Showing 72001 words to 75000 words out of 129261 words
muka zauna. A wajen kuka na ya tsananta na shiga bajewa Kady sirrin zuciyata ba tare da la'akari da cewa wannan ce had'uwarmu ta farko ba. Madadin na ga ta tausaya min sai na ga ta saki murmushi ta yi tsaki ta
ce "Ke ki godewa Allah ma kina haihuwar matsalarki mai sauk'ice. Ni nan da ki ke gani na ban tab'a haifewa mijina k'wansa ba, sai dai na haife k'waya-k'wayan y'an uwansa." Na ware idona ina kallonta ta girgiza min kai "K'warai kuwa, Mijina ba ya haihuwa a
mma shi kansa bai sani ba kuma ba mazauni bane, a duk sanda ya yi tafiya anan nake shek'e ayata da k'annensa guda biyu d'aya cikinsu d'aya ma'ana uwa d'aya ce ta haifesu d'aya kuma ubansu d'aya. Kuma y'ay'an suka d'ebo dangi ta yarda ba yarda za'a yi ace b
a nasa bane, ba ma wannan ba ko mutuwa ya yi za su iya cin gadonsa tunda gadon nasa na iyayensu ne, wannan yasa hankalina kwance yake, balle ta ki matsalar ma mai sauk'i ce, shin ba shi da k'ani?" Wata zufa ta shiga karyo min murya a sark'e na ce "Yana da
shi mana." Ta tab'e baki "Yana da aure?" Na d'aga mata kaya "Ya yi aure da matarsa da yaransa biyu maza" "Shikkenan kin ga ta yarda za ki samu namiji kenan." Cikin tsoro da firgici na ce "Kamar yaya Zina kike so na aikata?" Ta girgiza kai cikin tabbatar mi
n da zancenta "Zina mai tsafta kenan Zinar cikin gida, hankalinki kwance zaki haifi d'a namiji, ki kuma ajiyeshi a gidan a zuwan d'an gidan ne ya d'ebo kamanni da komai na mutanen gidan, ta yarda ba mai tuhumarki." Murya har rawa take wajen ce mata "Kady b
a zan iya ba, ta ina zan iya janyo hankalin Gadanga?" "Ta kissa da kisissina da zarar kin haihu a lokacin za ki fara kai masa hari idan ya k'i ta lislama sai a biyo masa ta bayan gida. Duniyar nan fa yanzu haka take." Na yarfe gumin goshina ina girgiza kai
idan har na yarda da batunta tabbas abinda zan haifa zai zama JININ D'AN BORNO...
(Ku yi hak'uri idan na samu sauk'i zan k'ara muku yawan typing d'in ciwon kai nake.ALKALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE?
08033748387
𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍
✍
️
31.
Cikin Tso
ron lamarin na dinga girgiza kaina kafin na mik'e idanuna cikin na Kady da take min kallon shashasha "Ai shikkenan ki je idan kin yi shawara zaki nemo ni da kanki. Kawo wayarki na saka miki numberta" na mik'a mata wayar kasancewar lokacin wayar hannu ta d'
an fara zaga gari. Ta daddanna ta saka min numberrta sannan ta rungumeni kad'an ta ce "Allah ya raba lafiya, ni fa farkon ganina da ke na zata ba kya jin hausa wallahi. Sam ba ki yi kama da y'an k'asata ba." Na jijjiga kai "kin canka daidai ba ni da kowa a
Nigerian nan duk dangi suna jordan aure ne ya kawo
ni nan." Ta ce "Ayya insha Allah yanzu kuwa Zan zame miki y'ar uwa in dai kin karbeni da mutunci." D'aga mata kai na yi kafin nace "Why not? Ina maraba da ke, ni ko sunanki ma ban sani ba muna ta surutu."
Ta girgiza kai "Muna magana mai amfani zaki ce ba surutu ba, sunana Kadija amma an fi kira na da Kady." Na fad'a mata sunana nima ina tafiya ta rakani har bakin mota in da driver yake jirana.
Tun daga lokacin muka d'inke da Kady ta zame min abokiyar shaw
ara, na ji dad'in had'uwa da ita k'warai da gaske. A hankali ta dinga tunzira zuciyata har na amince da abinda ta ce, muka fara shirin yarda za mu farwa Gadanga da zarar na haifi cikin jikina na yi arba'in zamu fara saka shi a tarko.
Duk da zuciyata tana r
awa da tsoro akan amincewar ko rashinta. Tabbas na san ba namijin da zai k'i ya kusanceni a yarda Allah ya kyautata min halittata. Amma ina tsoron bayyana hakan da Gadanga mutumin da ya zamo daga cikin jinsin mutane miskilallu, ta ya zan janyo hankalinsa?
Kada na je ya tona min asiri don haka na k'udundune shawarar Kady na saka ta a gefe na shiga neman mafita da kaina. Ba k'ok'arin da ba tayi ba akan na amince da batunta sai dai na ce mata wallahi ina tsoro. Ta gaji ta k'yaleni had'e da cewa idan kin shirya
d'aukan cikin namijin ki sanar da ni." Na d'aga mata kai kawai.
__________
A duk shekara na kan zauna na yi kwalemar kayan bayarwa a d'akina, na kwashi kayan yara da yawa buhu guda da k'atuwar ghana must go, kuma duk sanda na tashi bayarwa masu yi ma
na hidimar gida nake bawa. Su yi ta godiya suna min addu'oi.
Wannan karon san da na had'a kayan sai na ji zuciyata tana son na bawa Buzu sabon mai gadin da aka kawo gidanmu. Shekararsa guda kenan kuma muna d'an d'asawa da shi saboda yawan kyauta da nake m
asa. Da na gama tattara kayan sai na sanya Najwa ta kirashi ya d'au kayan gaba d'aya idan ya tashi tafiya garinsu sai ya tafi musu da shi.
Da kirarin da ya saba min ya shigo falon. Cikin harahensu na buzanci "Idan ka ji Kiran Uwar larabawa alheri ne, wann
an yaran da izinin ubangiji sai sun zame miki abin alfahari, farar mace mai farar zuciya. Na saki murmushi ina wasa da gashin Munira da take cinyata na ce "Buzu ka bari ka iya hausar kafin ka dinga Yi, ni wani abin ma idan ka fad'a bana ganeshi, tunda nima
hausar ba wai ta isheni ba ne." Ya yi dariya kawai yana kallon kayan da suke zube a gabana. Na ce "Buzu kayana ne da na yara na had'a na ji kace kana aike garinku sai ka aika musu da shi." Bakinsa ya washe kafin ya ce "Kash ina ma Allah d'iyoyi mata ya ba
ni da sun mori kaya, to tsiyar abin sai dai mutanen gari su mora. Yara na goma sha biyar daga iyayensu mata biyu amma kaf ba wacce ta tab'a haifa min mace duk da so na da haihuwar y'ar d'iya." Sak na yi ina kallonsa jin furucinsa kafin na ce "Kana nufin ka
f zuri'arka maza ne?" Ya d'aga min kansa cike da tabbatarwa "Wallahi Hajjaju nake gaya miki kaf d'insu maza ne guda sha biyar da su masha Allah, haka zuri'ar mu take da wuya ki ga an haifi mace daga yayyena maza har mata kuwa, ina ga d'iyoyi biyu ne
mata a
cikinsu, shima daga tsatson wata k'anwata, San da aka haifesu ba kiga irin murnar da ahalinmu suka shiga ba. Da zarar kin je Habasha kika ce kina neman gidan Abu rijalun to za'a kai ki gidanmu. Tunda ba b'oyayyu ba ne mu muna da sarauta a garin." Na tsaya
ina kallonsa baki na sake zuciyata da tunani iri-iri a cikinta. Ciki kuwa har da tunanin Allah ne ya kawo min buzu mai gadi don na samu d'a namiji daga tsatsonsa. Idan haka ne kuwa ya zama dole na yi wani abu kafin lokaci ya k'ure min. Na sallameshi ina m
asa godiya zuciyata cike da farin ciki. Shima ya fice cike da farin ciki.
Tun daga lokacin na gadarwa kaina zama na zurfafe bincike akan yarda zan samu Buzu mai gadi ya amince da buk'atata. Duk da ina k'yank'ayamin kasancewa da shi. Hankalina duk ya tafi
akan tunanin yarda zan samu d'a namiji. Musamman ganin yarda Hammad ya girma kuma Komai Umar sai yace sai shi shine babba. Idan na kawo masa maganar Najwa ce babba sai yace ai Hammad shine namiji nan gaba ita kanta Najwan wa zai zame mata ba k'ani ba, mus
amman tazarar ta su ba yawa ba ce da ita." Ban yarda da shi ba gani nake son kansa ne kawai idan ya ga na yi fushi da shi sai ya tattara dukkan nutsuwarsa a kaina ya shiga k'okarin lallai sai ya fahimtar da ni su yara mata da kike gani da zarar ka aurar da
su, sun bar k'ark'ashinka kenan sun koma k'ark'ashin kulawar mijinsa ta ya zan bawa Najwa damar kula da dukiyata idan ta saba da kud'i kuma ta k'i aure fa. San da suka gama secondary school ba yarda ban yi ba ya tura Najwa K'asar England karatu amma ya k'
i bud'ar bakinsa sai ce min yayi dama Namji ce amma ba Zan tura mace wata k'asa karatu ba. Wannan kalami nasa yasa na yarda na amince ita mace bata da wani value a idon iyayenta maza. Ba su d'auketa komai ba. Hakan yasa na k'udirce a raina ko ta wace hanya
sai nima na haifi namiji.
Kady ta fad'o min a rai don haka na shirya tsaf na ce Umar zan je gidan Kady. Yana kallona ransa a b'ace ya ce "Har ga Allah Sakna bana son huld'ar ki da Kady don dai ba yarda zan yi dake ne, ke ban isa na hanaki ba dama Sadiya
ce na san ina ce mata ta daina kaza zata daina."
Murya a cunkushe ina jan tsaki na ce "Sadiya ka ce ita taga zata iya rayuwar gidadanci, ni rayuwa mai y'anci zan yi irin yarda na ga yarda ake yi a gidanmu, bata yarda zan zamewa miji kamar baiwa." Girgiza k
ai kawai ya yi duk da alamunsa sun nuna ya ji haushi amma ya shanye b'acin ransa, sau tari hakan ce take kasancewa bai isa ya ce min ga abinda yake so ba na bi, kullum ra'ayi na nake bi fiye da nasa. Na fice ina jinsa Yana cewa "Allah ya shirya min ke Sakn
a, son ki ne ya yi min yawa shi yasa nake kasa d'aukan mataki a kanki." Ni kad'ai na saki murmushi ni da kaina na San da damar son da yake min nake zabga masa rashin kirki shi kuma yake kasa hukunta ni ba irin Sadiya ba da take karb'ar hukuncinsa a koda y
aushe.
Kady da murmushi ta tarbeni tana fad'in "Mhmd Mhmnn manyan mata ka ga ta Umar ba da kanki a sare. Mai tsoron cin amanar Umar." Murmushi na saki kawai ina zama na ce "Biko na zo kwana biyu na ga ba na ganinki." Kady ta girgiza kai "Ina kuwa za ki
ganni a gidanki in je mijinki yana min wani gani-gani shi yasa na janye jikina da ke." Na gyara zama ina tab'e baki "Ni ba wannan ya kawoni ba, zuwa na yi akan zancenmu na kwanaki." Dariyar shak'iyanci ta yi sosai kafin tace "Kin ga uwar bari kenan wa ya
gaya miki Borno gabas take ina jinki ya ake ciki?" fuska a had'e na
ce "Ba fa waccan maganar ta kawo ni ba,
sam ba zan iya wannan kwamacalar ba, Buzu mai gadin mu na hango a yanzu shine nake ganin kamar zai cika min burina." Tsawon lokaci tana min wani iri
n bahagon kallo kafin ta ja ajiyar numfashi ta ce "Allah ya kyauta, amma wannan tunanin naki kamar ya gurb'ata ta ya zaki iya had'a jiki da mai gadi?" Na runtse ido jina jijjiaga kaina "Dole na kawar da maganr duk wata k'azanta kady, in dai burina zai cika
. Haihuwar d'a namiji shine cika makin farin cikin rayuwata." Baki sake take kallona kafin tace "Mhmn, to yanzu ta ina ki ke tunanin za'a fara?"
Na gyara zama kafin na ce "Sai na gyarashi tukun, ya zama mai tsafta na kuma jik'ashi da Naira kafin na bijirom
asa da buk'atata, amma fa ta hanyar aure ba zina ba..... sak'ek'e take kallona kafin ta ce "Aure kuma? Kamar yaya?" Na saki murmushi kafin na ce auren dai da kika sani mai suna aure." Tsaki ta ja ta ce "Shi kuma auren Umar d'in ki kaishi ina?"
Jikar Nash
e
❤
️
❤
️
❤
️
❤
️
❤
️
🙏
ALKALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE?
08033748387.
𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍
✍
️
💫
32.
Cije leb'ena na yi kafin na ce "Zan jingine auren nasa, ta hanyar da shi ma ba zai tab'a zata ba." Daga nan na gaya mata shawarar da na yanke. Sakin murmurshi t
a yi tana dunk'ule hannunta da d'aga min alamar jinjina ta ce "idan haka ne, tabbas sai na ce k'wak'walwarki ta fi tawa ja, kutmelesi ta yaya ki ka yi wannan tunanin? Kin ga shikkenan za ki haifi halastacciyya y'a inda ko nan gaba maganar ta tashi za ki sa
nar da jama'a da ubanta. Amma fa kin san dole a samo shaidu." Na jijjiga kai "Shaidu ba matsala ba ne, yanda nake tunanin zan saka Umar ya sake ni cikin sauk'i shine abin ji, amma zan shirya tafiya Jordan don na samo shawara mai b'ullewa." Ta d'aga kai "In
dai shawara ki ke nema, we ba sai kin je jordan ba, ki ba shi abin maye ya sha a lokacin sai ki tursasashi sai ya sake ki ki sa kuma ya rubuta a takarda, ta yarda duk bala'insa bai isa ya k'aryata ba, daga nan sai ki ce masa za ki yi zaman iddarki." Na d
'aga mata kai kafin na ce "To ta yaya? Zan zauna a gidansa har sai na yi zaman idda na samu ciki na haife sannan zan koma wa aurensa." Ta yi jim kafin ta ce "Dole ki san yarda ki ka tsara ki ka sako Ummeey a maganar ita ce zata zame mana garkuwa ta hanyar
ce masa za ki yi zaman y'ay'anki, amma fa ki tabbata saki uku ya yi miki, ki yi masa duk tijarar da zata saka dole sai bayan kin haihu kin d'aura aure da wani ko na awanni ne sannan ya sake ki shi kuma ya mayar da ke, duk da auren kisan wuta ba kyau amma
a wannan gab'ar dole haka za'a yi, tunda kin san ke ba auren kisan wutan za kiyi ba, already da aurenku da buzu, idan ya rasa wanda zai zab'o sai ki ce ke kina da shi, sai mu gabatar da buzu mai
gadi, daman mijinki ne kin ga bai zama auren kisan wuta ba."
Na jinjina lamarin kafin na amince da hakan za'a yi. Yanzu buk'atar yanda za mu shawo kanta da Umar ya sake ni kawai.
Tun daga lokacin na d'aura d'amabar yi wa Umar rashin mutunci, ba lamarin da yake bak'anta masa kamar yarda na yi shakulatun b'angaro d
a shi a rayuwar auren mu, a kuma duk sanda aka yi magana na kan sanar da shi danginsa ba sa so na ni na gaji da shi ya sakeni kawai. Na sha fad'a masa magana musamman akan mahaifiyarsa, amma ko gezau sai dai ya dinga min hawaye yana cewa na taimakeshi ni c
e rayuwarsa.
Ranar muna zaune da daddare na fece wanka sai zabga k'amshi nake, chewingum ne a bakina ina masa taunar rashin arziki. Kawai Umar ya shigo wata ajiyar zuciya ya saki zatonsa daidaitawa nake son mu yi, ni kuwa a zuciyata na yi alk'awarin dole
ne ma Umar yau ya sakeni kuma a cikin hankalinsa ba ba wai a maye kamar yarda da muka shirya ba. Ya zauna gefen hannun kujerar da nake yana jifana da murmushi, abin ya tab'a zuciyata amma na share na tsuke fuskata ina cigaba da taunar chewingum d'in da nak
e. Ya shiga nuna min yarda ya yi kewata amma idona cikin nasa na dinga zabga masa rashin mutunci, ga shi a yanayin da muke dole ya shiga damuwa saboda ya yi nisa ba ya jin kira. A tsawa ce na janye jikina na ce "Umar ban san kai tantirin mara zuciya bane s
ai yanzu, Haba mutum sai ka ce bunsuru na ce bana sonka bana sonka ka k'i yarda, to yau zan sake jaddada maka idan ka cika d'an halak cikin uwarka da ubanka ka sakeni kuma saki uku ba d'aya ba." Tunda nake ban tab'a ganin zallar b'acin ransa kamar na wanna
n ranar ba, fuskarsa ta had'e sosai sai hucin bak'in ciki yake murya a shak'e ya ce "Ko kece Hurul aini na sake ki saki uku.." Ya yi furucin wasu hawaye na zubar masa a k'unci, ya mik'e ya zira rigarsa. Sai na ga kawai ya durk'ushe ya kife kansa a kujera
ya saki wani irin rikirkitaccen kuka. Buga kansa yake yana fad'in "Why? Why? Sakna?" Ni kaina a yadarance na saki kukan ina rungumeshi Umar ka sakeni? Saki fa Umar?" Tsam ya rik'e ni a jikinsa sai saukar da numfashi yake yana "Na shiga uku Sakna, ban san m
e ya shiga kaina na aikata ba, ke kika jawo Sakna." Ji na yi numfashinsa ya yi d'if alamar ya d'auke. Da sauri na mik'e ina jijjiga shi "please Umar kada mu yi haka da kai don Allah ka tashi." A diririce cike da firgicin lamarin na shige toilet d'in d'akin
na d'ebo ruwa na watsa masa. Sai ga shi ya kawo numfashi mai nauyi, idanunsa cikin nawa ya mik'o min hannu, muryarsa can k'asa ya ce "Allah yasa mummmunan mafarki nake, ba a zahiri abubuwan da na gani Suka faru ba." Cikin yaudararrun hawaye na shiga gyad'
a masa kai kafin na ce "Mai afkuwa ta afku Umar ka sake ni har saki uku? Yanzu mai Zan ce da dangina? Musamman wad'anda dama suka tabbatar min nan gaba sai ka cutar da ni, mahaifiyata dama a kullum burinta kenan ka sakeni, ga shi yanzu ka aiwatar da hakan,
duk abinda ka ji na gaya maka ko nake maka, wallahi ba har cikin zuciyata bane, duk na yi ne don in tabbatar da son da kake min. Sai ga shi ka yi abinda muka haramta da juna har abada ko na ce sai na yi wani auren mijin ya sake ni sannan ka ke da damar ma
yar dani." Wani irin hawaye Umar ya saki, yana sake ja na jikinsa. Ni