Showing 99001 words to 102000 words out of 129261 words

Chapter 34 - YA ABIN YAKE complete

28 Aug 2026

63

Salman ta bata, ba tare da tsinkaye da tunanin mai lamarin zai jawo ba. "Yanzu ke Anty Sadiya sai ki amince Hammad ya had'a zuri'a da jinin macen da k'iri'kiri ta mayar da ke bora a wajen mijinki, way

e bai san irin cutarwar da waccan matar take miki ba, ai wallahi idan nice yanzu za'a fara wasan ba KK ba ko shugaban k'asa ne ubanta ba zan bari d'ana ya maye mata gurbin miji ba, ai ko don na cusawa uwarta bak'in ciki ta d'and'ana itama ta ji sai na tuje

wannan auren Hammad da ikonki ne, kema a yanzu za ki ja zaran na ki mulkin, ki nuna power da ikonki haba Anty mana kada ki bada ni mana." Sadiyar ta yi tsai da ranta tana jin shawarar da y'ar uwarta ta bata abar d'auka ce, ya kamata itama ta wargaza farin

cikin D'an Borno musamman Sakna ta cusawa ta ta y'ar bak'in ciki, abinda ta so yi da kenan wata zuciyar ta dinga kwad'aita mata kud'i da arzikin KK sai dai yau Salma ta farkar da ita daga mafarkin da take, ya kamata itama ta murd'a kambunta ta ja zarenta t

abbas! Ta saki ajiyar zuciya "K'warai Salma, kin tunasar da ni abinda zuciyata da hasashena suka manta, saboda kwad'ayin dukiya, amma ta ina kika ga zan fara?" Salma ta saki murmushin jin dad'i ta ce "Ta yau zaki fara ana shan ruwa ki tarasu a falon Didin

ki sanar da su buk'atar Ki Hammad ya saki Hamda, ke ba ki amince da auren ba, kuma duk juyin da za'a yi ki kafe a kan hakan, ai kin gane, yanzu za kiga kema kin zama sarauniya an zo ana lalla'ba Ki, ki jajirce kice wallahi za ki tsine masa idan bai saketa

ba." Sadiya ta saki murmushi ta kuma amince da shawarar da jaririyar k'anwarta ta d'orata a kai saboda rashin wayo, jaririya mana tunda Salma sa'ar d'anta na uku ne wato Hameed, ta saki dariya tana tuno yarda Sakna da Didi za su durk'ushe a gabanta suna ne

man ta amince da auren, ita kuma ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana izzar mulki da rantsuwar Hammad d'in sai ya saki Hamdan...

🤣🤣



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍







ALKALAMIN JIKAR NASHE

📲

YA ABIN YAKE? 43.

*08033748387*

Wani irin kallo Di

di take mata kamar ta ga abin kyankyami, ta mayar da kallonta kan Hamdan da take k'ok'arin mik'ewa ta ja wani dogon tsaki kafin ta ce "Ammo ce ta aiko ki ba Ammi ba, ni za'a kawowa kinibibin banza, wato ta ga uban yarinya mai kud'i ne shine za'a zo a kanai

nayeta, to wallahi ki gayawa Sakina ta fita idona, uban me ma ta baki ki kawo mata, wato yanzu zata nuna min ita ta haifi y'ar bayan da ta banzagatar da lamarinta, zube kayan mu ga wace uwar ce a ciki?" Munira gaba d'aya ranta ya b'aci jin abinda Didin ta

fad'a duk da ta san gaskiya ta fad'a amma ai Ammin ta yi nadama me yasa ba za'a bar abinda ya wuce ya wuce ba, ita kuwa Hamda zuciyarta fara k'al ko bakomai Didin yau ta biya ta, da Ammin me ta sani nata ita kam ko ina zata bugi k'irji tace Didi ce babarta

, sai Abbu shima ba zata mance kulawarsa gareta ba. "Ki ke kallo na ko duka

na za ki yi? Zube kayan nan naga me aka k'unshe za'a je a bata, tun yanzu wato za'a fara koya mata bak'in halin asiri, to wallahi ba zan yarda ba eehe." Asma'u ce ta kashe maganar

ta hanyar cewa "Haba Didi, duk me ya kawo haka? Ya za'a yi kice sai sun ware kin ga abinda ke ciki." "Ki kiyayani Asma'u babu ruwanki ta bud'e naga me yake ciki? Na sani ko maganin mallaka ne ta bata a mallake min jika kamar yarda aka mallake ubansa." Ciki

n takaici Munira bata san sanda ta zazzage kayan ba ta ce "Ga shi nan, kayan gyaran aurene da ake bawa duk wata mace idan za'a mata aure, wannan ki dinga sha da yoghurt wannan zuma ce wancan kuma turaren tsuguno ne, sai kuma tace a gaya miki ki dinga shafa

wancan a fuskarki every morning kafin ki yi wanka na gyaran fuska ne kafin a sallace a fara muku gyaran jiki." Didi ta ja tsuka "Zancen banza zancen wofi, ce mata na yi ba zan siya mata kayan gyaran ba, tun yaushe ma Asma'u ta fara mata kinibabbiya kawai,

d'auki ki mayar mata." Asma'u ta yi saurin cewa "A'a Didi, ba za'a mayar ba, ko wanne da irin aikinsa wannan na san na can garinsu ne, ki ce mata an gode." Asma'u ta kwashe kayan ta na mayarwa leda, Munira ta juya ranta a b'ace ta fice daga falon.

Ana

shan ruwa ya shiga falon Didin, don yau Nanna bata nan a gidansu zata sha ruwa, fuskarsa a d'an had'e take don haushin Hamda yake ji kamar me? Ace mace ta yi banza da mijinta kuma ta ganshi amma ta d'auke kanta, ko gaisuwa a haka za suyi ta su rayuwar aure

n kenan bai isa ya sata ba, bai isa ya hanata ba?

K'ananan kaya ne a jikinsa na companyn Ck da suka matuk'ar amsar gogaggiyar fatarsa, sosai ta yi kwalliya fuskarta fal annanshuwa musamman aminyarta ta sun iso ita da yayyanta maza guda biyu. Riga ce dogu

wa a jikinta da ta fitar da duk wani shape na jikinta, sai hula irin ta turban d'in da ake ya yi ta d'an zameta ta yi baya, kwantaccen gashin da yake gaban goshinta ya bayyana bak'i sid'ik da shi, ta yi kyau sosai duk da ba kwalliya ta yi ba, idanunsa ya s

auke cikin nata cike da takaicin yanayin shigar da take jikinta ga kuma Maza a wajen, ransa a b'ace ya dinga hurga mata harara. Didi tana ganinsa ta ce "A'a ka daina fushin ne ka shigo?" Sake tsare girarsa ya Yi sosai Yana amsa gaisuwar da suke masa ya kal

li Didi "Ban da matata mai k'aunata bata nan, ban ga mai Zai kawo ni nan ba." Asma'u ta guntse dariyar da take shirin kamata don ta lura sosai Hammad yake Jin haushin hanashi keb'ewa da Hamda da aka yi. Hamda kuwa ranta a b'ace bata san sanda ta d'ago ta w

urga masa wani kallo ba ya yi kamar bai ganta Ba Kafin ya kalli Sa'ada ya ce "Yarinyar kirki zubo min abinci maza ki kawo min shiyyata." Ya saka kai ya fice ji yake kamar ya mak'ure Hamda ya hukuntata da y'ar banzar shigar da ta yi. Didi tace "Zancen Banza

, abincin ma ka yi masa zuciya mana yaro Sai cin tsiya." Sa'ada na shirya abincin ASMA ta kalli Hamda ta ce "Maza ki rakata ku kai masa k'afarki k'afarta kuma." Hamda ta d'aga kai alamar amsawa ko Umma Asman bata ja kunnenta ba, takaicin maganar da ya jefe

ta da ita ba Zai saka ta zauna ba, ya tafi can wajen matar tasa, ina ruwanta....

Kusan mintuna biyar suna knocking a bakin k'ofar sashen nasa bai bud'e ba, kamar ya san da ita aka zo ya d'au lokaci kafin ya bud'e, fuskarsa a d'aure yake dubanta, yana mamak

in yarda lokaci d'aya ta birkice masa kamar ba Hamdan da ya sani ba, mai son sa da jin maganarsa, ta bi ta hau maganar Didi ta zauna a kai kamar wani fad'ar annabi, idanunsa cikin nata yana k'are mata kallo, kallon da ya takurata ta sunkui da kai, gaba d'a

ya kallon ya saka mata wata irin nutsuwar da bata shirya yinta ba, ita kuwa Sa'ada dariya ce take son kamata ganin yarda ma suka manta da ita a

wajen har sai da ta yi gyaran murya sannan Hammad ya ankare ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya kafin ya mik'

a hannu ya amshi basket d'in abincin da yake hannun Sa'ada ya ce "Je ki abinki Sa'ada akwai aikin da

Zata min yanzu zata taho." Hamda tayi raurau da idonta kafin ta ce "Wallahi Didi tace min kada na dad'e ka ga fad'a zata min." Ya watsa mata wani irin kall

o da yasa Sa'ada wata irin dariya ta so kub'uce mata ta juya da sauri ta wuce don ba su saba y'ar wasa da Yaya Hammad d'in ba, amma kallon da yake jifan Hamdan da shi abin so ne ga kowacce mace mijinta ko saurayinta ya dinga mata shi, kallo mai nuna zallar

so da nuna kewa ga wanda akewa shi, hannunta na rawa ta mik'a masa flask d'in kunun "Please Yaya Hammad ka karb'a kafin kasa Didi ta tara min mutane..." "Masifar Didi da tsinuwar mala'iku wanne kika fi gudu? Idan ba zaki shigo ki je kawai." Hawaye ne ya f

ara k'ok'arin zubo mata kafin ta saka k'afa cikin falon gabanta na fad'uwa, ta tsaya cak a bayan kujera shi kuwa tab'e bakinsa ya yi ya cigaba da zuba abincinsa lura da yayi da ko cewa ya yi ta zuba masa yarda take a tsorace ba zata zuba ba, shi har mamaki

nta ma yake kada fa ta zamo masa bagidajiya ba irin Nanna da take kanainayeshi ba, da sonsa da ba son ransa take fincikar ra'ayinsa sau tari. Ya fara kurb'ar kunun idanunsa suna yawo a kanta ta ji yace "Wani sabon salo kika samu? Sai kace sabon aure ba zak

i dawo nan kusa da ni ki zauna ba? Saboda kina tsoron Didi ko?" Ya taune leb'ensa d'aya kafin ya furzar da huci ya ce "Idan kika ce haka zaki min wallahi a gadon Didin zan zo na karb'i hak'kina haka kawai saboda wata bidi'a ta banza da wofi ki yi ta d'auka

n zunubi da azimin nan, ke kika jiyo ni ina da wata matar yau ma rashinta ne yasa nake binki duk da ba ni na jawoki ba, ke zaki je ki yi ta kwana rungumar filo ai dama Sabonki ne tun kina budurwa."

Wani irin kallo take jifansa da shi kamar ta zunduma masa

ihu jin abinda yake ce mata, ita zai gayawa wani yana da mata ai ta fisa sani dama ita ta kawo kanta har da zai tsaya ci mata mutunci, haushi da takaicin kalamansa yasa ta juya a zuciye ta fice daga falon duk da tana ji yana k'wala mata kira. Ya saki ajiya

r zuciya yana jin takaicin yarda bakinsa ya ja shi ya sake b'allowa kansa ruwa ya santa sarai da d'an banzan kishi, ba waya a hannunta balle ya kirata.

Tana zuwa falon ta tarar da bak'i a falon Didin atamfofine da laces da shaddodi take ta bud'ewa, sai wa

su akwatina biyu da kit a gefe, kasancewar zuciyarta ba dad'i yasa ta yi k'ok'arin shigewa d'aki bayan ta gayar da bak'in mazan da suke zaune. Didi ta ce "Ke Hamda zo nan ai sak'on naki ne, KK ne ya aiko ko da yake wannan ni ya aikowa ya ce a rabawa dangi,

wancan akwatinan dai su ne naki." Hamda ta koma ba don ta so ba ta hau bud'e kayan sabuwar wayar tafi tafiya da imaninta wacce take cikin kit d'in sai dantsatsetsiyar sark'ar gold wacce da gani babu tambaya dollars ta sha kuka wajen siyanta, akwatinan kuw

a laces ne dandatsa-dandatsa da atamfofi super sai mayafansu HD Veils da jakunkuna uku da takalmansu, a ranta ta yi farin ciki da kayan amma yarda zuciyarta take tunzira da kalaman Hammad yasa fuskarta bata nuna ba, Sa'ada kuwa sai tsalle take tana d'aga I

phone 14 pro max tana cewa wallahi yarinya kin shigo gari. Bata tab'a komai a kayan ba ta mik'e ta shige d'aki, tana shiga ta yi wurgi da d'ankwalin kanta gashinta ya wargaje, sai sannan wani kuka mai k'arfi yazo mata, ji take da tana da hali da ta fasa au

ren Hammad d'in don ita tana daga cikin jinsin mata masu zafin kishi. Kuka ta yi sosai bata fito falon ba har sai da Sa'ada ta shigo kiranta Didi ta tara ayarin gidan wai zata yi rabon kayan sallahr da KK ya kawo.

Fuskarta a kumbure ta fita, duk wanda ya

kalli idanunta ya san ba k'aramin kuka ta sha ba, shi

kansa Hammad hankalinsa a tashe yake dubanta ji yake da da hali da ya kai mata runguma ya rarrasheta, amma ina ko arzikin kallo bata samu ba, sai ma harara da ta wurga masa ta yi k'asa da kanta. Abbu n

e ya lura da yanayinta ya ce "Zo nan Hamda me ya sameki haka? Naga kamar kin yi kuka?" Girgiza kai kawai ta yi tana k'ok'arin mayar da hawayen da suke son sake zubo mata, murya a dashe ta k'arasa kusa da Abbun tana girgiza kai ta ce "Bakomai had'e da galla

wa Hammad harara." Didi ta ce "Kaima dai Ummaru da shirme ka ke, kukan me zata yi banda na farin cikin samun uba kamar KK ga uban kaya da ya d'and'aso mata ga shegiyar waya." Hamda ta zabga mata wani kallo kafin cikin takaici ta ce "Ni ba kukan da nake ba

kenan, ke wannan ya dameki ai dama tun kafin Ya zo Abbu yana mana duk abinda muke so." Sosai Abbu da Ammi suka ji dad'in amsar da Hamda ta bawa Didi, idan ita ta manta gwara Hamdan ta mata matashiya kuma ya san ko nan gaba Hamdan ba zata gujeshi ba. Didi t

a ce "Y'ar banza mai ido a tsakar ka, duk tsiyar Ki dai da KK d'in zaki tunk'aho.." ta sake zunb'ura baki "Ni wallahi da Abbu zan yi tunk'aho tunda shi ya yi d'awainiya da ni har na girma." "Ke kika jiyo, ba wannan yasa na tara ku ba, kai Hammad tunda Sadi

ya ta k'i zuwa bak'in cikin duniya ya isheta kaje ka kira min ita ko zuciyarta zata buga sai ta ga wannan kab'akin arzikin, don ina lura da ita tunda lamarin nan ya faru shikkenan Sadiya halin uwarta ya fara bayyana tare da ita, yo uwarta banda dai idan ta

so mutuniyar kirki ce ai da ba ta zama aminiyata ba, don ko farar k'asa aka shafe min d'aki da ita sai hassadar ta ta nuna, ta dinga nurk'ufanci kenan, sai dai Akwai kyauta, kawaici da alkunya sumumu kasau ce ta gaske.." Hammad ya datsi leb'ensa banda idan

uwan su Abbu yau kam da ya ganar da Didi kurenta. Ya saka kai ya fice yana ji tana fad'in "Sai dai hararar duka dai ba zan daku ba, ja'iri mai idanuwa kamar na muzuru."

Yana saka kai d'akin Mahmah ya ji tana waya tana fad'in "Sakna nace miki yanzu fa zan

je don na ji ance duk ta tara mutane wai za tayi rabon kayan sallah, to yanzu zan je wallahi nace and Atabau bana son auren....." Hammad ya tura k'ofar idanunsa zube cikin na mahaifiyarsa yana jin takaicin yarda Salma take neman jirkita masa zuciyar Mahma

hnsa mai adalci, baya son laifin da yake tsakaninta da Ammi ya shafi aurensa da Hamda, su d'in ma k'ok'arin sa kullum su fuskanci juna su zauna lafiya duka-duka duniyar ma nawa ce, ya saki ajiyar zuciya yana zama a kujerar da take gefen gadon a hankali ya

ce "A sani na dake Mahmah uwace da za'a yi alfahari da ita, duk gidan nan an shaida cewa ba kya barin kishin da ke tsakaninku da Ammi ya shafi mu y'ay'a, abubuwa nawa kika shanye sai yanzu da rayuwar ta zo gangara za'a samu wasu can daga gefe su zuga min k

e Mahmah, don Allah kada zuciyarki ta amince da zugarsu su zo su saka ki ki yi abinda zai zubar mana da

K'imarki da mutuncinki da

Ake gani, kowa fa ya shaida hak'uri da juriyarki a zaman aure wanda muke fata ya dalilin haka Ubangiji ya yi miki sakamako da

jannatul Aaliyah. Don Allah Mahmah ki janye wancan furucin da na ji kina yi a waya ko ma da wa kike yi na tabbata Ba shawara mai kyau yake baki ba wacce duk wani mai sonki zai ba ki, ki d'auki Hamda kamar y'a insha Allahu ba za ki yi dana sanin aurenmu ba,

sai kin yi alfahari da haka sai kince gwara da aka yi, kuma ni Mahmah wallahi ko wa na aura ba zan bari ta rainaki ba, Zan jajirce wajen kare martabarki da k'imarki, kuma in dai tana sona dole ta miki biyayya." Sosai zuciyarta ta samu nutsuwa har ta ji ta

na jin kunyar abinda ta so aikatawa duk da Allah ya dubi zuciyarta bata aikata ba, ita kanta ta san ba halinta bane sharrin shaid'an ne da karakainar zuciya suka so dulmiyar da ita, ta godewa Allah da ubangiji ya kawo

Hammad ya ankarar da ita abinda zuciya

rta da tunaninta suka so su gusar mata, Sai ta samu kanta da jin kunyar Hammad d'in shi kansa ta yarda yana d'an cikinta shi ya zauna yana tunasar da ita abinda ta manta, kaiconta da ta so jawowa kanta da zuri'arta abin kunya, da da wani idon zata dubi Ham

da yarinyar da ta rik'eta tamkar Uwa take ganin daraja, k'ima da mutuncinta, sau tari Idan Uwarta ta tunzirota tana kuka idan Didi bata nan, nan wajenta take zuwa ta samu sauk'in zuciya. Ta gyara zamanta tana sakin wata ajiyar zuciya ta murnar rashin aiwat

ar da k'udirinta ta tabbata da mutuncinta ya zube a idanun duk jama'ar gidan. Hammad ya saki murmushin samun nasara kafin ya mik'e da kansa ya yafa mata mayafin yana fad'in "Alhamdulillah, Da Allah yasa ki ka fahimceni yanzu ma Didi ce ke nemanki, kowa ya

halarta banda ke." Ta mik'e jikinta a sanyaye ta bi bayansa zuciyarta tana jin farin ciki a hankali ta furta "Madalla da kai ubangiji madalla da samun Y'ay'a na gari ko da su kad'ai aka barni ba abinda zance sai Alhamdulillah!"

A falon kowa ya hallara,

ta samu zuciyarta da tsinkewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login