Showing 42001 words to 45000 words out of 129261 words

Chapter 15 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

79

kud'in goro yake musu bai tab'a kallon mace ya ji yana sonta ko ya furta mata ba. duk da karakaina da matan suke a kansa da nuna masa soyayya baya jin komai a ransa game da su, shi yasa a yanzun yake mamakin kansa da har ya shiga hurumin

Hamda yake tausaya mata, bai San dalili ba, ko don kasancewarta.... tsam ya yi da ransa yana cije leb'e kafin ya sauke ganinsa akan Nanna da take taku tamkar wahainiya duk don ta ja ra'ayinsa, Sai dai ta makaro don sau tari ko a b'angaren mu'amalar aure Na

nnan ce dai take kawo kanta gareshi ba dai shi ya nemeta ba. Ya lumshe ido bayan ya ja hucin ajiyar zuciya sannan ya danna button motar ta yi unlocking kanta, hakan ya Bawa Nanna damar shiga gaban motar, bayan ta sake d'aure fuskarta tamau,

Duk da gargad'i

n da Dida ta yi mata bata ji ba, burinta ta samu ta lallashe shi ya janye tafiyar da waccan bak'ar yarinyar da haka kawai ta ji ta tsaneta.

Murya a shak'e ya ce "Gaisuwar ma sai na rok'a?" Ta kuwa daddage ta cono baki kamar yarda k'ananun yara suke shi sa

i abin ma ya bashi dariya, amma ya gintse yana sake lalubo k'wayar idanunta ya ce "Me Yasa ba kya son zaman lafiya ne Nanna? Yarinyar nan fa ba ta da wani gata sai nawa idan na barta anan ina ki ke so ta jefa rayuwarta?" "Dida ta ce zata rik'eta." Kai tsay

e ta ba shi amsa. Shi kuwa yana murmushi ya shafi gefen kumatunsa ya ce "Akan me Dida zata rik'eta alhali nine mahaifinta kuma ina raye?" Wani abu ya tokare k'irjin Nanna ta d'ago a fisge tana kallonsa "Da gaske kenan ka amsa kai ne ka yi cikin nata? Innal

illahi wa inna ilaihirrajiuna. Don

Allah to ya aka yi ka aikata wannan d'anyen Ai kin?" Still yana murmushin ya ce "A yarda labari ya bayyana kansa ance giya na sha ina cikin maye na kusanci uwarta...

Ya ja wani numfashi ya fesar da iskar bakinsa "Any way

ba wannan ya kawo ni ba, ki zama ready jibi za mu wuce Birmingham kuma ki saka wa zuciyarkiΒ  hak'urin Zama da ita don ta riga ta zama wani sashe na family na. Amma fa idan kina son zaman lafiya da ni." Shiru tayi tama rasa abin cewa kafin ta saki wani mala

lacin murmushi ta girgiza kai "Idan kuma bana son zaman lafiya da kai fa?" "Ki wulak'antata" Direct ya bata amsa ba tare da ya ko kalleta ba. Nanna ta girgiza kai kawai tare da bud'e motar ta fice don tabbas idan ta cigaba da zama zata iya rusa masa kuka i

ta kuwa sam bata son ya ga karyewar zuciyarta. Ya je yayi ta tafiya da ita amma wallahi ita kanta yarinyar sai ta gudu da k'afafunta saboda izayar da zata dinga mata. Sam bata so yiwa y'ay'anta y'an uba ba Na halak ma balle wannan da ta zo ta haramtacciyar

hanya.

Tana fita yana jan motarsa da mugun speed don kada ma ta saka ran zai bi ta ya lallasheta. Nanna ta ja sillan k'afafunta ta shige gida ita da kanta ta san bata da wani muhimmanci a wajensa, bai damu da ita ba.

_________________

Bai isa gidan b

a sai da ya tsaya a wani mall ya siya mata kayan sawa don wanda tazo da su kala uku ne kacal kuma duk ta sakesu kullum wankewa ta ke ta Mayar, har underwears da kayan makeup duk Sai da ya siya mata.

Sannan ya samu wani trolley na zuba kaya mai kyau ya siya

mata har da hand bag da shoes da turaruka, kaya dai fal masha Allah kamar me.

Tana rakub'e zaune kan kujerar parlourn tayi shiru hannayenta zube a kuncinta. Ta ji murd'a k'ofarsa sam bata firgita ba don ta San shine illa iyaka gyara zamanta da tayi had'

e da saurin goge hawayen fuskarta, don bata mance gargad'insa na yau da safe ba. Ajiye kayan ya yi a tsakiyar parlourn yana amsa sannu da zuwan da take masa.

Direct d'aki ya wuce inda ya ke kwana kafin ya fito fes da shi cikin jallabiya mai gajeren hannu

sai zabga k'amshin turaren HuGO BOSS Yake.

Kayan ya duba kafin ya ce "Kika kasa bud'ewa ki ga ko menene?" "Wannan ne a gabanka" ta samu kanta da furtawa a zuciyarta. "Na samu wancan saurayin naki ba yarda ban yi da shi ba ya amince ayi Aurenku ya tabbata

r min bai shirya ba, har ce masa na yi sadaki kawai zai bayar amma ya k'i. Don haka ki k'addara a ranki dama ba mijinki bane. Na yanke shawarar da zarar mun je can idan kin kafe auren kike so akwai abokina Jamal mazaunin can sai na ba shi aurenki." Idanu t

a zuba masa kafin ta d'auke kai murya a sark'e ta ce "Ni ban ce aure nake so ba, na yi karatun Kawai." Dole ki yi aure don idan ba aure kika yi ba Nanna ba zata barki ki zauna lafiya a gidanta ba. Ki Zama ready kuma jibi zamu wuce umarni ne kuma ba shawara

ba. idan kuma kin ga ba zaki bi ni ba, kina da inda ya fini to ki gaya min na baki kud'in mota." Shiru ta yi masa kamar ta ce eeh

ba zata bi shi ba, amma da gaske bata da wanda ya fishi tunda an ce shine mahaifinta.

____________

Ranar da za su tafi tu

n wuri ta shirya tsaf cikin kammalalliyar shiga ta doguwar riga samfurin k'asar egypt. Kalar sea blue mai adon baby pink hakan yasa ta nad'e kanta da mayafin ruwan hoda. Ba k'aramin kyau ta yi ba duk da kasancewarta mai duhun kala hakan bai b'oye zahirin k

yan fuskarta ba, dirarren jikinta ya bayyana a cikin rigar. Ta zura tattausan takalmi a k'afarta kalar pink. Ta bi jikinta ta feshe da turaren Almukhalad' bayan ta shafa body mist na kamfanin oud. Sanda ta ji knocking d'insa sannan taja kyakykyawar trolley

d'inta.

Tsam yayi da ransa yana k'are mata kallo shi kansa bai lura da yarda ya tsatstsareta da ido ba, har Sai da ya ji muryarta tana cewa "Ya Hammad ina kwana?" Tsaki ya ja kafin ya ce "Lafiya lau, sunan nan ba zai fita daga bakinki ba ko?" Sunkuyar d

a kanta kawai ta yi don bata jure wa kallonsa musamman idan ya kafeta da idanunsa. Bai sake magana ba ya juya ya fice janye da tasa trolley d'in, ita ma ta bi bayansa, tana mamakin yarda gabanta ya ke tsananta fad'uwa a duk sanda suke tare ko ta shak'i dad

dad'an k'amshin turarensa.

A motar ma kasa nutsuwa ta yi, ta shiga danna wayarta tana game, har suka isa k'ofar gidan su Nanna sai sannan ya yi magana bayan ya rage sautin karatun Alk'uranin da yake ji "Ki shiga ki ce su fito, mun kusa makara kada mu yi m

issing flight." A diririce ta shiga kallonsa shi kuwa bai sake magana ba illa cigaba da waya da wanda zai karb'i motarsa da ya yi, yana sanar da shi su had'e a airport.

Zuciyarta na rawa ta bud'e motar ta fito. Sarai ta san gidan su Nanna don ba wannan ba

ne karan ta na farko a zuwa, sun sha zuwa da Didi biki ko suna ko gaisuwar mutuwa.

Tun daga waje ta fara sallama, tsoron Nanna ne fal a ranta, yanayin masifarta yana razanar da ita. Tsaf ta lura Nanna mafad'aciya ce ta gaske. Sab'anin mahaifiyarta Dida d

a ta kasance mai sauk'in hali.

Tura k'ofar ya yi dai-dai da fitowar Nanna daga d'aki, fuskarta a cukurkud'e da alama nasihar da Dida ta yi mata ce ta tunzira Mata zuciya ban da abin Nanna ai gaskiya Dida ta gaya mata d'a dai na kowa ne, kuma duk wanda ya

haihu ba halin k'warai bane gareshi ya wulak'anta zuri'ar wani, musamman tunda bai tara sani ga Allah ba balle ya san shi ba zai iya jarrabarsa da abinda ya jarrabi wani sashi daga cikin al'umma ba ki yi nazari da kyau Nanna duniya juyi-juyi ce, idan kin

rik'e nasihata za ta amfaneki zubar da ita kuwa zai iya zama da na sani a gareki. Ta mik'e ta fito ba tare da amincewa da shawarar mahaifiyar tata ba.

Kicib'us d'in da suka yi a bazata yasa zuciyar Kowannensu ta d'auke wuta na tsawon d'akikai, kafin Nanna

ta zabga mata harara ta kuma k'i amsa gaisuwar da take ta jera mata muryarta na rawa. Da gudu Kamla ta zo ta rungumeta a fusace Nanna ta janye ta had'e da jan kunnenta da k'arfi "Last warning da zan miki shine ba ke ba y'ay'ana.....Saboda ni y'ay'ana tsar

kakkune da aka haifesu da aure ke kuwa kwamacalar da take kan ki kad'ai ta isa a guje ki, bayan kasancewarki shegiya..." wata irin gigitacciyar tsawa Dida ta sakar mata fuskarta d'auke da b'acin rai ta kalli Khairi "Je ki kira mun Babanku a mota yau da kai

na zan ba shi umarnin ya saketa tunda ba ta jin maganata.."ALK'ALAMIN JIKAR NASHE

YA ABIN YAKE?

19...

08033748387

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

✍

πŸ½πŸ“–πŸ“–πŸ“–

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

Nanna jiki na rawa take kallon Dida da nufin bata hak'uri, sai dai Didan ko kallonta ba tayi ba, saboda

ranta ba k'aramin b'aci ya yi ba, Ta rasa wace irin k'wakwalwa ce da Nanna sam albasa ba tayi halin ruwa ba.

Ko da Khairi ta sanar masa da sauri ya fito daga motar duk zatonsa Nannan wani mugun abu tayi wa Hamda, tabbas yau da ta gane Kurenta.

Turus ya

yi a bakin k'ofar falon Didan ganin Hamdan lafiya lau take. Cikin sakin fuska Dida ta ce ya shigo ya zauna. Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya daure ya saka kai ya shiga.

Bayan amsa gaisuwarsa Dida ta ce "Gata nan Hammad tunda ba taji duk shawarar da na b

ata game da ta hak'ura ta rik'e yarinyar nan, ka saketa kawai saboda idan ka tafi da ita ba k'aramin tashin hankali zata sakawa zuciyarka ba. D'agowa ya yi idanunsa cikin na Nannan yana mamakin yarda gaba d'aya ta sauya kyawawan d'abiun da ya santa da su.

Tsaki kawai ya ja kafin a hankali cikin ladabi ya ce "Ki rabu da ita Dida, kada ma ki sawa zuciyarki b'acin ranta. Da zarar mun je can zan yi solving d'in abin ba dai yarinyar ce bata son gani ba, to muna zuwa zan aurar da ita ta tare a gidanta." Dida ta s

aki tsakin takaici "Bata isa ba wallahi, kai da gidanka kana da ikon kawo duk wanda kake son ya zauna tare da kai, sai dai ita ta bar gidan." Agogo ya kalla murya a cunkushe ya ce "Ki yi hak'uri, ya zame mata tilas ma ta gyara,

Yanzu za mu wuce kada mu yi

missing flight." "Shikkenan Hammad Allah ya tsare ya baka ikon sauke nauyin da yake kanka." Har bakin k'ofa ta raka su, tana sake jan kunnen Nanna cikin nasiha da lallashi. Jikinta dai ya yi sanyi a zahiri amma a bad'inance ita kad'ai ta san takaicin da ya

ke nuk'urk'usarta.Β 

______________________

A tsorace Hamda take sosai a cikin jirgin, musamman kasancewar wannan shine first flight d'in ta. Duk ta bi ta takure kanta ta kasa sukuni, yana lura da duk wani motsinta shi yasa ya ce Khairi ta koma kusa d

a ita. Khairi kuwa ta murje idonta ta koma duk da hararar k'asan ido da Mommynta take zabga mata.

Tun tana tsoro har ta saki jikinta ta zauna ganin tafiyar ba nan kusa bace. Abincin jirgin ne dai sam ta kasa ci saboda aman da take ji, kuma ma yanayin abi

cin nasu bai yi mata ba.

Kusan asuba suka sauka a k'asar ta England cikin birnin Birmingham, sam ba tayi tunanin garin da sanyi har haka ba shi yasa bata tanadi rigar sanyi ba, shima kuma bai yi azancin siyo mata rigar sanyin ba. Sosai ta dinga rawar d'

ari hak'oranta na kafkaf kamar za su datse harshenta. Samun kansa ya yi kawai da zare jibgegiyar rigar sanyin da take jikinsa ya mik'a mata. Hannu na rawa ta damk'i rigar ta saka. Tana jin nutsuwa na sauka a ranta. Tsaki Nanna ta ja a fili tana mamakin dal

ilinsa na kaffa-kaffa da yarinyar har da wani cire rigarsa ya bata, bayan ta san shi da matuk'ar jin sanyi. Bai damu da kallon da take wurga masa ba yayi gaba cikin takunsa na k'asaita.

K'arfe 8:00 daidai suka isa bakin gidan su. Ya saka mukulli ya bud'

e y'ar madaidaiciyar k'ofa. Gidan na nan tsaf da shi kasancewar yayi wa mai hidimar gidan waya tun shekaranjiya shi yasa ya gyara gidan tas. Sai zabga k'amshi yake. Ta samu kujera ta rab'e ganin ba wanda ya bi ta kanta. Hannayenta zube a k'uncinta tana mam

akin yarda rayuwa take juyin waina da ita. Dubi dai yarda lamarin ubangiji yake ikonsa a kanta ko a mafarki ba ta tab'a zatan zuwa k'asar nan ba, sai ga shi Allah ya kawota. Sai dai rashin sanin irin rayuwar da zata yi ne yake fad'ar mata da gaba daga yana

yin matar gidan ta fuskanci k'warai ba tayi na'am da zamowarta cikin gidanta ba.

Ita kuwa Khairi suna shiga d'aki Nanna ta saka su a gaba da jan kunne, ko da wasa ku ka shiga sabgar shegiyar y'ar can wallahi sai na ci mutuncinku. Kamla idonta ya kawo ru

wa sam bata son Mom take hanata huld'a da Hamda, saboda tana son ta sosai. Hakan yasa dole Khairi ta zauna ba tare da ta kira Hamdan sun shiga d'aki ba.

Har ya watsa ruwa ya kwanta don

Ya huta, sai ya tuna da ita ya san bai zama lallai Nanna ta kaita mas

auki ba, ba ma wannan ba yana lura da ita a jirgi ba wani abincin kirki ta ci ba. Don haka ya mik'e da sauri ya fita. Hasashensa kuwa ya zama gaskiya don tana rakab'e a kujera ta lula duniyar barci ita kad'ai ce a parlourn kamar mayya, ta takure jikinta da

alama sanyi take ji sosai.

Hannu yasa ya d'an buga bayanta da sauri ta mik'e a d'an firgice idanunta sun yi nauyi saboda barcin da yake cikinsu. "Me yasa baki shiga d'aki ba?" Ta ware idonta kafin ta ce "Ba'a nuna min d'akinba ai." Tsaki ya ja ya mik'e

hannunsa jaye da trolley d'inta ya ce "Biyo ni." Murd'a d'akin su Khairi ya yi ga mamakinsa sai ya ji shi a kulle abinda ba a yi kenan rufe d'aki a gidan ko menene dalilin hakan. Ya shiga Knocking k'ofar da d'an k'arfi. Cikin barci Khairi ta farka tana fad

'in "Waye?" "Bud'e" ta ji muryar Daddynta, hannu ta sa ta murd'a sai ta ji d'akin is locked sai sannan ta tuna Mommynsu ce ta gark'ame d'akin duk don kada Hamda ta shigo. Murya a tsorace ta ce "Daddy Mom ce ta rufe da key." Da k'arfi ya ce "For What reason

?" Jikin Khairi ya soma rawa don sam bata son tashin hankali a rayuwarta ga shi ta ji Daddy kamar ransa ya yi mugun b'aci, ta kasa cewa komai sai zare ido take. Da sauri Hammad ya juya ga Hamda kawai ya sake ce mata biyo ni."

Direct d'akinsa ya wuce da it

a, dole ne ma ya yi maganin Nanna. Ya bud'e wardrobe ya d'au abinda zai buk'ata ya kalleta "Zauna anan kafin na gyara miki wancan d'akin."Β  Ta bi d'akin da kallo had'uwa da tsaruwar d'akin kad'ai ya isa ya burgeka balle yarda d'akin ya rik'e turarensa k'am

tamkar anan ake had'a samfurin turaren kafin ta yi magana ya fice daga bedroom d'in nasa. Ta bi bayansa da kallo kafin ta sauke wata sassauk'ar ajiyar zuciya. Da zata iya kwanciya za tayi kawai amma ta fi so ta watsa ruwa tukun. Don haka direct ta fad'a h

ad'adden toilet d'in nasa.

Shi kuwa yana fita d'akin Nanna ya wuce direct, Fuskarsa a had'e sosai. Ya tura k'ofar ya shiga. Nannan tana zaune gaban dressing mirror ta na shafa mai ta ganshi ya shigo da kaya a hannunsa ya zube kan gado. Sannan ya hau gado

n ya yi kwanciyarsa ba tare da yayi mata magana ba. Cikin mamaki take kallonsa "Ban gane ba Yallab'ai, ina naka d'akin?" Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Yana wajen Hamda." Da sauri ta mik'e har towel d'inta yana shirin zamewa ta ce "Wani irin abu ne wannan

zaka d'au master bedroom ka bata alhali akwai guest room." Ya d'ago yana tsatstsareta da ido da tilas ya sata risnar da nata idon "Na fiki sanin da guest room d'in na bata nawan. Saboda ita ba guest ba ce yarda kike tak'ama da gidan nan itama haka take ta

k'ama da shi." "Wallahi k'arya ne ni da nake matar gida har ka had'ani da ita?" Murmushi ya saki kawai ya ja filo ya kwanta "zuwa ki fitar da ita daga bedroom d'in nan shine kuskure mafi girma da zaki aikata a rayuwar aurenmu, duk ba ke kika jawo ba da ba

ki tilastani zuwa Nigeria ta ya kike tunanin duk wad'annan abubuwan za su faru, don haka duk abinda ya faru ke kika janyo." Daga haka ya lumshe idonsa ya bar ta a tsaye zuciyarta na kissima mata al'amura da dama. Da kyar ta ja sillan k'afafunta ta zira dog

uwar riga mara nauyi sannan ita ma ta bi gefensa ta kwanta, kusan zata iya cewa wannan shine karo na farko da ya kwanta a d'akinta, kullum ita take kai kanta wajensa. Tsaki ta ja tana tunanin Hamda kwance can a lumtsumemen gadonsu.

Sun sha barci sosai do

n sai da yunwa ta fara nuk'urk'usar ko wannensu sannan suka tashi. Hamda ma yunwar ce ta farkar da ita sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login