yake mata ba san da K'irjin yake a gyare tsam da shi. Murmushi ya d'an saki tare da d'an janyota jikinsa don ya lura  matse take sosai kada ya shiga hak'k'inta.

Didi ta kalli Asma'u Ta ce "D'

an banza ni dama na san sharrin Takina ne, ai kuwa watan jin kunyar Takina ya kama." Asma'u dariya ta yi kawai zuciyarta na sauka daga b'acin rai da yake addabarta ko bakomai yanzu ta hak'kak'e Hammad ba shi ya yi cikin Hamda ba.

________________

Tun a

suba da ta farka ta kasa komawa dama barcin da kyar ya d'auketa. Hakan yasa ta mik'e ta gyara gidan tsaf sannan ta fesa wanka aka kuma yi shigar wata doguwar riga mai d'an banzan kyau rigar ta bi ta kwanta a jikinta had'e da fitar da duk wata sura ta y'a m

ace da take jikinta. Mayafi ta samu ta d'an yane kanta da shi don ita kanta ta ji kunyar shigar tata. Sai zabga k'amshi take haushinta d'aya rashin irin humrorin Nanna balle turaren wuta sai air freshners da humidifier ta bi ta bad'e gidan da su.

Kafin 8:

00 ta gama komai har chips ta soya da kwai sai black tea da gasasshen kifi. Tana zaune ta tasa abincin a gaba sam ta kasa ci kishi ne yake nuk'urk'usar zuciyarta. Ta jiyo dirin motarsa da sauri ta gyara zamanta.

Tsawon mintuna biyu ya shigo cikin parlourn

fuskarsa fal murmushin farin cikin ganinta. Tana sunne kai ganin yarda ya tsaya yana bin sassan jikinta da kallo tace "Ya Hammad ina kwana?" Shiru bai amsa ba hakan yasa ta d'ago da niyyar sake gaisheshi tunaninta ko bai ji ba. Take kuwa idanunsu suka sar

kafe cikin na juna yana jifanta da wani irin narkakken kallo. Ya mik'a mata hannu alamar ta zo jikinsa. Nok'e kai ta yi cikin matsananciyar kunya duk da tana buk'atar hakan. Hannu yasa ya mik'ar da ita tsaye ya manne jikinsu sosai tamkar zai mayar da ita c

iki. A kunne ya rad'a mata "K'auyis kawai, ni bana son gaisuwar y'an k'auye haka Nanna take gaishe ni duk Safiya." Ya fad'a yana manna mata sumbata a lab'ba. Saura k'iris ta fad'i saboda yarda jikinta yake shaking ga haushin maganar matarsa da ya soko mata

. Ta yi kicin-kicin da fuska kamar ta fashe da

kuka.Sam bai lura da ita ba balle ya san ta na yi. Shi kansa gani ya yi k'afafu nasa sun kasa d'aukansa shi yasa ya sunkuce ta zuwa bedroom Sai dai yana direta ta hau janye jiki tana kuka da had'a shi da Allah

akan ya bari ba ta so. Ya runtse idonsa jin kukan nata ya yawaita kawai ya kyaleta yana ji shima kamar ya saka mata kuka. Da kyar ya shige toilet ya sakarwa kansa shower.

Ko da ya fito tuni ta fice daga d'akin tana mayar da numfashi ta tsorata da lamari

n sosai don haka tayi masa haka idan ban da haka ita mai son ta faranta masa ce.

Ko da ya fito kallo d'aya ya yi mata ya zauna daga gefe yana zubawa tray d'in abincinta ido da alama ko Ci ba ta yi ba. Ya d'an ja tsaki a ransa ya ce haka auren k'ananan ya

ra yake ban da haka lokacin Nanna da kanta ta dinga uzzira masa. "Abincin ma gudunsa ki ke?" Ta d'ago kai tana jin kunyar had'a ido da shi "Bar kallo na sai kace cinyeki na ce miki zan yi kika zauna kina zunduman ihu, daga yau ba zaki sake gani na ba sai k

in nemo ni da k'afafunki dad'inta ina da inda zan sauke buk'atuna da ko ban shirya ba za'a biyoni cikin farin ciki da kwanciyar hankali." Ji tayi zuciyarta na wani irin tururi ta mik'e da sauri ta shige d'aki tana sakin kuka. Hammad ya saki murmushi ya san

kishi ne yake damunta. Ya mik'e ya bita. A tsakiyar gadon ya sameta tana kuka ya saki ajiyar zuciya ganin yarda yau murararn ya ga dirarru kuma lallausun cinyoyinta. Bai hau gadon ba gudun kada ya sake janyowa kansa "Ki tashi ki je ki rufe gidan zan fita.

" Wani irin juyi ta yi da ya saka shi bin ta gadon bai shirya ba. Ina nan lamarin ya fi gaban wasa ganin idona na shirin makancewa da azama na juya na bar d'akin. Ina mamakin yarda Hammad ya murje idanunsa yake aikatawa k'aramar yarinya son ransa.

_____

_________

Didi tsaf ta shirya cikin shaddarta samfurin getzner ta kashe d'aurinta na tsofaffi ta zauna zaman dirshan a falonta. Yanayin fuskarta kawai zaka kalla ka san yau a shirye take ta ci zarafin kowa a gidan. Ta gutsiri goronta kafin ta cilla shi a

baki ta ce "Atama'u kira min uban kowa da uwar kowa na gidannan da wanda ma ba ta gidan nan. A zo a ganni na tamu lafiya d'an bak'in ciki te ya mutu burina na ga ranar tonon atirin Takina."

Jikar Nashe



🏽

ALKALAMIN JIKAR NASHE.

YA ABIN YAKE?

23.

0803

3748387.

Asma'u danne dariyarta ta yi, don ita kanta maganar Didin dariya take bata sai dai ta san da zarar

ta yi dariyar yau ba ubanta Utmanu ba har kakanta sai ya sha zagi. Didi ta sake gyara zamanta ta ce "Ki je ki kilasu yau zaki ga futkar almura. Wan

nan karan Asma'u gagara k'unshe dariyar ta yi sai da ta yi saurin fita daga falon sannan ta saki murmushi.

B'angaren Mahmah ta fara shiga ta sameta zaune bisa sallaya da alama sallah ta idar ta zuba tagumi hannu bibbiyu. Lamarin gidan gaba d'aya ya fara

fice mata a kai musamman matsalar mai gidan da bai d'auke ta a bakin komai ba. Ga matsalar Hammad da ya gagara fayyace mata gaskiyar lamari.

Sam bata san da shigowar Asma'un ba da take tsaye ta jera mata sallam ta fi biyar. Har sai da

Ta gaji cikin tausay

awa ta k'arasa wajenta had'e da dafa bayanta sannan ta yi firfgitgit ta farko daga dogon tunanin da ta tafi idanunta ta d'ago tana sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya bayan ta ga Asma'un durk'ushe a gabanta.

Asma'u ji ta yi kamar ta saka kuka ganin irin

ramar da Sadiya ta yi a tsukun wannan lokacin "Tunanin me kike yi Sadiya?" Murmushin yak'i ta saki da son danne damuwarta ta girgiza kai "Bakomai" "A'a wallahi zance ne ma ki ce bakomai kin luluk'a can duniyar tunani sannan ki ce min bakomai." Ta fad'a tan

a jan hannunta cikin son kwantar mata da hankali ta ce "In dai matsalar nan ce ta Hammad ki kwantar da hankalinki ya tsumma a randa, zan iya yi miki rantsuwar da babu kaffara Hammad ba shi da alak'a da Hamda balle har a ce shi ya yi cikinta, haba Allah ba

zai jarrabemu da wannan masifar ba, ita dai ta san yarda ta samo cikin d'iyarta." Sadiya ta girgiza kai had'e da share guntuwar k'wallar da ta zubo mata ta ce "Idan ke baki yarda shi ya yi cikin ba ai ragowar mutanen gidan sun yarda. Ji fa yarda ubansa mah

aifi ya yi masa korar kare daga gidan nan ba tare da ya tsaya ya ji ta bakinsa ba. Shi kuma ya tsallake ya bar k'asar nan bai damu ya sanar da ni yarda abin yake ba." Asma'u ta girgiza kai ta ce "Duk wannan ya faru ne sakamakon d'aukewar maganar Didi amma

yanzu ai komai zai daidaita tunda bakin Didin ya bud'e itace ma ta ce na tattaro mata kanku dukka." Da sauri ta kalleta kafin ta ce "Da gaske?" Tana murmushi ta ce "Ki je idonki ya gane miki." Suka mik'e gaba d'aya ranta fari k'al tana tunanin dukka matsal

a ta zo k'arshe da izinin Allah tunda bakin Didin ya bud'e.

Ita sashen Didin ta tafi da sauri. Ita kuma Asma'u ta nufi sashen Ammi Sakina. Ta dad'e tana knocking kafin Munira ta zo ta bud'e cikin fara'a da girmamawa ta shiga gaisheta Asma'u ta dafa kanta

itama tana jin Munira a ranta kuma tana son ta musamman don yanayin halayenta da ya farrak'a da na y'an uwanta "Munira ya makaranta?" Munira tana murmushi tace "Hutu ake" Asma'u ta danna kai cikin falon tana fad'in "Suma sun so zuwa yanayin karatun na sune

ya yi zafi na ce su bari sai an yi hutu." Tana nufin yaranta.

A hakimce ta tarar da Sakina da Kady a zaune a tsakiyar carpet d'in da yake falon. Sun baje tarkacen kayan ciye-ciye iri-iri da suka gama ci. Gefe d'aya kuma kayan kitchen ne na amare suke ta

dubawa. Sallamarta ya sa suka yi saurin d'aga kai. Sakna ta yi kicin-kicin da fuska don haushin zuwan Asma'un take ji musamman da suka saka Didi a gaba da magungunan karya asiri. Ba ta damu da yanayin kallon banzan da take mata ba, ta samu kujera ta zauna

fuskarta d'auke da murmushi na zallar mugunta ta ce "Barkanku da safiya matar Yaya, sak'o daga Didi tana son ganin

kowa a fadarta har mai gidanki." Da sauri ta d'aga kai tana kallonta tana shirin rud'ewa ta ce "Didi kuma?" Asma'u ta d'aga kai cikin ginshir

a da k'asaita ta ce "Yes Didi dai ta mu ta gargajiya Allah ya bud'i bakinta yau." Daga haka ta mik'e "Mintuna ashirin ta bawa kowa ya hallara a gabanta." Wannan karan k'iris ya rage Ammi bata saki gudawa a wando ba. Gaba d'aya ta gama rud'ewa har bata san

sanda Asma'u ta fice daga d'akin ba. Kady ta ja tsaki kafin ta ce "Tashin hankali matsala sabuwa! Amma in dai haka ne malamin nan ya yaudaremu da ya ce bakin almura ba zai tab'a bud'uwa ba." Sakina ta mik'e ranta a jagule ta ce "Ta ya bakinta ba zai bud'u

ba alhalin shegiyar matar nan ta zo k'asar nan mijinta fa shehin malami ne."

Asma'u da take leb'e a bakin k'ofa ta yi saurin sakin murmushi sannan ta sake komawa falon idanunta cikin na Sakina da ta sake firgita da ganinta ta ce "Am sorry wayata na manta."

Ta zura hannu ta d'au wayar da ta danna recording a kujera ta fice tana sakar musu murmushi zuciyarta fal farincikin samun nasarar nad'e maganganunsu ko wannan ya isheta kafa k'wakkwarar shaida.

Sakina bata kawo cewa recording ta yi ba amma murmushin da

ta gani a fuskar Asma'u ya tabbatar mata duk ta ji abinda suke cewa ta rik'e kanta had'e da fad'in "Kai wannan mata akwai almura." Ta shige sashen Abbu don ta taso shi.

Gaba d'aya an hallara a falon Didin har da su Gadanga da Lauratu kuma Didin bata nuna

wa kowa ta fara magana ba.

Ta sake gyara zamanta kafa d'aya kan d'aya kafin ta b'antari goro ta sake sawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login