Showing 1 words to 3000 words out of 111085 words
[6/25, 11:52 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 1.
*Gargad'i*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani
ɓ
angare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a
ɗ
aura min shi a
wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Alhaji Hamid.
Yana zaune a cikin mota ya fito daga wani super market da ya yi siyayya, yana ƙoƙarin tayar da motar sai ga kira ya shigo wayarsa, da ya ga sunan d
aya bayyana akan wayar ai da ya saki lallausar murmushi kafin ya
ɗ
aga yana mai cewa.
Amincin Allah ya tabbata a gareki hasken idaniya, yanzu na fito daga super market domin siyayyarki.
Uhum na
ɗ
auka ka matan da ni ne ai,
ɗ
an naga yinin yau baka kira ni b
a.
Ta fa
ɗ
a a shagwa
ɓ
e. Hamid ya yi
ɗ
ar dariya.
Aiki ne yasha kaina amma kina raina Madeenar Hamid da fatan kina lafiya.
Ni bana jin da
ɗ
i dan zazza
ɓ
i ke damuna na rashin ganinka.
To kisha kuruminki ina tafe bayan sallar magrib In Sha Allah, yanzu haka g
ida na nufa na kimtsa kafin na zo.
To beb sai na ganka dan ina kewarka sosai ka kula min da kanka.
An gama ranki ya da
ɗ
e Madeenar Hamid.
Ya fa
ɗ
a cikin yalwar farin ciki itama ta saki murmushi mai sauti daga haka suka kashe kiran, Hamid ya sauke gauron n
umfashi tare da jinsa cikin wani yanayi na shauƙin soyayya, bai ta
ɓ
a tunanin akwai
ɗ
an
ɗ
anon so irin wanda yake ji akan Madeena ba, saboda koda yayi auren farko lokacin yana cikin duhun kai akan sanin da
ɗ
in soyayya, duk da ya yi boko dan digree gareshi a fa
nnin kasuwanci amma akwai tarin kuriciya a kansa, musamman matar daya aura Sakina ta kasance kidahuma ba wani ilimi gareta ba, hasalima a gidansu daga primary mace bata ƙara wani karatu ake yi mata aure, na islamiya ma na allo ne shima bata sauke ba, kuma
ya aureta cikin ƙuriciya dan tana 'yar shekara sha hu
ɗ
u shi kuma yana da shekara ashirin da biyar, shiyasa rayuwar aurensu banda tarin wauta da sakarci ba abinda suka sani, sauƙin ta ma cikin rufin asari suka yi shi domin mahaifinsa Nuhu tsohon soja ne da
yayi retire, kuma yana da comfanin sabulu wanda Hamid ke gudanar da shi, Abba shi ne yayi masa aure bai san wani wahala da angwaye kesha ba, har kawo yanzu da aurensu shekara sha biyar suna cikin wadata dan babban gida filat gareshi kusa da na iyayensa ya
yi gini, wanda 'yar ƙaramar ƙofa ya fitar a tsakani dan sauƙaƙa hanyar shiga, da ku
ɗ
insa yayi ginin saboda Hamid mutum ne mai himman da niman na kansa, duk da yana kula da companyn mahaifinsu to sai da ya ha
ɗ
a da kasuwancin motoci da yake shigo dasu daga ƙ
asar waje, yaransu hu
ɗ
u ta farko itace Mufeeda sai Nuhu mai sunan Abbansa sai Yaƙub da autarsu Rauda wacce a yanzu haka Sakina ta yayeta 'yar shekara biyu da rabi.
Tun lokacin da Allah ya ha
ɗ
a Hamid da Madeena a bikin wani abokinsa wanda Madeena itama ƙa
war amarya ce, a ganin farko da yayi mata Allah ya
ɗ
aura masa mugun sonta da hangen ita ce daidai da sa'ar aurensa, musamman yadda yake jinsa da
ɗ
anyan ku
ɗ
i to yana buƙatar matar nunawa sa'a da kece raini dan kuwa Sakina ba tada zubin matan da zai iya fita
taro da ita, ga rashin wayewa da rashin ilimi duk da tana da kyanta dan black beauty ce, amma sam Hamid baya ganin kyanta, ko dan sun jima a tare ne da kuma son kasancewa da farar mace yasa yake jin haka ƙila, domin Madina fara ce gata da tsayi dan ba za
a sanya ta a jerin gajeru ba kuma tsayin na ta bai yi yawa ba ga shape Masha Allah domin akwai hips da dukiyar fulani, ga kuma manyan idanu da kuma dimple, a takaice itace irin matan nan da ake kira full option, domin ta ha
ɗ
a komai rashin sumar kai ne ka
ɗ
a
i yayi mata cikas amma bata tsaya hakan ba sai da ta ƙara da na atach, sannan tana da ilimin zamini sosai dan tayi digree a fannin masscom sannan ta kuma yi masters, islamiya ba laifi tana da sani sai dai tafi mayar da hankali wajen boko, wajen shiga kuwa
ba a magana dan ta iya
ɗ
aukar wanka da iya kwalliya, sannan ta iya bulbula turare a jikinta dan duk inda ta gibta sai ya
ɗ
auki ƙamshinta, wannan dalilin yasa Hamid ya riƙe mata wuta akan lallai sai ya mallaketa, dan Madina ba irin matar da za a kalla a wuc
e bane tana buƙatar a killaceta a guri
ɗ
aya, kuma yayi sa'a a gun Madina dan ya samu kar
ɓ
uwa domin shima ba baya ba wajen iya shiga da kashewa kansa ku
ɗ
i, dan fa yana cin guminsa, duk da baƙine shi amma Kana ganinsa kasan hutu ya zauna, yana da kyansa daid
ai misali kuma yana da tsayi bai da tumbi dan bai yarda cin da
ɗ
i ya sauya masa halittarsa ba yana kulawa da hakan sosai, gashi
ɗ
an gaye saboda shigar manyan kaya ko ƙananun kaya babu wanda baya kar
ɓ
ansa, yana da matuƙar tsafta da kuma son mai tsafta, shiya
sa yadda yake ganin Madina tsaftsaf kullum shi yake ƙara masa sonta da hangen in ya aureta zata share masa hawayensa, domin Sakina ba tada kula da tsaftar gidansa duk da tana iya nata ƙoƙarin kuma tayi tayi ya
ɗ
aukar mata 'yar aiki yace shi baya so, ƙazant
ar ta da yake gani shine ma ya ƙara masa ƙaimin ƙara aure, kuma ga dukkan alamun da yake gani yayi gamdakatar dan Madina yake hange itace mai share masa hawaye da maye gurbin duk abubuwan da Sakina bata yi masa, yanzu ne yake jinsa zai yi rayuwar aure mai
da
ɗ
i a da can wasan yara ne yayi, duk ya ƙosa wata guda daya rage na aurensu yayi dan a hannu yake kamar bai da mata, domin Madina ce sanyin idaniyarsa.
Haka ya cigaba da tuƙi yana tunaninta har ya isa gida, ya buga hon mai gadi ya bu
ɗ
e masa gate ya shig
a kana ya adana motar, ya fito riƙe da ƙaramin farar leda daya siyawa yaransa kayan ciye ciye dan koda ya siyawa Madina nata bai manta da su ba yana matuƙar son yaransa, ya tsaya a jikin mota ya kwalawa Ibro mai bawa fulawa ruwa da gyaran farfajiya kira, y
a tawo da saurinsa yana risinawa tare da gaisheshi ya amsa fuska sake.
Yauwa Ibro ga motata ina so a wanketa amma banda ciki, ba zan jima ba zan fito dan akwai in da zani.
To yalla
ɓ
ai a fito lafiya.
Ibro yace cikin sauri ya nufi inda kayan aikinsa ya ke
domin ya gabatar da aikin Alhaji. Hamid yana tura ƙofar falo da sallama ya hango tsakiyar falon da datti nan take annurin fuskarsa ya ƙaurace ya maye da
ɓ
acin rai, haka ya ƙarasa ciki ya tsaya yana ƙarewa falon kallo, ba kowa a ciki sai hayaniyar yaran da
ya ke ji a kitchen, ya kalli carpet
ɗ
in dake tsakiyar falon da yake kalar fari da brown amma har ya fara sauyawa zuwa kalar datti, ga ledan biscut da sweet a kai ga kuma icen alayyahu da aka yi amfani da shi aka barshi,
pillon kujerun duk a ƙasa ga plate
ɗ
in abinci da aka ci aka barshi duk an zubar, cikin ƙunan zuciya ya shiga kwalawa Sakina kira kamar tarar aradu.
Sakina! Sakina!! Sakinaaa.
Cikin sauri ta fito daga kitchen tana amsa kiran tare da yi masa sannu da zuwa, Hamid bai amsa ba ya bita da wani
irin kallon tsana.
Wannan wani iri hauka ne zan zo naga falo kamar filin dambe, yanzu da ace da baƙo na shigo haka zaki saka na ji kunya, a matsayina na Alhaji Hamid ya dace aga falon gidana haka kaca kaca, wlh tallahi na gaji da wannan ƙazantar taki, ayi
mace sai ka ce tunkiya uwar tam
ɓ
ele, taya ma bazan ƙara aure ba kina irin wannan jakancin, madadin na shigo naji falo ya
ɗ
auki ƙamshin turaren wuta, ina can waje ina hura hanci da fankama mutane na ga Alai Hamid ina yaƙe baki dajin ni wani shege ne, amma
matata ba abun ke ba ilimin ba kuma tsafta, in je taro dake ana zuba ruwan turanci kina zare ido kamar kyanwar data ci barkono kina baje hanci kamar kinji warin ja
ɓ
a, to Wlh da sake Sakina aure ba fashi nan da wata guda Madina zata zo ta wanke min baƙin ci
kin da kike ƙunsa mini.
Abban Mufeeda ina iya kokarina kuma ka ce baka so ka dawo ka tadda ban gama girkin dare ba, kuma ina ta sauri ne na gama da kitchen kafin na fito falo na gyara kan ka shigo fa.
Ta ƙare maganar hawaye yana cika mata ido dan sosai m
aganganunsa suka ƙona mata zuciya, duk da yaci ace ta saba da irin cin zarafin da yake yi mata wani sa'ilin ma a gaban yaransu, Hamid ya ja guntun tsaki.
Amma ai na fada miki ki riƙa fara yin komai da wuri kafin lokaci ya ƙure miki, idan kin
ɗ
aura girkin
ai sai ki zo ki gyara nan
ɗ
in...
Hamid ya kake so nayi ne, kuma kace Waina kake so nayi maka yau, ga ƙullun bai tashi mini da wuri ba dan ban da
ɗ
e da gama suyar ba, yanzu ne na samu damar
ɗ
aura miya ina wanke ganye ne ka shigo, kuma saurin da nake yi na g
ama na zo na gyara nan. Kasan halin yaran nan in sun dawo makaranta
ɓ
ata guri suke yi ga Mufeeda Hajiya ta aiko kiranta tana can gidan bata dawo ba dama...
Dama me? ai kin iya jero magana kamar wacce ta ha
ɗ
iyi Radio, wlh rashin ilimi ba ƙaramin cutar dake
yake yi ba Sakina, dole zan zo na fara shirya yadda zaki koma makaranta koda yaƙi da jahilci ne ki samu wataƙila zaki san yadda kan duniya take ciki, shiyasa ko taron makarantar yaran nan ban yarda kije ba dan karki bani kunya. Ki kuma gyara gidan nan kaf
in na fito daga
ɗ
akina na ji yana ƙamshi, shashasha sai anyi magana ki riƙa fuskar tausayi kina sunsun da kai uwa mumina.
Ya ƙare maganar yana danƙara mata harara kana yayi gaba ya wuce
ɗ
akinsa, Sakina da ido ta bishi wanda hawaye cike fal da idonta kamar
zasu zubo mata, sauke numfashi tayi tana girgiza kai ta juya dan ta koma kitchen sai taga yaran sun tsaya suna kallonta, wato komai ya faru a kan idonsu, baba ƙarami
ɗ
an shekara sha
ɗ
aya shi ne yace.
Mama kiyi haƙuri ba zamu ƙara
ɓ
ata falon ba tunda fa
ɗ
a
Abba yake yi miki.
Baba ƙarami bana son surutu maza kaje ka kwashe jakar makarantarku ka kai
ɗ
aki.
To yace kana ya nufi inda jakarsu na makaranta yake ya
ɗ
auka ya nufi
ɗ
aki, ita kuma tsintsiya ta
ɗ
auka ta fara gyaran falon, ba jimawa ta gyara falon ta s
aka turaren wuta a burner sai ta wuce kitchen dan duba sanwar miyanta, sai dai zuciyarta kunshe yake da tsananin damuwar abin da Hamid yake yi mata tun da ƙuruciyarta har kawo yanzu, babu abinda yafi kona mata rai sama da yadda yake zaginta da jahila, ga k
omai tayi bata ta
ɓ
a burgeshi, tunda ya ha
ɗ
u da Madina ya rushe sauran
ɓ
ar
ɓ
ashin son da yake yi mata, ga tarin wulaƙanci daya ƙara, ita tun tana jin zafin kishin auren da zai yi har ta haƙura tana burin wannan amarya tazo gidan ko zata huta da cin kashin da
Hamid ke yi mata.
Rahma ce matar MG
[6/25, 11:52 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 2.
Sakina tana idar da sallar magrib ta dawo falo ta zauna bayan ta yi wankanta ta saka doguwar rigar shadda da hula ba
ƙ
a, powder kawai ta shafa da man baki dan ko tayi kwalliyar uban gayya ba yabawa yake yi ba, wani sa'ilin ma in ta shafa janbaki cewa yake bai yi mata kyau sai tayi kamar akuya taci dusa, in tayi ja gira kam wai kamar ta dambara kwalta, dole sai dai ta haƙ
ura da kwalliyar ta bar wa 'yan zamani suyi ita yayin ta ya wuce ko tayi bata fasali, shiyasa ta tattara duk wata kwalliya ta aje shi gefe ta cigaba da sabgarta, tana zama da mintuna sai ga Mufeeda ta shigo riƙe da kwando da kuloli aciki, da mamaki ta bita
da kallo har ta ƙaraso tana cewa.
Mama wai Hajiya tace ki saka musu waina bata samu
ɗ
aura girkin dare ba.
Haba Mufeeda kina sane da wainar nan ba da yawa na yita ba shiyasa ban yi da niyyar aika mata da shi ba, waye ma yace ki sanar da ita waina nayi.
Cewar Sakina da ta katse mata hanzari cike da fa
ɗ
a, Mufeeda ta mele fuska cike da damuwa.
Mama tambayata tayi me kika girka shine na fa
ɗ
a mata, kuma wlh nace mata bada yawa kika yi ba.
Ai kema kin san ta da kwazzaba sai taci, dan haka wanda nayi niyyar k
u tafi makaranta dashi da safe shi zan bata kwaci indimie 'yar kullun da kuka saba tafiya da shi, koda yaushe ina nuna miki ki riƙa tunani akan irin haka amma abanza, dalla muje na saka mata.
Cewar Sakina ceke da takaici, haka ta wuce Mufeeda na binta a b
aya nan ta kashe gas ganin miyarta ta yi ta zubawa Hajiyar waina takwas da miya a
ɗ
ayan kular tare da ƙashi biyu da tsoka
ɗ
aya ta bawa Mufeeda tare ta a jaddada mata akan ta dawo yanzu tazo tayi sallah ta san bata yi ba saboda baƙin aikin da Hajiyar ta sak
ata. Sai ta dawo falo ta zauna ta cigaba da kallon shirin sirrin ma'aurata a tashar sahad tv, dan yana matuƙar burgeta a nan take ƙara sanin halin maza bisaga labaren da mutanen shirin suke bayarwa, shiyasa ta ƙara kwantar da hankalinta ta rage damuwar ƙar
in auren da Hamid zai yi tunda ba fashi sai yayi, ido zata zuba masa ta ga iya gudun wuransa tasan dai wulaƙanci sai ta sha shi kwando kwando, haƙuri da juriya shine zai zaunar da ita musamman saboda yaranta. Tana nan a zaune sai ga Mufeeda ta dawo da kulo
lin, sheƙeƙe ta ke kwallonta wannan karan tasan dama sai Hajiya ta raina dan ita sam ba tada godiyar Allah, tace cikin ha
ɗ
e rai.
Ehen ta ce ki dawo in ƙara mata ko?
Eh wai bazai ishe ta ita da Alhaji ba sannan Jidda ma ta dawo ko ita ka
ɗ
ai zata cinye shi
tace.
Wannan tsohuwar da shegen ƙulafuci Wlh, ni ban isa nayi girki iya ni da iyalina ba sai ta saka rai, to ai shikenan tunda kin ja mana cin tuwo dan wainar ba zata ishe mu ba. Muje na ƙara musu guda biyu suci da haƙuri...
Iyeee Sakina ni kike yiwa
ɗ
i
bar albarka haka, to duk abinda kika fa
ɗ
a a kunnena, ashe ba kida mutunci, abincin da
ɗ
ana ya kawo shine kike fa
ɗ
ar son ranki akan nace ki zuba mini, to kome zaki fa
ɗ
a ki fa
ɗ
a amma wlh wainar nan ita zamu ci mu ƙoshi mu kwanta, ke Mufeeda muje kitchen
ɗ
in
na zuba da kaina sai kiyi duk abinda zaki yi.
Cewar Hajiya data shigo falon buguzum buguzum kamar zata kifa ta wuce kitchen tana cigaba da sababi, Sakina dai sosa kai tayi tana mele baki dan tasan tayi
ɓ
arin zance kuma taji kunyar maganar data yi, dan tas
an uwa uwa ce kawai dai Hajiyar ce take cikata har take wasu maganganu cikin
ɓ
acin rai, Hajiya kam kusan rabin wainar ta kwashe ta zube kashin miyar sai guda
ɗ
aya da tsoka biyu ta bari ta fito tana sababi riƙe da kwandon.
Shiyasa na goyi bayan Hamidu ya ƙ
ara aure tunda ke kin zama tijararriya mara
ɗ
a'a, ai da uwarki ce ba zaki hanata abincin ba, Allah yasa ya samu
ɗ
iyar arziki ba mai rowa ba irinki.
Ta ƙare maganar tana dalla mata harara da kwafa ta wuce, Mufeeda ta ƙaraso falon tana cewa.
Mama kiyi haƙ
uri laifina ne dana fa
ɗ
a mata da duk haka bai faru ba. Kuma kusan rabi ta kwashe fa sai ki barwa Abba wannan mu ko cous cous ne zan dafa mana muci da miyar bari nayi sallah.
Sakina waje ta samu ta zauna takaici ya cikata dan ta kasa magana ma, Mufeeda ta
wuce
ɗ
aki duk jiki a sanyaye tana jin haushin kanta akan meyasa ta sanar da Hajiya waina suka yi, alƙawari ta dinga yiwa kanta akan ba zata sake wannan wautar ba tunda tasan halinta ba tum yau take yiwa Mamansu haka ba. Sakina kam miƙewa tayi ta shiga kitc
hen
ɗ