Showing 81001 words to 84000 words out of 129261 words

Chapter 28 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

60

da hawaye, dole

ne ma ya yi maganin Nanna ta hanyar da bata zata ba don ya tabbata ita take sake ingiza masa uwa.

Abbu da kyar ya bud'e idanunsa da ya ji sun masa nauyi, fatansa da burinsa duka lamarin ya zama mafarki. Amma ganinsu kewaye da shi ya tabbatar masa ba ma

farki bane zahiri ne duk abinda yake faruwar. Kewaye mutanen d'akin ya yi da idanunsa yana amsa musu sannun da suke masa. Idanunsa ya sauka cikin na Sakna da duk take a firgice. A karo na farko a rayuwa ya ji tsanarta da tarin haushinta ya saukar masa a zu

ciya, duk da shima da laifinsa me yasa bai fito ya sanar da duniya sun rabu ba, ya biye tata suka aikata son zuciya. Runtse idanunsa ya sake yi ba tare da ya sake mata kallo na biyu ba, yana son Sakna sosai kuma har a lokacin bai Ji son nata ya ragu a zuci

yarsa ba sai da ya had'u ya cakud'e da k'iyayyarta da kuma jin haushinta duk lokaci guda.

Hamdala duk d'akin aka shiga yi, tare dafatan k'arin lafiya a gareshi. Dama tun safe suka sake dawowa duba shi, ganin har lokacin bai farka ba hankalinsu yake a tas

he.

Da d'aid'aya suka dinga ficewa jin Gadanga ya ce "Yakamata mu bawa matansa waje su gyara shi, tunda hannayensa sun d'an yi nauyi kuma ina da tabbacin zai buk'aci shiga toilet." Didi ta ja tsaki kafin ta ce "Kai dai Gadanga da tsiya ka ke wallahi, matan

sa su gyara shi ko matarsa? Ai Yanzu ba shi da wata mata da ta ta wuce Tadiya." Tsit Abbu ya yi akan gadon yana sauraran furucin Didi. Shi akan kansa yana buk'atar sakin Sakna amma bakinsa ya yi nauyi wajen furta furucin. Yana jiyo shashshek'ar kukan Sakna

n hankalinta tashe, Didi tana iza k'eyarta zuwa waje "Wallahi sai kin fita, haba a yi mace mayya tun dare bake korarki kin k'i tafiya ko y'arki ba ki je kin gani ba, to ko tale aka halicceku da Umalu sai na rabaku wallahi." Tana turata k'ofar ta ja da k'ar

fi ta datseta.

Gadanga ransa a b'ace yake kallon Didi kafin ya ce "Amma fa hakan bai dace ba Didi, tunda dai shi Yayan ba ki ji ya ce miki ya saketa ba, yanzu wa kike so ya raka shi toilet ya gyara jikinsa?"

"Tadiya ce zata lakashi ai Umalun ba lasa k'afa

ya yi ba, ka ga Gadanga ka fita idona na lufe." Gadanga ya rik'e kansa idanunsa cikin na Yayansa da ya hango yarda zuciyarsa take bugu da sauri da sauri. Da kansa ya taimakawa Sadiya suka saka shi a toilet sannan ya fice ya bar Sadiyan, tana tsaye ta b'at

a rai ta kuma kasa yiwa Abbun komai sai kallon jin haushi take wurga masa. Abbun ya d'ago muryarsa a k'asa sosai ya ce "Idan ba zaki iya ba, Ai gwara ki kirawo wanda zai yi, kin barni sanyi yana dukana." Sai sannan ta lura da rawar sanyin da yake. Hakan ya

sa ta d'au towel d'in ta fara shirin tsaftace masa jiki ba nuna tausayawa bakomai balle kwantar masa da hankali, wanda a condition d'in da yake bai kamata ace ta nuna masa b'acin ran ba, ta yarda Sakna ta yi mata fintink'au kenan.

**********

Idanunsa

a lumshe hannayensa zube bisa k'uncinsa ya yi nisa cikin tunanin da yake, yayinda Hamda take barcinta peacefully bayan ya taimaka mata ta yi wanka. Da gaske lamarin Mahmah yana tab'a zuciyarsa ya rasa ta yarda zai b'ullowa lamarin.

Turo k'ofar da Umma Asm

a ta yi, shi ya farkar da shi daga zuzzurfan tunanin da ya tafi. Sai dai tana ganinsa ta san tunani yake. Da murmushi a fuskarta ta ce "Sannu Hammad, mun bar ka da jinya,

Sai yanzu hankulanmu suka kwanta Yaya ya farka da lafiyarsa sai dai hannunsa da k'irj

insa da suka yi masa nauyi." Hammad ya ja ajiyar zuciya yana gyara zamansa, cike da k'warin gwiwa da jarumtar da ya arowa kansa ya gaisheta. Ta yi tsam da ranta tana sake karantar yanayinsa kafin ta ce "Me ya faru ne? Na ganka a wannan yanayin?" Nutsuwa ya

yi sosai kafin ya sanar da ita abinda Mahmah ta ce, kafin ya gama tuni duk wani annurin fuskarta ya b'ace b'at, mamakin sauyin Sadiyar take yi, matar da aka santa da kyawawan halaye ta yaya lokaci guda ta rikid'e ta koma haka? Ta ja ajiyar numfashi kafin

ta dafa shi "Ka kwantar da hankalinka Hammad, babu abinda zai faru insha Allah, amma a yanzu dai Kada a tursasa mata ta zo tana maka furuci mara kyau, ka bar Hamdan a wajen Didi kafin komai ya lafa, don na san uwarta ba zata rik'e ta ba, tunda har yanzu ma

bata zo dubata ba, ka barta a wajen Didi na san ta yarda Zan b'ullowa Didin insha Allah ba za'a samu matsala ba." Ya amince da shawararta ba don zuciyarsa ta so ba, sai don sanin cewa a yanzu hakan shine mafita a gareshi da Hamdan ma gaba d'aya, takaicins

a d'aya yarda Zai yi kewar Hamdan kafin komai ya lafa. Daga haka ya mik'e ya je duba Abbu ya bar Umma Asma tare da Hamdan da take sauraransu kamar mai barci Sai dai tun shigowar Umman ta su ta farka daga barcin kuma komai suka fad'a a cikin kunnenta. Ina m

a Allah Zai bayyana mata ubanta da duk talaucinsa ta bi shi garinsu ta huta da yarda ake ta walagigi da rayuwarta.

____________

Cikin masifa da gadara ta zube idanunta cikin nata, ranta a matuk'ar b'ace take sake jifansa da duk kalaman da suka zo sama

n harshenta. Da gaske haushinsa take ji sosai tun bayan da ya bayyana Hamda a matsayin matarsa. Kasancewarta mai Tsananin kishi ya sa take sake bayyana haukanta tuburan, yana zaune yana kallonta cike da takaicin rashin mutuncin da take zuba masa "Wallahi d

ole ka saketa, idan kuma ka k'i sai na bayyanawa duniya Kamla ba y'ata bace a can waje ka je ka yi cikinta ka kawo min ita a ranar da aka haifeta tare da kafa min sharad'in da ka San dole ba Zan k'etare shi ba, ka ce lallai sai na rik'eta na kuma sanar da

duniya ni na haifeta idan ba haka ba a bakacin aure na, don haka a yau nake son sanar da ni wacece Kamla?" Idanunsa a firgice ya d'ago yana watsa mata wani banzan kallo...



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

*08033748387

*



YA ABIN YAKE?

36.

Babu alamar razana ko firgici a fuskarsa, ya sake dubanta ido cikin ido ya ce "Nanna kenan, ba na shakkar ki gayawa duniya ni na yi cikin Kamla na haifeta,

Kamar yarda ban ji kunya ba da aka danganta ni da Hamda, sai dai Z

an sake tabbatar miki waccan maganar da na kafa miki sharad'i a kanta tana nan ban janyeba, don haka idan kin shirya karb'ar takardar sallama rubutawa ba zai zame min aiki ba." Daga haka ya saka kai ya fice ya bar Nanna da wani irin tsoro da tashin hankali

, ita kanta ta San ba ta da muhimmanci a wajensa, idan ban da haka me yasa a koda yaushe ba ya jin shakkar furta mata zai iya rabuwa da ita. Ta saki murmushin takaicin yarda ya mayar da ita wawuya ya fice ya barta. A tunaninta zai ji tsoro idan ta yi masa

barazana da fallasa waccan sirrin madadin haka sai ta hango dakiyarsa da juriya akan lamarin. Ta tabbata ko fad'an ta yi ba zai damu ba.

Ta zauna a gefen gadon d'akin Mahmahn tana cigaba da tattara kayanta gidansu take son zuwa taga Dida tunda ta zo ba su

had'u ba.

Mahmah ce ta tura k'ofa ta shigo d'akin idanunta akan Nanna da ta lura da zallar tashin hankalin da ya mamaye fuskarta, ta d'auke kai ba tare da ta tambayeta ba, don itama hankalinmata ba a kwance yake ba. "Ina zaki? Na ga kina tattara kaya?" Mur

ya na rawa tana ji tamkar ta rusa ihu ko ta huta da nauyin da k'irjinta ya yi, cikin rawar murya ta ce "Gida zani Mahmah." Tsawon lokaci ta d'auka tana nazarinta tabbas ta hango damuwa kwance a k'asan ranta kuma kamar tana k'okarin

b'oye mata wani abin. Ta

dafata "Nanna bana son ki saka damuwa a ranki, insha Allah auren Hamda da Hammad kamar na saka an warwareshi da son zuciyarsa ko babu, don nima ba zan so ki yi boranci a gidan aurenki ba, hakan ba zata faru ba insha Allah, kuma zuwa gida a wannan k'adamin

ba kama ki ba, kin san dai kina zuwa Dida zata isheki da tabayoyi k'arshenta idan ta ji shirinmu ta ruguza mana tsari da wa'azinta da nasihar da ta saba, don haka ki bari mu aiwatar da komai kawai ta ji labari idan komai ya kankama." Nanna ta ja ajiyar zu

ciya tana jin kamar ta gayawa Mahmah waccan sirrin tana tsoron furucin Hammad a kanta, don haka ta ja baki ta tsuke tana jan ajiyar zuciya, shawarar Mahmah itace abar d'auka gwara ta kasa ta tsare har sai ta ga abinda ya turewa buzu nad'i. Zaman aure da Ha

mmad yanzu ta fara, kuma ba zata amince ta yi boranci a gidansa ba. Don haka ta dire jakar had'e da mik'ewa ta ce "Bari inje can sashen namu tunda kin saka an gyara." "Yauwa maza je ki, kada ma ya samu damar da zai sake zuwa wajen waccan yarinyar, ki tabba

ta kin janye hankalinsa." Ta fice tana jin k'warin gwiwa a ranta.

*********

Hamda jiki ya yi sauki har likita ya bata sallama. A kuma rana d'aya aka sallemesu da Abbu bayan an d'ora shi akan magani an kuma zayyana wa iyalinsa dokokin da za su kiyaye mas

a. Ammi dai tuni ta janye jikinta daga asibitin ganin ba wanda yake marabtar ta har gwara ma Gadanga, amma idanun Didi ma tsoro suke bata, ranar k'arshe da ta zo ta tabbatar mata idan ta sake zuwa a take a wajen zata saka Gadanga ya saketa wannan ne dalili

n da yasa su Najwa suka hanata komawa zuwa asibitin. Su dai suna zuwa kuma har Hamda sun je sun duba zuciyoyinsu cike da tausayin yarda ta zamo bare a cikinsu ga shi bata samu tausayin uwa ba. Munira ranar a wajenta ta wuni.

Suna komawa gida Najwa da ta

zo daga Abuja ta saka Ammin a gaba da nasiha akan lamarin Hamdan, "Don Allah Ammi ki tausaya mata, ki daina nuna mata k'iyayyar da kike mata, zafin zai mata yawa ki tuna fa ba laifinta bane Ammi, duk ke kika jawo mata wannan matsalar sannan kuma ki kasa ja

nta a jiki ki nuna mata kulawa." Ammi ta d'auke hawayen idanunta, a karo na farko ta kalli idanunwan babbar y'arta ta saki ajiyar zuciya ta ce "Ni kaina Najwa a yanzu ina takaicin yarda na bazangatar da lamarin Hamda na yi kuma d na sani matuk'a da gaske,

amma zallar kunyar Hamda ce ta sa na kasa kusantar ta a yanzu. Kunyarta na ke ji Najwa ban san ya zan mata bayani ta fuskanceni ba, na dad'e ina cutar da ita, cutar da ko d'an rik'o ba zaka yiwa ita ba, tunda nake Hamda bata tab'a jin d'umin jikina ba, ban

tab'a mata wanka da kaina ba, balle tsarkin fitsari ko kashi, zan iya k'irga sau nawa na bata mama na ta sha, ban tab'a kallonta na mata magana mai sanyi ba, kullum sai hantara da cin mutunci, da musgunawa, idan bata da lafiya ban san ya take ta warke ba

tunda bana kaita asibiti, duk da haka a kullum cikin kyautata min take ko bata da lafiya bata fasa yi min aiki, ni da kaina na san ban kyauta ba Najwa ta ya zan gyara tsakani na da ita?" Kuka ne sosai ya kece mata, Najwa kanta kukan take irin wannan ranar

ta dinga gujewa Ammi tun a lokutan baya da take gallazawa Hamdan ga shi ta zo a cikinsu ba wanda Ammin ta bari ya kyautawa Hamdan don a lokacin ma ta sha fad'a musu bata k'i Hamdan ta rasa ranta ba sanadiyyar bak'anta mata da ke. Kuka sosai su ka yi kafin

Najwan ta share hawayenta ta dafa Ammin kafin ta ce "Ki nuna mata soyayya, ki jata a jiki ki bata kulawa ta yarda za ki goge wancan bak'in fetin da kika sakawa zuciyarta duk da goguwar tasa zai zama aiki ne ja." Ammi ta share hawayen, numfashinta da kyar y

ake fita saboda yarda take kukan sosai abubuwa goma da ashirin sun

cakud'e mata, ga rashin ragayyar da ta hango a idanun Abbun ga fargabar sakin da Didi ta ce sai an mata, idan da abinda ta fiso a rayuwarta to rayuwar aure da Abbu ne, jikinta a sanyaye ta

mik'e tana jan istigfari a zuciyarta.

**********

Didi na kishingid'e a falonta ita da Lauratu tana matsa mata k'afafunta. Umma Asma da Hamda suka yi sallama cikin falon, a firgice Didi ta mik'e tana kallon Umma Asma da Hamdan fuskarta a had'e ta ce "As

ma'u lafiya ko?" Murmushi ta yi jikinta a sanyaye ta shige gaba had'e da cewa Hamda "Shigo mana, Ki ka ja kika tsaya, ko nan d'in bak'onki ne?" Da kyar ta ja k'afafunta ta isa gefen kujerar da Didin take ta d'an rank'wafa da niyyar gaisheta.

Didi ta watsa

mata wani kallo ciki-ciki ta amsa gaisuwar ta ta had'e da cewa "Maza ki wuce wajen uwalki, Ai yanzu ba ki da mahalli anan, to fisabilillahi fa, me ye had'i na da ke? Da d'in ma da ki ka ga na jaki a jiki na zata jinin Umalu ce, amma yanzu tunda na gane ba

bu abinda ya had'aki da Umalu ma balle kuma ni, son ki a likkafa ki ja sillan k'afafunki ki yi wajen uwalki kafin shi Umalun ya San yalda zai yi da ita, tunda ina nan na zuba ido tai Takina ta bal gidan nan wallahi." Jikin Hamda a sanyaye ta mik'e da niyya

r barin wajen, Umma Asma ta saka baki ta kira sunanta "Hamda, maza wuce cikin d'akinki." Ganin babu Wasa a fuskar Asmaun Yasa Hamda ta shige ainahin d'akinta na b'angaren Didin. Didi ta saki baki tana kallon d'iyar tata cike da mamaki ta ce "Ba Shakka, Shi

n Asma'u yaushe kika maye gulbin uwata ba ni da labali? To wallahi ki je ki fice kin da waccan k'anwal shegiyal kafin na had'aku na ci muku mutunci, zancen banza zancen wofi me ya had'ani da ita?" Asma'u fuska a d'aure ta ce "Abinda ya had'aku shine Auren

Hammad da ta yi, don haka tilas ba ta da Inda ya fi nan, don Allah Didi ki tausayawa yarinyar nan ki rik'eta, ni fa na san Didin mu mai hak'uri ce, yara nawa kika rik'e a gwarzoma balle wannan da dama ta taso a wajenki kin san dai ballagazar uwarta ba rik'

eta za ta yi ba, ga Sadiya da shashanci ta ce Hammad sai ya saketa to ina ki ke so ta je? Ki tuna fa d'a na kowa ne, kuma hakan da za ki yi sai ya zama silar shigarki aljanna." Didi ta saki ranta musamman ganin yarda Asma'u ta ke sake kambama lamarin tausa

yi da jin k'anta sai ga shi tana sakin murmushi ta ce "Allah na tuba dama ni me ta yi min? Da Allah ya rufa mana asili ma uwal ta hanyal halal ta samal da ita, zan lik'eta amma ki tabbata kin ja kunnen d'an ki wallahi ba shi ba hanyal nan d'akin kada in ga

k'afafunsa dama anan, lokaci na ne nima yanzu wallahi sai na mulza kambuna, ai ni ya yi min daidai da ya rama min abinda ubansa ya yi min ya je ya yi aule ba tale da Sanin kowa ba, ki gaya masa ba shi ba sashen nan te ya take neman aule daga falko idan na

ga dama na ta Tadiya dole ta amince ya d'au matalsa idan na ga ba a kyautata min kuma wallahi na bawa wani aulenta."

Jikar Nashe ce



🏽



🏽📄





















🙏

Afuwa insha Allah yanzu yara sun koma school daga gobe za ku dinga ganin dogon posting nagode. I

n sha Allah



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

YA ABIN YAKE?

37.

*08033748387*

Zaku samu complete a Arewabooks idan kuka shiga wannan link d



in ga masu cewa na tura musu daga farko.

Ya ABIN YAKE complete @Arewa books

Danna wannan link din, kada a manta da follow

Arewabooks. @nazeefah

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

*08033748387*

37.

Dariya sosai Didi ta bawa Asma'u, ita dai ta yi farin ci

ki da Didin ta amince da Zaman Hamdan a wajenta, ba ruwanta da abinda za ta yiwa Hammad wannan tsakaninsu ne su gyarota a can. Lauratu kuwa haushi abin ya bata, sam bata so Yayarta tata ta jajib'o musu Hamdan ba, ta so a barta a hannun uwarta ta ga yarda z

ata yi da ita sai dai bata furta ba ta ja baki ta tsuke ganin sam Asma'un ba wasa a fuskarta.

***********

Sadiya ce zaune a gefensa yana kwance a d'akinsa fuskarsa na bayyanar da damuwa b'aro-b'aro, so yake Yace Sadiyan ta matsa masa k'afa tunda ya tab

batar da Sakna tana nan da ba sai ya rok'a ba ma da kanta zata ja shi jikinta ta dinga matsa masa k'afar tana kuma lallab'ashi har sai ya yi barci, amma ji yarda Sadiya ta saka shi a gaba kawai da kallo fuska ko alamar murmushi babu balle ya hango tausayaw

a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login