Showing 66001 words to 69000 words out of 129261 words

Chapter 23 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

64

ciki ina y'ar yarinyata da ni zaka ce min ina da ciki." Gefen kunneta ya d'an c

iza kad'an yana shafa kumatunta still a kunne ya sake rad'a mata "Y'ar yarinya kuma ta iya amsar sak'o ba?" "Ni dai ka tafi kada matarka ta zo ta ganka." Matsarta ya sake yi sosai "Menene don ta ganni ina ce halak d'ina ce sai

Na ce matata ce." Hamda ta ta

b'e baki "Ji sai ka ce gaske mutumin da ko magana baka iya yi min a gabanta." Hannunta ya murza sosai Kafin ya ce "Ba tsoro bane, zallar mamaki nake son na shayar da zuri'ar D'an Borno. Wanda labarin aure na da ke gobe zai girgiza su kin ga tilas Abbu zai

tuhumi Ammi Uban da ya yi cikin ki.? Hawaye ya kawo idonta kafin ta shige jikinsa cikin kuka ta ce "Please Yaya Hammad Are you sure ni ba shegiya ba ce?" Bayanta ya hau shafawa "Da gaske ke ba shegiya ba ce da ubanki Hamda, kuma duk family sun San shi." Ta

sake k'ank'ameshi "To wanene?" Ta fad'a da d'an shashshekar kuka Hammad ya saki hucin ajiyar zuciya a kunnenta kafin ya ce "Ko ma waye tilas gobe za ki Ji shi. Na riga na d'aukar mata alk'awari da bakina dai ba Zan tona mata asiri ba. Sai dai tun a lokaci

n na tabbatarwa kaina Zan aureki wannan dalililn shi Zai tona mata asiri tunda dai wa Ai ba ya auren k'anwarsa ko? Don haka tul fil azal da son aurenki da tarin k'aunarki na girma a zuciyata tun kina k''aramarki." Ya fad'a yana juye mata abincin "Maza ki j

e ki ci, ki tabbatar kuma kin koma barci gobe I yanzu na tabbatar ba shamakin da zai hana ni kwana dake a jikina ko?"

Sunkuyar da kanta ta yi ita kanta tana kewarsa sosai fiye da tunaninsa.

Ya rakata har d'akin da cup d'in shayinta sannan ya juyo ya koma f

alo makwancinsa.

_______________

Barci ne sosai ya d'aukesu don sai kusan sha biyun rana suka mik'e shima da kyar. Hamda ta samu kanta da wanka har da gyaran gashi ya kuma yi mata kyau sosai ta murza wet lips a bakin nata mai k'amshin strawberry.

Zama t

a yi a gefen gadon sam ba ta son fita don haka ta yi zamanta tana aukin game a wayarta tunda ya ce sai after magriba za su je gidan. Yau fes ta tashi zuciyarta fresh take jinta. Ba mamaki hakan yana cikin farin cikin yau duniya zata san wacece ita? Ita kan

ta zata san wanene mahaifinta don haka take zakwad'in zuwanta gidan.

Nanna kuwa fes ta fito cikin hamshak'iyar shiga, zazzafan lace ta saka gold hannu da wuya sai zabga k'amshi take duk da zuciyarta ba dad'i tana jin haushin Hammad haka dai ta daure ta s

higa kitchen don samar musu abinda za su ci su yi bud'a baki tunda ya kafe shigar dare za su yiwa gidan nasu.

Girkin cin mutum biyu kawai tayi. Yarda ta ke jin haushin Hamda bata jin zata iya yi mata abinci. K'amshin girkin ya ziyarci hancin Hamda ta ji b

abu abinda take son ci irin abinda aka dafa. Don haka cikin dakiya ta fito falon. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta sauke ganinta akan Nanna. Da itama ta tsuke fuskarta tun bayan ganin fitowar Hamdan. Hammad dai yana zaune a gefe yana kallon yarda suke musaya

r kallo kamar za su amayar da wuta a bakinsu. Hamdan ta kalleta kamar an mata dole ta bud'e bakinta da kyar ta ce "Maman kamla ina yini an sha ruwa lafiya?" Idan kai da baka wajen ka amsa to Nanna ma ta amsa. Hamda ba ta damu da rashin amsawarba ta k'arasa

dinning d'in saboda yawunta ya gama tsinkewa da abincin Nannan duk da ba wata tsiya bace illa indomie da k'wai ta sunkuci plate d'in da Nanna ta zubawa Hammad abinci ta yi hanyar bedroom d'inta. Da sauri Nanna ta ce "Kan uba, ke kin isa in dafa abinci ki

ci." Zata bita Hammad ya rik'eta idanunsa narai-narai ya ce "Haba Nanna please mana, ki barta ta ci kina ga laulayin ciki ta ke." Idanu ta zuba masa murya a dashe ta ce "Kai ya aka yi ka san laulayin cikin ta ke?" Ya basar da maganar ta hanyar janyo plate

d'in da ta zuba nata abincin ya d'ebo indomien da fork cikin salon da ya san yana gigita ta ya kuma saukar da fushinta ko wane iri ne ya ce "Ha, kin ji Sweetie na." Kamar k'aramar yarinya kuwa haka ta bud'e bakinta sai dai takaicin Hamda na nan a zuciyarta

.

Sai da Hamda ta ci ta yi nak sannan ta saki hamdala tana murmushi hango idanun Nannan cikin masifa. Zamanta ta yi a d'aki ta k'i fita har san da Hammad ya k'walo mata kira. Tsaki ta yi ta mik'e tana nad'e mayafinta da d'aukan hand bag d'inta. Ta sake

feshe jikinta da turare sannan ta maka Glass samfurin Gucci a idanunta wanda ake kira No respect.

A wajen gidan ta sameshi yana magana da mai gadi. Nanna kuwa ta hakimce a gaban mota. Hamda ta bud'e bayan motar ta shiga. Tare da cewa Nanna "Sannu Maman

Kamla." A zafafe ta juyo zata fara mata masifa kenan Hammad ya shigo don haka ta had'iye fad'an nata.

Harabar gidan a cike take da alama ahalin gidan suna nan. Don dama duk yawanci da azimi goma

ga azimi a gidan ahalin d'an borno suke shan ruwa. Sai a

sannan zuciyar Hamda ta shiga matsanancin bugu. Ta kasa fita daga motar har sai da Hammad ya bud'e idanunsa cikin nata murya can k'asa ya ce ko sai na fito da ke?" Ta watsa masa wani kallo mai nuni da kamar zai iya? Ya girgiza kansa had'a da d'aga yatsansa

d'aya daga yau ne dai gobe kowa ya san matsayinki a wajena."

Jikinta a sanyaye ta fito ta bi bayansa. Ahalin d'an Borno Nanna suka fara gani kafin Hammad ya yi sallama shima ya shiga sai Hamda. Aka kuma ci sa'a kowa da kowa yana falon Didin saboda ya fi

kowane falo girma a gidan. Mutanen gurin cak suka yi da mamakin ganinsu musamman Ammi da cikinta ya yi wata irin hautsinawa cikin tsananin firgici ta sauke kallonta kan Hammad. Didi kuwa da fara'a ta dinga cewa maraba lale da mutanen bilningam maza Ku shi

go. Inye Hamdede haka kika zambad'a kyau daga zuwanki k'asar mutane.... Abbu ya d'ago a zafafe ya sauke mugun kallonsa akan Hammad cikin tsawa ya ce...."

ALKALAMIN JIKAR NASHE.

YA ABIN YAKE?

Pg 28

Me ka dawo yi Cikin zuri'ata bayan tuni na zareka d

aga cikinta.." Tuni kowa ya d'ago ana kallon Abbu fuskar kowa b'aro-b'aro da mamakin furucinsa musamman wad'anda ba su san zancenba don ba kowa bane ya sani a cikin family daga Abbun sai Ammi Didi da Mahmah. Sai kuma Asma'u Sadiya da Gadanga sai ahalin Ham

mad. In ban da su babu wanda ya San wannan badak'alar da take faruwa a dangin. "Ka fice min daga gida kafin na yi mai gaba d'aya na tsine maka." "Ta tabbata da a yi tsinanannu biyu a zuli'alku don kana tine mata ni ma don tine maka." Didi ta fad's fuskarta

taf da jin haushin furucin Ummaru "Kai Umalu na lula baka tan zulu ba, to bali nima na fito maka a mutum kamar yalda kake so. Idan banda shashashanci an tab'a yanke shari'a ba a ji ta bakin mutum biyu duka ba. Wato ita ce mai gaskiya da ba zata fad'I k'al

ya ba." Ta nuna musu wajen zama. Hammad ya zauna ransa a had'e kowa ya zuba masa ido. Suma su Hamdan suka zauna Didi ta sa aka zuba musu abinci. Hamda kuwa ta samu abincin ta fara ci sosai don abincin ya yi Mata. Sinasir ne da miyar taushe da ta ji naman r

ago da kabewa.

Ammi kuwa gaba d'aya zufa ta ke duk da sanyin a'cn da yake kwarara a falon. Da gaske a tsorace take ga shi kanta ya k'ulle ta rasa ma tunanin da zata yi. Duk addu'ar da tazo bakinta take ja. Tabbas Hammad ya shammaceta a lokacin da ta mant

a da waccan matsalar sai ga shi ya dawo mata da ita bagatatan. Ta runtse ido ji take a lokacin notunan kanta suna shirin kuncewa saboda matsanancin tunani da ta zurfafa.

Kowa ya yi tsit baka jin k'arar komai sai ta cokula. Zuciyar Sadiya Asma'u da Lauratu

yau fes

ranar da suka dad'e suna jira yau gata tazo. Hammad abincinsa yake ci cike da nutsuwa duk da kallon banzan da Abbu yake zabga masa bai damu ba sai ma sakin murmushin k'asan kumatu yake yau zan shayar da Abbu ruwan mamaki shine abinda yake ayyanawa

a ransa. Kuma dalilin murmurshin nasa kenan.

Sai da kowa ya yi nak, ga wanda suka ci abincin fa kenan sannan Didi ta juya ta kalli Hammad da yake fad'in Alhamdulillah bayan ya saki gyatsa ta ce "Hammad ya bayan saduwa? Ya kuma aka ji da wannan abu da ya

falu?" Ya gyara zamansa a k'asan daddumar kafin ya ce "Bayan saduwa sai Hamdala abubuwan alheri da dama sun faru Hajiya Didi ciki kuwa har da aurena da Hamda."

D'aukacin mutanen da suke falon ba wanda gabansa bai fad'i ba da jin furucin Hammad da ya zo

musu bagatatan. Harta Didi sai da ta runtse idonta ta bud'e sannan ta tabbatar abinda take ji ba mafarki ba ne. Shi da Hamda da suka san lamarin ne kawai babu alamar gigita a fuskarsu. Amma d'aukacin mutanen da suke falon idanunsa a waje yake alamar firgic

i da razani a tatttare da su. Tunaninsu d'aya ne tabbas Hammad ya samu tab'in kwanya idan banda haka ta yaya zai ce wai ya auri k'anwarsa da suke uba d'aya.

Nanna kuwa suman zaune ta yi tana jifan Hammad d'in da wani irin kallo. Ita dai gata nan a zaune i

ta ba sumammiya ba ita ba farkakkiya ba.

K'arar marin da Gadanga ya zube a k'uncin Hammad ne ya dawo da su suman wuncin gadin da suka yi. Idanunsu akan Hammad da ya rik'e kumatunsa yana jifan gadanga da wani irin kallo da murmushin takaici murya a shak'e

ya ce "Me yasa zaka mareni?" Gadanga cikin zafin rai ya ce "Marinka na yi saboda ka dawo cikin nutsuwarka, ka yi mana filla-filla ka sanar damu abinda kake nufi da aurenku da Hamda, tunda ba a garin gab'a-gab'a muke ba. Kuma ko a kafirai ban yi zaton sun y

arjewa kansu Auren y'an uwansu da su ke uba d'aya ba."

Hammad ya sake shafa k'uncinsa kafin ya girgiza kansa idanunsa cikin na Hamda da take jin marin da aka yi masa tamkar k'uncinta aka daka. Ya d'an sakar mata murmushi kafin ya ce "Gata nan ku tambayet

a da aurena a kanta ko babu? Kuma ta tare a gidana ko a'a?" Da sauri Asma'u ta kama ta "Hamda gaya mana gaskiya shin abinda Hammad yake fad'a gaskiya ne?" Hamda ta yi k'asa da kanta tana d'aga kai alamar gaskiya ne. Jikin Gwaggo Asma'u na b'ari ta ce "Inna

lillahi wa inna ilaihirraji'una. Tabbas akwai lauje cikin nad'i idan banda haka ta yaya Hammad da iliminsa da komai zai je ya auri k'anwarsa sai kace wanda ya samu tab'in k'wak'walwa." "Tab'in k'wak'walwa na nawa? Ku yanzu ku ka San haka ni tuni dama na sa

ni kuma na tabbatar a cikin rashin hankalin ya je ya haikewa matata ga shi nan yanzu yazo ya sake tafka haukan ta hanyar auren k'anwarsa jininsa ku fice min da shi daga gidannan kafin na yanke hukunci mai muni don wallahi Zan iya sawa a b'atar min da shi."

Abbu ya fad'a cikin wata irin murya jikinsa na b'ari hannunsa na rawa yake nuna Gadanga "Fita min da shi Gadanga kafin na kashe shi ku zo kuna da na sani." Daga haka ya zauna idaunsa suna jirkicewa suna canja launi saboda zallar bak'in ciki.

A firgice s

u Asma'u suke da jin furucin Abbu, suma kenan balle Sadiya da ta ji kanta ya zama

kamar dutse hak'oranta sun fara rawa suna kakkafewa tsoro take ji sosai kada zancen Abbu ya tabbata ace Da gaske Hammad ya samu tab'in k'wak'walwa. Idan ban da haka ta yaya z

ai aikata wannan kwamacalar? Zuciyarta ce kawai take bugu.

Ita kanta Hamda maganar Abbu ta jijjigata, Idan ya kasance hakan ta tabbata ya zata yi da cikin da yake mak'ale a jikinta? Wace amsa zata bawa duniya don gane da tarin tambayoyin da za'a dinga m

ata. Ta runtse ido ta bud'e tana fatan taji Hammad ya ce wani abu amma bai ce ba, sai murmushi kawai yake yana wa kowa kallon k'asan ido.

Zuciyar kowa dakan uku-uku take. A zafafe Didi da ta gaji da jiran cewar Hammad d'in ta ce "Kai don ubanka ka fito

ka yi magana ka wanke kanka, ka bar mutane a cikin duhu ko so kake zuciyoyinmu su buga." Ya d'ago idanunsa cikin na Didi ya girgiza kai yana sakin murmushi kafin ya ce "Ai Abbu ya baku amsa tunda ya ce mahaukaci ne ni. Na yarda ni mahaukacin ne ayi min huk

uncin da ya dace da ni musamman ga cikina na nan a jikin Hamda ku min afuwa.." A gigice Mahmah ta zuba masa marika har biyu a duk k'uncinsa. Ya rik'e k'uncin yana kallonta cike da tausayawa halinta da take ciki daga ganinta ka san zuciyarta bata aiki yarda

ya kamata. Gani ya yi kawai ta zube a jikinsa tana fad'in "Ka fito ka fad'I gaskiya Hammad kada kasa zuciyata ta buga ka yiwa y'an uwanka asarata..." Muryarta na rawa cikin kuka da gigita take fad'a. Tausayin uwa ne ya ratsa shi ban da ita yau da ya k'yal

esu su yi ta d'aukansa a mahaukacin. Ya kama tafukan hannunta ya sanya kansa a ciki kawai ya saki wani mahaukacin kuka da ya hargitsa duk zuk'atan mazauna wajen kada dai Hamda ta ji labari. Gaba d'aya ta yi firgai-firgai da ita.

Tsawon lokaci ya d'ago ya

zube idanunsa cikin na Ammi. Wani irin kallo yake mata da yasa kowa ya mayar da hankalinsa kanta. Kallon nasa ne yasa jikinta ya dinga rawa alamun gaskiya ya bayyana b'aro-b'aro a fuskarta tun kafin ya yi magana idanunsa suka fara bata tsoro. Yana murmushi

ya nuna ta da yatsa "Ki sanar da su gaskiyar yarda abin yake? Alk'awari na d'aukar miki ba zan gayawa kowa ba. Kuma na cika miki alk'awarinki don haka da bakinki ki sanar da su yarda ABIN YAKE?" Tun kafin ta fara magana wasu suka tabbatar da rashin gaskiy

arya zuk'atansu suka fara saukuwa daga b'acin ran da suke ciki. Idanu suka zuba mata suna jiran cewarta. Ammi ta yi k'asa da idanunta tsoro ya cika ta fal, bata san yarda Umar Abbu zai fassara lamarin ba. Bata san kuma da me mutanen wajen za su kalleta ba

idan ta gaya musu gaskiyar yarda abin yake. Ta share zufar da ta karyo mata kafin cikin rawar murya ta kalli Abbu ta fara magana....

Jikar Nashe taku ce



🏽



🏽





















🙏

ALKALAMIN JIKAR NASHE.

YA ABIN YAKE

29.

08033748387.

"Ka gafarce ni Umar,

ha'k'ik'a na san na cuceka bisa son zuciya da sharrin shaid'an, sai dai hakan ya faru ne saboda d'amfaruwa da zuciya ta tayi na son haihuwar d'a namiji. Amma ina tabbatar muku Hamda d'iyar halak ce da aure na samu cikinta ba kamar yarda zuciyarku take hasa

she ba."

A tunzire Didi ta zuba mata ido cikin b'acin rai ta ce "Takina bana ton itkancin banza da wofi ta yaya zaki ce da aule kika haifi Hamda an tab'a aule akan aule ne? Ko a garinku haka ake ni dai ina gidan nan ban ji san da Ummalu ya take ki ba. Don

haka ki tanal da mu yarda kika tamu cikin tegiyar y'alki"

Shiru Sakina ta yi zuciyarta na dakan uku-uku ta kasa cewa komai illa murza wani zobe da yake hannunta. Razani da firgici ne a cikin ranta shi yasa ta kasa d'aga kai ta kalli kowa. Musamman yarda

take jin sautin kukan Abbu har nan inda take zaune. Alamar lamarin ya gama gigita tunaninsa. Tunda zata iya k'irga sau nawa ta ga hawayensa amma bata tab'a ganin yana kuka da shashshek'a ba. Hakan ya sake d'aga hankalinta yanzu ma kenan ina ga ya ji gaski

yar abinda ya wakana.

Asma'u a harzuk'e ta kalli Hammad cikin tsawa ta ce masa "Kai don ubanka tunda ta k'i fad'ar abinda ya wakana kai tunda ka san komai sai ka sanar mana." Hammad ya hau girgiza kai yana tuno da ranar da zai iya kiranta bak'ar rana a

tarihin rayuwarsa, a duk sanda ya tuna kuma sai ya zubda hawaye yake jin sanyi a ransa. Yanzunma hawayen ya share yana sakin murmushi kad'an ya ce "Ita zata fad'a muku da bakinta Umma, a tun lokacin da abin ya faru na tabbatar musu da ba zan fad'awa kowa b

a alk'awari na d'auka bayan sun tursasani bisa son zuciyarsu, ta hanyar d'aukan hotona tsirara shimfid'e akan gadonta, da camera suka kuma wanko hotunan suka nuna min tare da tabbatar min idan maganar ta fito to wallahi za su alak'anta ni da cewa ni ne naj

e har d'aki na yi mata fyad'e. A lokacin hankalina ya tashi har aka dinga kaini asibiti kuna tunanin motsuwar k'wak'walwa ya sameni, da gaske ni kaina a lokacin gani nake kamar na haukace bani da nutsuwa ko kad'an. Shi yasa na uzzira sai da aka kaini Birmi

ngham karatu saboda da zarar na rufe ido lamarin nake gani da kuma hotunana tsirara. Na san bani da mafita kuma ko na fito na fad'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login