Showing 27001 words to 30000 words out of 178317 words

Chapter 10 - LU'ULU'U COMPLETE

akan wani abu can da bashi da cikakken muhimmanci ga rayuwarta,don haka saita fidda daya daga cikin wayoyinta tana jin bari ta duba sashen saqonnin email dinta ta rage yawan saqonnin da suke jiranta.

Saqo na farko na biyu......ana uku idanunta suka sauka ga adireshin saqon da ya sanyata jan wani qaqqarfan tsaki da yaja hankalin aisa. Daga kanta tayi tana duban akhnan da taqi koda duban sashen da aisa din take,har yanzun idanunta nakan wayar,don haka itama aisa din saita bagarar taci gaba dayin abinda take.

Tsaki na biyun data sake ja shi ya sanya aisa yin magana wannan karon,ta aje wayarta saman cinyarta ta soke yatsunta guri guda tana dubanta.

"Wanda bai kashe zomon ba.....kuma ko ratayar zomonma ba'a bashi ba......na meye zaa cika masa kunnuwa?" Tayi maganar tana tsuke fuskarta guri guda.

Sau daya tak ta daga kai ta kalli aisa da almond shape eyes dinnan nata dake gayawa aisa ta tara maganganu ne da yawa qasan ranta amma miskilanci ya hanata fada,sai tayi abinda aisa din tafi tsana wato maida kanta kan wayarta.

Mutum biyun nan dai..... Mutum biyun nan da har kullum suke hargitsa zaman lafiyar wayarta. Zai wahala ta dauki wayarta ta gama dukka shige da ficenta a waya ba tare da taci karo da saqon dayansu ba. Ta rasa mene ne hakan?,wai tamkar ita daya ce macen da tayi saura a duniya ne?.

"Babe........the pic was so hot......thanks to aisa". Cak ta tsaya tana sake maimaita karanta saqon da ya fito daga gurin naadir......haifaffen qasar nigeria da kasuwanci ya kawoshi niger din.

"Thanks to aisa?" Ta karanta maganarsa ta qarshe. Jikinta ne ya bata wani abu,sai kawai ta sauka ta koma zuwa account dinta ba IG. Private account ne da ba kowa yake da ikon ganin abinda kake aiwatarwa,sai wanda kayi accepting dinsa,wanda duka duka nata mutanen da tayi accepting basu da yawa,ciki kuwa harda aisa.

Kai tsaye ta wuce ga sunan aisa din,ta zarce kan abubuwan da tayi posting a dukka satin.

Babban hotonta yana daya daga cikin abubuwan data saka a satin.......hoton daya samu likes da comment me tarin yawa wanda kusan mafi rinjaye da harshen faransanci ne. Hotuna ne guda biyu,guda daya nata,dayan kuma ta da aisa ne a diori hamani international airport,ranar da suka baro Niamey kenan zasu shigo zinder. Tana sanye da wata doguwar riga cikin ire iren dogayen rigunanta navy blue. Sosai color din rigar ya amshi fatarta da take jazur kaman zaka latsa hannunka jini ya fito,hakanan eye glasses din da tayi amfani dashi me duhun kala ya sake ajiye mata wani kyau na musamman,hancinta da zagayayyar fuskarta sun sake fallasa sirrin kyanta. Bata taba zaton haka rigar tayi mata kyau ba sai a wannan hoton,sai wani abu yazo ya tokare mata a wuya tana bin comments din mazan dake qasan hoton nata tana dubansu a matsayin sakarkarin da basu san ciwon kansu ba. Tarin sakarkarun kuma data bawa damar kalle fuskar da ita karan kanta wadda Allah ya mallakawa ita darajarta take gani,wannan wanne irin aikin watsar da mutunci aisa ta jawo mata?.

"Me kika aikata kenan haka aisa?" Ta jefa tambayar kai tsaye ga aisa din tana haska mata fuskar wayartata me babban screen dake riqe a hannunta daidai sanda motarsu ke kutsa kai AJY.

Fuska aisa ta tsuke itama,tana dinke girar sama da qasa.

"Mene kuwa?,shikenan mutum bazaiyi nishadi ba?" Ta jefa mata tambayar itama tana rutsata da nata manyan idanun. Kallon aisa ta sakeyi sosai sannan ta janye wayar a tsakaninsu ba tare data janye daga dubanta ba.

"Supprime ça(Delete it)"

"Baiyi niyya ba" Aisa ta fada hankalinta kwance tana maida dubanta ga qofar tana qoqarin budewa jin motar ta tsaya.

Bata ankara ba ta tsinci hannun akhnan saman cinyarta,ta dauke wayarta cak tana jefata cikin handbag dinta,daidai sanda aka bude mata side din da take,abinda ya hana aisa yunqurin amsar wayar kenan,don ita dinma sarautar na yawo a jininta,kuma tasan yin wani motsi ko yunquri zai iya zama abun kallo a tsakaninsu ko ya zubda musi kima.

"Karki yunqurin yin wani abu mara da wayata biftu.......mallakata ce".

" Idan banyi ba tabbas ban haifu ba cikin sultane" Ta amsa mata ba tare daya waiwayo ga aisa din ba.

First class take zama a duk sanda tahau jirgi komai qanqantar tafiyar. Tunda kuma suka shiga din ta karanci akwai wanda ke shirin takura mata.

Matashine da jin ke zagayawa a jikinsa tare da nuna zallar quruciya kudi da kuma wani sassanyan kyau. Yanayin kallon qurillarsa ya gama takurata kafin sannu a hankali ya qona mata rai,sai kawai ta fiddo eye glasses dinta masu duhu ta lullube qwayar idanunta dashi,sannan ta miqe bayanta jikin kujerar da take kai,ta kuma buda madame Bovary na marubucin nan dan qasar French Gustave Flaubert. Duk da novel din ya qunshi soyayya......amma jarumtar star din novel din,attitude nata da character nata sunyi mata sosai.

Sanda jirgi ya daidaita sararin samaniya da tafiyar da bata haura awa daya ba da mintuna ta rufe novel din,tana jin yadda shauqin labain ke dibanta,amma sai ta zabi ta bawa kwanyarta wani space nayin shuru ta zauna silent don bawa kwanyarta wata qaramar nutsuwa




zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*00239166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*MY NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 11



Matashine da jin ke zagayawa a jikinsa tare da nuna zallar quruciya kudi da kuma wani sassanyan kyau. Yanayin kallon qurillarsa ya gama takurata kafin sannu a hankali ya qona mata rai,sai kawai ta fiddo eye glasses dinta masu duhu ta lullube qwayar idanunta dashi,sannan ta miqe bayanta jikin kujerar da take kai,ta kuma buda madame Bovary na marubucin nan dan qasar French Gustave Flaubert. Duk da novel din ya qunshi soyayya......amma jarumtar star din novel din,attitude nata da character nata sunyi mata sosai.

Sanda jirgi ya daidaita sararin samaniya da tafiyar da bata haura awa daya ba da mintuna ta rufe novel din,tana jin yadda shauqin labain ke dibanta,amma sai ta zabi ta bawa kwanyarta wani space nayin shuru ta zauna silent don bawa kwanyarta wata qaramar nutsuwa.

Dan qaramin blanket da aka basu tayi amfani dashi ta qarasa lullube jikinta,sai fuskarta kawai dake a waje. Ta liqe idanunta da abun rufe idanu tana juyar da fuskarta window tana sauke sassanyar ajiyar zuciya.

"Biftu" Aisa ta kira sunanta a kausashe. Yi tayi kamar bata jita ba,abinda ya sake sanya aisa maimaita kiran nata har sau uku amma tayi burus da ita.

Hannu tasa ta zare abunda ta rufe idonta dashi,cikin hasala tana cewa.

"Don wulaqanci kina jina ina kiranki?.........ki bani wayata saikici gaba da kurmancinki ba damuwar aisa bane" Duk maganan da aisa din keyi idanu kawai akhnan ta zuba mata harta gama. Sai ta qarasa yaye blanket din kawai ta zauna sosai,ta dauki jakarta da sauran tarkacenta ta raba aisa din tana wuceta.

Da kallon harara aisa ta bita,jirgin ya dauki shuru kowa yana harkar gabansa,bataso kuma tayi abinda zaiyi kiran hankalin mutane a kansu,don haka taja qwafa qasa qasa,tana tunanin meye zata mata da zai zafafeta itama ta rama?.

Murmushi ya saki a hankali ganin ta koma can wani seat din daban ta narke cikin kujera tana maida blanket dinta,saidai yanzun bata lullube idanunta ba,a maimakon haka ma saita maida dubanta ga window tana ganin yadda suke keta gajimare.

A nutse ya miqe yana barin seat dinsa,ya taka a hankali zuwa inda take,wanda har ya isa din bataji motsinsa ba sai daya zauna kusa da ita.

"Hey cutie" Ya fada da siririyar muryarsa da kadan ya rage ta soma kamanceceniya data mata saboda zaqinta. Da hanzari ta waiwayo tana watsa masa blue eyes dinnan nata. Kallon daya saukar masa da wani irin matsanancin faduwar gaba.

"Tsarki ya tabbata ga ubangiji ya furta a fili yana qarewa fuskarta kallo. Baisan kallonta daga nesa ya rage mata kyau ba sai daya matso kusa da ita.

"Sunana ruslan........" Katsewa maganarsa tayi saboda wani lumshe ido da tayi gami da budesu lokaci daya,wanda suke gaya masa

"Sai me?.....me ya shafeni?".

"Bala'i" Ya fada cikin ransa yana jin yadda wani gumi ya fara yanko masa. Yasha ji cikin abokansa suna firar nau'ikan mata masu tsananin aji.......yadda wasu matan suka qware wajen baiwa namiji amsa da iya qwayar idanuwansu,bai taba dauka da gaske bane......bai kuma taba dauka magana da idanu kawai zata saka ka fahimci me mace ke nufi ba sai yanzu.

"Ammmm.......kiyi haquri......ban nema izini ba ko?......duk da naga kamar daga daya daga cikin masarautunmu kika fito ko?". Wani abu ne yazo ya tsaye mata iya wuya,bata taba tsammanin saqon data aike masa bai isheshi haka ba.......

"Baka fahimta ne?" Ta fara tana juya hannunta gamida da ware yatsun hannun.

"Subhanallahi" Bakinsa ya motsa ya furta can qasan maqoshinsa yana jin maqogoronsa yana bushewa. Komai nata me burgewa ne.....me kuma daukan hankali ne.......komai nata daga kusa yafi kyau da qayatarwa.......tabbas idan yace a kowanne qarni irinta kadan Allah ke halitta cikin mata baiyi kuskure ba.

Sanda yakai qarshen wannan tunanin tuni harta cusa earpiece a kunnenta,ta lullube idanunta ta kuma ja blanket dinta ta rufa har kanta ruf zuciyarta na mata suya.

Bayan first class a flight batasan kuma wanne guri zata shiga ta boyewa idanuwa ba.......ashe har first class dinma an fara samun mutane marasa aji irin wannan mutumin da ko sunansa ma bata gama fahimta ba ballantana ta riqe.

Ya fahimci zamansa a wajen bazai amfana masa komai ba,bazai kuma maganta masa komai ba,don haka ya miqe tsam daga gurin,zuciyarsa tana bashi shawarar ya tunkari aisa,don ya fahimci kamar ta fita sauqin kai da iya mu'amala,wataqila ta samo masa kanta.

Bata ko sake bude fuskarta ba bare tasan yabar wajen ko baibar wajen ba. Har suka gama awannin da zasuyi,jirgi kuma ya saukesu a Diory hamani international airport.

A nan ta taras da driver dinta da kuma security dinta mutum uku suna jiranta,wadanda suka kasance tsaffin sojoji da suka samu horo me kyau suka kuma goge ta fannin tsaro da kuma bada tsaron.

Tayi zaton a motar aisa zata sake ce mata wani abu,amna sai taga bata qara cewa da ita komai ba,hasalima Mac book ne a hannunta take wani sabgar daban,sannu a hankali har suka isa unguwar tasu.

Commune I,unguwa ce data kasance mazaunin al'ummar dake da sukunin rayuwa sosai koda cikin Niamey din ma. Area ce data qunshi manyan gurare,kamar ofishin jakadancin qasar amurka manyan makarantu masu tsada da daraja na 'ya'yan masu hannu da shuni da sauransu.

Avenue dinsu suka shiga wanda ke cike da security dake kula da motsi da kuma kai kawo na avenue din gaba daya. Tun daga gate na farko security din dake tsaron gurin ke saluting motar. Motar masarautar agadez fitacciyar mota ce,daba wani guri da zata ratsa ba tare da ta fita daban ba.

Gida me number shida anan motocin sukaci burki,basu ko danna horn ba babbar qofar da zata sadaka da farfajiyar harabar gidan me wani irin adon qarafuna masu daukan hankali dake nuna sarauta a jikinsu suka bude motocin suka shige ciki.

Kusan kowanne ma'aikaci dake cikin gidan tsaye yake yana jiran isowarta,isowar data sanya kowa sake shiga nutsuwarsa har zuwa sanda birra ta bude mata motar ta sanyo qafafunta waje.

"Barka da sauka.......maraba da isowa........Bienvenue chez nous(barka da dawowa gida)..........Content de vous revior(muna farinciki da dawowarki gida)". Hannu ta daga musu sannan ta juya zuwa cikin gidan hankalinta yana kan hannatou. Wani lokaci irin wannan yanayin yana kasancewa takura a tare da ita,duk da kasancewarta mutum me tsananin jin girman da take dashi.......amma yanzun bataga dalilim taruwrasu ba dukka haka suna marabtarta. Inda kowa yayi zamansa zata nemeshi idan buqatar hakan ta taso.

Wata dabi'a ce a cikin jininta,sam bataso bata kuma qaunar a dinga shiga al'amuranta muddin ba itace ta gayyatoka ba. Ita dinma tana da dabi'ar yin halin ko in kula da al'amuran wasu,koda ya shafeta ballantana bai shafeta ba.

Hannatou ita ta kasance kamar wata idanu na me martaba a nam Niamey gidan da akhnan ke rayuwa......hadima ce itama da asalin kakanninta suka kasance bayi ne ga kakan akhnan sarki muhammad agg bin muhammad agg abba.

Tana da wani matsayi daya sha banbam dana sauran dukka hadimai da bayi,don hatta iyayenta basu mutu a mazaunin bayi ba,sun samu 'yancin kansu tun zamanin sarki muhammad agg din.

Tana iya yiwa akhnan gyara,tana iya nusasheta kan wasu abubuwan ta sigar shawara da hikima da dabaru da Allah ya hore mata a shekarunta da Allah ya bata.

Akwai sabo tsakaninta da akhnan din a yawancin lokuta,duk da sabon bai hanata aiwatar da duk abinda take ganin yayi daidai da tsafinta da rayuwarta ba,koda kuwa a hangen hannatou hakan ba daidai bane. Tun tana da shekaru goma a duniya hannatou ke tare da ita,kebantacciyar hadimar da ta dauki nauyi da dawainiyar wahalarta tun kafin tasan kanta,wannan dalilin ya sanya da wasu abubuwan akhan din take sauraren hannatou din,ta kuma sake da ita har sama da yadda take sakewa dasu birra kuwa,duk da yadda suke 'yan kusa kusa da al'amuranta.

Ajiyar zuciya ta saki me nauyi sanda ta zauna sosai saman gadon nata gana kuma sheqar daddara iskar da dakin nata ke bayarwa. Tana matuqar qaunar dakin qwarai da gaske,dakin yana da wani irin yanayi na musamman da kuma tsarin ginin da ya dace da zabin akhnan din. Ba dakin kawai ba,gidan gaba daya na musamman ne a wajenta,saboda yadda take samun sakewa sosai da kalar yanayin da tafi buqata a rayuwarta. Ba gidan bama,ita kanta Niamey na daya daga cikin garuruwan da take so sosai,saboda tana bata irin yanayi da nutsuwar da take buqata a yawancin lokuta fiye da agadez.

"Mun dauka zaki kai zuwa wani satinne biftu" Hannatou dake maida luggage din akhnan inda ya kamata ace suna zaune ta fada,da sunan da banda hannatou din ba wani cikin hadimai dake kiranta dashi sai ahalinta kawai.

"Na gama abinda ya kaini hannatou.........dama kawai rigima ce irin ta sultane" Murmushi hannatou ta saki kawai,ta sani indai biftu din ta fadi haka sultane din yayi wani da baiyi daidai da tsarinta ko abinda takeso ba kenan.

"Ran sarki ya dade......kullum hangensa shine yadda biftu zata zama mutum ta musamman......"

"Banda a nan hannatou.......na taba ganin inda aka tursasawa mace tayi aure bisa dole?" Ta fadi da alama maganar har yanzun bai qare ba a ranta. Abinda hannatou keyi ta bari,ta dawo gefan akhanan tana taimaka mata wajen fidda takalmin qafarta da take cirewa da qyar,tabbacin hidimta mata a komai nata da zatayi ya zame mata jiki.......bata iya yin komai da komai wa kanta a karan kanta kenan inaga hidimar da ba ta jikinta ba.

"Koda yaushe sultane me gaskiya ne.......sultane me hangen nesa ne.....zai kuma ci gaba da kasancewa hakan har abada koda akan kanki ne biftu........a ganina da zaki bude zuciyarki ki fahimci maganganunsu da zaifi alkhairi da alfanu......aure cikar diya mace da qarin darajarta ne......."

"Wacce daraja hannatou?......ina daraja wajen zama qarqashin wani bisa dokokinsa da umarninsa........ina daraja wajen rayuwa cikin mafarkin wani ba naka mafarkin na qashin kanka ba?" Tayi maganar tana waro manyan idanunta wane kamar waddda taga wani abun tsoro daban.

Kai hannatou ta girgiza tana murmurshi,ba shakka sai yau ta gasgata akwai tarin tasirin quruciya akan akhanan ba 'yar kadan ba.......ta sani da dadewa cewa duk abinda yazo bakinta tana fadi muddin iya gaskiyarta kenan,sai a yau ta sake yadda da hakan. Ta manta su din suna rayuwa ne qarqashin umarnin wasu mafarkin wasu kuma rayuwar wasu?,amma hakan bai rage musu komai ba saima daraja da suka samu ta silar hakan da ingantacciya kuma amintacciyar rayuwa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login