Showing 102001 words to 105000 words out of 129261 words

Chapter 35 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

59

ta fad'i tunanin da tuni a cikin jama'ar nan zata zo ta zuba rashin mutunci. Didi ta zuba mata ido cikin takaici ta ce "Ba shakka Sadiya, wato nema ki ke duk wasu d'abiu na Sakina da ta zubar da su, ke ki tattara ki yayima ki

zubawa kan ki, ana yabonki Sallah za ki kasa alwala, idan banda haka mutun nawa na aika kiranki ki ka yi burus da ni sai yanzu da d'anki ya je ya lallab'o ki sannan za ki zo ko?" Girgiza kai Ta yi kawai had'e da zama cike da kasala ta ce "Ki yi hak'uri D

idi, ba k'in zuwa na yi ba bana jin dad'i ne." Didi ta girgiza kai "Ko da na ji, nan ina nan ina mamakin yarda ki ke nema ki canja daga ainahin sunanki na Halimatu wato mai hak'uri, ai duk wata Halima da hak'uri aka santa idan ba so ki ke ki zama masifatu

ba,yo fisabilillahi waye bai san kalar hak'urin da kika yi a gidan nan ba, k'iri-k'iri Umaru ya dinga banbanta ki da abokiyar zamanki kai wallahi Umaru ina jiye maka tashi ranar alk'iyama da shanyayyen jiki Idan Sadiya bata yafe maka hak'kintaba kai da mat

arka." K'asa Abbu ya yi da kansa yana jin kunyar yaransa Su Hammad da suke zube a wajen, wani abu ne na tausayin Sadiya ya taso tun daga yatsansa ya lullib'e idanunsa, kunyarta yake ji sosai da ta yaranta, yau kam Didi ta b'aro masa aiki ta kuma ankarar da

shi abinda ya dad'e yana son gyarawa son zuciya da sharrin shaid'an had'e da bin k'awace-k'awacen duniya ya hana shi ankarewa, sai yau da Didi ta taso da maganar takaicin kansa ya kamashi ya kasa had'a ido da kowa a d'akin musamman Sadiyar da ta sauke nat

a idanun a kansa tana son taga yarda zai yi, Ba shi da laifi a wani b'arin Sadiyar ce ta janyo koma mai ya faru, wata zuciyar kuma na k'addamar masa da laifinsa da hasko masa tarin kuskuren da ya tattafka a tsawon zamansu da Sadiyar, ya wajaba kam a garesh

i ya nemi yafiyar ta kafin abinda Didin ta fad'a ya tabbata a kansa ya tashi da shanyayyen b'arin jikin, yana kallon idanun da Humaid ya zuba masa ya tabbata Ba tun yau yaron yake rik'e da shi a ransa ba, don duk ya fi su Hammad zafin zuciya. Ya gyara zama

nsa idanunsa cikin na Sadiyar yana sakar mata da murmushi zuciyarsa na hasko masa tarin kyawawan halayenta da nagartarta duk da ta b'angare d'aya take da cikas hakan ba zai zama hujja a gareshi da zai kasa yi mata adalci ba, d'auke kai ta yi tana fuskantar

Didi da ta fara Rabon sufofinta, zuciyarta fes ta tabbata daga yanayin murmushin da ya sakar mata sak'on Didi ya isar masa burinta ya yi aiki da hakan su yi zamansu lafiya cikin aminci da k'aunar juna, abu d'aya ne Ba zata iya wannan kwamacalar soyayyar t

a zamani, za dai ta k'okarta wanda ta ga zata iya, tausa, shafa masa mai amma banda duk wani kalar barikanci da Sakna take yi, wannan kam ta barwa yara ita da kanta ta yarda da maganar bahaushe da ya ce 'In An girma a san an girma'

Didi ta dinga zarar

Super exclusive da Hkg lace masu matuk'ar tana mik'a musu, bakinta washe sai fara'a take, yarda ta bawa kowa haka ta mik'awa Ammi tana muzurai, Ammi murmushi ta yi bata bi ta kanta ba, ta tabbatar yanzu lokacin Didin ne na yin duk yarda ta ga dama, kuma ba

ta da power ko ikon da zata hanata hakan, ita yanzu burinta Hamda ta saki jiki da ita kamar kowane d'anta. Shi kuwa Hammad gaba d'aya baya cikin nutsuwa, ransa duk ya dagule ganin yarda idanun Hamdansa ya nuna tana cikin damuwa, da zarar sun had'a ido kuma

take zuba masa harara.

Ana gamawa kowa ya mik'e, ganin duk iyaye duk sun fita yasa ya kalli Hamda fuska a d'aure don kada ma Didi taga fuskar da zata kawo masa wargi ya ce "Mu je waje ki karb'i sak'o" Didi ta watso masa ido "Ba zata ba, idan sak'on Allah

da annabi ne a kawo mata nan mana, in dai ba sak'on tsotse-tsotse da lashe-lashe ba, nema kake ka bud'ewa yarinya ido kamar yarda ka bud'ewa waccan matar taka ido." Duk zantukan Didi akan kunnen Ammi, gaba d'aya hankalinta tashi ya yi abinda Didi dama tak

e koyawa Hamda kenan gudun miji, lallai Didi bata d'orata a kan turba mai kyau ba, har zata koma ta yi magana sai ta tuna kwararaton Didi don haka ta fice jikinta a salub'e tana ayyana ya zama dole ta ga Hamda kafin tasa Mijinta ya fara jin haushinta. Hamm

ad kuwa a zafafe yake kallon Didin murya a cunkushe ya ce "Raina ni kike so ta yi? Ina cewa ta zo kina ba zata zo ba?" Didi ta gyara zama tana tab'e baki "Ai na san zuwan ba na Allah da annabi bane, ka yi gaggawar kawo lefe kafin na yarda ta dinga bin ka."

Ya gyara zama idanunsa cikin na Hamda da taga tsagwaron b'acin ransa a ranar kalar wanda bata tab'a gani ba, kamar ya mik'e ta bi shi amma idan ta tuno abinda ya ce mata sai itama taga gwara ta bi ta Didin ta kyaleshi wato yau a rashin matarsa yake nemant

a kamar yarda ya ce. Idanunsa jajur ya ciji leb'ensa had'e da mik'ewa ya yiwa kansa alk'awarin sai ya koyawa Hamda hankali kafin Didi ta saka raini ya shiga tsakaninsu, ba zai yarda ba duk son da yake mata ba zai bari ta raina shi ba.

A zuciye ya mik'e ya

fice daga falon, Umma Asma tana d'aka bata san duk wainar da ake Toyawa ba, sai Sa'ada da takaicin Hamda ya sa ta mik'e ta shige d'aki tana mamakin wautar Hamda, mijinki yana binki yana lalla'ba Ki har ki bari fushinsa ya sauka kan fuskarsa tana jiye mata

ranar da Hammad zai sauke kwandon fushinta a kanta, banda shashancin Hamda y'an matan yanzu da idanunsu yake a waye ita kuwa Didi na nema ta zamar da ita y'ar zamaninsu banda wauta yanzu wa ke gudun namiji.

Itama Hamdan jiki a salub'e ta mik'e ta bi bayan

Sa'adan tana shiga ta zube a gefen gado tana jin wani irin feeling na son kasancewa da mijinta, musamman magungunan da take sha suna aikinsu yarda ya kamata a jikinta, kuma ta d'and'ana zak'in abin ta ji, don haka yanzu yake wahalar da ita, ta lumshe ido

tana jin yarda duk tunanin Hammad ya dabaibaye zuciyarta. Sa'ada ta yi tsaki tana zuba mata harara ganin yarda ta cukuikuye filo ta janye filon "Aikin banza ga inda can zaki je ki samu nutsuwa kin zo kin wani k'ank'ame filo." Ta d'an bud'e idanunta da suka

mata nauyi tana kallon Sa'ada da gaske tana buk'atar nutsuwar amma tana gudun jarabar Didi, "Kin wani bi kin takure kanki saboda wannan tsohuwar da bata san annabi ya faku ba, da wannan azimin kin d'auki zunubin mijinki don wallahi na gano tsananin b'acin

ransa, ki tashi ki je na tabbata Didi yanzu ta yi barci ki samu ku rage wa kanku zafi, wallahi ba zance kin je wajensa ba, kin san Umma a d'akin

Didi take kwana ba ma zata zo nan ba sai asuba, idan kin fito ki saka Yaya Hammad d'in ya kirani da kaina zan

bud'e miki k'ofa." Hamda ta d'an saki ajiyar zuciya "Ba zan iya ba Sa'ada bar shi kawai." "Kada Allah yasa ki iya d'in, Allah yasa shi yana da wata matar ko a darennan zai iya zuwa can gidansu ya d'auko a barsa idan matsuwar tasa ta kai ke ce abin ji da ba

abinda za ki iya sai rungumar filo." Wani abu ne ya tokare wa Hamda ta dinga kallon Sa'ada a wani irin yanayi tana jin takaicin maganarta kishi mai girman gaske ya fara k'ok'arin toshe mata numfashi, sai ta ji gaba d'aya Hammad d'in ma haushinsa take ji b

a kuma zata je ba ya je ya nemi matar tasa. Sa'ada ta zuba mata ido tana kallon k'wallar da ta kwaranyo mata duk da k'ok'arin mayar da ita da take, a hankali ta ce "Kan uba ba dai tsananin kishin naki har ya kai haka ba?" Ta fad'a jikin Sa'adan tana kuka "

Ya wuce haka Sa'ada, har addu'a nake ubangiji ya yaye min kishin nan amma kamar k'ara tunzira lamarin nake a zuciyata, Sa'ada irinmu ba su kamanci auren mai mata ba, gudun kada kishi ya ja mu mu fad'a halaka, Musamman Ina son Y. Hammad son da ban had'a shi

da komai ba, ko sunan matarsa wallahi bana son ji, ji nake kamar na fasa aurensa." Sa'ada ta d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi, tana hango tarin matsaltsalun da za'a fuskanta a zaman Hamda da Nanna, murya a sauk'ak'e ta ce "Ki sake dagewa da addu'a, sa

nnan kuma ki jajirce wajen kula da shi, ta yarda zaki kwance masa duk wata hadda tasa ya zama baya tunani da hangen kowace mace sai ke. Amma kina wannan abin kalar na k'auyanci ai Nanna tsaf zata samu riba a wajenki wallahi ta k'waceshi don duk son da miji

yake maka matuk'ar baka amsa buk'atarsa a lokacin da ya zo miki wallahi fita ransa kike." Hamda ta share hawayenta, "Farkon aurenmu ba haka nake masa ba, shi kansa ya sani yanzu ma ba wai maganar su Didi ba ce ta saka ba guje shi, haushi ya bani duk sanda

muka had'u sai ya min maganar matarsa ni kuma bana so. Kuma ki gaya masa na fi son zama gidan Abuja kusa da shi, don wallahi ba zan yarda ya bar ni a kano ba, ya d'au matarsa su tafi Abuja ban yarda da wannan tsarin ba." Sa'ada dariya ta yi sosai har tana

rik'e ciki ganin yarda Hamdan take masifa ta ce "Ke da mijinki me yasa ba zaki gaya masa ba?" Hamda ta datse leb'enta ta ce "Ba zan sake masa magana bane, har sai na tare ba dai saura 5weeks ba." Sa'ada cikin takaici take kallonta "Au nufinki har 5weeks z

a ku yi a haka yana jin haushinki? Cab a haka zaki mallakeshi? Ga waya nan yanzu ki d'auka ki kirashi ki bashi hak'uri, idan kuma ya k'i kice ya zo nan ni sai in fita falo na muku gadi." Ta zunb'uro baki tana kallon wayar kamar zata kira sai kuma ta ajiye

tana kallon hoton da Sa'ada ta saka mata a screen d'in wayar, Hammad ne yana sakin murmushi jikinsa sanye da jar rigar polo da facing cap a kansa, ta d'auke kanta murya a cunkushe ta ce "Rabu da shi ba." Sa'ada ta wafci wayar ta danna sunan da ta mata savi

ng na Hammad wato 'k'albeey na'. Kusan bugu nawa kafin ya d'auka don ya san numberr Hamdan tunda tsohon layinta ta saka a wayar idanunsa a lumshe ya saka wayar a kunnensa ko a lokacin tunaninta ne ya cika masa zuciya, Sa'ada ta saka mata wayar a kunne ta m

ik'e ta fice daga d'akin "Ki yi magana ko na kashe, ana so ana kaiwa kasuwa." Cikin takaicin furucinsa ta ce "Ni ba ni na kiraka ba Sa'ada ce." Daga can ya saki wani zazzafan murmushi da taji sautinsa ya sake maye duk wani feeling da take ji, tsigar jikint

a sai ta shi take "Ba ke kika kira ba Sa'ada ce to me yasa na ji muryar ki?" Wannan karan sai da ta runtse ido jin da salon da ya mata maganar, cikin wata irin Husky Voice, "A haka za muyi rayuwar auren kina gudu na? Saboda wata al'ada can, shi yasa yanzu

na fasa kaiki Abujar ki zauna a Kano na tafi da mai kula da ni...." D'if ta kashe wayar tana sakin wani hucin b'acin rai Hammad kuwa murmushi ya yi ya tabbata ya sake tunzira zuciyarta ya rasa irin wannan kishi na Hamda ki auri mace da mijinta amma ya ga

alama ta doke Nanna da kishi. Ya sake kiranta tsawon lokaci kafin ta d'aga "Ki kawo min abinci, wallahi yunwa nake ji babu abinda na ci, ko kin fi so na d'au azimin haka ga yunwa ga mutuwar sha'awarki da take neman kassarani please ki zo kin ji y'ar

Aljann

a ta, ba abinda zan miki." "Ka tabbata?" ya d'aga kai daga can yana murmushi "Am sure ko kallonki ba zan yi ba." "To na taho da Sa'ada?" "Kada ma ki fara idan ba so ki ke itama Sa'adan na fara son ta ba." Da sauri ta ware ido ta ce "Sa'adan?" Ya d'aga kai

"Yes, Sa'adan itama ba mace bace, idan ina yawan ganinta ai zan iya fara son ta." Kashe wayar ta yi da sauri kafin ta mik'e dama ta yi wankanta tas kayan barci ne ma a jikinta sai ta zunbula hijabi had'e da ambula turare a jikinta had'in Humran da Ammi ta

kawo mata ta cilla wani chewingum mai mugun k'amshi a bakinta.

Sa'ada na zaune a falo ta ga ta zo ta shige kitchen murmushi kawai ta saki, tana ji ta yi warming d'in abinci da peppe soup, sannan ta fito da kwandon abincin, Sa'ada ta bi bayanta tana murmus

hi tana shirin rufe k'ofar a hankali ta rad'a mata "Asuba ta gari Hamda yau za'a sha amarci kut balle kin sha uban gyara kece d'azu har da hanani kazar da Umma ta dafa miki, ai yau zaki gane kin ci kaza, ga zuma kika dinga lasa kina lumshe ido, zaki lumshe

ido mai dalili ai yanzu." Gabanta na fad'uwa ta dubi Sa'ada kafin ta ce "Kada ma ki fara rufe k'ofa yanzu zan dawo." Cike da shak'iyanci Sa'ada ta ce "Ni kuwa na san haka." Sai da ta wuce a hankali ta ce "Tunda Hammad d'in tsoranki yake ba."

Cike da con

fidence ta tura k'ofar, ba kowa a falon sai k'arar T.v da yake kallon tashar saudiyya, ta ajiye abincin had'e da zama a falon tana tunanin ta inda zata fara nemansa, ga shi ta bar wayarta a gida, falon babu wadatar haske sosai, tsawon mintuna tana zaune ka

fin ta ji ya turo k'ofar d'akin ya fito sanye yake cikin Riga fara tas armless sai gajeran wando da ko gwiwa bai rufe masa ba. Ta saba ganinsa a haka amma yau kam da ta gan shi sai da gabanta ya buga. Yana murmushi ya zauna daf da ita kan kujera yana k'ok'

arin shiga jikinta, murya a d'ashe ta ce "Ka fa d'au alk'awarin ba abinda zaka min?" Humrar ta da yanayin yarda ta yi magana ne yake fisgar hankalinsa har bai san sanda ya jata jikinsa ba, wata irin shafa yake mata yana hura mata kunne "Kema kin san ba ni

wannan k'warin gwiwar in ganki a gabana na k'yale, haba Hamda ba kya tausayina? Ni ne fa k'albeeynki kwana nawa jiki na bai had'u da mahad'insa ba, har fa rama na yi." Shiru ta yi masa jikinta ita kanta rawa yake saboda yanayin sak'on da yake aika mata was

u irin sak'o ne masu zafi. Murya na rawa ta ce "Ba ka ci abinci ba." Ganin har yanzu bata samu nutsuwa ba ya sa ya mik'e da ita cak a hannu suka shiga bedroom, yana shimfid'eta ya kashe wutar d'akin had'e da kai mata wata irin zafaffiyar runguma da yasa ba

kinta yai tsita tana jin sa ya raba ta da Hijabin ta daga nan duk wani labari ya canja ba ta ma da bakin yi musu ko k'in bin umarninsa amsar sak'o take ko ta ina itama tana aika masa da nata zafafan sak'on da ba zan iya kwatanta rubuta su ba, saboda girman

lamarin na bar mai karatu dai ya hasko sha'anin a zuciyarsa ya wannan daren zai iya kasancew daren da Hamda ta amshi duk wani gyara daga b'abgaren iyayenta aka ci aka sha duk wani abin gyara da zai gigitar da hankali d'a namiji, na tabbatar tabbas abin ba

dama.



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

YA ABIN YAKE? 43.

*08033748387*

Wani irin kallo Didi take mata kamar ta ga abin kyankyami, ta mayar da kallonta kan Hamdan da take k'ok'arin mik'ewa ta ja wani dogon tsaki kafin ta ce "Ammo ce ta a

iko ki ba Ammi ba, ni za'a kawowa kinibibin banza, wato ta ga uban yarinya mai kud'i ne shine za'a zo a kanainayeta, to wallahi ki gayawa Sakina ta fita idona, uban me ma ta baki ki kawo mata, wato yanzu zata nuna min ita ta haifi y'ar bayan da ta banzagat

ar da lamarinta, zube kayan mu ga wace uwar ce a ciki?" Munira gaba d'aya ranta ya b'aci jin abinda Didin ta fad'a duk da ta san gaskiya ta fad'a amma ai Ammin ta yi nadama me yasa ba za'a bar abinda ya wuce ya wuce ba, ita kuwa Hamda zuciyarta fara k'al k

o bakomai Didin yau ta biya ta, da Ammin me ta sani nata ita kam ko ina zata bugi k'irji tace Didi ce babarta, sai Abbu shima ba zata mance kulawarsa gareta ba. "Ki ke kallo na ko duka na za ki yi? Zube kayan nan naga me aka k'unshe za'a je a bata, tun yan

zu wato za'a fara koya mata bak'in halin asiri, to wallahi ba zan yarda ba eehe." Asma'u ce ta kashe maganar ta hanyar cewa "Haba Didi, duk me ya kawo haka? Ya za'a yi kice sai sun ware kin ga abinda ke ciki." "Ki kiyayani Asma'u babu ruwanki ta bud'e naga

me yake ciki? Na sani ko maganin mallaka ne ta bata a mallake min jika kamar yarda aka mallake ubansa." Cikin takaici Munira bata san sanda ta zazzage kayan ba ta ce "Ga shi nan, kayan gyaran aurene da ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login